← Book details Alwashi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 30

Sashe 17

Alwashi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaban motar tashiga batare da ta kalleshiba amma kamshin turarensa na beautiful oud sai cika hancinta yake sallama sukayi da mami tanaji mamin nace masa yakula da ita sosai sannan banda matsanta mata,kuma indai taji yayi mata wani abu to sai ransa yabaci, kasancewar yan miskilancin suna kusa ko amsawa baiyi ba,

Jan motar yayi suka fita suka nufi gidanshi babu wanda ya kalli wani bare har yayi magana nan tafara tunanin to ko shima fushin yake?

Lokacin da suka karasa gidan, trolley dinta taja ta nufi ciki batare data dubi side din dayake ba,gidan tsaf tsaf taganshi kamar tana nan, a bedroom dinta tazauna kan bed side drewar tayi tagumi sai kuma tafara kuka,

Handbag dinta wacce tafita da ita ranar data bishi hotel ta suma ya dauko yabita dakinta, cilla mata jakar yayi saman kan bed dinta yajuya zai fita,

"Yaya yusleem..."

Takira sunanshi, cak yatsaya batare da yajiyo ba,

"Meyasa ka zabi wannan mummunar sana'ar acikin rayuwarka? Duk sana'o'in duniya karasa wacce zakayi sai wannan? Kasan kuwa irin mummunan tanadin da Allah yayiwa masu irin wannan sana'ar? Meyasa ka zabi duniyarka akan lahirarka?"

Ahankali yajuya yafara takawa ya nufi inda take tana zaune hawaye nafaman bulbula daga idonta kamar anbude fanfo.....

*_Ummi Shatu_*👌🏻® *HASKE WRITERS ASSO.* _(Home of expert & perfect writers)_

*ALWASHI...!*💍
_(Labarin Hafsat)_

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_Dedicated to MISS XOXO_

_Gaisuwa da babbar murya ga masoya masu karanta alwashi..._

*28*

****Agabanta ya tsugunna yana kallon fuskarta karo nafarko a zamantakewarsu da ya tsaya ya kalleta,

"Yaya yusleem ko kasan kuwa tarin zunubin da yake kan duk wani wanda yake aikata irin wannan dabi'ar? Irinfa wannan laifin al'umar wani annabi sukayi Allah ya halakar dasu sannan acikin littafinsa mai tsarki ya sanar damu nau'o'in azabar da ya tanadarwa duk wani wanda ya kasance yana aikata irin wannan halayyar...."

Tausassun hannayensa yakai yadora akan nata har lokacin dai idanuwansa suna kan fuskarta sannan sun juye daga farare zuwa jajaye,

"Ba laifina bane, karki ga laifina, komai yana faruwa ne da dalili, wallahi irin rayuwar da na tsinci kaina abaya ta kunci, talauci, tsangwama, tsana da kuma kyara itace tayi sanadiyyar fadawata cikin wannan mummunan halin..."

Kallonta yayi da jan idanuwanshi tareda kwantar da kanshi bisa cinyarta yanajin zuciyarshi tana yi masa zafi wanda bai taba jin irinsa ba,

"Yaya yusleem nikuma sai nake ganin wannan ba dalili bane ko hujja da har zaka jefa kanka cikin halaka..."

"Wannan daliline mai karfi NANAH...."

"Nikuma agareni ba dalili bane domin wannan abun da kake aikatawa yafi dukkanin abubuwan da ka zayyano muni,haba yaya yusleem kamanta labarin wani mutum da annabi yafada mana mai tsawaita tafiya yana mai gizo mai k'ura k'ura yadaga hannayensa zuwa sama yana cewa ya ubangiji ya ubangiji amma annabi yace ba a amsa masaba saboda abincinsa haramun ne,abin shansa haramun, tufafinsa haramun sannan yayi guzuri da haram...."

Dago da kanshi yayi ya kalleta sakamakon jin saukar hawayenta akan wuyanshi,

"NANAH arayuwar baya na tsinci kaina cikin mawuyacin hali, mahaifinmu Alhaji Ahmad Mela mu Goma Sha biyar ya haifa sannan matanshi uku kowacce tanada yara biyar,

Ya mutu ya barmu tun muna kanana, acikin yaransa mu ukune manya daga Shu'aib sai Mukhtar sai ni, dukkaninmu kanmu daya, kasancewar dama gidan ba azaman lafiya yasa tun rasuwar mahaifinmu kowa ya kama 'yayanshi yarike bayan anraba gado,kuma kin san zumuncin yanzu yanda yake na ganin ido ne,

Nanah a lokacin wallahi duk da ni yarone ban wuce shekara 24 ba ina yin iya bakin kokarina wurin nemowa mahaifiyata da kannena abinda zamuci amma mami bata gani kullum cikin kusheni take da zagi cewar ni banida zuciya zan bari wai talauci ya kasheta,

Nayi iyakar iyawata ganin na fahimtar da ita amma taki fahimta ita kawai burinta lokaci daya inyi kudi inzama millionaire dan kawai ta bawa kishiyoyinta haushi,

Idan kinga irin sana'o'in danayi makaskanta sai kin tausaya min, har turin baro wallahi nayi, na saida pure water, nayi kanikanci,nayi jiran shago duk wai dan inrufawa kaina da yan uwana asiri amma mami bata gani koda yaushe bata da magana sai nacewa, ita bazan burgeta ba muddin ban tashi nanemo kudi duk inda yake nazama mai kudiba,mami duk tabi ta tsangwameni ta tsaneni akan kawai ban zama mai kudiba,

Da wannan kananan sana'o'in nasamu nakammala degree amma abin haushi babu aikin yi dole nakoma gareji naci gaba da gyaran mota,

Sau da dama ku mata kune kuke cusawa mutum ra'ayin da baiyi niyyaba nanah, a lokacin idan nasiyowa mami abu nakawo mata ko atamfa ko takalmi sai ta raina kiri kiri zata nuna min ban burgeta ba kuma bata ji dadiba wani lokacin ma har takara da fadin "ni ba irin wannan harkar tsiyar nakeso kayimin ba, ni so nake karinka Kawo min kaya masu tsada akwati akwati yanda nima zan fantama, amma kai kullum abubuwa ba arziki kaki katashi kayi arziki yanda mahaifinku ya mutu bai bar muku komaiba kaima haka zaka mutu baka bar komai ba?"

Irin Wadannan maganganun da mami kemin sune suke tsaya min araina inji zuciyata takasa samun nutsuwa saboda ni aganina ina iyakar kokarina amma komai nayi bata gode min kuma bazata samin albarka ba,

Acikin wannan yanayin wan mahaifinmu yabani yarsa Rahina in aura, sam Rahinan bata sona saboda kawai banda abin hannu sai rufin asiri,

Dakyar ita da uwarta suka amince akayi auren saboda babu yanda zasuyi, bayan aurenmu da Rahina nashiga matsanancin hali saboda zan siyo mata kayan cefane in aiko mata dashi daga gareji amma wallahi nanah yanda aka Kawo kayan nan haka zan dawo insamu kayana tabarshi awurin bata taba ba, idan abin lalacewa ne to sai dai ya lalace, bazata yimin girki ba idan nayi magana tace ita bazata dafawa matsiyaci abinci ba mai k'ashin tsiya wanda bashida rabon arziki,

Bazata yi sharaba,baza tai wanke wanke ba babu abinda takeyi abinci ma mahaifiyarta ce ke aiko mata daga gidansu batare da mahaifinta yasaniba, kullum idan naje gaida mami dakyar take amsawa, idan nadawo gida Rahina ta tareni da masifa da bakaken maganganu wani lokacin ma sai tace bazan shiga dakinta ba ita ubanta bai siya mata gado da katifa dan matsiyaci ba dama kuma tunda akayi auren bata barni na kusanceta ba domin kullum da wuka akasan pillow take kwana wai duk ranar da nayi yunkurin zuwa inda take sai ta kasheni,

Kullum a falo nake kwana ita kuma tana cikin daki wata rana ma idan bata gadamaba rufe kofa take sai dai inkwana awaje idan nafadawa mami sai ta goyi da bayanta tamkar ba itace ta haifeni ba, duk da irin wannan abubuwan da Rahina kemin bai hana zuciyata fara sonta ba amma ita hankalinta ba akaina yakeba domin haka mahaifiyarta zata zo har gida su hadu su zageni tass suna kirana da matsiyaci marar arziki,

In takaice miki zance daga karshe sakani agaba sukayi saida nasaki Rahina duk da ina sonta ashe wani mai kudi tasamu suke soyayyarsu da aurena, aranar da nasaketa sukazo suka kwashe kayanta Hafsat nayi kuka irin kukan da ban tabayiba domin ina sonta duk da rashin kyautatawar da take yimin,

Kwana biyu nadauka agida ban fitaba saboda damuwa, da daddare ina kwance ni kadai adaki na dauki wayata nashiga facebook nan naga wani yaturo min da friend request babu bata lokaci nayi accepting,

Bayan mun gaisa yake cemin a ina nake nafada masa, sai yacemin wai ina dan harkoki nace masa ehh to ana dan tabawa saboda ni ban gane abinda yake nufiba haka mukaci gaba da yin hira yace shi dan majalissa ne awani gari yakamata inje in sameshi,

Wallahi nanah ban taba sanin mutumin nan bana kirki bane saboda nayi tunanin ko aiki zai bani tunda nafada masa nagama karatu babu aikin yi,

Sallama nayiwa mami nashirya natafi wurinsa da takardu na amma koda naje sai labari yasha banban lokacin da yanuna min karara abinda yake son yi dani ashe gay ne ban saniba, a lokacin ban aminceba amma koda nazauna nayi tunani nahango irin tsangwamar da mutane kemin akan bani da arziki da irin halin ko inkula da mami ke nuna min da kuma yadda aka rabani da rahina sai kawai na amince shiyasa nace miki amafi yawan lokuta ku mata kone kuke zama silar faruwar komai domin dayawa daga cikinku bakuda godiyar Allah burinku kawai mutum yayi arziki batareda kun damu da sanin halalcin arzikin ko haramcinsa ba,

Kwanana uku awurinshi aranar da zan dawo yabani wata kyakkyawar mota banda tsabar kudi dubu dari biyar,

Tunda mami taga nafara arziki shikenan tahau murna tana cewa burinta yakusa cika sukuma mutane sai cewa suke Allah ne yayi min nasibi dare daya ya azurtani, wallahi nanah ko sau daya mami bata taba tambayata a ina nake samun kudiba ita kawai tunda nace mata wani uban gida nasamu yake buda min shikenan tahau murna tana saka min albarka,

Kuma har yau dinnan da nake miki magana mami bata taba tuhumata akan arzikin da nake dashiba gashi kuma acikin lokaci kankani na mallaki komai na jin dadin rayuwa kama tun daga gidaje, kamfanoni, motoci da komai da kika sani na jin dadin rayuwa domin mutanen dake cikin harkar nan masu fada ajine daga senators sai Reps sai Governors...."

Zamowa daga kan bedside drewar din Hafsat tayi tazauna dirshan akasa cikeda tashin hankali, matsawa kusa da ita yayi yasake dora kanshi akan cinyarta yafashe da wani kuka mai ban tausayi,

"Yaya yusleem daina kuka dan Allah, shi Allah mai yawan gafara ne domin yace yana gafarta zunabai gaba daya komai yawansu mutukar muka tuba kuma muka nemi gafararsa, nidai dan Allah so nake kabar aikata wannan dabi'ar domin bata dace dakai ba, kazanta ce, masu aikatata sun tabe duniya da lahira.."

Hannunta yakama ya matse cikin nashi,

"Nanah na daina, amma nasan rayuwata tana cikin hatsari domin wallahi sawa zasuyi akashe ni saboda zasuga kamar zan tona musu asiri ne kuma mafi yawansu manyan mutane ne.."

"Yaya yusleem insha Allah babu abinda zai sameka, insha Allah Allah zai kareka..."

Baiyi magana ba illah kukan da yaci gaba dayi mai tsuma zuciya,

Rarrashin duniya Hafsat tayi masa amma baiyi shiruba, ranar haka suka kwana azaune ido biyu har gari yawaye,

Alwala yayi yafita masallaci idanuwansa akunbure sunyi jajur, ita kanta Hafsat din kukan da tayi ba kadan bane,
Chapter 17 · 0% Book details