← Book details Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 37

Sashe 6

Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai wani hoton shima amma yafi wancan girma shi wannan da ganima ba awani daɗe dayin saba daga saman hoton an rubuta ARAB FAMILY da man yan baki, kowa yana zazzauna acikin palon wasu na daddana waya wasu kuma nayin magana ƙasa ƙasa daga gefe da Gafan hannun sa na dama matar sa ce uwar gidan hajiya umma sai gefan hagun sa mama bilki itace ta biyu dama matan ALHAJI IMRAN MUHD ARAB Biyu ne sannan yana da ƴaƴa guda goma sha uku 3, hajiya umma na da yara bakwai 7 ita kuma mama bilki yara shidda 6,
Ƴaƴan hajiya umma,
Hameed, Bello, shaddad, Aliyu, Abubakar,
Bahijja, sai autar su hauwa u suna kiranta da jiddah

Ƴaƴan mama bilki,
Hasheem, Mansur, Sambo, Yusuf,
Jamila, sai Saratu suna kiranta da SARA,

Kowa yana zaune a palon tare da Ƴaƴan sa matan ne kawai babu mutum biyu suma da yake auran nesa suka yi sara ɗiyar mama bilki da kuma Bahijja babbar ɗiya mace a gurin hajiya umma, dune kawai babu a taron muta nan gidan,

Gyaran murya alhaji IMRAN ARAB yayi cikin muryar dattaku da girma ya fara magana banga sulaim ba ko baya nan ne? Yayi tambayar yana kallon inda yaran sa maza suke baki ɗaya suma akan kujera suke zaune ko wanne da matar sa sai jikoki maza suma suna zaune daga ƙasa? Don bazai taɓa furta komai batare da rabin ran nashi nan akusa dashiba wato sulaim Tunda yafito bai ganshiba yaji duk ya takura,

Magana nake kunyi shiru

Gashinan zuwa yanzu insha Allah aranshi kuma yana addu'ar Allah yasa sulaim ɗin ya taho Tunda shidai kawai faɗaya yayi don yasanya yayan nasa bazai taɓa magana ba saboda sulaim shine ɗan fari a gurin sa, cewar daddyn Canada wadda dashi akayi sallar isha'i acikin estate ɗin nasu shida ɗan sa saleem da suka biyo jirgin yamma daga Lagos zuwa Kano,

Gudu yake cikin cikin mota sosai Haba sulaim kabi a hankali mana cewar saleem dake zaune a gefe,

Ni fa saurin da nake daban bawai na meeting ɗin nan bane duk yau banga baffa na ba wlh jinake tamkar kaina zai tarwatse idan ban ganshi ba, seriously yayi maganar tashi babu alamun wasa ko dariya,

Dariya saleem yasa don shi bai yi tunanin har yanxu wannan ƙaunar nan tsakani sulaim da kakan su alhaji imran ba wanda suke kira da baffa,

Dai dai lokacin da ya hau wannan titin dayi gabas wanda daga gefan titin akan ƙaramin allon akasa ALHAJI IMRAN MUHD ARAB STREET,

amma da naga da ƙafarka ka kezuwa part ɗin su baffa cewar saleem yana kallon sulaim don jin amsar shi,

Eh daƙafa nake zuwa hargobe yanxu baka ji abunda nafaɗa maka bane duk yaubangan shi ba, yafaɗa a ɗan daƙile alamar ya gaji da magana,

Oh eh haka ne

Dai dai iso warsu ƙaton gate din part din kakan nasu gate din yazuge da Kansa Yatura hancin motar ciki tare da jin qaruwar bugun zuciyar sa kofar shiga palon tafi kowace kofar palon dake cikin estate din Girma,

Da sallama suka tura kai cikin palon kowa hankalin su ya dawo kansu ɗaga idon sa yayi shima ya kalli mutanan cikin palon dai dai tsayawar bugun zuciyar sulaim kafin kowa a ankara yatsilale ƙasa asume,

Innnalillahi wa inna ilaihi raji'un alhaji imran ARAB ya futa cikin rawar murya wanda ya riga kowa tashi daga inda yake zuwa inda sulaim ya faɗi.

*Wannan kenan*...!

*Kudai kubiyoni cikin wannan littafin mai ɗauke da darussa kala kala acikin sa kuma har yanzu dai muna farko acikin littafin mai ɗauke da sarƙaƙiya ban al'ajabi makirci cuta bantausayi sai kuma uwa uba soyayya ❤️ wadda itace sular haduwar mu* 🤝✊

*💕AHALIN MU ƊAYA*💕

_COMMENT SHARE AND LIKE FISABILILLAH_🙏

*🖊️Alƙalami yafi takobi* ⚔️⚔️

*STORY BY,*°°°📖
💞Fatima Y zakariyya 💞
_😍Oum Ameerah_😍

*Taku har kullum*
_👑Gimbiyar writer's association_🫅

_Muje zuwa_✍️✍️✍️

https://chat.whatsapp.com/E8xhHJZMBnODAswBWNyIiF
Only group what's app

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V
WhatsApp channel

*🖊️📚Nazari writer's association*📚🖊️

_Kyakkyawan nazari kafin rubutu na ɗamfare da bin ƙa'idojin rubutu_

_Cikakkyan nazari kafin rubutu kan ƙyata duniyar adabin Hausa_

*🫅Sarauniyar 👑Nazari writer's association* 📚🖊️

🖊️🖊️Aƙalami yafi kobi⚔️⚔️

*💖 SPECIAL GIFT 🎁 TO MY BIG BROTHER Abba Maifata💯*

*AHALIN MU DAYA*

*NA*
💞Fatima Y zakariyya💞

{😍Ummu ameerah😍}

_____ Dedicated to aunty Salma 💎

*Page* 1️⃣1️⃣↔️1️⃣2️⃣📖

Inna lillahi wa inna ilaihi raji un, alhaji imran Arab ya furta cikin rawar murya wanda ya ruga kowa tashi daga inda yake zuwa inda sulaim ya faɗi,

Kamar wani ɗan ƙaramin yaro haka daddyn Canada ya ɗauke shi cak alhaji imran wanda hanka linsa gaba ɗaya ya gama tashi duk yabi ya ruɗe abunka da jikin tsufa har kyarma yake yi wajan kama sulaim yace akaishi cikin bedroom ɗin sa, haka daddyn Canada ya nufi ɗakin baffa da sulaim ɗauke a hannun sa,

Hankalin wasu ya tashi sosai a gurin ba ma kamar ummeetha mahaifiyar sulaim wadda kawai daurewa takeyi amma ji take kamar tabi su ɗakin baffan to ina babu ma fuskar yin hakan alhaji hameed Arab shi ko bai motsa daga inda yake ba saboda tsabar kawaici irin nasa acikin ransa kuwa addu'a yake yiwa ɗan nasa tare da jin daɗin yadda wasu daga cikin ƴan uwansa suka kula da abun da ya samu ɗan nasa kuma ai shi idan da sabo ma ai yasaba ganin hakan,

Wasu ko ransu fari tass kamar su zuba ruwa a ƙasa su sha dan murna duk wani ɗa da jika da yafito daga ɓan garan mama bilki farin ciki ne tab zuciyar su banda mutum ɗaya 2 uncle Yusuf bawan Allah jiya ke tamkar ciwon dake jikin sulaim ya dawo kansa saboda shidai Allah yasa masa ƙaunar sulaim tamkar ɗan da ya haifa acikin sa,

Su mai girma hasheem kuwa ba a magana saboda shi yasan komai akan hakan ma saboda haka ko a jikin sa da shida HE EXCELLENCY SAMBO tare da ɗan uwan su Mansur wanda duk wani makirci da mugunta daga gareshi yake fitowa,

Allah sarki baffa imran Arab ya rasa inda zaisa kansa ya ji daɗi sulaim yaƙi farfaɗowa an yayyafa masa ruwan amma abanxa sai danna masa ƙirjinsa saleem yake yana kara kunnan sa a ƙirjinsa amma shiru zuciyar sa ko harbawa batayi,

Saleem ne ya kalli uncle Yusuf yace uncle ko za aƙara kiran DR. Jabir ɗin ne,

Eh to bari inƙara kiran sa yana ciro waya da nufin ƙarakiran DR. Jabir ɗin suka ji sallama ƙofar shigowa bedroom ɗin,
Zaka iya shigowa cewar daddyn canada rafiq lafiya kuwa, kyakkyawan saurayin matashin da aka kira da taufiq ya amsa eh daddy dama Dr. Jabir ne yazo shida DR. Anisha,
Oky su shigo daga ciki,
To ya amsa tare da juyawa yafice don yi musu iso zuwa ciki yafito tare da kallon inda su DR. Jabir suke zaune yayi tare da faɗin zaku iya shiga,

OK atare suka yi sallama,
Yes kushigo mana suka shiga saidai suka gaisa da su tare da yi musu ya mejiki sannan DR. Jabir ya matsa kan gadon da sulaim yake kwance ya yafa aikinsa saboda wannan ba baƙobane a gurin su akan sulaim a dane idan yayi irin haka Hankalin su yake tashi sosai wani lokacin ma sai su yi zaton ko ya mutu ne saboda zuciyar sa da bata harbawa idan yayi irin wannan faɗuwar ada yana faɗuwa sai asibiti amma yanxu a gida kawai ake du bashi,

Saidai Dr. Jabir Yayi kusan 10mins akan sulaim ɗin kafin ya ɗan jiyo ya kalli mutanan dake cikin bedroom ɗin,
Doctor lpy kuwa cewar saleem da damuwa duk tagama bayyana akan fuskar shi,

Eh to gaskiya nayi mishi duk abunda yadace amma shiru,

Da sauri Dr. Anisha ta juya ta fita kai tsaye waje tayi tana fitowa palon su mommyn canada suka taso daniyar tambayar ta ya jikin sulaim din amma basu samu wannan damar ba dan bata bi ta kan kowa ba ta fice,

Parking space ta nufa inda suka ajiye mutar su ta buɗe gidan baya ta ɗaukko wani abu haka kamar IRON ta rufe motar ta dawo a sukwane tana sauri sosai kamar gudu ahaka har ta shiga ciki wannan karon saleema tasha gaban Dr. Anisha da sauri tace waike kinƙi gaya mana ya jikin nashi sai magana akeyi miki kinajin mutane wani irin kallo DR. Anisha tabi saleema dashi from head to toe

Ta raɓata ta wuce batare da ta bata amsaba
Da sallama ta shiga kai tsaye inda sulaim yake ta wuce ta yi joining ɗin wannan abun mai kamar IRON da computer sannan ta kunna tafara dannawa sulaim aƙirjinsa a hankali sai da tayi kusan sau ukku 3 sannan ta ajiye abun takara kunnan ta saitin zuciyar sa,

Da sauri ta ɗago tare da furta Awww sannan ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya aiko Hankalin kowa ya dawo kanta hadda DR. Jabir da sauri ya nufi gurin shima yana zuwa yace alhamdulillahi,

Doctor ya farfaɗo ne har haɗa baki su baffa imran suke wajan tambayar Dr. Anisha,

Eh kawai ta iya furta wa ta sake maida hankalinta akan sulaim wanda har yanxu idon shi na a rufe DR. Jabir yace amma zuciyar shi na bugawa very fast so hakan ba wani abun da muwa bane da alama dai kamar kullum wani abun tashin hankalin ya gani shiyasa shi shiga cikin wannan halin to yanxu kamata yayi Abarshi ya huta zansa masa, drift saboda zazzabin da ya rufe sa,

Gaba ɗaya basu ji daɗiba na farko sunji ɗadin farfaɗowar sa amma kuma rashin jin daɗin nasu Meye wannan abun tashin hankalin da sulaim yake gani wanda su baza iya ganinsa,.

Ruwa Dr. Jabir yasa masa saboda dama duk lokacin da yayi irin wannan sai ansamasa drift saboda zazzabin da yake rufe shi lokaci daya sai ruwan sa yaƙone da ya farfaɗo kuma sai Kaga kamar bashi ba,

Dr. Anisha ce ta haɗa komai basu sannan takalle su tayi murmushi tace kukwantar da hankalinku insha Allah komai zai daidaita yanzu dai yana buƙatar ta huta ne,
Chapter 6 · 0% Book details