← Book details Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 37

Sashe 18

Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*CREATED AND WRITTEN*
*BY*
*Fatima Y zakariyya*
_😍Oum Ameerah_😍

*NAZARI WRITER'S ASSOCIATION*📚
_Sarauniyar👸Nazari writer's association_

______Dedicated to aunty salma💎

*Page* 2⃣9️⃣↔️3️⃣0️⃣📖
Tsaye yake cikin wata shiga ta baƙakyan kaya cikin wani, ɗaki mai duhun gaske, wata ƙaramar fitila ce an kunna ta a an ajiye a ƙasa irin, aci bal bal ɗin nan,

ta ɗan haska iya inda yake tsaye, magana yake cikin kaushin murya, baza ka taɓa gane cewa, mai girma hasheem ba ne saboda adon kwallin da yayi wa fuskar sa, Indai ba sanin sa kayi sosaiba, gashi ɗakin babu wani wada taccan haske aciki, magana yake a gaban wani dogan mu dubi, baka iya ganin komai na cikin mudubin shi kaɗai ke iya mu tumin da yake magana dashi,

Daga cikin mudubin ne aka fara magana, hasheem kasani dole zaka yi abunda ƙungiya keso Idan ba haka ba, hukunci ne zai biyu baya zaɓi fa aka baka har biyu, amma shine kake wasa da da mar ka ko, dole kasa mu HATIMIN nan shine kawai zai sa mu mallaki ƙarfin iKon da babu wata ƙungiya da take da irin ta acikin ƙungiyoyin (secret).

Kafin mai girma hasheem yace komai wani duhu ya kawo ya mamaye cikin madubin,

Wani irin dogon numfashi mai girma hasheem yaja kafin ya ɗauki wani jan ƙalle ya lulluɓawa fuskar madubin, sannan ya matsa daga gabansa, yana muzurai a fili ya furta bazai yiwu ba dole ni zanzama mai ƙarfin iko na farko acikin ƙungiya,
Takawa yafara yi zuwa wani ɗaki domin ya canza shigar sa zuwa asalin tufafin daya shigo dasu wannan ɗakin, aransa kuwa cewa yayi ai dole na cigaba da yiwa Mansur da Sambo talala har nasamu, a samo inda HATIMIN nan yake, da haka ya shige cikin wani ɗakin da baza ka iya tantance komai na cikin saba saboda rashin wada taccan haske,

Guri sulaim ya samu yayi parking acikin harabar Event center ɗin, shiru babu wanda ya motsa acikin su, sulaim har ya ƙagara tafita tabashi guri don ya huta, ita kuma saleema jiran sa take ya fita su shiga cikin holl ɗin da ake taron,

Jin shirun yayi yawa ne gashi lokacin around 8:36PM saleema ta kalli sulaim kafin tace yaya sulaim zamu iya shiga ciki,

Bai ko kalli inda take ba bare ta sa ran zai bata amsa,

Aranta kuwa cewa tayi Allah yasa kada yace bazai shigaba,

Idan har ko hakan ne to nima da inshiga gurin nan gara mu koma gida, don har ta hango irin dariya da rashin mutuncin da friend ɗin ta zasu yi mata bayan tagama gaya wa su malika gasu nan tare, amma yanzu ace sugan ta ita kaɗai ta shiga, ai sai su raina ta ma,

Tana cikin wannan tunani sai ji tayi sulaim ya tada mota yayi rivers, ya juya ya nufi gate, tashin hankali bayyane ƙarara akan fuskar saleema take kallon sulaim, don babu fuskar tambayar shi ma,

Kafin tayi wani kwakkwaran motsi har yafice daga cikin gurin da gudun gaske, take saleema ta saddaƙar, gida ma zasu koma, ko kallon shi bata ƙara yi ba, idon ta kuwa ya ciko da kwalla tab, ta kawau da kai gefe, tana sharar hawaye,

Kwance suhailat take tana, tunanin me dalilin da yasa yaya saleem yahanata kula hafeez course meet ɗin ta, itafa iya tunanin ta bata ga dalilin ba, tana cikin wannan tunani ne kawai taji shigowar sms wayar ta, da tayi kamar bazata duba ba sai kuma ta miƙa hannun ta janyo wayar, tana daga nan kwance tabuɗe wayar, a fili tace oh yaya saleem ne, take ta buɗe sms babu wani tunani aranta,
_Hii pretty how are you I hope you're doing well, from the moment I met u, I knew that you were the one for me. Your Smile lights up my world, and your love completes me. I fall more in love with you every day, your beauty, kindness, and strength inspire me to be a better person, I am so lucky to have you by my side nd I really love you my suhailat_
_ina fata zaki karɓe ni a matsayin, ɗan uwa, yaya, masoyi_ sai akasa emoji na love ❤️

Suhailat wadda ke kwance saman makekyan bed ɗin ta ƙirar Dubai, bata san sanda wayar ta sulale daga hannun ta tafaɗi saman gadon, wani irin yana yi nakeji mamaki yana ta koda motsawa daga inda take kwance,
"a zuciyar ta ta furta ƴan ya ba mafarki nakeba, wannan ba yaya saleem ɗin da nasani bane, so fa kuma ni wai yana sona,"

Hmm ta sauke wata nannauyar a jiyar zuciya, kafin tasa, hannu ta janyo wayar ta ta, ta ƙara karanta saƙon don har a lokacin zuciyar ta ta kasa yadda da hakan, ganin abun take tamkar a mafarki, sai da ta karanta saƙon nan aƙalla ba'a ƙasara ba kusan sau 5 tanayi tana bita kamar karatu, daga ƙarshedai ajiye wayar tai ta tashi ta nufi toilet,

Aɓan garan saleem kuwa tun yana jiran ganin amsa daga Suhailat harma ya fidda rai koda haske ya gani a wayar tasa sai ya duba ya gani ko itace amma shiru,

ummeetha tace ta kalle shi tace ɗana saleem lafiya kuwa? Kazauna kayi shiru kaci abinci mana kafin mu tafi Part ɗin baffa,

Kallon ummeetha yayi da murmushi abisa kan kyakkyawar fuskar sa yace, ummeetha Meye zamuyi a part ɗin baffa kuma dukan mu?

Ɗazu aka sanar da taron gaggawa, tabashi amsa,

To ummeetha dama zanje can ɗin kafin na kwanta, ina so naga broo sulaim,

Hhhh ƴar dariya ummeetha ta tayi kafin tace au kaima yanzu binshi kake yi gaskiya kabada ni ba haka nasan zuciyar soja ba, da zolaya ummeetha tayi maganar,

Murmushi kawai saleem yayi don shi hankali sa duk baya a gurin burinsa yaga sms Suhailat ko kuma yagan ta ta sakko yin dinner amma shiru, zuciyar sa tabashi amsa da cewa, ai da alama ma baza ta sakko ba,

Kowa yana cin abincin sa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, amma banda saleem,

sakwara ce with egusi source Wanda taji naman kaza da ganda manya manya aciki, sai kuma farfesun kayan ciki a gefe da naman kai,

Mommy tasan saleem dason sakwara amma yanzu ko kallon gurin bai yiba tabbas akwai abunda ke zuciyar saleem wanda ke damunsa ga shima har yanayin sa yama canza, da har zata yi magana kuma sai taƙaleshi sai sun haɗu ita da shi zataji Meye matsalar ɗan nata yanzu kuwa ga abiiy, ga ummeetha, ga mijin ta uncle Bello, ga princess, bakuma ta so kowa ya shiga maganar, dan mommy badai son ƴaƴa ba shiyasa, SALEEMA keyin abunda taga dama kuma baza ta tsawatar mata ba baza kuma Tabari a hana ta abunda takeso ba, kuma duka ƴaƴan nata haka,

Kai tsaye sulaim ya nufi house ɗin, iyayen nasa, don ya gaidasu, badan haka ba da babu abunda zai kai shi nan ɗin Part ɗin baffa zai wuce da saleema saidai ta dawo, Tunda yasan anan ɗin take,

Saleema wadda ta cika tayi fomm jira kawai take ataɓata ta fashe, sulaim bai gama parking ba tabuɗe motar ta fita da sauri, tayi cikin part ɗin nasu,

Shiko hakan ko a jikin sa, ƙarasa parking yayi Sannan yafito shima ya nufi ciki,

Saleema batabi takan kowa ba ta wuce upstairs dan a yadda take ji tana buɗe baki zata iya fashewa da kuka,

Suma basu kula da shigowar ta taba hankalin kowa na akan abunda yake yi,

Da sallama sulaim ya shiga parlon, ganin babu kowa sai yayi tunanin ko suna dinner ne, dinning area ɗin ya nufa,

Da murmushi akan fuskokin su suke kallon sulaim ɗin, saleem wanda ɗago warsa kenan, tashi yayi ya rungume sulaim ɗin, _I missed u big man_ ya furta saitin kunnan sulaim ɗin,

Ɗan janye jiki sulaim yayi ƙadan, kafin yace, _missed u more_ mazan fama,

Dariya saleem ɗin yayi, kafin suka ƙarasa suka zauna,

"Daddy barkan ku da dare" cewar sulaim wanda ke kallon ummeetha itama dai dai ɗagowar ta takalleshi suka haɗa ido,

Murmushin ta wanda baya gushiwa idan har zata ga mafi soyuwa acikin ƴaƴan ta wato sulaim, shi ta sakar masa, ƙasa yayi dakansa, tsakanin ɗa da uwa sai Allah,

Daddy ne ya amsa, saida sulaim ya gaida kowa, saving ɗin shi mommy tayi tare da turawa gabansa, alamar yaci,

"nagode lovely mommy" ya furta hakan a hankali,

Batace masa komaiba suka ciga ba da dinner ɗin su banda saleem da ya zubawa abincin ido kamar mai son ganu wani abu, tunanin suhailat kawai yake, fatan sa Allah yasa ba saboda yayi mata wannan texs ɗin bane taƙi sakkowa dining ba,

Ɗana saleem lafiya kuwa? Alhaji hameed ya tambayeshi don yaga gaba ɗaya baya cikin walwalar sa gashi yaƙicin abinci,

Lafiya ƙalau abiiy bana jin daɗin jiki nane,

Ayya sannu, to Kazauna kawai ba sai kaje meeting ɗin ba,

Bari a kira Dr ya duba ka,"cewar sulaim yana danna waya,

Da sauri saleem yace masa a a kabari mugani akwai maganin da zansha idan banji daidai ba sai a kira,
mommy bata ji daɗin hakan ba taso ace yabari ankira DR ɗin,

Ɗan ɗaga kafaɗa sulaim ɗin yayi, tare da miƙewa," na barku lafiya,

Baza ka jira mu mu tafi tare ba Tunda muma part ɗin baffan zamuje, daddy ne yayi maganar,

Komawa sulaim yayi ya zauna batare da tace komai ba,

Ummeetha tace gashi saleema bata dawo ba,

Eh ko maybe a canza ta kwana gidan uncle tahir ɗin, cewar mommy

Eh ba mamaki"
Kunsan da tafiyar mu zuwa masarautar gabas ko?

Cikin murna da farin ciki princess tace ummeetha yaushe, ne tafiyar don ita Allah tana ƙaunar zuwa masarautar gabas gurin dangin ummeetha, saboda tana ƙaunar wasu al'adun cikin masarauta,

Zuwa jibi insha Allah kafin saleem ya wuce gurin aiki, ummeetha tabata amsa,

Naji daɗi sosai ummeetha saiku ma barni acan Tunda munsamu hutu ko,?

Hmmm, kawai ummeetha tace,

Kowa ya hallara, cikin babban meeting room ɗin alhaji imran Arab baffa, ɗai ɗai ku ne kawai babu aciki,

Bayan angabatar da taro kamar yadda akasaba, baffa ya bada dama idan dame magana zai iyayi game da abubuwan da suka tabbauna, game da ci gaban company's ɗin su na ƙasa shen waje, da kuma haɗin kai a tsakanin su, da Ira Iran family issues nasu,
Chapter 18 · 0% Book details