Sashe 32
Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
.......Suhaima nifa gaskiya inaso kifaɗa min wai ina kike zuwa kwana biyun nan amma kinƙi faɗamin, cikin zafin rai khaltum tayi maganar tare da shan gaban Suhaima wadda ke niyar fita, cak Suhaima ta tsaya tare da kai duban ta kan khaltum wadda ke tsaye a gaban ta tana jiran amsa,
Khaltum pls kibani hanya in wuce idan nadawo zakiji komai amma yanzu kina ɓatamin lokaci takai ƙarshan maganar tare da raɓawa ta gefan khaltum daniyar wucewa da sauri khaltum ta ƙara tare ta akaro na biyu, nifa kawai kifaɗamin Indai ba wani rashin gaskiyar kike aikatawa ba....
Kallon ta Suhaima tayi tare da ware manyan idanuwan ta akan fuskar khaltum wanda suka ɗai ake iya gani a fuskar tata kwayar idon ta ƙara zama ash mai turuwa saɓanin ada mai haske ce, da sauri khaltum taja baya tare da matsawa daga gaban ta batare da tace komai ba saboda ganin yadda Suhaima ta canza lokaci ɗaya, ganin tabata hanya ne hakan yaba ta damar sakai tafita da sauri, wata irin nannauyar ajiyar zuciya khaltum ta saki tare da dafe ƙirji ta koma gefan katifar su ta zauna tafara tunani kala kala tasaƙa wannan tawar ware wancan,
Mata ne zazzaune a tsakar gidan Hajiya fanteka zawara wa da ƴan mata kowacce da abunda takeyi batare da Suhaima tabi takan kowa ba ta fito cikin nutsuwa tafara raɓa su tana wucewa kanta a ƙasa, "anty ina yini" Cigaba da tafiya Suhaima tayi batare da tajiyo ba don bata kawo a ranta da ita akeba, da sauri matashiyar budurwar da tayi maganar ta tashi tabi bayan Suhaima sai da ta tabbatar tazo kusa da ita, akaro na biyu ta sake Faɗin " ina yini anty" tsayawa Suhaima tayi tajiyo a hankali tare da kallon mai magana abayan ta,
Oh Sajeedah ya kike Suhaima ce tayi maganar cikin fara'a duk da ba'a ganin fuskar, "lafiya ƙalau anty ashe biki manta niba gashi har sunana kika faɗa, kwana biyu bana ganin ku nayi tunanin ma kunbar nan ne" Suhaima tace A'a muna nan lafiya mun ɗanyi tafiya ne kwana biyu fatan kina cikin farin ciki, "sunkuyar da kai Sajeedah tayi da murmushi tace ina lafiya dama tun ranar da kika ce zaki nemeni ne naji shiru sannan banƙara ganin kiba sai yau ina doba ƙofar ɗakin ku sosai amma bana ganin fitowar kowa ko shigar wani", To shikenan yanzu sauri nake idan nadawo zan ne miki, " To adawo lafiya Sajeedah ta furta cikin sanyin murya" Suhaima ta lura yarinyar kamar akwai magana abakin ta to amma saboda sauri take shiyasa tace ba damuwa nagode Sajeedah amma tasa aranta tana dawowa zata nemi Sajeedan, "amma anty bansan sunan kiba" Suhaima wadda hattafara tafiya ta tsinci muryar Sajeedah akunnuwan ta SUHAIMA Sunana, tafaɗa batare da ta jiya ba ta cigaba da tafiya cikin sauri da alama dai uzirin ta babba ne,
Ɗaya daga cikin matan dake zaune a tsakar gidan, cikin sauri ta janyo Sajeedah tare da Faɗin ke gidan uban wa kikasan wannan mai kama da aljanar kuma sannan ba Hajiya fanteka tace kada wanda ya shiga harkar suba babu ruwan mu dasu suma babu ruwan su da mu kina ganin fuskokin su kullum a rufe alamar babu gaskiya a tare da su kina ganin yanzu ma da ta fito babu wanda tayi wa magana kanta a ƙasa ko cikin idon ta bata bari a gani saboda rashin gaskiya, jin surutun matar yaƙi ƙare wane Sajeedah ta janye hannun ta daga ruƙon da tayi mata batare da tace mata cikan kiba, haka sauran mutanan dake gurin suka haɗu akan Sajeedah kowa da abunda yake faɗa hadda masu cewa sai sun gayawa Hajiya fanteka idan ta dawo wasu kuma na zagin Su Suhaima,
Bayan fitar Suhaima daga cikin gidan wata baƙar mota ta hanga daga ɗan nesa da ƙofar gidan ƙirar TOYOTA hatta glasses ɗin motar tinted ne, murmushi Suhaima tayi mai sauti saboda taga wadda take cikin motar Hajiya fanteka ce zaune ita da wani alhaji a gidan gaba wani irin ƙaton mutum ne baƙi gashi lukuti sai faman hura hanci yake kamar botorami, saida ta ɗan jima tana kallon mutar kafin ta juya ta nufi titi, Ɓangaran Hajiya fanteka kuwa batasan Suhaima ta gansuba saboda tana ganin ai glass ɗin motar tinted ne, batasan Suhaima tafi ganin abunda ke acikin duhu ba sannan duk yadda take nesa da abu to tana iya ganin sa tar tar,
Waccan fa wace ce tafito daga cikin gidan ki fuskar ta a rufe? gashi naga ta daɗe tana kallon motar nan, wannan mutumin ne dake zaune gefan Hajiya fanteka a cikin mota yayi maganar yana kallon ta, hhhm saida ta numfasa kafin tace itace fa sheɗaniyar Yarin yar danake faɗa maka hatsabibiya komai nata ba irin na mutane ba bana son gani ta Sam kwana biyu, nane mesu narasa a gidan ita da ƴar uwar ta sannan kowa na tambaya zai ce bai ga sanda suka fita ba, shiru mutumin yayi alamar yana nazari yaɗan jima ahaka kafin ya kalli Hajiya fanteka yace tabbas akwai babban al-amari atare da Yarin yar nan dole sai kin kula sannan kinyi ta katsan tsan duk abunda zai kawo mana matsala acikin tafiyar mu kawar dashi muke, sama da shekara 30 babu wani abu daya shiga tsakanin mu da harkokin mu to kikula sosai, saida yakai ƙarshan maganar tashi Hajiya fanteka ta ɗora da cewa kada kadamu alhaji Talle zankula da komai a ɓangare na don nima banyar da da Yarin yar ba kwata kwata, da wannan maganar ya tashi motar suka fita daga Layin,