← Book details Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 37

Sashe 34

Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Ganin babu motsin kowa sannan babu alamar wani zai fito cike da kwarin gwaiwa Suhaima ta ƙarasa cikin kata faran parlourn tasamu guri saman kujera ta zauna, lumshe kyawawan idanuwan ta masu wani irin sihirtaccan kyau da jan hankali mai kallon su a wasu lokutan kuma subada tsoro ga wanda ya ɓata mata rai, sosai ta lunshe su sakamakon jin daɗin sanyin A. C yana ratsata tun daga tafin ƙafar ta har kai, ga wani dadda ɗan ƙamshin turare wanda tama rasa daga inda yake, dama tana matuƙar ƙaunar weather na sanyi sai hakan ya ƙara mata jin daɗi da nutsuwa,
Baffa ne zaune shida Uncle Yusuf a private parlour ɗin shi, hankalin su gaba ɗaya Yakoma kan wata ƙara mar T.V dake gaban su saman wani ɗan madai dai cin table, "cikin nutsuwa uncle Yusuf kai duban sa kan baffa kafin yace amma baffa wannan Yarin yar da alama bata da gaskiya gashi kace a shigo da ita hankali na sam ya kasa kwanci" yakai ƙarshan maganar tasa tare da ƙara kai dubansa kan T.V ɗin wanda Suhaima ce gata nan zaune a inda ta zauna kan kujera fuskar Nan a rufe kamar kullum sai ido kawai ake gani, ita ce suke gani kafin baffa yace wani abu kawai Suhaima tabuɗe idon ta tare da ɗan ɗaga kanta ta kalli saman parlourn sai tin CAMERA ɗin Wanda ita batasan ma da wani C.C.B.T ba a parlourn, lokacin da uncle Yusuf yaga Ash eyes 👀 ɗin ta saida ya zabura tare da Faɗin "baffa kagani ko wannan daka gani ma ba mutum bace kalli idanuwan tafa launin TOKA," yayi maganar tare da nuna fuskar Suhaima ta cikin T.V ɗin saida baffa ya ɗanyi gyaran murya sannan uncle Yusuf ya dai dai ta nutsuwar shi saboda shi ya ma manta a gaban baffa yake,
Shiru baffa yayi shima ya zubawa T.V ɗin ido yana kallon idanuwan Suhaima sosai wanda take ta juya su alamun ta kallon wani gurin a cikin parlourn, sai da baffa yayi nazarin ta sosai kafin yanisa, cikin dattaku irin nasa yafara magana da ɗan nasa uncle Yusuf, ".
...Yusuf ina son ganawa da Yarin yar nan saboda a jiki na nakejin ita ɗin ba cutar damu tazo yiba, sannan ina ganin kwarin gwaiwa a tattare da ita katuna fa tsawan kwana huɗu 4 tana zuwa nan kullum sai mun ganta har tagaji ta tafi, to akwai wani dalili mai ƙarfi dayasa takezuwa nan ɗin, saboda haka inaso abata dama, sannan maganar launin Ida nuwanta baka ganin cewa Allah zai iya halittar ta a haka ko fiye da hakan ma, idan ka duba ma ai Sulaim shima wani lokacin launin idon sa yana canza wa daga asalin brown ɗin Sa, Abu na ƙarshe danakeso kasani shine bana son kowa yasan da zuwan yarinyar nan cikin Ahalin mu daga ni sai kai shiyasa ma nace a kashe gaba ɗaya Cameras ɗin gidan nan har sai an shigo da ita, saboda akwai wani baƙon al-amari dan gane da Yarin yar inaso nagaba da ita ni kaɗai idan da yiwuwar wani yasani to zan haɗa taro zuwa gobe"
Sai da uncle Yusuf ya tabbatar baffa ya kai aya ya tsaya sannan yace"insha Allah baffa duk yadda kace haka za ayi, babu wanda zan sanar wa da wannan maganar matuƙar ba kai kabani dama ba, Allah yasa muji alkhairi akan Yarin yar,
"Ameen ina fatan haka cewar baffa kafin yace zaka iya tafiya zangana da ita Yarin yar kashigo da ita ciki"
Muƙewa uncle Yusuf yayi tare da Faɗin "to" aranshi kuma yana mamakin yadda akayi baffa yayi saurin amincewa da Yarin yar haka bugu da ƙari har cikin kuma yace a shiga da ita har babban parlourn sa, wanda idan aka cire su ƴaƴan sa to ko jikoki ba kowa ya isa shigaba sai Sulaim shine wanda bashi da wani shamaki da ko ina na cikin ARAB ESTATE sai dai inda bai so shigaba,
Ɓangaran Suhaima kuwa batasan wainar da ake toyawa ba sosai take jin sake wa aranta ta rage jin fargabar da take saboda addu'oin da take ta karan towa cikin iKon Allah abun ya lafa mata, har da jingina bayanta ajinkin lallausar kujerar wadda sai ka rante da audiga akayi ta bada soso ba, tare da lumshe idanuwan ta wani irin dadda ɗan bacci tafara ji yana fizgar ta, tana shirin kwantar da hanta saman kujerar yadda zata ɗan ji daɗi, kawai tafara jin alamar motsi ana tahowa da sauri ta gyara zaman ta tare da dai dai ta nutsuwar ta tayi ƙasa da kanta,
Da sallama uncle Yusuf ya shiga parlourn da take, acan ƙasan maƙoshin ta ta amsa sallamar take taji tsohuwar ƙiyayyar da take yiwa Ahalin Arab ta dawo sabuwa acikin ranta har wani zafi take ji acikin ran ta da zuciya, kallon ta uncle Yusuf yayi sosai ana ƙara karantar Suhaima wadda kanta ke ƙasa tasan da shigowar mutum amma tayi kamar batasan da hakan ba, "zaki iya biyo ni uncle Yusuf yafaɗa batare da ya zauna ba yayi gaba abunsa aransa yana tunanin to ko dai kurma ce bata magana ko kuma gaisuwa ne bata iya ba" Suhaima taji abunda yace saboda haka ta tashi tabi bayan sa zuwa parlourn da baffa yake zaune yana kallon duk abunda kefa ruwa har saida yaga suna bakin ƙofa zasu shiga sannan ya juya T.V ta kalli baya ta yanda mai shigowa bazai iya ganin abun da ke ciki ba, a ƙofar shiga uncle Yusuf ya tsaida Suhaima ta hanyar ɗaga mata hannu ba musu taja ta tsaya cak sai da yafara shiga baffa yabada izini sannan yayi mata iso zuwa ciki, kanta a ƙasa tayi sallama ƙasa-ƙasa sai da suka kai har inda baffa yake sannan uncle Yusuf ya russuna a gaban mahaifin nasu tare da Faɗin " baffa na barku lafiya" jin jina kai kawai baffan yayi shikuma yajuya ya fita zuwa house ɗin shi zuciyar sa duka babu daɗi saboda bai yadda da Suhaima ba a ransa kuma yana fatan Allah ya tsare mahaifin nasu da ga sharrin komai gashi baffan ya hana shi zama bare yaga abunda zai faru amma aransa yace dole zan sa ido sosai har naga fitowar Yarin yar,
Kallon Suhaima baffa yayi wadda take tsaye a kanshi lokaci ɗaya yaji ƙirjin sa ya buga da ƙarfi har sai da ya dafe shi ya furta "hazbunallahu wani'imal wakil" cikin zuciyar sa tare da jin Yarin yar har cikin ransa bai san kuma dalilin hakan ba gashi dai ko fuskar ta bai gani ba" ƴa ta samu guri ki zauna kinji" baffa ne yafaɗa cikin nutsuwa, Suhaima wadda tunda taji muryar baffa gaba ɗaya taji wani abu ya daki tsakiyar zuciyar ta wanda itama batasan dalilin hakan ba, lokaci ɗaya kuma taji daɗin kiranta da yayi da ƴar sa da yayi wanda batayi tsammanin hakan ba duk zaton ta ba zo a haka ba tayi tsammanin zasu wulaƙan ta ta ko suci mata mutunci, ko su sa akulle ta shiyasa itama tazo da shirin ta kullum da shirin tun karar su take tare da ɗaukar wa kanta alƙawarin sai ta wulaƙan a halin gidan ta tona musu asiri sannan ta kashe duk wani wanda yake da sa hannu a tarwatsa farin cikin rayuwar su tundaga ƙuruciya, kisa mai haɗe da tsanin azaba ɗaya bayan ɗaya saboda ita aranta take da yaƙi nin basu isa suyi mata komai ba dole ta ɗau fansar ta,
Sai da baffa ya ƙara Faɗin ko dai ƴar tawa kurma ce," cikin nutsuwa Suhaima ta russuna a gaban dattijon wanda taji gaba ɗaya jin nauyinsa yakama, ta furta " barka da yamma" bai amsa ba sai cewa da yi zauna sosai saman kujera, tashi Suhaima tayi ta zauna, sai da ta zauna sannan baffa yace, "barka dai sannan ya ɗora da cewa" a madadin Ahalin gidan nan inayi miki barka da zuwa, yaci gaba da cewa "Yarin Ya yau tsawon kwana huɗu 4 kenan kina zuwa nan kullum ina ganin zuwan ki da tafiyar ki ina so ki sanar dani dalilin zuwan ki nan ɗin saboda mu masu mara ba da kowa ne,
Ɗan jim Suhaima tayi don bata iya ƙarya ba tana son tafaɗa masa don ba tsoro take ji ba, sai kuma wani sashe na zuciyar ta yake bata umarni kan kada tafaɗa ɓoyewar shi zai bata damar ai watar da aikin ta yadda take so kafin lokacin bayyana musu gaskiyar yayi, take ta buɗe baki tace "babu wani abu dama gurbin aiki nake nema a gidan nan koda wanke-wanke ne da shara" ta kai ƙarshan maganar a ɗan sanyaye jin wani abu ya to kare mata a maƙoshi,
Shiru baffa yayi yana nazarin ta sosai, har saida Suhaima tafara tsarguwa jin shirun da yayi kaddai ace ya gano ta, katse mata tunani yayi ta hanyar Faɗin " To amma ƴa ta wani yace miki muna neman masu aiki ne ko kuma kawai zuwa kikai?" a a babu wanda yafaɗa min hasali ma bansan nan ɗin ba dalilin wani ɗan gidan nan ne da yayi mana alkhairi nida ƴar uwata shine ni biyo bayanshi ranar domin yi masa godiya kuma bansamu damar hakan ba, bayan naga inda ya shiga saina koma ganin babban gida ne sainayi tunanin dawo wa ko zansamu aikin yi saboda Kula da kanmu"
" To amma ina iyayan ki sun san kina zuwa nan ko su suka ce kine mi aiki" baffa ya ƙara jefa mata tambayar, babban abunda Suhaima ta tsana kenan tambaya, a taƙaice ta bashi amsa da " mu marayu ne Bamu da kowa dagani sai ƴar uwata" taɓoye mishi maganar mother, cike da tausaya wa baffa ya ɗago ya kalle ta sosai har cikin ranshi yaji son yarin yar tamkar shi yahaifeta Tunda ta shigo yake ji wani tsohon al-amari na taso masa amma yakasa tuna Meye wannan ɗin gashi har ga Allah ya yarda da ita ɗari bisa ɗari saboda yadda yaga tana magana cikin nutsuwa da kwarin gwaiwa, " cikin halin tausayi yace" Allahu akbar Allah yayi musu rahma, ina mai Baku hak'urin rashi, sannan mu ɗaukar masu aiki duk ƙarshan shekara kai tsaye ake kawo mana su daga wasu yankunan ƙasa shan da kuma na wannan ƙasar ba'a daɗe da ɗibar ma aikatan ko wane ɓangare da ke cikin gidin nan ba, amma kukan ku yazo ƙarshe ƴa ta zaku dawo nan keda ƴar uwar taki sai asamu inda za abaku kurinƙa kulawa dashi,
Karo na farko Suhaima ta ɗago kai don ganin wannan mutumin mai imani da tausayi yahar haka, a lokacin da tayi arba da fuskar baffa take taji wani ya kwanta mata acan ƙasan ranta take jin kamar tana da alaƙa dashi saboda yadda zuciyar ta ta karɓe shi lokaci guda duk da wutar tsana da kuma ƙiyayyar da takeyi wa mutanan gidan, kwar jinin sa da cikar kamalar sa da dattaku irin nasa taji cewar tabbas akwai sabon al-amari dake shirin faru, "a hankali kuma ta furta muna godiya sosai Ranka ya daɗe Allah yasaka da alkhairi"
Murmushi baffa yayi tare da Faɗin Allah yayi miki albarka zaki iya kirana da baffa saboda haka ƴa ƴa da jikoki ke kirana dashi, amma yanzu a ina kuke da zama sannan duk zuwa dakike bantaɓa ganin ki da ƴar uwar takiba, "shiru Suhaima tayi don ƙaryar ta takusa Ƙarewa dabara ce tafaɗo mata tace muna zaune a gurin wata mai saida abinci ne kuma tace nan da gobe zata sallame saboda itama zata yi tafiya zuwa garin su kuma dama a gidan ta muke da zama" jin jina kai kawai baffa yayi alamar gamsuwa da maganar taya, kafin yace yanzu zansa a ɗauke ki amai dake gidan naku sai kitaho da ƴar uwar taki zanyi magana akan inda za abaku ku zauna, amma ƴata kafin ki tafi inason ganin fuskar ki idan babu damuwa saboda idan kuka dawo za a wuce daku ne ba lallai kudawo tanan ba sai na ne meku sannan ba dole guri ɗaya zaku zauna ba keda ƴar uwar taki.
Babu musu Suhaima tasa hannu tare da fara kunce ɗaurin mayafin da ta rufe fuskar tadashi akaro na farko wani ko wata basu taɓa cewa tabuɗe fuskar ta kuma taboɗe ɗin saidai su gaji su ƙale ta hatta a garin su ko malaman su ɗai ɗai kune sukan fuskar Suhaima, amma wannan babu musu jitayi tamkar ana bata Umarnin buɗewa..!!
Chapter 34 · 0% Book details