← Book details Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 37

Sashe 23

Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Matso kiji matsawa anty jamilan tayi saitin kunnan ta mama bilki ta raɗa mata wata magana, kamar sababbin kamu gaba daya suka sheƙe da dariya abunsu kamar ba uwa da ƴa ba hadda tafawa"

"Tab lallai mama kin iya haɗa tuggu kinsan ma Kasar mutum, amma kuma abunda nake tunani ta yaya zamu samu HATIMIN nan kinga kowa fa yana so,"

"sannan kuma itama fa Hajiya maryam (ummeetha) dakike gani a tsaye take saboda kinsan mutanan me dugurin nan babaya ba suna"

"gashi ta ka mai mai ba musan inda zamu samoshiba" lokaci daya ƴar fara ar dake saman fuskar ta ta gushe"

"Ɗan shiru mama bilki tayi bayan tagama sauraran jamilan"

Eh gaskiya ba musan inda yake ba a yanzu amma za mu sani nan kusa sannan na fahimci kowa yiwa kansa yaƙin nan yake"

"to saboda haka zamu ciga ba da tafiya da hasheem, da Sambo, da Mansur han asamu nasarar samoshi daga ƙarshe nasan yadda nayi na raba su dashi"

"Azahiri dariya anty jamila ta saki tare da furta da kyau uwata nasan zakiyi kuma za ki iya"

"A zuciyar ta kuwa cewa tayi lallai ma ai wlh baza ta saɓu ba ku gama lissafin naku ni zan mallaki wannan HATIMIN mallakar"

"kodan na juya Abban Reeyam yadda nakeso da mitsiya tan dan ginsa wato mijin ta"

"Kamar daga sama saleem a tsinci muryar princess tana masa maga"

"good morning yaya saleem"

"Morning little princess"

"Dariya tayi har kyawawan haƙoron ta suka bayyana"

"Ina tamaga amma ba kaji ba sai yanzu hope dai lpy"?

"Tafaɗa tare da zama akusa dashi tana kallon sa"

"Lpy
yabata amsa a gajarce"

"Saboda baya son tada meshi da surutu shi kadai yasan abunda yake ji, sai kuma wata zuciyar tace masa to ka tambaye ta game da suhailat mana ko zaka samu wani abu akai"

"Aiko babu ɓata lokaci yajuya sosai ya fuskanci princess sannan yace"

"Ƙanwata bana ganin Suhailat 2days Allah yasa dai lafiya"?

"Ɗan ɗaga kai princess tayi alamun tana tunani kamar wata babbar mace," dama princess badai iyayiba da manyan ce"

"Nima dai naga bata fitowa yanzu sosai sai zata tafi school ummeetha ta tambaye ta lafiya"

"Tace lafiya kawai karatu ne yayi mata yawa ga exam." abinci ma kai mata akeyi upstairs"

"Saleem yaji daɗin jin tana lafiya ke nan tabbas shi take ɓoyewa kanta kenan"

"Suna zaune ummeetha ta sauke ita da abiiy"

"Gaida su saleem yayi da fara'a ɗauke a fuskokin su suka amsa masa"

"Abiiy yace tana nan ta cika ka da magana ko?

"Dariya Saleem yayi kafin yace Eh Abiiy tunɗazu tanan tana aikin nata"

"Har zillo princess take wajan cewa kai yaya saleem bakai ne ka tsaida niba kana tambaya ta ina aunty Suhailat shine zakace na adameka ko sarkin kuka idon ta har ya cika da hawaye"

"Shiko saleem jiya yi tamkar ya nitse don kunya Yarin yar nan tagama dani ya furta hakan aransa kansa a ƙasa saboda tsabar kunyar dayaji"

"Murmushi ummeetha kawai tayi ganin saleem ɗin duk ya wani diriri ce, tace"

"Ƙale ta yaro na kutaso muje dinning area breakfast is ready"

"Kafin mommyn ku da daddy su shigo bata rufe baki ba sai ga sunan"

"Gaba dayan su suka nufi dinning area ɗin"

Bayan sun gaisa ummeetha ta sanar musu angama komai gobe zasu wuce *MASARAUTAR GABAS* har ma ta sheda musu da wuwar yariman gabas ɗin wato Sultan"

"Mommy tace kice kenan sulaim ma zai iya bin mu kenan Tunda mutumin nasa ya dawo ƙasar"

"Eh to ba mamaki cewar ummeetha"
Don har cikin ranta bata kawo zai bi sun ba

__________________________
____________________
_____________

"Suhaima ko cewar DR. Muhibbah wadda ta shigo duba jikin khaltum bayan sun gama breakfast"

"Ciki da girmamawa Suhaima tace eh suna na kenan"

Dr.muhibbah taci gaba da cewa yauwa naga jiki yayi kyau sosai"

"DR. Sulaim yana hanyar zuwa idan yaƙarasu za a aiko kizo dama nayi miki alƙawarin yau zaki jikomai ko"

"Ɗaga kai Suhaima tayi alamar To daga can ƙasan zuciyar ta kuma tana mai mai ta sunan DR. Sulaim"

"Batare da sanin Meye dalilin yin hakan ba"

"Waye shi DR. Sulaim ɗin"?

"Babu shiri taji tambayar ta kwace mata da sauri ta dafe bakin ta"

"Murmushi Dr.muhibbah tayi sannan tace kibari yazo za kisan koshi waye"

Batajira cewar Suhaima ba ta juya ta nufi ƙofa cikin ɗan saga murya khaltum tace mun gode sosai"

Ɗaga kai kawai Dr.muhibbah tayi batare da tajiyo ba.!!!

*Comment nd share more like fisabilillah*🙏

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp channel

*AHALIN MU DAYA*

*CREATED AND WRITTEN*
*BY*
*Fatima Y zakariyya*
_😍Oum Ameerah_😍

*NAZARI WRITER'S ASSOCIATION*📚
_Sarauniyar👸Nazari writer's association_

______Dedicated to aunty salma💎

*Page* 3⃣ 7⃣↔️3️⃣8⃣📖

Batajira cewar Suhaima ba ta juya ta nufi ƙofa

"Cikin ɗan ɗaga murya khaltum tace mungode sosai"

"ɗaga kai kawai Dr.Muhibbah tayi batare da tajiyo ba"

"Cikin nutsuwa yagama breakfast din nashi amma duk hankalin shi yana kan asibiti"

"Ya rasa Meye dalilin hakan"

"Sallah ma sulaim yayiwa baffa sannan yanu Part din su ummeetha don ya shida musu tafiyar sa zuwa *BARNO STATE*"

"Yana fita suka haɗo da barrister Sulaiman ɗan gidan mai girma hasheem yana ƙoƙarin shiga perlon baffa sai sauri yake dagani wani abune yakawo sa"

"Ɗauke kai barrister Sulaiman yayi kamar baiga sulaim ba"

"Shiko sulaim bama shine agaban saba yi yayi kamar Bai san da wanzuwar mutun a gurin ba ya bude mota ya shiga ya fisge ta da gudun gaske"

"Kamar sakarai haka barrister Sulaiman yabi bayan motar da kallo"

"Cije lips ɗin sa yayi naƙasa cike da takaicin sulaim bai kula shiba"

"Da haka ya shige ciki afili yace zaka gane kuranka barganin kamar kafi kowa acikin dangi"

"Babu ko salla haka ya fada cikin perlon baffa yana tafaman surutu shi kadai"

"Ke kuma kukan Meye kike yi kida bakya rabo da kuka cewar Hajiya Turai tana kallon sabrina"

"kamar wadda ke jira haka sabrina ta zabura ta dago daga saman bed din da take kwance fuska duk hawaye"

"Haba mameey tunjiya nake kiran yaya sulaim amma baya picking call sannan Yanzu NA tashi tun ɗazun tana ta ringing amma yaki dauka na sake kira kuma busy"

Takai karshen maganar tata da cikin kuka sosai

"au dama ke saboda ɗan iskan yaron nan ne kike so kisawa kanki cutar hawan jini da ciwon zuciya Haba daughter na bana ce dole zaki aure shiba damuwar duk ta Meye? "

Bata ƙarasa ba suka tsinci muryar anty jamila tana magana daga bakin ƙofa"

"Lallai Yarin yar nan kin haɗa kaki da aiki wlh yanzu ke akan wannan mara lafiyar yaron kike so ki kashe kanki to Bismillah"

"Ki kashe kan naki bayankin mutu zai aure mata har hudu bashida wata asara ke kuma kinyi wa kanki"

"keko kamar ba mace ba"

Ta inda anty jamila take shiga ba tanan take fita ba"

"Hajiya Turai wadda tayi sororo tana kallon ta tama rasa Meye za tace ga baƙin cikin tana yiwa ƴar ta ɗaya tilo fada"

Cigaba da magana anty jamila tayi

"Jinai ance barrister Sulaiman yana sonki sosai amma shine kika tsaya kina fige wanna kazar asara rar ko?"

"Dame ye shi sulaim din yafi Sulaiman babu tsabar jaraba ce irin taki sai kuma kwadayin wannan kyan nasa kamar aljani da kuma kwadayin dukiya wadda shima ai Sulaiman din yana da ita"

"Kinga jamila bazai fa yiwu ba kizo ki rufe min ƴa da fada kamar ke kika haifa min ita"

"Ashe dama laɓe kikeyi mana bansani ba"

"Kuma maganar so baza ta aure wanda bata so ba dole ne ta zabi wanda yayi mata kuma ko waye dole ya aure ta" ehe

Tare ta anty jamila tayi ta hanyar cewa"

Au dama wai Turai kina da wannan kwarin gwaiwar amma aka marar miki ƴar taki amma kikayi shiru"

"Sheƙewa tayi da dariya sannan ta ciga da fadin ai wannan ihu bayan hari ne kikeyi ai kamata yayi kununa musu yadda kike son ƴar taki a gaban su bawai anan ba"

"Ƙuluwa iya Ƙuluwa Hajiya Turai tayi jitake kamar ta tashi ta rufe anty jamilan da duka amma babu hali"

Tabuɗe baki da niyar tayi magana sai anty jamilan ta riga ta ta hanyar cewa"

"Kinga duk ba wannan ne ya kawoni ba gurin ɗan uwa na nazo ayimin iso gurin sa"

Kafin Hajiya Turai tace komai wayar anty jamila ta ɗauki ruri juyawa tayi ta fita daga cikin bedroom din sabrinan tare da kai wayar saitin kunnan ta"

Wata muguwar harara Hajiya Turai tabi bayan anty jamila da ita cikin jin zafi da ƙunar rai "

" Tace ai da biki tafiba naga uban dazai yi miki ison wajan nashi"

Maganar Sabrina ce ta dawo da mameeyn cikin hayyacin ta"

"Lallai ma anty jamilan nan mameeyn kinga fa part ɗin mu tazo Sannan kuma har cikin bedroom ɗina kuma ta fadi abunda ranta yake so tatafi"

"murmushi Hajiya Turai tayi sannan ta ɗora da cewa kada ki damu kinji my lovely daughter"

"Zakiga yadda ƙarshan wasan zaizo akwai abunda ma haifinki yakeso ya mallaka da zarar yasameshi tasu taƙare sannan mukuma zamu koma, *GOVERNMENT HOUSE*"

"Wani irin ihu Sabrina tasa tare da rungume Mahaifiyar tata pls mameey da gaske kike? "

"Eh mnh na taba yi miki ƙarya ne"

Daga kai Sabrina tayi alamar a a"

Take taman ta da batun sulaim ta shigar murnar jin zasu koma *GOVERNMENT HOUSE*

"Mameey kinga za kizama *First lady* nikuma zanzama *star* acikin friend Di na kuma sannan dole yaya sulaim ya aure ni kodan ƙarfin ikon DADA na"

"Takai ƙarshan maganar cike da faɗaɗa murmushin kan fuskar ta"

"Haka ne daughter kada ki damu komai a hannun mu yake zaki zama yadda kike so kishiga inda kike so ki taka wanda kike so cewar Hajiya Turai tana kallon ƴar tata itama da murmushi bisa fuskar tata wadda daka gani kasan tasha man kanti"

"Yes Mameey Sabrina tafaɗa tare da durowa daga saman bed ɗin ta nufi toilet da alama ko salla ma bata yi ba"

Aɓan garan sulaim kuwa bayan ya sanar wa da su ummeetha tafiyar sa zuwa *BARNO STATE* da yamma cin ranar"

"Ummeetha ta nemi ya bari su tafi tare zuwa gobe"

"Yace mata Ai ya gama komai yayi booking flight ✈️ din yamma"
Chapter 23 · 0% Book details