← Book details Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 37

Sashe 31

Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Shima barka da Fitowa yayi masa Yana Mai da dubansa kan wayar Sa don lokacin zuwa lokaci sai yaqara duba saqon Suhailat Kuma har lokacin Yakasa Yi mata Reply,

Yarima Sultan yaga kamar Akwai Farin ciki atattare da Saleem Hakan yasa shi kasa yin hakuri ya furta,

kamar Akwai Farin ciki atare da baqona Kuma aboki na Saleem?

Saleem ya tsinci muryar Yarima Sultan a kunnuwan sa Yana magana,

Qara fadada murmushin shi yayi tare da Fadin Alhamdulillah Yarima,

Jinjina Kai Yarima Sultan yayi alamar gamsuwa dakuma Jin dadin Hakan,

Bayan ya bude laptop 💻 din dake ajiye gabansa saman table yaqara Fadin Yarima zai sojin meye silar wannan Farin ciki da abokin sa yake ciki,

Dasauri Saleem yaqara dagowa ceke da mamakin Yarima Sultan Bai taba tsammanin haka yake ba bashida girman Kai gashi da saurin sabo gashi Yana magana bakamar yadda yayi tsammani ba,

Duk Saleem Yana wannan tunani ne ba tare da sanin waye Yarima Sultan ba Yana masa wannan ne duk saboda Sulaim bugu daqari ma jinin su yahadu, sannan a wasu lokutan Yana son wasa da tsokana,

Aboki na Soyayya tana da Dadi idan ka samu Mai sonka Kuma kaiima kakeso to haka ne yafaru dani a Dan qanqanun lokaci Saleem ne kemagana cike da shauqin abun da yake fada,

Yarima Wanda duk yaji komai murmushi yayi Wanda harsaida tsiraran haqoran sa farare tass suka bayyana,

Kallon Inda Sulaim yake yayi har lokacin da murmushin akan fuskar sa,

Suna hada ido da Sulaim Wanda duk yanajin su duk da wayar shi yake dannawa kamar baisan sunayi ba,

Cike da basarwa Sulaim ya daure fuska don ya fahimci Yarima Sultan din acikin yanayin wasa yake,
Kuma yasan yanzu sai fara tsokanar sa gakuma yajj kalaman Saleem tamkar Wanda yakamu da ciwone hauka haka ya dauki Saleem din,

Ganin Sulaim ya ya dare fuska ne Yarima Sultan yamai da kallon sa kan Saleem shima Sulaim din yake kallo,

Murmushi suka sake a tare,

Kamar Yarima Sultan bazaice komai ba cikin nutsuwar da ya furta abokina Ashe da gaske ne so Yana da Dadi kenan?,

Saleem yace Eh Nima akwanakin da suka wuce bansan hakan ba wahalar sa da radadin sa kawai nakeji tare da danasanin fadawa ta cikin sa Amma a yau Inajin Babu abunda yakai soyayya Dadi,

Wani irin kallo Mai kama da harara Sulaim yayi wa Saleem danshi har cikin ransa da gaske yake Saleem yakamu da matsalar kwakwalwa,

Murmushi Saleem ya sakarwa Sulaim,

Take Sulaim yamiqe da niyar barmusu gurin,

Ai kana tafiya sai mun bika duk Inda zakaje Yarima Sultan ne yayi maganar Amma idon shi nakan Computer 💻 din gaban shi Yana dannawa,

Dafe Kai Sulaim yayi tare da Fadin Ya Rabb ya koma ya zauna Dan yasan tunda yafada to baza su rabu dashi din ba,

Kafin kowa yaqara cewa komai saqon zuwan jakadiyar sarki yazowa Yarima Sultan Take yabada izinin tashigo,

Zubewa tayi a gaban Sultan tayi gaisuwa tare da kirari kala kala harsaida yada Katar da ita ta hanyar daga mata hannu,

Zaki iya gabatar da saqon sarki zuwa ga Sultan Yarima yafada fuskar Nan tashi tamkar Wanda Bai taba Koda murmushi ba,

Tuba nake ranka ya dade sarkin mu nagobe Allah ya temakeka tare da yawan nasara sarki yace asanar Maka zaku karbi Bakuncin Dan sarkin *DAMATURU* yanzu yasamu isowar saqon,

Sannan maimartaba sarki yaqara dacewa Asanar wa Yarima Yana da damar yin ko wace irin shiga Amma da zaiyi shigar *DAWISU* 🦚 Sarki zai so haka,

Mai martaba yaqara dacewa Yarima Yana da manya manyan baqi a Taron daza agabatar da yammacin a wannan rana Yarima yashiya tarbar su,

Allah yaqara Maka lafiya nagaba tar da saqon sarki,

Cikin Isa Yarima Sultan yace Zaki iya tafiya Asanar wa maimarta ba Adalin sarki Sultan yakarbi saqon sa Kuma Yana godiya,

Nabarku lafiya tatashi tafita da sassarfa,

Yarima Sultan komai wa yayi kamar bashine yagama wasa da murmushi ba yanzun Nan Kyakkyawan Hannun sa yakai Mai dauke da dogayen yatsu yasa ya rufe computer din dake gaban sa da alama Bai kammala abunda yakeyi ba,

Sabo yagama tsara komai hatta kayan dazaiyi hawa dasu zuk ya tsara Amma yanzu anason rusa masa shirin sa dafe goshe yayi tare da Dan zamewa ya jingina bayansa jikin kuje rar,

Sauri sauri gudu gudu haka jakadiya ke tafiya tamkar zata fadi ta nufi sashan gidan Galadima Kallon jakadiya HAJIYA MAI SORO tayi tare da Fadin ke Kuma lafiya Zaki fadamin parlour haka kamar wadda aka koro?

Rankiya dade uwar daki na tuba nake Tafe nake da labari zuwa ga *GIMBIYA SULTANA*

Meke Tafe dake zuwa gare ta hajiya Mai soro takara tambayar jakadiya,

Ina son sanar wa GIMBIYA SULTANA cewa Yarima Sultan shigar DAWISU 🦚 zaiyi a gurin Taron sa na anjima,

Sosai hajiya Mai soro tadawo da hankalin ta kan Jakadiya tare da Fadin wane tabbaci kike dashi akan maganar ki?,

Yanzu Mai martaba sarki ya turani na shedawa Yarima Sultan Hakan,

Aiki Mai kyau jakadiya kije kicigaba da SA idon ki sosai komai kika gani kizo da wuri kisanar min,
Yanzu saka mokwan wannan albishir din kinada kyauta ta musamman zata riskike zuwa jimawa Zaki iya tafiya,

Kihuta lafiya uwar dakina cewar jakadiya tafice,

Wani irin shu'umin murmushi hajiya Mai soro tayi Mai wayar fassarawa wayar dake gefan ta tadauka tareda Danna Kira,

Hajiya Mai soro itace matar Galadima wato qanin sarki Mai suna Murtala Shareef yanada Yara biyu Mudassir da Sultana,

💗💗💗
____---_____ *KANO*

*UNGUWAR KWANDILA*

Suhaima nifa gaskiya inaso kifada min wai Ina kike zuwa kwana biyun Nan Amma kin ƙi faɗamin Kaltum ce tafaɗin hakan cikin zafin rai tare da shan gaban Suhaima wadda ke niyar fita..!!

*Like nd share comments fisabilillah🙏*

What's app channel👇

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

_AHALIN MU DAYA_

💗💗💗

*CREATED AND WRITTEN*
*BY*
*Fatima Y zakariyya*
_😍Oum Ameerah_😍

*Nazari writer's association📚*

_Sarauniyar👸 Nazari writer's✍️_
_(THE QUEEN👑)_

________Dedicated to anty salma💎

*Page* 4️⃣7️⃣↔️4️⃣8️⃣📖

____---____*KANO*

_UNGUWAR KWANDILA_
Chapter 31 · 0% Book details