← Book details Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 37

Sashe 25

Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bataji daɗin hakan ba sam taso ace tayi magana dashi sosai amma ya ta iya ta amsa masa da" oky"

"iya ganin sa ma faran ta mata rai yake dole tabi Dr.jabir gidan koda kuwa Dr. Sulaim ɗin zaiji haushi akalla dai ta sake ganin sa"

"Daga nan ma sai ta gaida baffa da su ummeetha Tunda dama tana zuwa lokaci zuwa lokaci"

*️⃣*️⃣*️⃣

"Cikin ma ɗauka kin mamaki Suhaima ta sake murza ido akaro na biyu anya ba idan tane yake yi mata gizo ba"

"Khaltum nayi mata magana amma batabi ta kantaba tafita da sauri ta nufi office din Dr.Muhibbah don ta tabbatar mata da gaske ne abunda take gani ko kuma dai almara ne"

"Da sallama tashi ga tana shiga Dr.Muhibbah tace a a Suhaima lafiya dai ko zauna ga guri nan tafaɗa tare da nuna mata kujerar gaban ta"

"Zama Suhaima tayi tare da miƙawa Dr.Muhibbah wannan file ɗin da Dr. Sulaim yamiƙa WA wannan security din yabata"

"karɓa Dr.Muhibbah tayi ta shiga dubawa fuskantar ta da murmushi tace _your welcome Suhaima_

" Kin hadu da Dr. Sulaim kenan Ai wannan na sallama ne aka baku yanzu zaku iya tafiya"

Cikin sarƙewar murya Suhaima tace amma Dr. Biki fahimce niba wannan manya manyan kudin su zamu biya? "

Yanda Suhaima tayi maganar akwai ruɗu acikin muryar ta"

Wani murmushin Dr.Muhibbah tasakya yi mata kafin tace"

A a Suhaima ai angama komai ba a buƙatar koda naira 5 ɗinku komai kyauta Dr. Sulaim yayi muku wannan kudin da aka kashe ne wanda dama dole ne a file din sallama ana rubuta wa mutum gaba daya kudin da yakashe"

Kallon Dr.Muhibbah take da alama takasa yadda da maganar tata,

"Aran ta tace to idan banyadda da itaba dawa zan yadda kaf cikin asibitin nan"

Da sauri Suhaima tace dole na koma gurin wannan mutumin mai ban haushi bata ƙara jiran cewar Dr.Muhibbah ba tamike tafita da sauri,

Dr.Muhibbah nayi mata magana amma ina hankalin ta yayi can,

Dole nagansa na tambaye shi dalilin da yasa yayi mana suka wannan ɗin don gaskiya ni ban yadda dashiba

"Tana tafi zuwa office din da tana magana ita kadai kamar sabuwar cinkai"

"Knocking ta shiga yi amma shiru babu amsa sannan ƙofar a rufe take sosai"

"Wani security ne ya ƙaraso inda take tare da fadin baiwar Allah yallabai yafita yanzun nan"

"Saidai kiyi hakuri zuwa gobe don da alama yatashi aiki yau"

"Ina bazan iya jira sai gobe ba kafaɗa min inda yayi yanzu dan Allah"

Yafita yanzun nan ina tunanin ko mota bai kai ga shigaba yanzu"

"Tunkafin ya ƙarasa yi mata bayanin ta nufi hanyar da zata sada ta da babbar harabar asibitin"

Cikin rashin sa a tana zuwa motar shi tana fita daga cikin asibitin ba don ta hango shi sanda yake shigaba da baza ta iya tantance shi din ne ko bashi bane"

Da gudu Suhaima ta nufi bakin gate din tana fita ta shiga tsarar mai napep saboda tabi bayan Dr. Sulaim ɗin gani takeyi idan ya tafi to shikenan har abada baza ta samu ganin saba, Allah ya temaketa saboda titi ne tayi saurin samun napep din,

Wani mai napep ne ya tsaya agaban ta tunkafin ya gama tsayawa tafaɗa ciki tare da ce masa motar nan nakeso kabi bayan ta duk inda tayi,

Da sauri Tafaɗa cikin napep din tare da nuna masa motar da sulaim yake ciki wadda suke tafiya sannu ahankali hakan yabawa mai napep din damar bibiyar motar cikin kwanciyar hankali...!!!

*TOFA GA SUHAIMA AHANYAR ZUWA ARAB ESTATE INDA TA DAƊE TA NEMA, KOYA ZATA KAYA KUDAI KUBIYO NI*

*Comment share and more like fisabilillah🙏*

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp channel

*AHALIN MU DAYA*

*CREATED AND WRITTEN*
*BY*
*Fatima Y zakariyya*
_😍Oum Ameerah_😍

*NAZARI WRITER'S ASSOCIATION*📚
_Sarauniyar👸Nazari writer's association_

______Dedicated to aunty salma💎

*Page* 3️⃣9️⃣↔️4️⃣0️⃣📖

"Da sauri Suhaima tafaɗa cikin napep din tare da nunawa me napep ɗin motar da Sulaim yake ciki, wanda motar ke tafiya sannu ahan kali hakan yabawa me napep ɗin damar bibiyar motar cikin kwanciyar hankali batare da tabace masa gani ba"

"tafiya suke tun Suhaima na saran sun kusa harma ta fidda rai ta zubawa sarautar Allah ido tana kallo"

"gani sukai motar Sulaim ta tsaya cak a dai dai wani katafaran *super market* amma babu wanda yafito daga cikin motar babu kuma alamar za afito din"

"take shima me napep din ya nemi guri daga dan nesa kadan da inda motar ta tsaya shima yayi parking a gurin"

"tunani Suhaima tafara yi cikin ranta tace to wannan nufin sa nan dama zaizo"

To ai nan bai yi miki kama da gida ba ko?"

" Zuciyar ta tabata amsa"

"to ko dai na sauka kawai naje na tambaye shi abunda nakeso naji"

"kada kuma na sauka kawai suja motar su tafi yazanyi kenan"

"Dan gaskiya ni banyadda da wannan mutumin ba dole akwai abunda yake nufi damu idan bahaka ba ta yaya zai biya mana waɗannan manya manyan kuɗa ɗan duk da shine mai asibitin dole akwai wani dalili"

"ita kaɗai take tafaman tambayoyin ta kuma tana bawa kan ta amsa"

"gaskiya Hajiya na gaji zaki iya sauka kisamu wani kibiya ni iya kudin na daga inda na dakko ki"

"Suhaima wadda ta tsunduma duniyar tunani ce ta tsinkayi muryar me napep din yana yi mata magana"

"mtss ta saki dan guntun tsaki ƙasa ƙasa sannan tace Haba malam idan kayi hakuri ai munkusa zuwa
Tafaɗi hakan ne batari da sanin shin yazo inda zaizo ne ko kuma siyayya zaiyi to kuma ai da yazo zai shiga har ciki ne da motar sannan da siyayya zaiyi da yafita ya shiga zuwa ciki"

Bata kai ƙarshen maganar zucin ba taƙarajin me napep din na mata magana aƙaro na biyu 2"

"au dama kinsan inda zamuje kenan to ai da wucewa mukayi kai tsaye da wannan tsaiwar da muke yi saboda kina ɓatamin lokaci nida na fito sana'a sannan kuma duk acikin kudin kine"

"Har Tabuɗe baki kenan zata yi magana kawai ta hango wani yanufi motar da Sulaim yake ciki hannun sa riƙe da wasu manyan jakunkuna shaƙe da kaya aciki"

"bayan wanda ya ɗakko jakunkunan ya tsaya saitin glass din motar yayi magana wadda bazata huce ƴan sakanni"

"sannan ya zagaya ya bayan motar ya bude ma ajinkaya bayan motar ya zuba kayan aciki sannan ya rufe"

"jira ake yana rufe bayan motar tun kafin ya mutumin Yakoma cikin *Super market* akaja motar da gudun gaske saɓanin farko da take tafiya a hankali"

"tun kafin Suhaima tace wani abu tuni mai napep din shima ya zura a guje yabi bayan motar"

"kallon tsarin unguwar Suhaima ta shiga yi wanda gaba ɗaya ya tafi da tunanin ta"

"wasu manya manyan gine gine take gani Tunda suka shigo gate din farko na unguwar ga dogayen benaye gashi ko ina kwalta ne duk Layin da suka shiga suka fita sai taga wani sabon titin ne abunda bata taɓa gani ba a zahirin rayuwar ta ba sai dai a films "

"a lokacin motar ta koma tafiya a hankali fiye da farko da alama sun iso inda suke son zuwa"

"wani abu da Suhaima bata taba ji ba tun bayan girman ta shine a yau take ji aran ta"

"tsoro da wani irin matsananci faɗuwar gaba Tunda suka taho take jin hakan har dafe ƙirji take tare da ambaton Allah a zuciyar ta"

"wahala bata ta taɓa sa Suhaima sarewa daga abun da ta ɗaura aniyar aikata shi"

"Hajiya ai gaskiya sai dai ki sauka anan kishiga da ƙafar ki idan sun sanki kenan nikuma kibani kuɗina na tafi don wlh ni da asanin ɗakko ki nakeyi saboda so kike kijamin masifa ana zaune cikin rufin asiri kisa akamani banjiba bangane ba Atoh me napep ne keta faman masifa shi kaɗai saboda ita Suhaima hankalin ta ba Agurin sa yakeba"

"jin alamun sun tsaya ne yasa Suhaima dawowa cikin tunanin ta tare da fadin malan yana ga ka tsaya anan ina motar da muke bi?"

"tsabar ganin ta raina masa wayo har jiyo wa saida yayi ya kalle ta kafin yace"

"nufin ki duk abunda nafaɗa miki biki jiba kenan nifa kinga zaki iya sauka nikuma nasamu nabar gurin nan don wlh ban yadda dake ba kin sa mun biyo bayan mota mun zo wannan unguwar da ko kuɗa sai ka daɗe kafin kaga wulgawar guda ɗaya bare mutum ɗan Adam kina ganin Tunda muka zo ko kukan tsuntsu babu a gurin nan gashi kinkama kin rufe fuska"

"cikin tsawa da wata irin murya wadda Suhaiman bata taɓa yiba tace dalla malan ina motar da muke bi take?"

"bawan Allah jikin sa har rawa yake wajen cemata ta shiga wannan *ESTATE* din dake gaban mu yakai ɗan ya tsan sa yanuna mata"

"to mu shiga mana tafaɗa cike da umarni"

"Hajiya ai irin wadannan gida jan ba'a taba shigar su idan har basu san da zuwan mutum ba kina ganifa gate din da na'ura mai kwakwalwa yake aiki ga *Camera's* tako ina"

"ganin duk ya yabi ya tsorata ne yasa Suhaima jin bata kyau taba tsawar da tayi masa aƙalla dai ko ba komai ya girmeta gashi ya temaka mata"

"cikin sanyin murya tace kayi hakuri amma yanzu Meye mafita don dole ina son ganin mutumin dake cikin motar nan"

"ni bansani ba wlh mafitar ɗaya ce muku ma kawai dan yanzu ko kin samu damar shiga wannan estate din wanda kike Nema baza ki gamshiba saboda kamar unguwa guda haka take ko daga nan ki hango kigani fa"

"kallon ta ta mayar gurin gate din dayake Dan nisa dasu kadan"

"idon ta bai sauka akan komai ba sai wannan manya manyan rubutun da akayi asaman gate ɗin wanda aka rubuta sunan estate din"

*ARAB ESTATE !* *ARAB ESTATE!!* *ARAB ESTATE!!!*

"sau uku tana mai maita sunan a fili cike da ruɗan Suhaima tacewa me napep din dan Allah ka taya ni duba abunda nake gani ne"

"shidai duk yabi ya tsorata da lamarin Suhaima gaba daya a tsorace yake addu'a yake aransa Allah yaraba shi da wannan yarinyar lafiya"

"da gaske ne abunda nake gani?"

"eh eh da gaske ne haka aka rubuta yabata amsa cikin rawar murya"
Chapter 25 · 0% Book details