← Book details Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 37

Sashe 35

Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

🌹🌹🌹
___________-------___________

_BARNO STATE_
_Masarautar Gabas_

........Shirye shiryen hawan da yarima Sultan zai gabatar ake tayi daga kowane ɓangare nacikin masarautar kowa yana ta hidima sai ka rantse bikin salla ko bikin aure akeyi acikin masarautar ɓangaran Ummul bait baƙi ne sosai daga wasu masarautun na kusa da nanesa,
Hajiya mai soro ce zaune saman kujera sai kuma wata doguwar matashiyar budurwa zaune tana fuskantar Hajiya mai soro, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya dagane kasan akwai mulki a tare da ita magana tafara tare da kai hannu ta dai dai ta zaman siririyar BARIMAR zinaran dake hancin ta, " umma kuna da tabbas akan maganar da jakadiya ta kawo nacewa yarima shigar ɗawisu zaiyi?" ta kai ƙarshan maganar tare da kallon Hajiya mai soro wadda suke kira da ummah, "tabbas wannan maganar haka take Sultana saboda mahaifan ki shima ya ƙara tabbatar min da maganar" ɗan Farr Gimbiya Sultana tayi da ido kafin tace "to shikenan a shirya min komai Tunda zuwa 4 ne za a fara gabatar da taron kuma sannan a ƙara yawan ƙaututtuka ga yarima Sultan wanda zan gabatar dasu a gareshi don ina sane da isowar Shaheedah cikin masarautar nan zuwa nan da jimawa, cikin isa da izza take maganar tamkar itace mahaifiyar lokaci zuwa lokaci tana ɗan kaɗa ƙafar ta a hankali"
Tana kai ƙarshan maganar tata tamiƙe tabar parlourn zuwa nata ɗakin, kallo Hajiya mai soro tabiya dashi dan ita kaɗai tasan abunda suka shirya wa yarima sultan a wannan hawan da zaiyi Sunyi alƙawarin ko yayi hawan bazai sakko lafiya ba, don ita fa duk yadda takeson Sultana ta auri Yarima sultan bai kai yadda take ƙaunar taga mijin ta akan mulki ba wato Galadima ƙanin sarki saboda haka take son idan har mijin ta bai samu damar hawa jaragar sarki ba to ƴar ta ta auri sarkin gobe Wato Yarima Sultan sai su samu sugama dashi da mahaifin sa sarki Yusuf Shareef su mulki yankin GABAS ita da mijin ta Murtala shareef,
Tana cikin wannan tunanin tasamu isowar jakadiya take ta bada izinin ta shigo dama ita take jira, da sauri jakadiya ta ƙaraso tare da zuɓewa a gaban Hajiya mai soro ta kwashi gaisuwa, saida ta bata damar magana sannan ta ɗora da cewa, "Ranki ya daɗe an gabatar da komai yadda kuka tsara, komai na ai watar dashi yadda ya kamata hatta dokin dazai yi hawan dashi nabawa sarkin doki ya shafa maganin a bindin Dokin kamar yadda kika bada umarni, kallon ta Hajiya mai soro tayi " aiki mai kyau jakadiya to shi wanda nace ki binne akan hanyar sa tazuwa ɗakin taron kinyi hakan? Ƙara russunawa jakadiya tayi tace a a ranki shi daɗe hanyar Da yarima Sultan zai bi babu gurin da za a binne wani abu saboda babu ƙasa amma dai munyi amfani da ta kalmin da zai sa yayin tafiyar sa zuwa gurin,
Dakyau naji daɗin hakan zaki ita tafiya amma yaya ɓangaran Fulanin sarki (ummu Safwan) babu wani abu da take shiryawa ko wani makirci, "eh to ranki shi daɗe bani da labari a taɓan garan ta saboda ta hana bada izinin shiga amma nasan duk wani shirin ta akan Yarima da Gimbiya Siyama ne... Tunkafin jakadiya takai ƙarshe Hajiya mai soro ta daka mata tsawa tare da Faɗin a gidan ubanwa tazama gimbiya ƴar ruƙo cefa acikin masarautar nan taya zata zama gimbiya?".
Saida jakadiya ta ɗan tsorata tare da Faɗin tuba nake uwar ɗaki na uwar mu maganin kukan mu Allah ya huci zuciyar ki da yaddar ubangijin sama sai Galadima yazama sarkin Gabas, "wani katsaitaccan murmushi Hajiya mai soro tayi tare da faɗin kin wanke laifinki Yalabarin gimbiya Shaheedah?
Yanzu naji ana sanar da tafiya ɗakko ta daga filin jirgi ta iso cewar jakadiya, shiru Hajiya mai soro tayi kafin tace zaki iya tafiya kome kenan ki sanar dani cikin gaggawa, "jakadiya ta amsa da cewa angama uwar mu maganin kukan mu nabarki lafiya"
Chapter 35 · 0% Book details