← Book details Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 37

Sashe 33

Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

_.....RAILWAY QUARTERS ARAB ESTATE_
Tsaye Suhaima take a gaban babban gate ɗin Estate ɗin tana kallon manya manyan gida jan dake ciki amma babu hanyar shiga yaushine zuwan ta na huɗu 4 kullum saidai ta gaji da tsaiwa da zagaye ta koma gida duk zuwan da take koda mahaluƙi ɗaya bata taɓa gani ya fito ko ya shiga ba tasha yin mamakin to ko dai babu mutane ne a gida jan abun na kulle mata kai, amma a yau taci alwashin sai tashi estate ɗin nan Koda kuwa shine silar Rayuwar ta koda zai zama idan ta shiga shine zai zama bugun numfashin ta na ƙarshe,
Bayan ta nutsa cikin tunanin da take tasamu guri ta zauna dagacan gefe kaɗan jikin wata ƴar ƙaramar bishiya mai kyau ganyen jikin ta sai ƙalli yake, babu zato ba tsammani abun tamkar a majigi tafara ganin wannan tangame man gate ɗin yana zugewa da kanshi sannu a hankali yana buɗewa da mamaki Suhaima taciga ba da kallon iKon Allah gashi dai taga babu wani ɗan Adam a gurin koda mutum ɗaya bare tace shi yake buɗewa, a ranar da tafara zuwa gurin taga faruwar hakan amma sai tayi tunanin gezo ne idanuwan ta sukai mata ko kuma don tana cikin tashin hankali ne shiyasa,
Batare da tsayawa wani dogon tunani ba Suhaima ta tura kai cikin Estate ɗin batare da jin ko ɗar acikin zuciyar taba cikin nutsuwa tafara tafiya akan dogon titin da yayi ciki sosai daga inda take bata iya ganin ƙarshan sa saboda yayi kwana kaɗan, kamar wadda akabawa umarnin ta juya, da sauri ta waiwaya baya ganin gate ɗin tayi Yakoma ya zugewa da kanshi kamar yadda yake tun farko, Take taji wani irin mummunan faɗuwar gaba take taji wani irin yanayi ya lulluɓeta cikin ranta tafara tunanin tabbas akwai wani babban al-amari acikin gidan nan saboda tasan bata taɓa jin irin yanayin nan sai idan wani abu zai faru da ita ko kuma zai faru da wani a gaban ta, tafiya ta cigaba da yi faɗuwar gaban ta na ƙaruwa da duk wani Taku da zata yi izuwa ciki, takun mutane taji abayan ta alamar ana nufu inda take cikin mamaki Suhaima ta cigaba da tafiya batare da ta juya ba,
Amma tana jin takun naƙara kusan to inda take, magana tafara ji da wani kalar yari wanda ita bata mataɓa jin irin sa batare da sanin Meye ake faɗaba ta cigaba da tafiya abun ta ƙinjinta sai lugude yake saboda tsabar faɗuwar gaba, ta tabbata ba tsoro take jiba to amma kuma akwai baƙon yanayi atattare da ita gashi jikin ta ya ɗauki wani irin zafi duk da sanyi da ake agari ga kuma sanyi yamma ya sauka don yanayin garin hadda HAZO, maza ne su biyu suka tare ta kallon su tayi ɗaya bayan ɗaya tun daga sama har ƙasa Uniform ne a jikin su da alama Securities ne don hadda bindiga a Saƙale a wuyan ko wannan su, dukan su BUZAYE Ne magana ɗaya yake yi mata cikin harshen su na Buzaye amma dai batasan Meye yake faɗa ba, ɗayan ne ya lura bata gane maganar ɗan uwan nasa, sai ya matso cikin Hausar shi da bata fita sosai yace mata "kibuɗe fuskar ki yanzun nan sannan kifaɗa mana zuwan Meye kike wannan gurin yau kwana huɗu kenan kullum sai kinzo"
Mamaki ne ya kama Suhaima a ranta tace ashe dama suna kallo na to ta ina suke ganina nikuma bana ganin su, kamar yasan abun da take tunani kenan ya ƙara ce mata "kullum sai munganki ta Camera fuska a rufe baki da gaskiya dole a kama ki nan ba gurin wasa bane" jin yadda yake magana dalla dalla Hausar tashi abun dariya hakan yasa Suhaima yin dariya ƙasa ƙasa batare da tace masa komai ba sannan bata da niyar cire mayafin fuskar ta ta, kafin yace komai Telephone ɗin hannun sa irin ta police aka fara magana daga ciki, magana yafara amma bata gane abunda yake faɗa shima na cikin wayar batasan Meye yake cewa ba duk da ana iya jin komai abu ɗaya ta fahimta shima kuma a ƙarshan wayar ne security ɗin ya faɗa "to yallaɓai" shi kaɗai ta iya gane wa, kallon ta yayi tare da Faɗin kibiyo yafaɗa tare da yin gaba babu musu Suhaima tabi bayan sa shikuma ɗayan security ɗin ya koma inda suka fito,
Tafiya suke tun Suhaima nasa ran ganin sun isa inda zasu je har tafara gajiya tacire rai tana bin ko ina da kallo cike da mamakin irin gine ginan cikin Estate ɗin wani irin haske mai jan hankali tafara hangowa kusa dasu kaɗan, har ta matsu su ƙarasa gurin taga hankyan Meye haka cikin Taku kaɗan suka isa inda wannan hasken yake, masha Allah Suhaima tafaɗa a fili, ganin wannan haɗaɗan kuma tsararran ROUNDABOUT ɗin dake a tsakiyar titi nan cikin Estate ɗin shagala tayi wajan kallon sa batare da sannin wannan security ɗin yayi gaba yabar taba baƙaramin jan hankalin ta wannan ruwan dake fitowa daga ƙasa yayi ba ga duwatsun dake kwance cikin sa sai suka ƙarawa ruwan kyau wanda yake fari tasss, saida ta kai hannu tasha wa ɗan nan kyawawan furannin dake zagaye da gurin, tama rasa me zata tsaya kallo komai ya nagurin ya matuƙar burgeta, ɗaga kanta sama tayi tare da kai duban ta kan wannan doguwar bishiyar kwakwan dake a tsakiyar cikin Roundabout ɗin saida ta ɗau lokaci mai tsayi kafin ta dawo da kanta ƙasa,
Ganin wannan security ɗin yayi mata nisa ne hakan yasa ta bin bayan shi a sukwane tana isa kusa dashi, sai ga wata mota nan tayi parking a gaban su ba shiri suka tsaya cak, wani ne yafito daga cikin motar da alama driver ne, kallon Suhaima yayi tare da Faɗin kishiga muje tare da buɗe mata back side na motar saida ta ɗanyi jim kafin ta sa kai ta shiga, za gayawa driver ɗin yayi, ya shiga kai tsaye ya zarce kan titin ALHAJI IMRAN ARAB STREET, Zare ido Suhaima tashigayi ganin kamar suna shirin barin gari kuma wai duk a cikin Estate ɗaya, amma aranta ko ɗar babu na alamar tsoro saidai kawai tanajin matsanancin faɗuwar gaba, bayan sun shiga house ɗin Alhaji imran har bakin ƙofar shiga cikin babban parlourn saida driver yakai ta sannan yace tashiga ciki, ba musu ta nufi ƙofar glass door ɗin ta zuge kafin tashiga da sallama ƙasa ƙasa jin ta taka wani abu mai laushin gaske hakan ne yasa ta saurin ɗagowa takai duban ta idan ta taka da ƙafar tata wani lallausan carpet ne tamkar audiga cikin jin daɗin yanayin ta ƙara nitsa kyakkyawar ƙafar ta aciki fara tasss mai ɗauke da dogayen yatsu, ganin babu kowa acikin ƙaton parlourn ne yasa Suhaima ƙara taka watayi zuwa ciki tare da kallon cikin make kyan haɗaɗan parlourn wanda ya tafi da tunanin gaba ɗaya, ganin babu motsin kowa sannan babu alamar wani zai fito cike da kwarin gwaiwa Suhaima ta ƙarasa ciki tasamu ta zauna kan kujera..!!

Ayi hkr da wannan
_F pen's_

What's app channel👇

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp group👇

https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs

_AHALIN MU DAYA_

💗💗💗

_CREATED AND WRITTEN_
_BY_

_Fatima Y zakariyya_
_😍Oum Ameerah_😍

*Nazari writer's ass......📚*

_Sarauniyar👸 Nazari writer's✍️_
_(THE QUEEN👑)_

________Dedicated to anty salma💎

*Page* 4️⃣9⃣↔️5⃣0⃣📖
Chapter 33 · 0% Book details