← Book details Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 37

Sashe 28

Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiko Sulaim maganganun nata sunfara hawar masa kai dama shi ba don Sultan din ya matsaba da bazai zo yau sugaisaba sai gobe idan su ummeethar sunzo sai ya shigo
Gani yake gwaggon nada haya niya ga tada takura shiyasa baya marmarin zuwa inda take,

Kafin gwaggo murja ta ƙara furta komai Suka jiyo muryar baba waziri yana shigowa da sallama,

Amsawa suka yi bandan Sulaim ko ya amsa a zuciyar sa Oho,

Marhaban lale da zuwan ku ashe manyan baƙi ne damu yanzu nasamu labarin iso warku baba waziri ne ya furta hakan dai dai yana zama saman kujera,

Barkan ku da zuwa,

Barka dai baba waziri Sultan ne ya amsa,

Barka da warhaka fatan munsameku cikin ameenci cewar sulaim,

Lafiya alhamdulillah ashe mutanan Kano tadabo ne a masarautar tamu to muna maraba dakai,

Hira suka taɓa sama sama rabin hirar madai gwaggo murja ce da mijin nata sai kuma Yarima sultan shima dai jefi jefi,

Akwai girmamawa tsakanin baba waziri da Yarima Sultan bashida raini sam bashida kuma girman kan shedai akwa izzah wanda dama ba araba jinin sarauta da wannan,

Saɓanin sauran ƴan uwan sa wanda suke uba ɗaya basa ganin kowa da gashi sun raina kowa mahaifin su ne kaɗai abun girmamawa wato *SARKI YUSUF SHAREEF*

ganin dare yafara yine gashi Sultan yasan Sulaim bazai yadda su koma Part ɗin sa a mota ba to gara su tashi su tafi tun yanzu koya samu ya huta,

To bari mu wuce gwaggo munbar ku lafiya

Sulaim wanda duk ya gama gajiya dama jiya ke kamar akan Ƙaya yake yariga Sultan din tashi tsaye da haka suka yi sallama da baba waziri suka nufi ƙofa,

gwaggo murja tace Allah ya shirye ka dunkum kawai kuma wlh ka shirya dole mu aurar dakai a shekarar nan ko kana so ko baka so mutum har yazama riƙaƙƙyan tuzuru amma babu aure Allah ya kyauta,

Sulaim wanda duk yaji abunda tace ransa ne ya ƙara ɓaci amma baiko juyaba bare tasa ran zai bata amsa,

Shidai Yarima Sultan aransa yace wai dai gwaggo bata so nayi hira da aminina cikin daɗin rai,

A parlourn farko suka zazzauna kafin su je su kwanta alkyabbar Sultan ya cire sannan ya zauna cikin siririyar murya yace wash Allah _Am tired_

Kallon shi sulaim yayi shima ya gajin yasakar masa murmushi,
Sannan yace kaifa duk ka lala ce da raganta yanzu Meye kayi naga jiya anan?,

Ido Sultan yazaro waje yace yanzu duk wannan tafiyar da muka yi ba aiki bace aini rabon da nayi irin wannan tafiyar tun wancan zuwan naka kafin na tafiya Koria,

Jinjina kai Sulaim yayi alamar lallai ma,

Lafiyayyan juice ne wanda akayi shi da zallan kayan marmari sai ƙamshi yake yi ga sanyi acikin wani Ƙaya taccan jog wanda koshi ka kalla zaka iya ji ka ƙoshi da abunda ke ciki tsabar kyan jog din wata amentacciyar kuyangar UMMUL BAIT ta kawo parlourn Sultan saida akayi mata iso sannan ta samu izinin shiga kai saƙon shima dan Yarima sultan din yaji ance ƴar aikyan daga gurin ummul bait tazo shiyasa yace ace mata tashigo,

Sai da ta ajeye tiran da aka ɗoro jog ɗin lemon a kan table din dake tsakiyar parlourn sannan ta zube ƙasa ta ce Allah yaƙarawa yarima lafiya sarkin gobe da izinin ubangijin sama,

Gimbiya kuma uwar gida tace a gayawa ɗan ta da yazo tana masa bangajiya sannan wannan ita ta haɗa tace a kawo masa yasha cikin salama,

Ƙara russuna wa tayi sosai kafin tace tuba nake Ranka ya daɗe ɗan zaki magaji kake kafi gwani,

Zaki iya tafiya cewar yarima Sultan,

Tashi tayi da sauri tare da furta na barku lafiya,

Bayan tafita Yarima ya kalli Sulaim wanda yaɗan kishingi ɗa kaɗan saman kujera,

Yace to ga saƙonan daga UMMUL BAIT nakane kai kaɗai asha daɗi lafiya,

Sosai Sulaim yayi murmushi sannan yace godiya mara iyaka zuwa ga uwata ya futa hakan tare da tashi yaje inda aka ajeye juice din ya ɗauki cup guda ɗaya ya zuba sannan ya koma inda ya tashi ya zauna,

Baƙaramin daɗin juice din yaji ba ga ƙamshin kayan marmarin sai tashi yake ga sanyi mai ratsa zuciya,

Kallon inda sultan yake yayi yace masa ba kaji daɗi ba kamar kada nabar sha gaskiya banji daɗi ba da babu kai acikin nikadai zan shanye,

Dariya Yarima sultan yayi tare da cewa ba komai kasha kai kaɗai Tunda kai akeso,
Kafin sulaim yace komai sultan din yaɗora da cewa,

Yauwa na gaya maka akwai taro gobe insha Allah za a kawo kayan hawa hadda naka nasa a kawo pls aminina kada kace baza kasa kaba, dayau za ayi taron hawan sai nace Abarshi zuwa gobe saboda kai,

Sulaim wanda yake sauraran Sultan babu abunda ya ce masa kawai ya jisa ne,

*WASHE GARI* 🌅

Wai Meye yake faruwa a masarautar nan ne nake tajin haya niya,

Wata budurwa ce ta tambayi ta kusa da ita itama bazata haura shekarun ɗayar ba,

Lallai ma SIYAMA bakiji sanar warda ake tayi ba tunjiya cewar akwai taron murnar dawowar Yarima Sultan sannan kuma shima kanshi zaiyi Hawa na musamman,

Zunbur wadda aka kira da da suna Siyama ta tashi zaune tare da Faɗin dan Allah da gaske ne ZARAH kinsan dayake jiya ban kwana a nan ba shiyasa banjiba,

Gaskiya Zarah zo kitaya ni duba kayan da zansa order yanzu akawomin fitattatu don bazan yadda wannan GIMBIYAR SHAHEEDAN ta fini kyau ba wlh,

Kinsanta badai iyayi ba kuma nasan kodan YARIMA dole zataje gurin Hawan da zaiyi..!

Share
And
Like fisabilillah 🙏

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp channel

*AHALIN MU DAYA*

💗💗💗

*Nazari writer's association📚✍️*

_Sarauniyar nazari writer's👸_
*(THE QUEEN👑)*

*CREATED AND WRITTEN*
*BY*
*Fatima Y zakariyya*
_😍Oum Ameerah_😍

______Dedicated to aunty salma💎

*Page* 4️⃣3⃣↔️4️⃣4⃣📖

Gaskiya zarah zo kitaya ni duba kayan da zansa order yanzu
Saboda fitattun kaya nakeso dan bazan yadda wannan Gimbiya shaheedan tafini kyau ba wlh,

Kinsan ta badai iyayi ba kuma nasan kodan Yarima dole zataje gurin hawan da zaiyi,

Tana maganar tare da janyo wayar ta ta shiga duba wasu Gowns with veils a media duk wanda ta duba sai tace baiyi mata maba

Laaa zarah matso kiga wata riga tayi kyau gashi veil ɗinta babba ne da sauri wadda akakira da zarah ta matso ta kalli screen din wayar don ganin rigar,

Dariya sosai zarah ta shiga yi kamar wata zautacciya kallon ta siyama tayi tare da fadin Haba zarah kefa baki da kirki Meye kike wa dariya haka,

Saida zarah ta tayi mai isar ta kafin ta ce yanzu ke siyama sai kace biki waye ba yaza ai kice zaki sa MOROCCO 🇲🇦Gown saikace zakije walima gashi veil din ta yayi Miki girma yanda kike hakan nan ba kida tsayi sosai,

Harara siyama tabi zarah dashi tare da fadin kinga naji yanzu Meye shawarar ki,

Yauwa yanzu kikai magana cewar zarah tana gyara zama a saman bed din da suke duk a zaune,

Siyama kinsan yadin karan miski a gidan sarauta baƙaramin tufafi bane mai dara ja ina ganin idan har kikayi shigar sa baƙaramin kyau zakiyi ba yanda kike chocolate colour din nan Idan kikasa kalar haske zakiyi kyau sosai,

Wata kuyanga ce ta yi sallama daga bakin ƙofar bedroom din da suke ciki,

Zarah ce ta amsa tare da fadin za'a iya shigowa

Russuna wa tayi tare da fadin barkan ku da safiya, still Zarah ce ta ƙara amsawa tare da fadin me ke tafi dake?

Uwar da kina Fulanin sarki ita tace a sanar muku tana son ganin ku yanzu a parlourn ta,

To muna tafe yanzu

Tashi sukai ko wacce ta saka doguwar rigar abaya suna yane kansu da viel din rigar suka fice,

Zama Zarah da Siyama sukai a kusa da ita tare da fadin ranki ya daɗi mun amsa kira gamu,

Kallon su Fulani tayi tana zaune ta ɗora ƙafa ɗaya bisa ɗaya jikin ta sanye da atamfa ɗinki doguwar riga tasha aiki da stone tundaga sama har ƙasa sai alkyabba asama,

Magana tafara yi musu cikin isa da ƙasaita kalma bayan kalma haka ta shiga yi musu magana, kunsan da taro a masarautar nan amma shine kuke kwance a ɗaki har wannan lokacin kuke nan baza ku shirya komai ba ke Siyama har kiran wayar kinayi bata shiga saboda inaso kuzo ku zabi kayan da zakusa,

Saboda akwai manya manyan baki da ƴaƴan sarakuna wanda duk zasu halarci wannan taron ina so sosai Siyama kija hankalin Sultan a gurin akwai kyau tuttukan dana ta nada wanda zaki bashi yayin gabatar da kyauta,

Murmushi sosai Siyama tayi tare da fadin muna godiya ummu Allah ya ƙara lafiya Allah yasa YARIMA SAFWAN shine magajin masarautar nan,

Wani irin daɗi mara misaltuwa Fulani tajiba saboda wannan shine babban burin ta arayuwa naganin babban dan ta wato SAFWAN yazama magajin baban sa sarki Yusuf shareef,

Sai da ta lumshe ido kafin ta amsa da ameen,

Sannan ta ɗan kai dubanta kan Zarah wadda take jira taji ita wane tanadi akayi mata,

Amma ga mamaki zarah taji Fulani tace kuntashi kuje za a kawo muku komai,

Babu musu suka tashi tare da fadin ki huta lafiya,

*FULANIN SARKI WADDA SUKE KIRA DA UMMU SAFWAN*
Ita ce matar sarki ta biyu kuma amarya tana da ƴaƴa guda ɗaya ta rasu dama ita kadai ce mace kuma ta fari sai maza biyu da suka rage Safwan, sai dan uwansa Al'amin suna kiranshi da AMIN,
Siyama da zarah ƴaƴan yayyin tane ta ɗakko su ruƙo, bata da wani bure da yawuce Ganin bayan YARIMA SULTAN Saboda an tabbatar mata idan har yana raye to ɗan ta YARIMA SAFWAN bazai taba gadon sarautar mahaifin saba,
Shine dalilin da yasa take ta neman hanyar da zata gabayan Sultan din ta rasa anbata tabbacin baza a iya kashe shiba saidai ta dalilin matar sa, Sai takeso ta hada Siyama ƴar yayar ta da taɗakko ruƙo da yarima Sultan don cikar mafarkin ta,

Cikin kyakkyawar shiga ta shadda light blue suka fito cikin shirin zuwa fada dan gaisa wa da mai martaba,

Yarima sultan ya dai dai ta zaman Jabbar dake jikinshi fara mai adon ruwan zaiba sai walwali yake a saman kayan nashi kamar jiya sunyi kyau sosai fadawa ne sunkai takwas abayan su domin rakiya zuwa fada,
Chapter 28 · 0% Book details