Sashe 36
Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
🦋 Princess ce ki tafiya sannu a hankali cikin sanɗa a wani Ƙaya taccan (garden) mai girma ya haɗu iya haɗuwa ga wasu kyawawan shuke shuke a gurin sai wani irin ƙamshi yake mai daɗin gaske ga wasu haɗaɗɗun runfuna da suke ciki guda uku ko wace runfa da akwai kujeru biyu acikin ta da ɗan ƙaramin table a tsakiyar su, ga yanayin garin hazo akeyi cikin jin daɗin weather ɗin taɗan yi tsalle tare da faɗin masha Allah can kuma tafara murmushi saboda ta hango wani ɗan ƙaramin ruwa yana ta gudana fari tasss kana iya ganin komai dake cikin sa, cikin ranta tace nasamu ruwan da za rinƙa yin wanka aciki har mubar masarautar nan da sauri ta ƙara sauri zuwa bakin ɗan ƙaramin ruwan mai ƙayatar wa batare da wani tunani ko bata lokaci ba Princess ta zuge zif ɗin doguwar a bayar dake jikin ta zif ne wanda tun daga sama har ƙasa ta gaba, ta rage daga ita sai dogon wando baƙi wanda ya kama jikin ta sosai sai black T-shirt Mai ɗan ƙaramin hannu wadda itama da kaɗan ta rufe mata cibiya idan tayi kwakkwarar motsima za a iya ganin cibiyar tata, viel ɗin rigar wanda ta ɗan yafa shi akanta shima tacire shi tare da warware yalwataccan gashin kanta baƙi wilik wanda har gadon bayan ta sai ƙalli yake da wani irin ƙamshi naman gashi saboda yana samon gyara koda yashe saida tagama kintsawa sannan ta riƙe ƙugu tana kallon ruwan sai kuma ta tsugunna takai hannu tataɓa taji ko da sanyi, gama makin ta sai taji ruwan ɗumi kamar wanda aka tafasa aka suka da nasanyi duk sanyi da ake a garin amma kuma ruwan dake buɗe a sararin subahana, ace bai ɗau sanyi ba, lokaci ɗaya kuma ta kawar da tunanin da tatuna ai suma na Estate ɗin su haka yake akwai Heater aciki idan sanyi yayi sanyi tana kunna kanta, Kamar Wadda aka cilla cikin ruwan haka Princess Salma tafaɗa ruwan cike da nishaɗi da jin daɗi take wasa da ruwan wanda yayi mata daɗi sosai sai ta nitsa kanta aciki ta fito dashi, gaba ɗaya gashin kanta ya jiƙe sharkaf da ruwa ya kwanta saman fuskar ta da bayan ta, tanusta sosai cikin duniyar farin ciki, can tajiyo wayar na ruri alamar ana kiran ta wadda ta ajiye ta saman wani dutse dake kusa da ruwan, jin mai kiran yaƙi ba saura rawa ne yasa tafara yunƙurin fito wa daga cikin ruwan amma ina takasa tayi tayi tafito amma takasa take tafara kuka tana ɗaga hannu alamar a temaka mata duk da tasan babu kowa a gurin tana ta yunƙuri tare da ihu iya ƙarfin ta, Babu tsammani princess taji an kamo hannun ta tare da ɗagota daga cikin ruwan cak ta runtse idanuwan ta jin anyi sama da ita kwantar da ita yayi saman faffaɗan ƙirjin sa tamkar wanda. Ya ɗauki ƴar tsana haka ya juya batare da ya ɗauki komai na princess salma ba, sai da sukai nisa sannan ta gane cewar anfito da ita daga ruwan saboda tsabar ruɗani data shiga, ahankali tafara ɗagowa jin alamun tafiya ake da ita kuma sannan kamar a hannun mutum take, idanuwan tane suka sauka cikin kyawawan nashi idanuwan, ƙara zaro ido waje tayi tare da son gano wannan waye haka saboda yasa marks ya rufe fuskar shi dashi iya idanuwan sa kawai ake iya gani sai kuma lallausan sajansa, wata irin isaka aka buso ga hazo da matsanancin sanyi babu shiri Salma ta ƙara shige wa jikin Sa tare daƙara tura kanta cikin ƙirjin sa sabon wani irin gigitaccan sanyi da taji ya kwashe ta ga jikin ta a jiƙe yake sharkaf da ruwa babu shiri tafara rawar sanyi bakinta har ƙara yake haƙoran ta na sama na dukan na ƙasa, Cikin sassarfa ya ƙarasa shiga ɓangaran nasa dayake ta ƙofar baya ne babu wanda yahaɗu dashi, kai tsaye ya nufi bedroom ɗin sa da ita saɓe a hannun sa, kwantar da ita yayi saman tangame man bed ɗinsa Wanda aka shinfiɗa masa lallausan bedsheet white colour Komai na bedroom ɗin white colour NE hakan yabawa ɗakin yin wani irin haske mai kyau, gado ne irin na sarakai mai rumfa asaman shi gefe da gefan bed ɗin bedside lights ne sai Kuma wani hayaƙin turaren wuta dayake tashi shi kin wani irin salo mai jan hankali ga dadda ɗan ƙamshi, Bayan ya kwantar da ita yaja lallausan blanket mai kyaurin gaske ya lulluɓeta dashi ganin har lokacin rawar sanyi take hakan yasa shi kunna masuburbuɗar zafi wato (room heater) kallon a gogon dake maƙale a bangon ɗakin yayi ganin 3:25pm hakan yasa shi faɗa wa toilet daniyar yin wanka, Tashi princess tai saboda jin ɗumi take tako ina gashi dai kayan jikin ta a jiƙe suke amma ta rage jin sanyi sosai, kallon ɗakin tashigayi ganin komai fari hakan ya burge ta tare da ƙayatar da zuciyar ta, ganin ta tayi a tsakiyar makekyan gadon wanda zai ɗauki irin ta 20 kowa kuma a wadace ƙafar ta tazuro a hankali ta sakko, mamaki ta farayi to shin wannan waye ya ɗakko ta daga cikin ruwan, aranta kuma tana tunanin tabbas tasan wannan ƙamshin turaran wanda ya ɗakko ta wanda gaba ɗaya itama ya kama mata jiki, tana cikin wannan tunanin ne tafara jin motsin mutum abayan ta, cak ta tsaya amma takasa juyawa saboda tsabar tsananin tsoro, jin shiru ne yasa ta juyawa cikin a hankali, "Laaa laaa laaa Yarima Sultan sai kuma tayi saurin dafe bakin ta ganin ya kafeta da manyan idanuwan sa take tafara tarayu abunda ya faru acikin ranta tace kaddai ace Yarima ne ya ɗakko ni daga ruwa to idan bashiba waye?, Raɓata yayi yawuce wanda fitowar sa kenan daga wanka ya zura jallabiya kafin yashirya zuwa wajan taro saboda yaga lokaci ya kusa, guri yasamu saman wata kujera wadda ke a ɗakin itama fara ce tass tamkar ba a taɓa zama a kanta ba, Ganin bashi da niyar yi mata magana hakan yasa ta Faɗin yaya yarima barka da yamma, kallon ƙasan ido yarima sultan yayi mata wanda ita bata ma kula da hakan ba, saida ya mula ya sha iska kafin yace" Meye yakawo ki ɓangaran nan sannan ya akayi kika iya shigowa" a jere yayi mata tambayoyin, Ranka ya daɗe niba bansan yadda akayi nazo nan ɗin ba nidai kawai nasan munje sashen Ummul bait nida su ummeetha shine na fito na barsu acan saboda nafiso inzagaya cikin masarautar, bansan ta yadda nazo nan ɗin ba fakar idon fadawan dake ƙofar shigo wa nayi sannan nasamu na shigo saboda naga babu yawan jama'a a gurin yanzu gashi bazan iya komawa bama saboda bazan gane hanya ba, Baisan lokacin da ya shagala wajan kallon princess ba wanda take maganar cikin shagwaba tare da turo ɗan ƙaramin bakin ta gaba, jin shiru ne yasa ta ɗago dakai tana kallon sa, suna haɗa ido ya kyauda kansa cike da basarwa tare da ɗaure da ƙara ɗaure fuska sosai, Cikin isa da izza irin tashi yace kin isheni da magana maza kiɓa cemin daga gani yanzun nan, Kamar me jira princess ta nufi ƙofar da sauri batare da ta ƙara cea komai ba, jin ƙofar tayi a rufe ƙara kama handle ɗin tayi daniyar buɗewa still a rufe jiya wa tayi ta kalle shi idanuwan ta cike taf da kwalla tace Yaya yarima ƙofar a rufe take, Baice komai ba tashi yayi ya nufi inda take tsaye saida yaje gab da ita sannan ya tsaya yana kallon ta cikin ido ba shiri tayi ƙasa da nata idon amma tana jin nashi ya mata yawo a jikin ta hawayen idanuwan ta suka fara gangaro wa saman kuma tun ta don ita har ga Allah tsoran shima take yi gani take kamar zai hukunta ta ko yasa a hukunta ta, "ke yanzu ko cewa akayi ki fita ahaka sai kifita biki ga kayan dake jikin ki bane? Tsintar muryar Yarima tayi cikin kunnuwan ta, take ta fara kallon jikin ta don ita tama manta yadda take cike da jin kunya ta ɗanja da baya, shima juyawa yayi ganin lokaci na ƙure masa gashi yana son ganin Aminin sa Sulaim, Kayan da me martaba ya aiko masa dasu yafara dubawa cikin nutsuwa komai rainbow colour ne yanayin Gashin ɗawisu, sai rawani launin baƙi sai takalmi irin nasara kai da kwalliyar zinare ajiki, cikin nutsuwa princess salma ta ƙarasa inda yake duba kayan ta tsaya, tare da Faɗin " ama tsayi na na ƙanwar aminin yarima kuma ƙanwa ga Yarima Sultan sarkin gobe da yaddar Allah ina mai roƙon alfarma akan yarima kada yasa kayan dake hannun sa a yanzu, zai fi da cewa ga adalin shugaba yasan wannan kayan zasufi kyau a gareshi ta furta hakan tare da nuna wasu saitin kayan dake ajiye a gefe wanda dama shima kanshi yariman su yayi niyar sawa, Ganin irin kallon da yarima Sultan yake yimata ne yasa ta saurin cewa tuba nake Ranka shi daɗe Allah ya sanyaya zunciyar Yariman gabas taƙai ƙarshan maganar tare da kama kunnuwan ta duka biyun, har cikin ransa yaji daɗin abunda tayi amma saboda mulki sam babu alamun hakan a kan furkar shi, "dama kawai na faɗi hakanne saboda nasan akwai ƴaƴan sarakuna wanda zasu zo dayawa da ƴaƴan manya kuma dole za asamu wanda yayi shigar ɗawisu saboda shigar sarakai ce, nikuma ina ganin ka fita daban acikin su sai yafi ƙayatar wa, Ƙasa tayi dakan ta cikin sanyin murya tace dan Allah yaya yarima kabuɗe min ƙofa nima zanje nashirya saboda nasan ummeetha ma nane mana yanzu, Batare da yarima yace komai ba ya ɗauki wayar sa ya nufi wata ƙofa dake maƙale a cikin ɗakin, aransa yake mamakin Yarin yar nan irin ƙarfin halin ta gashi bata shakkar yi masa magana, take yafara jin haushin kansa taya akai ma ya kawo ta bedroom ɗin sa dayake ta tabbacin babu wata mace da ta taɓa taka hanyar da yake idan ba itaba ko a mazan ma mutum ɗaya ne shine Sulaim banda shi babu wanda ya taɓa shiga sai ita gashi har saman bed ɗin sa, cikin jin zafin hakan ya tura ƙofar ɗakin yashiga, amma kuma sai yaji wani ɓangaran na