← Book details Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 37

Sashe 26

Ahalinmu Daya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"kamar iska haka me napep din nan ya gano Suhaima a dai dai gate din shiga estate din"

"aiko kamar mai jira yafara ƙoƙarin tada napep din ya gudu saboda har cikin ransa ya yadda Suhaima ba mutun bace saboda ko shi da yake acikin napep iya saurin da zaiyi kenan shi banga sanda ta fita daga ciki bama bare har ta kai gurin gate din nan"

"kamar wanda akayi masa baki napep din taƙi tashi bawan Allah duk da sanyi ake a gari amma gumine yake tsatstsafo masa gashi babu alamun mutun ko daya a wannan unguwa"

"Suhaima wadda ke tsaye a bakin gate din tana hango gine ginan cikin estate din ta rasa ta wace hanya zata bi ta shiga ciki"

"kwayar idon ta ta canza daga ash ta koma rainbow colours"

Wani irin zafi take ji daga can ƙasan zuciyar ta sai tafasa takeyi ga wani irin kunci da ya lulluɓe ta take wasu siraran hawaye suka biyo kuncin ta komai ya dawo mata sabo"

"Asanadin muta nan cikin gidan nan narasa duk wani farin ciki na babu alkhaeri tattare da su babu Allah acikin zuciyoyin su suɗin azzalumai ne masu cutar da zuƙatan bayin Allah kuka sosai Suhaima tasa tana bubbuga gate din da gaba ɗaya ƙarfin ta ita kadai take maganganun ta"

"wlh sai na ƙone ku baki daya ko ku bude ko kada ku bude dole zanshigo kuma sai na shafe labarin kowa acikin ku a lokacin da bakuda wata madafa saina lalata rayuwar kowa dake cikin wannan ahalin"

"har wani irin jijjiga Suhaima ma take tsabar kuka da masifa amma babu alamun gate din zai bude sannan babu alamar wani zai zo inda take"

"bayan dukan gate din da take da hannun ta har wani jijjigashi take amma babu alamun zai motsa bare tasa rai da wani abu"

"har gwada shiga tayi ta ƴan dogayen ƙofofin gate din amma ina duk da siran tatta takasa"

"me napep da yake ta ƙoƙarin tada abun hawan sa amma napep din nan taki tashi har fita yayi ya tura amma taƙi"

"Duk abunda Suhaima take yana kallon ta amma bai san abunda take fada ba kuma bai san kuka takeyi ba shidai burinsu sa kawai yabar wannan unguwar cikin salama"

"kamar wadda aka tsikara haka Suhaima ta miƙe daga tsugunnan da take lokaci daya kuma babu hawaye a idon ta"

"Dole zan dawo kujira zuwa na tafaɗa a fili cikin wata da shashshiyar murya mara sauti sosai ƙarshan ku yazo"

"Tana kaiwa nan ta juya kamar ba itace tagama kuka yanzu ba"

"kayi hakuri mu koma naɓata maka lokaci dayawa gashi babu kudi a hannu na yanzu sai munkoma asibitin zai shiga na dakko maka"

"kamar saukar aradu haka me napep din nan yaji maganar a kunnuwan sa yana dagowa yayi tozali da Suhaima tsaye akansa amma kanta a ƙasa yake bata bari sun hada ido ba"

"bata jira cewar saba ta shige cikin napep din sabunta ta zauna"

"wani abu daya ƙara sawa me napep din tsoro da tantama akan yarinyar a wannan karon ya kunna napep din ta tashi cikin ikon Allah"

"yau Allah ya haɗani da ajali na cewar mutumin a acikin zuciyar sa kamar yasa ihu haka yake ji to amma anan ai sunan ihun ka banza"

"saboda babu wanda zai jika bare ma har akawo maka dauki"

"yana tada napep din Suhaima ta hango gate din yana zugewa a hankali da kansa yana bude wata dan ƙare riyar mota tafito daga ciki"

"ba tayi wunkurin komai ba ita kadai tasan abunda ta tsara acikin ranta"

"ya sunan unguwar nan? ta tambaye mai napep din"

*RAILWAY QUARTER'S*. Yabata amsa a gajarce don shi burinsa kawai yaga sun komai ta fita tabar masa abun hawan sa lafiya"

"yauwa nagode bari nashiga na dakko maka kudin naka na wane?"

"kawai ki bayar babu komai"

"To jirani ina zuwa dayake har cikin harabar asibitin a shigar da ita ba tasha wahala wajan yin doguwar tafiya daga bakin gate din asibitin zuwa cikin *RECEPTION* din asibitin ba"

"sai da ya bari ta ta shiga ya daina hango ta sannan taja napep din sa da gudun gaske yafice daga cikin asibitin"

"babu ko sallama haka Suhaima ta tura kaicikin dakin da khaltum ke ciki"

"da sauri khaltum din tace mata tunɗazun nake jiranki muci abinci amma shiru banganki ba wai ina kikaje ne?"

"Sam bata kula da halin da Suhaima take ciki ba"

"kai tsaye Suhaima ta wuce gadon da ta kwanta ta dauki rigar ta wadda ta cire ta shiga laluba al'jihun rigar taciru kuɗi aciki sannan ta ajiye rigar ta nufi ƙofa"

"har ta kai bakin ƙofa khaltum tace amma kinaji inayi miki magana kinyi shiru lafiya kuwa gashi naga sai wani sauri kikeyi"

"ɗan dakata wa Suhaima tayi batare da tajiyo ba tace kitashi ki shirya yanzu zandawo mutafi gida"

"batare da ta jira cewar khaltum din ba ta fice daga room din"

"da kallo khaltum tabi bayan Suhaima ma sai kuma ta ɗan taɓe baki kadan tare da fadin wlh bazan tafi ba sai nagama cinye kayan daɗin da aka kawo mana tayi maganar a fili cikin halin ko in kula"

"dube dube Suhaima ta shiga yi tana neman me napep din amma bata ga alamar ire iren saba a harabar asibitin har bakin gate din ta duba amma babu shi"

"babu yadda ta iya haka ta koma ciki jikin ta duk babu daɗi addu'a tayi Allah ya ƙara haɗa tada shi kodan tabiya shi haƙƙin sa idan kuma aka ɗau lokaci basu haɗu ba sai tayi masa sadaƙa da kudin"

"tana tafe tana tunani abubuwa duk sun cunkushe ma har ta gota ƙofar office din DR. Sulaim sai kuma ta dawo ta tsaya cak tana bin ƙofar da kallo tun daga sama har ƙasa a ɗazun ma bata kula da sunan ma mallaki office din ba sai yanzu"

*DR. SULAIM HAMEED ARAB P. R. C*

"Tagani rubuce saman ƙofar runtse ido tayi tafara tarayo abubuwan da suka wuce kafin wannan lokacin"

"Tunani tafara yi Awa 4 da suka wuce bata san komai game da asibitin nan ba sannan a awanni 4 da suka wuce tunanin ta daidai yake a awanni 4 da suka wuce bata taɓa tunanin zata samu Arab Estate nan kusa ba acikin awanni 4 da suka wuce komai da ya faru after 10 years ya dawo Mata farko kamar yau ya faru kuma duk sune sanadi"

"Ashe akwai dalili mai ƙarfi da yasa wannan mutumin ya temakemu ashe sun dawo ne don su ƙarasa kashe mu"

"To wlh bazan bar hakan yafaruba dole sai na ɗau fansa kuma saina fara tarwatsa rayuwar ahalin nan"

Ita kadai take suru Tanta babu mai taya ta duk tabi ta hargitse a ɗan kan kanin lokaci"

___________________________
_____________________
_______________
*️⃣
"cikin kyakkyawar shiga ta alfarma Sulaim ke tafiya cikin nutsuwa da cikar kamalar sa"

"shadda ce a jikin sa brown colour Mai duhu anyi Mata dinkin *FORNEX* zaran da akayi aikin shima brown colour ne amma Mai haske yayi kyau sosai rigar iya gwaiwar sa itama kanta hular zaran da akayi aikin Brown ne shima mai haske idan ka gani sai kayi tunanin ɗikin hular da aikin dake jikin shaddar duk mutun daya ne yayi su ga wani brown shoe sai kalli yake kyakkyawar ƙafar sa sai taƙara yin kyau aciki wani irin ƙamshine ke tashi a jikin sa wanda mutum idan ya shaƙa bazai so ya dainaji ba kuma duk inda ya zauna sai yabar ƙamshin nasa haɗaɗɗan agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannun sa ya duba 5:11pm"

"sosai ummeetha tayi masa addu'a tare da fatan sauka lafiya ita kaɗai ce a parlon babu kowa duk sun tafi gidan bikin ƴar gidan uncle tahir yayan mommy"

"Hakan yasa sulaim jin dadi sosai babu mai tsaida shi "

"kai tsaye suka nufi Airport dama saida yafara yiwa baffa bankwana shima yayi masa addu'a sosai kafin ya nufi Part din nasu"

🌹🌹🌹

*BARNO STATE*
*MASARAUTAR GABAS*

Masarauta ce mai tsohon tarihi da ƙarfin mulki arziƙi da kuma tsantsar izzah,

" cike da ƙasai ta matashin saurayin ke tafiya cikin aji da nutsuwa mulki ya gama ratsa ko ina nasa ga wasu fadawa guda 4 abayan sa suna take masa baya"

" wani katafaran perlon alfarma ya nufa dai dai ƙofar shiga fadawan nan suka tsaya cak suka ƙame tare da fadin Ranka ya dade a fito lafiya"

"Saboda sun sani babu wanda ke shiga wannan parlon sai wanda yakasan ce najikin Yarima sultan ko kuma shakikin abokin sa wato Sulaim wanda duk ya kwana ya tashi a cikin masarautar gabas asan waye Sulaim a gurin Yarima Sultan"

"cike da izzah ya ƙarasa shiga perlon cike ganin sa yasa Sulaim ɗan tashi daga kishin gedan da yake tamkar shine yariman"

"hannu Yarima Sultan yabode wa aminin nasa ba musu sulaim ya Mike suka rungume juna"

"barka da zuwa daular Sultan ya fada asaitin kunnan sulaim "

"barka dai mutanan Koria"

"fatan ka iso lafiya?" sultan din ya tambayi sulaim"

"lafiya fatan kaima haka"

"Zama suka yi atare kan wata kujerar alfarma tamkar gadon sarauta haka kujerar take"

"cikin muryar sa mai daɗin sauraro yafara magana"

"nayi kewar ka sosai amini na cewar yarima sultan yana kallon sulaim"

"abunda bantaba ganiba shi sulaim yayi wato murmushi shima bawai can ba"

"kafin yace ba kayi kewa taba da kayi ke wata da ka dawo Nigeria ko sau daya baka ziyar ce niba amma ni zuwa na Koria uku 3 ganin ka"

"ayya yanzu dai ba lokacin ƙorafi bane kasamu ka huta sosai kaci abinci sai muje kai gaida *UMMUL BAIT* na nufin uwar gida wato mahaifiyar Yarima sultan itace suke kira da UMMUL BAIT.!!!

*SHARE AND LIKE FISABILILLAH*

*AHALIN MU DAYA*

💗💗💗

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp channel

*CREATED AND WRITTEN*
*BY*
*Fatima Y zakariyya*
_😍Oum Ameerah_😍

______Dedicated to aunty salma💎

*Page* 4️⃣1️⃣↔️4️⃣2️⃣📖

"Ayya yanzu dai ba lokacin ƙorafi bane kasamu ka huta sosai kaci abinci sai muje sai muje ka gaida *UMMUL BAIT*

" Ɗan ɗaga kai Sulaim yayi batare da yayi magana ba"

"miƙewa yarima Sultan yayi tare da Sulaim sukanufi wata hanya acikin parlourn kamar corridor sai gashi yaqara fita wani babban parlourn mai dauke da 4 bedroom sai kuma upstairs,
Chapter 26 · 0% Book details