← Book details Abadan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 103

Sashe 99

Abadan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana baje saman carfet din falon maryam tana hidimar zuba masa abinci don a qasa yake cin abinci abinsa yace yaa samu ladan sunna na irin zaman da ma'aiki yakeyi idan zaici abinci(irin zaman yana taimakawa qwarai wajen hana mutum yin mugun qoshi daya sabawa addini,haka yana hana yin tumbi)bayan sun gama shiryawa sanye yake da gajeran wando shi kadai ne ajikinsa sanyin a.c na ratsashi,ta riga data saba da kallo irin ma abdallah,indai yana kusa to fa dukkan idanunsa na kanta,bata damu ba hasalima jin dadin hakan takeyi don ya sanshi farin sani,ba macen data isa ya tsaya yana kallonta to din me ita din halaliyarsa zata hanashi more kallonta,bayan ya gaya mata ba sau daya ba basau biyu ba kallonta ba qaramin jefashi yake cikin nishadi da sabuwar duniya yake ba

Sai data lakuce masa hanci sannan tace ''mr kallo''
''na amince''ya fada yana murmushi,ta tura masa plate din abincin wanda ta cika da lafiyayyen alkubus da yayi kyau ya taahi yayi shar,da kwanon tangaran mai kyau dauke da miyar taushe wadda tasha tantaqwashi da naman kasuwa da manshanu ita kuma ta jawo wani jug na plastic tare da wani kwanon tangaran da abun zuba sugar ta bude ta fara hada garin kwaki da suger da soyayyar gyada,cak ya tsaya yana dubanta ita kam batasan yana yi ba har wani tsinkewa yawunta yake kamar wadda taga wani abin dadi,sai da ya kira sunanta sannan ta dago kai tana amsawa,ganin yadda fuskarsa tayi kicin kicin ya sanya jikinta yin sanyi,don ko kusa bata qaunar ta zama sanadin bacin ransa

''amma yaya mukayi da ke kwana ukun da suka wuce a jere.....ranar farko kika cemin sha'awarsa kike na barki kika ci kayanki,rana ta biyu kika ce min bakinki ba dadi da kika ci na jiya kinji dadi bana so amma sabida farincikinki na barki,shekaran jiya harda magiyarki da qwallarki na barki kici,jiya kuwa da kika tashi sai kika shaqeshi kika cika cikinki taf da shi kafin ma na dawo,da na dawo saboda tsabar qoshin da kikayi loma daya na abinci kika ci kika fara amai,sanann yauma dai a gain kice min shi zakici?''sai ya girgiza kai
''bazai yiwu ba maryam,sai kace wanda ake ciwon yunwa a gidansa,aiko wani ke neman taimako a guna bazan bashi garin kwaki ba bare iyalina''tuni qwalla ta cika idonta,ga qoshi ga kwanan yunwa,tana son ta kyautatawa abdallah amma wlh idan taci abincin ji take kamar numfaahinta zai dauke,ba bata lokaci hawaye suka fara silmiyo mata,idonshi ya runtse don babu abinda yaqi jinin gani irin hawayenta
''ya salamullahi,daga magana sai kuka?''
''Kinga matsonan muci abincin ko yaya ne,idan muka gama sai ki gayan meye damuwarki,idan ma duka nau'ikan abincin ne baki so ki lissafa irin wadanda kike so kona wacce qasa ne in sha Allahu ni abdallah mai nemo miki ne kinji dear,amma wanann hawayen qona min zuciya yake''ya fada yana daga mata hannu alamum ta taho,ba musu ta matso jikinsa tana goge hawayen kanta a qasa,cike da son ta faranta ransa tasa cokali ta fara ci,loma biyu kadai tayi taji wani abu ya dunqule mata sai amai tun tana yinsa tana fidda abincin da taci,da garin kwakin da tasha dazun har ya koma bata iya harar da komai,gaba daya hankalinshi a tashe yake gani yake shine sila da ya takura ta,haka ya dauketa cak yagyarata ya gyara gurin,bai samu nutsuwa ba sai da yaga bacci yayi awon gaba da ita,duk son da yakewa alkubus din da qyar ya iya cin yanka uku

🍃🍂🍃🍂🍃🍂

cikin baccinsa ya dinga jin qamshin girki,da sauri ya farka ya mutstsuka ido,ya duba gefansa bata nan,kenan ita ke aikin girki a kitchen qarfe tara na safe?,da azama ya diro daga gadon ya doshi kitchen din

tsayawa kawai yayi yana kallonta tamkar ba ita ta gama sheqa amai jiya ba?,tayi kwalliayarta tayi kyau kamar ka saceta ka gudu,ta matse cikin wata riga mai roba wadda iya qibarka iya yadda zata kamaka iya kacinta qauri an mata tsaga daga gabanta daga qaurin qasa zuwa gwiwa,ta gyara gashinta yayi kyau sosai,ji tayi kawai an rungumeta ta baya sai ta saki yar qaramar dariya
''kasan kuwa irin tsoron daka bani?''
''nima ai kin bani tsoro baby,ke da baki da lafiya ina ke ina kitchen fisabilillahi''waigowa tayi suna fuskantar fuskarta qunshe da murmushi juna yana zagaye da qugunta,ta shafi sajensa kana tace
''ras nake jina shariky,ina mai tabbatar maka idan za'a saka tsere sai na wuceka''dariya ya saka ya sumbaci kumatunta
''babu musu don naga alama,wai baby meye sirrin ne?''ya fada yana kashe mata ido,itama maida masa martani tayi
''name fa?''
sai da ya jujjuyata ya sake kallonta sannan yace''gani nayi sai wani kyau kike qarawa,fatankin nan har tafi tawa laushi,kumatunki kamar kin boye qwai,brown oily eyes dinki kamar an kuma diga musu zaiba da oil,ke tsaho ne kawai har yau na fiki ba.....''kasa qarasa maganar yayi saboda manna bakinta da tayi cikin nashi,sai da ta dan birkitashi sanann ta cire tana duban bakin nasa
''wannan bakin nawa kada ya cinyeni''sake janta,jikinsa yayi yana dariya
''Allah am seriouse,meye sirrin''
''matso na gaya maka''sai tayi dage don duk tsahonta abdallan ya fita ta kai bakinta kunnensa ta shiga jero masa
lumshe ido ya dinga yi yana saurarenta tare da sake shigewa jikinta,banji komai ba face kalmarta ta qarshe
''kaga kuwa kaine sirrin''dukkansu murmushi suka saki mai,hade da dariya dariya,ya kamo fuskarta ya hada goshinsa da nata shima yana mayar mata da martanin kalmomin,sun kusa kwashe a qalla minti goma a haka har ruwan shayin da ta dora ya fara qonewa sannan ta ankara ta zame jikinta da sauri tana cewa
''you see,shi yasa idan ina abu mai muhimmanci banso kazo ka riskeni,don sawa kake ina mantawa da kowa da komai ciki harda kaina''shi ya qarasa hada kayan karin tana tayashi da wasu abubuwan kana suka,yi wanka suka shirya don yaune ranar da abdallahn ke raba tallafi gidan gajiyayyu da asibitoci wanann karon kuma tare zasu shi da mami,maryam ma ta kafe itama sai taje don baza'a samu ladan babu ita ba

*********

tafe suke cikin motar gwanin sha 'awa don baka banbance waye danta,tsakanin abdallah da maryam,shike jan motar maryam na gefansa,yayin da motar security dinsa biyu ke gabansu biyu ke bayansu,yawanci indai tare da maryam ne cikin fitarsa bai yarda driver yayi tuqi wai don kada a gane masa ita,mami na baya tana duba wasu takardu jefi jefi suna hira da abdallah

''yauwa mami''
''uhmmm''taje dashi kanta na kan takardunta ,tasan tunda ya fadi haka tambaya gareshi
''dama wani lokaci mata na daina cin abinci sai wani abun daban?''bata bawa tambayar tasa muhimmanci ba,don a zatonta shirmene kawai irin na abdallah din haka tace da shi
''kamar yaya kenan?''
''mami maryam,na rasa meke damunta,safe rana dare garin kwaki mai tsamin nan,abinci saidai ta dafa min kawai ni nayita narka,jiya da na matsa mata sai taci amai tayi mami,ni tausayinta ma nake ji''
wannan karom saida ta dago ta dubeta,kunya kamar tayi me ta kama hannun abdallahn a sace ta matse cikin nata
''wayyo hannu na diyana''ya fada yana yamutsa fuska kamar qaramin yaro,da sauri ta sako hannun nasa taja hijabinta ta lullube fuskarta
''kada ka sake matsa mata kan cin abinda bataso,ka barta''cikin damuwa yace
''amma mami gari fa?,bazai mata komai ba?''
''eh yana yi ne zata daina nan kusa''ta fada zuciyarta tamkar qanqara,addu'a take cikin ranta Allah yasa hasashenta ne zai tabbata

Ya sake rausayar da kai
''amma mami ni gani nake kamar yana tsotse jinin mutum ko ruwa jikinsa''
''ba daya,nace maka zata daina ne fa''
''to Allah yasa''ya fada cike da hope,donshi har ga Allah abun na damunsa,gani yake wata cutar ce ta samu maryam dinsa,shi yasa ya sanar da mamin nufinsa idan ya gaya mata akwai wani maganin ta bata,kasa cewa komai maryam tayi,lallai ta yarda Abdallah gabuntar dan fari da tabarar auta na tabashi sosai,a hankali mamin tace
''ki kula kawai da kanki maryam,duk lokacin da kika ji wani sauyi a tattare da ke kumin magana,kada kuce zakuji kunyata,ni mamarku ce baku da kamata''kanta aqasa ta amsa da to,shi kuwa gogan cewa yayi
''ni dama maganin kawai kika rubuta mata mami Allah na tsani naga tana shan garin kwakin nan''murmushi ta dan saki
''bakasan komai nada qa'ida ba,ba'a rubutawa mutum magani kai tsaye,indai kawai kuka ga alamun canjin wani abu ko matsala to ku sanar da ni''
''to mami''ya amsa mata yana ci gaba datuqinshi

a gurin ajjiye ababen hawa suka yi oarking duka motocin nasu,mami ta riga fita saboda isowar shugaban asibitin din ya tarbeta,abdallah na qoqarin fita maryam tayi saurin riqoshi da qarfi har sai da ya dawo ya zauna don bai zata ba,ido ya kashe mata guda daya yana fadin
''ya akayi baby da magana ne?''kicin kicin tayi
''yanzu shariky don kawai ina cin garin kwaki sai ka gayama mami don Allah?''ido ya dan zaro
''to menene don mace kina shan gari dear na?,na tsammaci ciwo ne shi yasa na gaya mata ko zata rubuta miki magani''
''kada ka sake don wallahi ka bani kunya''kiss ya bata a goshi kana yace
''is ok,afuwan my sister''dariya ma ya bata tana zaune ya zagayo ya bude mata side dinta ta fito bayan ya sake gyara mata zaman hijabinta,duk yama tasa gun tsayawa don gaba daya atsarge yake,gani yake wai kallonta ake,security din ma da suka saba binsa a baya yace suyi gaba su zasu biyo bayan nasu,don kada wai su dinga kallonsu ta baya
Chapter 99 · 0% Book details