← Book details Abadan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 103

Sashe 51

Abadan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

hisham baisan halin da ake ciki ba,bai an kara ba sai da yake duba kamfanin yin flower na abdallahn ya tadda adnan dare dare kan kujerarshi kamar wanda ya gada daga gurin ubanshi,da ya sami mamin ya mata maanar ranar ya ga bala'in da bai taba gani ba gurinta,har da ja mishi kunnen matiqar bai dauke idonhi daga lamuransu ba zata sa ahanaahi shigowa gidan kamar yadda tasa aka hana duk wani dan uwanta ko na maryam zuwa gidan,tilas ya ka bakinshi on ya san daina zuwanshi gidan ba qaramin tagayyra zai haifarwa abdallah da maryam ba,ya dai cika da mamakin canzawar mamin lokaci guda,tsana nin biyayya da bi sau da qafa da takewa nene

🎄🌲🎄🌲🎄

Sau biyu tana leqowa taga ko bacci ya daukeshi?wanka take son tayi ta sauya kayan bacci ta kwanta,a karo na uku ta tadda idanunshi ruf alamun ya samu bacci kenan,ta jima tsaye akansa tana qare masa kallo,a hankali ta sanya hannunta cikin tattausan sumarshi,yana buqatar a rage masa ita saidai bazai iya magana ba,cikin ranta ta qudirci gayawa hisham gobe ko zai iya masa yana da clipper tunda ita bata iya ba,jin ya motsa ya sanyata saurin janye hannunta tsoronta kada ya farka,sai da taga ya bar motsin kana ta tofa masa fatiha da yatul kursiyyun da take yawan tofa mishi akai akai ta juya ta isa bakin cupboard dinsu ta soma cire doguwan rigan jikinta

a hankali ya bude idanunshi ya zuba mata ido duka batasan me akeyi ba,ta janyo towel ta daura tayi banaki,ya lumshe idona wani dan murmushi ya subuce masa,maryam maryam bai san maryam ba sai yanzun,yanzun ne yasan maryam,cikin tunaninshi yaji tana qoqarin itowa ya maza ya maida idanunshi ya lumshe,yana iua hagota tana shiryawa tsigar jikinhi na tashi,ji yake ina ma yana da lafiyar da zai nuna mata irin soyayyarta dake danqare ciki zuciyarshi,har ta kammala ta zura rigar baccinta ta dora dan hijabinta a kai

Bata taba yarda ta kwanta kan gadon matuqar idonshi biyu,sai bacci ya daukeshi take lallabowa ta kwanta ga tsammaninta duk bai sani ba,saidai data kwanta din ko cikin bacci yake zai farka saboda wani dumi na musamman yake ji daga garta,yau din ma lallabowa tayi ta kwanta gefanshi bayan ta gama qare masa kllo kamar yadda ta saba,a hankali gajiya ta mamayeta,bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,a irin wannan lokacinne shima yake samun damar qare mata nashi kallon,yakan tsinci kansh ciki wani irin nishadi a lokacin
ya daga hannunshi da niyyar janyota cikin jikinshi ya kusa sau goma amma ya kasa,ya saki nannuyan ajiuyar zuciya yanajin radadin hakan cikin ranshi.

cikin sa'a tayi wani juyi tashin farko sai gata cikin jikinshi,murmushi yayi yana godewa Allah tare da dora kanshi saman kanta,duk da hijabin jikinta hakan bai hanashi jin dumi da qamshinta ba
sannu a hankali sai kuma ya dinga jin motsi kamar ana hawowa saman da suke,yaci gaba da kallon bakin qofar don ya tabbatar yau maryam tayi mantuwa bata rufe qofofin ba,idanunshi fes kan qofar yaji an turo an shigo,tashin farko aka dallare dakin da fitila mai tsananin haske kai tsaye hasken ya iso har inda suke
''wal masakinu bakayi bacci ba?''yaji an fada kana aka kunna duka qwayayen dakin,fuskar adnan ta bayyana
''gwara ma da bakayi baccin ba ai kaga ka gani da idonka tunda gani ya kori ji ko?,yau zan cika burina,zan kwanta da matarka agabanka,zan cusa maka baqinciki abdallah irin wanda na dade ina sha akanka,ka fini kyau,ka fini matsayi ka fini kudi ka fini nasaba hakanqn ka fini farinjini,yau zan kuma nakastaka kafin lokain da muka diba maka na mutuwarka ya cika,kabi bayan tsohonka ku hade acan kafin tsohuwarka ta biyoku''

gadan gadan ya hauro gadon yasa hannunshi ya janyo maryam dake jikinshi wanda hakan ya sanyata farkawa afirgice,ba qaramin kaduwa tayi da ganinshi cikin dakinsu ba cikin takiyar dare,bata ankara ba ya sabule hijabnta ya wurgar take gashinta mai tsaho da santsi ya warwatsu,runtse idonshi abdalah yayi yana jin tamkar an ciro zuciyarsa ana tststsagata,kamar an karata kusa da tukuba turiri kawai take maa,ya bude idonshi yaga yadda ake dambe tsakanin adnan da maryam,gashi kwance bashi da ikon tsinana komai,qoqari yake na daga hannunshi saidai hakan ya faskar,ihi yakeso ya kurama na baqinciki da takaici amma ko bakin ya kasa motsawa,sai ya koma kiran sunayn Allah ciin zuciyarshi tare da yunqurin motsa hannun nashi

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
🌺 *ABADAN*🌺
💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖🌺💖🌺
💖🌺💖
🌺💖
💖

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖
🌺💖🌺💖
🌺💖🌺
💖🌺
💖
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*_home of expert and perfect writers_*

▶4⃣2⃣

*assalamu alaikum warahmatullah,zuwa ga masoyan ABADAN,kamar yadda aka saba 😄 duk lokacin da littafi ke tafiya readers kanyi qorafi kan wani abu da ya shafi jaruman cikin littafin,wannan karon ma hakan ta faru,abinda nakeso ku sani shine bangaren rayuwar maryama true life story ne banbanci shine ita wadda abun ya faru a kanta kishiyar uwa ce ta mata hakan ba kishiyar suruka ba,hakanan na samu saqo daga gurin daya daga cikin makaranta ita kuma bangaren abdallah ne ta sani a gaske ya faru da wani da ta sani,kada ku manta babu yadda Allah baya iya jarrabtar bayinsa,gwargwadon imaninka da Allah gwargwadon girman jarrabawarka,na yarda da addu'a fiye da zaton mai zato☝🏽don ta yimin rana ta bani kariyar da har a nade duniya babu wani abu daya isa yamin kwatankwacin abinda ta yimin,na gani a zahiri na gani a mafarki,a rayuwa babu dole a lokacin da ka roqa Allah ya baka a take,yana iya jinkirta maka gwargwadon yadda yaso,kuyi haquri kuci gaba da bin littafin a duk yadda yazo muku don mu samu cimma manufofi da alfanu da gaci da nake son kaiku,idan kuma abun na damunka 😂,a shawarce ka tara littafin har sai an wuce inda baka son ji sai ka ci gaba da karatunka hankali kwance,na gode matuqa da gaske don nasan duka qauna ce,nima ina qaunarku a duk inda kuke,MRS MUHAMMAD DINKU CE*👑

Ji yake tamkar ya kashe adnan,bai kuma jin ciwon lalurar data sameshi ba irin yau,saboda ya riga da yayi amanna dukkan wani abu da zaya samu bawa da sanin ubangijinsa,hakanan bazai jarrabceka ba tare da wata manufa da take alkhairi ce a tattare da kai
bai gaza ba ci gaba yayi da ambaton sunan Allah cike da neman agaji don yana jin cikin zuciya da gangar jikinsa matuqar wani abu ya faru da maryam mutuwa zaiyi

a gigice ta sake dawowa jikin abdallan ta maqale shi tana neman agaji ta cukuikuye jikinta ta dunqule guri guda,tsabar gigita ta mance da halin da abdallan yake ciki,cikin dariyar mugunta ya biyota,ya tsaua a gabansu dukkansu ya qare musu kallo kana yace
''kin daga hannu kin mare ni ga zatonki kin ci bulus?,bakisan dama na jima ina sha'awarki ba hanyar kawar da ita kawai nake nema?,sai gashi yau Allah ya ara min dama ta yaya zan yi sake ta kufcemin''
ya kalli abdallah da idanunshi suka kada suka koma jazur,dukkan wata jijiya ta kanshi ta gama fitowa rada rada
''hmmm,sarkin zuciya,ka qaraci quncin zuciyarka amma babu abinda zaka iya yau sai na cika buri na''ya sake yin kanta gadan gadan,ya miqa hannu da niyyar damqota
cikin qaraji da kuka mai quna tace
''kaji tsoron Allah,yana kallonka,yana kallin duka abinda kake aikatawa''

ga tarin mamakinta sai taga ya qyalqyale da dariya
''ki bari idan na kammala sai ki gaya min duk abinda kike son gayamin,amma a yanzu babu abinda nake ganewa kinji ko''
ya sake yunqura zai fincikota yayib da take sake lacewa jikin abdallah kamar zata koma cikinsa
cikin hikima ta ubangiji hannun sa bai qarasa kanta ba yaji saukar wani abu mai azaba a qeyarshi,ga mamakinsa ya juya don yaga wanda ya masa wannan aika aika,abdallah ne yana daga kwance yaji tamkar an kakkatse duk wani abu daya hana hannayenshi biyun motsi,cikin hikimar Allah ya bashi sa'ar janyo plate din tangaran da maryam ta zuba abinci dazu Allah ya sa mata mantuwa bata dauke shi ba,don bata barin kwano ko daya ba'a muhallinsa ba ko ba'a wanke ba

sai kuma ya juyo yayo kan abdallah,saidai ina tuni jini ya fara dibarsa ya sona tangal tangal,ganin gaka ya sa maryan saurin maida hijabinta,qofa taje ta bude ta dakin kana ta dawo ta dinga tura adnan da ragowar qarfinta tana hankadashi yana dawowa amma da yake jini yaci qarfin sa sai ta samu nasarar tunkudashi har qasan benan yana qoqarin biyota ta dawo benan a guje ta datse qofar falon kana ta shige bedroom din ma ta saka muqulli tana maida numfashi

babu abinda qirjinta yake sai dagawa sama da qasa kamar numfashinta zai dauke,har yazu tsoron bai saketa ba,ji take kamar adnan din zai dawo,hannu ta ga abdallah na dago mata da alamun ta taho,mafaka take nema ibda zata sanya kanta taji sanyi,inda zata sanya fuskarta tayi kuka,babu musa ta isa gadon cikin sassarfa ta hada jikinsa da nata,cusa kanta tayi cikin qirjinsa wani kuka ya qwace mata

shafa kanta kawai abdallah yake yana hadiyar zuciya,godiya yake ma Allah maras adadi da ya bashi damar tserar da mutuncin iyalinshi,maryam ta riga da ta zama jinin jikinshi,sukan qirjinshi kukanta yake,saidai babu bakin hanawan babu kuma cikakkiyar lafiyar rarrashi,a hankali ta dinga jin nutsuwarta na dawowa,ta dinga sauke ajiyar zuciya kadan kadan
hannun abdallah ta tuna taga yana motsi dazun,a hankali ta zagaya hannunta ta saman cikinsa ta laluba dayan hannun abdallahn,tafin hannunta ta zura cikin nasa ga mamakinta sai taji ya sanya yatsunsa cikin nata ya hade hannayan nasu gam,wata sassanyar ajiyar zuciya ta saki
''alhamdulillahil lazi bini'imatihi tatimmus saalihaat''ta fada cikin zuciyarta tare da rufe idanunta,wani farinciki taji yana ratsata,atleast tasan cewa wani ci gaba ya fara samuwa game da lafiyar abdallahn
dukkaninsu a daren babu wanda ya iya runtsawa,zuciyoyinsu tamkar anyi gobara kada ma abdallah yaji labari,ita kam takan samu sassauci kadan duk yayin data motsa yatsunta dake cikin nasa wanda yaqi sakinsu taji nashi hannun ya motsa

🍂🍃🍂🍃🍂🍃
Chapter 51 · 0% Book details