Sashe 23
Abadan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da ke,duk abinda ya tambayeki kada kiyo nauyin baki ki sanar masa da gaskiya kinji ko?'' ba zata iya musu da mamin ba tilas ta amsa da to sannan ta fito yana jingine jikin motarshi ta isa gareshi,da fara'arsa yake fadin ''barka da isowa,tun dazun nake jira har ma na fidda rai?'' ''uhmmmm''kadai ta iya cewa taja bakinta tayi shiru tana sauraren bayanan hisham,ya rufe da fadin ''ina son inji gaskiyar abunda yake ranki'' tayi shiru kamar ba zata ce komai ba,bata jin ko dis a ranta zata iya hada dangatar aure da duk wani abu da ya shafi abdalla, *MUTUNCI* shi take nemawa kanta, *DARAJARTA* itace mafi muhimmanci fiye da komai a gurinta,har sai da hisham ya sake maimaita tambayarshi ''ya hisham na gode da mutuntawa da karramawar da kamin har ka furta kana sona,saidai ina mai baka haquri tare da addu'ar Allah ya baka wadda ta fini komai da komai,amma bani da ra'ayin soyayya,kayi haquri idan hakan ya bata maka rai'' shiru yayi na wani dan lokaci da alamu baiji dadin,amsar da ya samu daga gareta ba ''babu komai maryam,ita dama harka ta soyayya babu batuntilas,na gode nima da yadda kika mutuntani,amma ina nan ina jira har zuwa lokacin da kika ji jin aminta da soyayya'' murmushin yaqe tayi,ita kadai tasan me take ji cikin zuciyarya,wani irin qunci take mata,kyautar dubu goma hisham din yayi mata,da ta doje tace bazata amsa ba yace shina kam yayi niyya bai fasawa,dolenta ta amsa ta masa godiya sanna ta juya don komawa ciki tuni an kashe qwayayen waiting parlour babu haske sai wanda ke fitowa daga sashen mami da nene,tazo tsakiyar parlour din taji an fincikota baya,razana tayi matuqa,tuni idanunta suka fito wajevta bude bakinta da niyyar qwalla qara saidai bata samu damar hakan ba,sakamakon hadata da bango da kayi aka saka wani lallausan tafin hannu aka danne bakin nata,qamshin daddadan turare ya mamaye hancinta,qirjinta ya shiga dagawa da sauka numfashinta ya soma tsere,minti kusan daya sannan taga haske kadan ya bayyana atsakninsu ,haaken screen ne na waya,fuskarsa ta fara gani abdallah ne,sanye da t.shirt fara sol cotting mai gajeren hannu wadda ta fito da murdadden damtsensa,kauda da qwayar idanunta tayi ta daina kallon fuskarshi sakamakon yadda take babu alamun rahama ko kadan a cikinta murya a kausashe kuma qasa qasa yake fadin ''kin taimaki kanki da baki amsa masa kina sonshi ba,wallahi koda wasa kika amsa kina son wani da ya jibanceni kin shiga uku,baki kai ajin da zaki shiga rayuwar abokan huldata ba,ki qara gaba zaki iya samun wanda ke muradinki acan wata rayuwar ba tamu ba,bana aon cusa kai cikin lamura na da katsa landan tun ba yau ba na gaya miki,ki kiyaye don samun zaman lafiyarki da ci gaba da aikinki cikin gidan nan'' kamar jira ake ya kammala maganarshi haske ya mamaye falon,jdanun zubaida suka sauka kansu yayin da nashi idanu suka sauka kan fuskarta da hawaye ya aoma gangarowa,wani abu ne ya riqe mata maqogaro wanda koda an bata damar maida masa martani ba zata iya ba alokacin,saboda baqincikin da ta hadiya ba kadan bane,tsanarsa da tsanar halayensa uka sake linkuwa cikin zuciyarta ''kai din banza,abokan mu'amalar taka ma din banza,baka isa maryama ta soka ba,saboda daraja mutunci da karamci take bida ba tarin dukiya ko kyau ba''abunda take ta son ta amayar masa kenan saidai abundaya tokare tan ya hanata fada cikin zafi baqinciki da kishi zubaida ta iso gabansu ''abdallah''abunda ta iya ambata kenan cikin karyar da kai hawaye ya soma mata zirya,sam bai damu da ganinta agun ba,duba daya ya mata ya maida idobsa kan maruam ya cire hanunshi yana jan tsaki,ya ja mayafinta ya goge hawayen ta da ya soma taba masa hannu ''indai bakiji abunda na gaya miki ba yanzu kika fara kuka''ya kewayeta da,zafinsa ya fice asashen,ita dinma gyalenta ta ja kawai ta shige sashen nasu,abida ce kawaia falo da tayi zaman kallo tana kuma dakon dawowar abdallah don yace ta zauna ta jira shi batasan gatse ya mata ba lokacin baccinshi yayi,dakinta ta wuce ta danna qofar ta rufe kana ta saki kuka,me tayi masa?,ita tace tana son hisham ne ko kuwa,ahikeban talaka ba komai bane agun wasu masu kudin,talaka bai cika mugum ba,ko talaka baisan ciwon kanshi ba,taqamarshi ta isheta,tana jingidansu zata bar masa shi yafi mata sauqi,ga fargabar yanayin gidansu ga taqama da gadararshi da wanne zata ji? *mrs muhammad ce* [9/17, 12:52 PM] 80k: *ABADAN* *WRITTEN BY* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *_Daga abu hurairah yarda Allah ta qara tabbata a gareshi yace:manzan Allah s.a.w yace:yana daga cikin kyawun musuluncin mutum,ya bar abunda babu ruwansa_* *_a wani hadisin kuma manzan Allah s.a.w yana cewa:jibrilu bai gushe ba yana min wasiyya da maqoci,har sai da nayi tsammanin/zaton maqoci zai iya gadon maqocinshi(saboda girman haqqin dake kan maqoci akan maqocinsa)_* washegari a makare ta tashi saboda rashin baccin kirki,kitchen ta shiga ta shirya musu breakfast,adana kebabi,tavouk koftesi a abincin turkia sairuwan shayi chips da soyayyen qwai,cikin lkkaci qanqani gidan y game da qamshi,bata bar kit hen din ba baba uwani ta shigo ''af,makara kikayi ne yau maryamu''murmushi tayi tace ''wlh kuwa baba uwani'' gaisawa sukayi sannan ta bar mata kitchen din ta koma dakin sha biyu na rana ta fito tayi sarving nasu mami ce da abida,cikin mamaki abida ke cin abincin tana tantamar yinsa akayi ko restaurant aka je aka siyo?,abincin yan turkey a nijeria,kusan ma har yafi nasun dadi sakamakon banancin spices da muke da shi so take ta sanarwa mami qudirinta na barin gidan saidai ta gaza,nauyinta take ji sosai,alkhairan mamin a gurinta na da yawa,da haka har suka kammala cin abincin ba tare da ta ce mata komai ba kafin ta bar gurin mamin le sanar da ita gyaran gida da canza kayayyakin da suke duk shekara idan ya rage saura kwanaki bakwai azumi ''akwai ma'aikatan dake,zuwa,suna aikin nan da jibi zaki gansu,abunda kawai nake so kimin alfarmarshi shine zaku shiga kasuwa kiyo soyayyar kitchen dukkan abunda ya kamata wanda za'a buqaceshi'' ta dan saki murmushi''diuarki ce ni mami kamar yadda kike fadi,ba alfarma bace umarni zaki bani kawai na bi'' ''na gode diyata Allah yayi miki albarka'' wanna halaye na mamin na daya daga cikin abinda ke sata sake jinta cikin zuciyarta koda ta kammala abincin dare,sashen ta sake bari,gurin baba uwani ta kuma wuni,kiran wayarta da mami tayi da daddare shi ya fiddota ziwa,sashen mamin,a hanya suka ci karo da zahariyya na shirin fita cikin motarta,wani kallo ta jefi maryam din da shi wanda ya tilasta maryam neman tsari da ita cikin shirin fita ta samu mamin ''maryam yau kwanan asibiti zanyi bazan dawo ba sai gobe idan Allah ya kaimu,ga gidan nan na barshi hannunki'' ''to mami''ta fada tana amsar jakar hannunta don yima mamin rakiya zuwa motarta daidai lokacin abida ta fito sanye da riga da wando,kunnenta maqale da earpiece ''mami ina zuwa?'' ''af,na mamce kina cikin gidan'' hara rar maryam abida tayi ''mamee kika manta da ni amma wannan ki kasa mantawa,da ita''bata lura da hararar da take ma maryam din ba tayi dariya ''to ai kece din sarkin kwanciya,klum kina kwance a gado kamar ruwa,zan tafi asibiti ne ina kuma tsammanin kwana zanyi'' ''q'nnnn,si kin dawo''ta fadi tana kwanciya saman doguwar kujera yayin da suka fice ita da maryamu mami na shirin shiga motar taga shigowar abdallah gidan,hakan ya sanya ta dakata har ya iso inda suke ta sanar mishi fitarta ta dora da ''am....abdallah,inason in ganka daman'' ''to mami ai gani'' janye jikinta maryam tayi ta koma gefe don basu damar ganawa,daidai duk da hakan tana jiyo abunda mamin ke cewa ''har yanzu banga alamun jituwa tsakaninka da bida ba abdallah me yake faruwa?'' ''mami ba komai kawai dai rawan kanta ne yake bani haushi,azarbabi rashin aji da kamun kai,kuma ma ban samu zama bane kinga soaai,kwana biyin cases sun mana yawa a office,bainciken wadanda suka saci kudin talakawa'' ''duka naji,saidai inaso ka ajjiye dukka wani uzirinka,ka tabbata kun fahimci juna kai da ita,maganar halayenta kuwa kana da damar canza ta tunda tana sonka,ya kamata ace i yanzu ka ajjiye iyali,don nima ina da buqatar ganin qana nan yara suna gilmawa,ina fata ka fahimceni da kyau abdallah?'' ''na fahimta mami,saidai koda jikokin sunzo ta yaya wadan nan patient,naki zasu barki ki sake da family dinki,suna qwace min ke kina kwanan office''ya qarashe maganar cikin sigar zolaya murmushi tayi don ta san dama sai yayi qorafi,haka take fama da shi duk lokacin da zata kwanan asibiti '?idan na biye maka abdallah sai ka makarar da ni''ta dan daga murya kadan ta kira maryama,cikin nutsatstsen takunta ta iso,gidan baya mamin ta shige sannab maryama ta miqa mata jakar tana cewa ''a dawo lafiya mami'' ''Allah yasa maryama,a kula da gida'' ''insha Alahu mami Allah ya bada sa'a'' mamin ta juya ga abdallah dake tsaye yana jinsu,hannayenshi harde saman qirjinshi,har ga Allah yaji dadin yadda ta nuna caring wa mahaifiyarshi ''abdallah sai na dawo,banda tsokane tsokane?''mami ta fada tana dariya ''mami sai kace yaron goye,zaki jawo a raina abdallahnki fa''ya fada yana shigeqa ahima gidan bayan ''a'ah,ya haka?''ta tambayeshi ''zanje na rakaki ne mami'' ''yabzun fa kaima ka dawo daga aiki,na uafe ka shiga ciki ka huta,abida na parlour tana jiranka'' ''idan ina tare da mami mancewa nake da duk wata mace,a naje asibitin naja masu kunne duk wansa ya barki kikayi aiki duka dare baki runtsa ba ni da shi ne,driver muje''haka drivan yaja sauran securitu dinshi suka dafa musu baya maryam ta dawo cikin gida tana jiniina yawan qaunar dake tsakanin mamin da abdallah a inda ta bar abida anan ta taras da ita,bata tanka mata ba,tana gab da shiga dakinta taji tace ''ke zonan,''tayi kamar ba zata kula ta ba don ta tsani irin wannan kiran sai kuma taga baquwar mami ce ko ba komai taci darajarta ''wai me kika dafawa mutane?''kafin ta kai ga bata amsa kuma sai taji tace ''jeki kawai,sai abdallah soulmate ya iso kyazo kiyi serving namu'' ta gama shirin kwanciyarta tsaf ta tuna ta manta da littafin addu'o'inta cikin kitchen,hijabinta ta zura ta fito don ta dauko abdallah ne cikin falon gefanshi abida ce zaune ta sanya ahi a gaba tamkar zasu hade,magana auke qasa,qasa,son bata iya jiyo me suke cewa,tayi kamar ta koma sai kuma ta fasa tayi ahigewarta kitchen,tana qoqarin