← Book details Abadan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 103

Sashe 22

Abadan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻 [9/17, 12:52 PM] 80k: *ABADAN* *WRITTEN BY* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *_daga abu hurairah yardar Allah ta qara tabbata a gareshi yace:manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gareshi yace:ba zaku shiga aljanna ba har sai kunyi imani,ba zakuyi imani ba har sai kunso junanku,shin bana nuna muku abunda idan kuna aikatashi zaku so junanku ba?KU YADA SALLAMA A TSAKANINKU_* cikin kwana ukun mami ta hana gidan sakat da shirye shiryen tarbar abida,ragowar daki biyun dake maqotaka da nata aka bude,kusan komai irin na nata dakin ne sai dan bambancin abunda ba'a rasa ba,ganin yadda mamin ta dauki zuwan abida da muhimmanci ya sanya maryam itama sake shirya kitchen Ranar da zata iso din jirgin da yake sauka sha biyu na rana ne zai sauka da ita,tana jin mami na sanar da abdallah ya,haqura da fitar yau yaje a taro abidan da shi ''kai mami barta kawai,fita ta ta yau mai muhimmanci ce,driver yaje kawai ya daukota,ba dai tana gidan ba almost two to three months fa zatayi tare da mu'' qarfe sha daya maryam ta gama kintsa dining da kalolin abincin nijeria africa da kuma qasar da abidan ta baro wato turkiya,dakinta ta shige tayi wanka,don aikin bai barta tayi wankan ba,riga da zani ta zaba ta shirya cikinsu dukkansu normal dinki ne irin na riga da zani plain na asali,ba qaramin fidda sigarta yayi ba yanayin dakin akwai fidda shape din mu ba irin dinkin mu na yanzu ba mai tattara dake cika mace ya badda shape dinki,bata fito a dakin ba sai da ta jiyo surutu sama sama cikim parlour din mami qarfe daya saura kwata na rana mutum uku ne cikin parlour din harda mami ta hudu,tashin farko zuciyarta ta bada abida cikin su ukun,sanye take da doguwar riga baqa mai azabar kyau da tsada irin mai robar nan dake bin jikin mutum,fara ce qal don har tafi maryam fari duk da dai akwai bambanci,farinta mai dau ne babu sirkin ja aciki ko kadan,zaka iya kiranta gajeriya don bata cika tsawo ba,tana da kyau kam ba laifi don kallon farko zaka kirata kyakkyawa,bata da qiba da yawa saidai jikinta acike yake babu lobawar rama mami ce ta soma ganinta fitowarta ''yauwa maryam kin fito?'' ''eh mami na fito baqin sun qaraso,sannunku da zuwa'' ta fada tana dubansu,daya ce kadai ta amsa sabanin biyun ciki harda abidar wadda ta dago kai ta dubeta,kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace ''nidai kam ba baqiwa bace ina tsammanin kece baquwar'' murmusho maryam din ta danyi ''eh to,kusan haka dinne''ta bata amsa tana kallon fuskarta wanda take bisa screen din tsadaddar wayarta ''maryam kuje da ita ki nuna mata dakinta'' ''to mami''ta fadi tana yin gaba ''wa zai daukar miki trolly din?''abida ta ce tana hakimce a zaune tamkar ba ita za'a nunawa dakin ba bata ce komai ba ta dawo,ta dubi akwatinan da kallo,qwaya biyu ne masu azabar kyau wanda ko ba'a fadi maka ba kasan cewa ba na talaka bane,ta daga dogon sandan dake jikin akwatin wanda zai bata damar janshi akan tayoyinshi ta kwantar da ita ta jata zuwa ciki ta sake dawowa don daukar dayar,saura mami da abidar kawai yanzun cikin falon still abidan na hakimce,nuni ta mata da handbag dinta big mama tace ''shigarmin da wannan ma'' ''barshi,maryam bari baba uwani tazo zata shigar miki da su,aikin maryam a gidan nan girki ne kawai''mami tace da abida,sai ta bar abinda take yi din ta dubi maryam sannan ta dubi mami ''ok,ai duka daya ne mami,dan aiki dan aiki ne da mai girki da mai shara duka 'yan aiki ne'' ''to kam anan gidan akwai banbanci,kowa matsayinshi daban'' dan tabe baki tayi sannan ta saki murmushi kana ta canza topic din ''gaskiya mami abdallah bai kyauta min ba,yaushe rabona da nijeria ammayau kawai ya gaza kashe aikin gabansa yaje ya dauko ni'' ''kinsan dai halin abdallah sarai tun ba yau ba,aikinshi na da muhimmanci matuqa a gunshi,ba dan qaramin abu bane zai sanya shi qin fita aiki ranakun ayyuka ba'' maryam dake tsaye tana jiran tasowar abida duk ta qosa,ta dan gyara tsaiwarta ''mu qarasa na nuna miki dakin'' ''jeki kawai gidan ba baqona bane'' bata kuma tanka ta ba tayi komawarta daki,saida da ta dqidaici lokacin da ya kamata tayi serving nasu sannan ta fito,saita taddasu tuni sunyi nisa da fara cin abincin,son haka ta qarsa ficewa daga bangaren gaba daya,boys quaters ta zagaya inda anan gidan baba uwani yake da fara'a ta tarbeta ''maraba da maryamu,sai yau Allah yayi za'a zo mana''murmushi tayi har fararen jerarrun haqwaranta suka bayyana ta gaida baba uwanin da baquwar da ta taras tayi hirarsu suka sha sosai don bata baro bangaren ba sai da akayi sallar isha'i sukaci tuwon dawar da baban ta girka,don dama tana kewarsa matsalar su mutanen cikin gidan basa cinsa shi yasa ma bata girkashi ita daya ta taho iskar damuna na kadata,cikin parking space ta jiyo motsi,ta dan juya kadan hisham ne abokin abdallah,a tunaninta basu ganta ba don haka ta kau da kai tayi gaba ''haba 'yan mata irin wannan shan qamshi haka?,a qalla dai ai ko gaisawa kya tsaya muyi ko?,duk da cewa ma zuwan don ke nayi shi''inji hisham wanda ya sha gabanta,qirjnta ne ya shiga dukan uku uku,fatan ta kada Allah yasa ya furta mata kalmar so,don ita tsoro ma take bata,ta jita daga bakunan maza da yawa saidai babu abunda ta tsinana mata a qagauce ta ce masa ''ina wuni'' ''lafiya qalau maryam diya na ya gida ya aiki?'' kai ta dago ta kalleshi jin ya ambaceta da sunan da schoolmate da classmate dinta zuwa friends ke kiranta da shi ''lafiya qalau,ina son ganinki amma bari idan mun gama da abdallah zan kiraki,da fatan ba zaki qi zuwa ba'' ''Allah ya bani iko''ta fada da gaggawa tana wucewa don ganin abdallah na isowa gurin duk da haka bata kasa jin abunda yake fada ba kasancewar sun biyota ne a baya ''hisham,wlh hisham ka fita a ido na,kai me yasa baka jin shawara sai shegen taurin kai?''dariya ya qyalqyale da ita ''kai kuma mai yasa kake da girman kai da kafiya,Allah bai haramtamin harinya ba na gani inaso to kuwa ba zaka hanani ba'' ''ok haka kace?''ya fadi cikin huci yana dubanshi ''yes,haka nace,idan kuma kai ke sonta ai sai ka fada sai in janye maka'' a zafafe ya soma fadin ''na rantse hisham zaka jawo mu samu sabani mai girma da kai,in rasa inda zanyi ajiyar soyayyata sai gun house girl kuku?,ina da dukiyar da zata iya bani duk kalar macen da nake so na aura,ko 'yar wane kuma ko awanne qasa take,wanda nake tare da shi ma yafi qarfin auran house girl,indai ko zaka ci gaba kan qudirinka ka tabbatar cewa yana daidai ne da datse igiyar abotarmu''yayi gaba cikin hanzari abunka da qaqqarfan mutum ko cikin parlour din ma dambarwar da suka dinga yi kenan sai da mami ta shiga maganar ''hisham ka qyale rigimar abdallah,maruam ta cika macen da za'a so,tana da dukkan halaye managarta,uwa uba kyau,don haka babu hujjar da abdalla yake da ita da zai hanaka neman maryama,ni na goyi bayanka saidai idan ita tace bata so'' ''toh...nima haka na gani mami,nace masa ya fada idan yana so ne shima sai....'' ''dakata hisham,don ina nema maka hanya mai bullewa kake cimin fuska?,to kayi na farko kayi na qarshe,duk lokacin da ka sake cewa inasn waccar abar wallahi sai na fasa bakinka'' ba hisham ba hatta mami abun ya bata dariya,abdallah mai rikicin gangan inji hisham,a haka abida tq fito ta taddaau,wannan karon ma cikin shigar doguwar riga take mai sulbi saidai armless ce,a mutunce suka gaisa da hisham don sunsan juna,ta juya ga abdallah ''soulmate,me yasa kamin haka don Allah,na diro naija da daukin ganinka sai kuna kayi tafiyarka aiki sai yanzu zan ganka?'' ''da kika ganni yanzun ma ki godewa Allah,a tsare gobe ne haduwarmu,haka ne?''da sauri hisham ya shiga maganar ganin abdallah nason qarawa kwabar ruwa ''shareshi don Allah,kanshi ne ke hayaqi tun dazun'' tuni abida ta rudevta dawo kukerar da abdallan ke kai tana tambayar wa ya taba mata ruhinta,tsam mami ta miqe ta basu guri,banza ya bawa ajiyarta don haka kawai yake jin ransa na zafi ''wlh abdallah nan naki rigimamme ne sai kinyi da gaske,haka kawai ya haqiqance wai bazan auri maryam ba?'' ''wace maryam?''ta tambaya tana duban abdallah ''mai shirya masa abinci kullum yana dirkewa'' ido ta,zubawa abdallan,lokaci guda wani kishin maruam din ya dirar mata,take taji ta tsaneta ''amma soul mate mene hujjarka na hana hi....'' a fusace ya miqe ''ke dakata min,kinsan banson titsiye ko?''yaja tsaki ya juya zai fice a sashen kuka abida ta saki,wannan wane irin jaraba ce,daga dirarta a qasar ko kwana batayo ba abdallah ya aona bata mata rai,lallai abunda kake so shike wahalar da kai kukanta bai dameshi ba ya juya ya fice,da sauri hisham yace ''kiyi haquri bari,na sameahi ranshi ne a bace''cikin hanzari ya bi bayanshi amma da yake gwanin sauri ne tuni ya miqe balcony yayi sashensa bai damu da hade girar sama da ta qasa da ya sakeyi ba duk don kada ya masa qorafin abunda ya yiwa abida ya hau masa fada tare da cewa yaje ya lallasheta ''wa?,ni?Allah ya tsareni,bani da lokacin lallaahin mace wallahi,ruwanta ta ci gaba da sona ruwanta tace ta haqura,amma babu lokacin rarrashin mace a rayuwata indai ba mahaifiyata ba'' karab cikin kunnen maryamu dake kwance saman gadonta don sun iso saitin window dinta,miqewa tayi ta zauna saman gadon,wani irin haushi da tsanar abdallah suka kamata wanne irin nau'in mitum ne shi? taqama da gadararsa sunyi yawa,dukiya?ita ke rudarshi ko kyawun da yake da shi?,haushi da takaici suka kamata tamkar da ita suke maganar,haushinsa ta dinga ji sosai,da tana da iko sai ta masa dukan tsiya ko zata samu sauqin abunda take ji haushinsu abida ya kuma kamata don me suna mata da Allah ya yiwa baiwa da ado da kunya su dinga watsi da baiwar,so hauka ne?,ta godewa Allah da bai dora mata wannan masifar ba,gwara da Allah ya bar zuciyarta wankakkiya kuma kubutacciya daga dukkan soyayyar wani kusan awanni biyu da shigewarsu mami ta turo qofar dakin ta shigo fuskarta qunshe da murmushi ''maryamu diyata,jeki harabar gida hisham abokin abdallah na son magana
Chapter 22 · 0% Book details