← Book details Abadan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 103

Sashe 72

Abadan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

''me nayi miki da kika zo kina mafarki da ni?,kin daga mana hankali muna ta nemanki tun la'asar gaahi har magariba ta gota ana shirin yin isha'i ashe ke mafarkina na ma kika zo kina yi?''ya fada fuskaraa dauke da murmushi wanda sai ka kuka sosai zaka gane shi kwance kan fuskarshi
haushin kanta ya kamata,kunya da taoro suka dirar mata,kada dai ace kamata yayi tana ambatar sunansa,kai amma kam da ya gama da ita,duk da ba haske bane tarwai cikin dakin sai data harareshi
''waya damu da kai da zaiyi mafarkinka? kai kadaine mai sunan?''
hannayenshi ya ware na alamun ba ruwana
''bani na kar zomon ba,ratayar ma ba'a bani ba,kuma ni din ma na dade da sanin ba'a damu da ni ba,tsabar haushina ne yasa kike ambatar suna na cikin mafarki cikin yanayi ma shauqi ko?''ya tambaueta tana tsatstsareta da kallon nan nashi,bata san me zata ce masa ba duk da barazanar kare kanta da takeyi ba,sai kawai ya juya kekenshi zai fita yana dariya qasa qasa

''ko yanzu kasuwa ta tashi dan koli yaci riba,na bada darasi abdallah ba rago bane,ki fadi abinda ke damunki idan ya kama taimako sai a taimaka miki''ya fice daga dakin,ba qaramin quluwa tayi ba,ya akayo ya sake ma ya kamata tana mafarkinsa,ta ciji yatsa tayi dana sanin ma yin barcin nan gaba daya,dole haka ta sauko daga gadon tazo ta wucesu suna zaune abinsu hisham tsoho alhaji inna wuro da abdallah,garwashi ne da wasu magunguna gaban tsoho alhajin wanda da alamu duka hade haden abdallah ne,taje ta dauro alwala tana jinshi yana basu labari

''gadonki taje ta naushe miki inna,taji laushin katifa tana ta mafarki barkatai,inaga alhaji sai ka bata magani ma don ina zaton akwai wani aljani abdullahi mai irin suna na da ya kamata''dariya ya basu yayin da ita kuma ta sake quluwa
ta daura alwalarta ta wuce dakin inna wuron ta tada sallarta

Cikin kwanakin gaba daya tayi qaura dakin inna wuro nan take kwana saboda hisham na gidan tare suke kwana da abdallan,iyakarta da tsakar gida ta fito ta taya inna wuro aikace aikace ta koma daki abunta,sam ta hana haduwar da abdallah duk cikin qoqarin tana hana kanta jin duk wani feelings dake barazanar kamata,kusan tayi a banza tunda ko shi bai ganta ba ita tana ganin giftawarsa ko ta jiyo muryarsa shi da su tsoho alhaji wanda ya duqufa ka'in da na'in wajen magungunan abdallah wanda alhmdlh cikin jikinsa yan jin wani irin sakewa da sukuni

Ko daya inna wuro bata ce mata uffan ba kan zaman daki data aura,sai ta tuqe kana zakaji tace
''ummm,Allah ya kyauta,kowa dai ya debo da zafi bakinsa''ta fuskanci sarai da ita take

cikon kwana na ukun tana kwance kan qaramin gadon inna wuron misalin uku na yammaci da littafin riyadul jannah a hannunta tana dubawa,yaye labulen inna wuron tayi tana fadin
''ki tashi kije ki gyara dakinsu hashimu,shida malam sun fita bayan gari debo ganye,amma fa idan zaki iya(da yake haka innan ke kiransa)''
ta fuskanci kamar da zafin ta innar ta fada,bata ce mata komai ba ta ajjiye littafin gefan gadon bayan ta saka alama,hijabinta ta,ciro ta ware ta saka kana ta fice innan ta bita da kallo tana tabe baki
''Allah dai ya sawwaqewa matan maraya wallahi''ta jita amma bata tanka ba

tsaye tayi a bakin qofar dakin zuciyarta na wani irin bugawa,kamar ta juya ta koma haka ta dinga ji,fargabar shiga takeji,jin motsin futowar inna wuro daga daki ya sanyata yin saurin daga labulen ta fada dakin tare da sallama idanunta a qasa
kan kujerar dakin wannan karon ta tadda shi zaune,yayi kyau cikin baqar rigar jallabiyya data haska fatarshi,a haka sai kayi tsammanin lafiyanshi qalau saboda kyan da yayi,ganinshin da batayi ba kwana biyu sai taga kamar an canza shi ne,wayarshi ce a hannunshi yana danne danne,da alama wani muhimmin abu yakeyi,amsa mata yayi kallon farko kadai yayi mata yaci gaba da abunda yake kamar bai santa ba
tana kallon kan katifar da kaya ke baje a aki da sauran tarkace tace
''zan danyi gayaran daki ne''
''oh,na bayar baki gidan ne har nasa a gayara din ma''
wani abu ya dan taba ranta sai tayi shiru wanda hakan yasanya ya dago kai ya saci kallonta
qasa qasa taji yace
''if u luv some one be sure to hold them close,if u don't some one else will''

''me kace?''ta fada cikin son nuna mishi bata ji abinda ya fada din ba
''no,ba dake nake ba,bismillah''ya fada yana ci gaba da abinda yake yi
katifar ta soma kintsawa,tana aikin amma jikinta na gaya mata kallonta yake,batayi qarya ba don gaba daya ya bar hankalinshi daga kan wayar ya maida kanta,duk wani motsi nata na kan idonshi,cikin zuciyarsa hakanan yaji tana burgeshi,bai taba zaton zai samu macen da zaiso ta wofantar da soyayyarshi ba,bil haqqi da gaskiya take son nuna masa iyakarsa

Wannan karon duk yadda yaso kauda idonshi kada ta kamashi yana kallonta abun ya faskara sai da suka hada ido,kamar kuma an manne idon ya kasa daukewa,ta juya ga zatonta zai daina kallonta amma sai taga yaci gaba,bata rai tayi
''gabana faduwa yake idan aka fiya samun na mujiya''murmushi ya sake yana janyo laptop dake gefansa
''ayyah am sorry''ya fada yana kunna system,bayan ta saitu ya shiga gun hotuna ya bude daya daga cikin hotunan ciki

Gefanshi taje zata dauke abun sallar dake shimfide a gun idanunta ya kai kan system din,hoton mero ne ya cika screen wanda da alama shi abdallah yake kalla
batasan ta fincike laptop din a hannunshi ba saida ya dago ya zuba mata idanunshi
''me kuma nayi?,ai na daina kallon naki ko?''ya fada a shagwabe kamar qaramin yaro
bata kula shi ba saida tayo shutting down fuska a hade cikin zuciyarta a tsinke tace
''saika tsagaita na gama gyara na tukun,baxaiyiwu ina gyaran kaya ana min janye janyen wani shirgin ba''ta fada tana canzawa computer mazauni nesa da shi
idan banda jarumtae daya aro ya tabbatar babu abinda zai hanashi fashewa da dariya

sai ya wayance da dora hannunsa guda daya kan tattausan sumarshi
''oh Allah na,mami na kin barni gashi ana nan ana gara miki ni''
shi da yayi maganar da ita kanta sai maganar ta soki zuciyarsu,tabbas ba kadan ba sukayi rashi da kewar uwa ta gari irin mamin

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

Sosai ta qaranta baccinta don tayi imanin babu masifar da addu'a bata da maganinta,tana samun nutsuwa qwarai da gaske saidai gaba daya hankalinta ya karkata ga abdallah da maryam

yammacin ranar lahadi tana gida bayan ta kira baba uwaani,su biyu ne cikin parlour din,a yanzun kam da baya ga 'yan uwanta baaba uwani ce ta biyu wadda take shawara da ita
''amma hajiya tunanin da nayi,ba zamu zauna bamusan inda suke ba,mai zai hana mu nemi gidansu maryam ko suna da labarin inda suke?''
cike da gamsuwa mami ke gyada kai
''qwarai da gaske baaba,wannan shawara ce mai kyau,amma cikin ni da ke babu wanda yasan gidansu maryamu tunda a lokacin bikinta bamu samu damar zuwa ba tunda ya hade da na abdallah''
''eh hakane hajiya,amma ai da hajiya ruqayya aka kai lefan maryam dinko,ina zaton ki tambayeta zata iya tuna gidan''
''af,qwarai kuwa,bari nayi kiranta''

Cikin sa'a kuwa ta samu ruqayyan qanwarta ta tabbatar mata zata gane gidan,a nan suka shirya tafiyar nayan sallar la'asar don zata tsaya ta sallami mai gidanta zaiyi tafiya da azahar

Su uku ne cikin motar hajiya bintun ruqayya sai baaba uwani,jifa jifa suke tattaunawa kan batun har suka isa unguwarsu maryam din,sukayi parking qofar gidansu kana suka dunguma zuwa cikin gidan

Gidan yana nan yadda yake daga soro zuwa tsakar gidan suka fara sallama,inna hadiza dake kan tabarma a tsakar gidan ta amsa musu don babu kowa a tsakar gidan idan ka debe ita da huwaila dake kitchen tana fama da tuwon dare
kallo daya tayi musu ta fahimci daga irin gidan da ta fito,don haka jiki na rawa ta miqe tana fadin
''lale marabanku,sannunku da zuwa''mami batasan wace ba amma ruqayya tuni ta tunata saboda diban albarkar data yi danar kawo lefe,sake karkade musu tabarmar da take kai tayi tana fadin
''bismillanku ko zauna,ko daga ciki zamu shiga?''
ruqayya ce ta karbe cikin tabe baki tana girgiza kai
''mama muka zo nema,maman maryam''turus tayi kamar bata ji abinda suke fada din ba,don ita har yau babu abinda ta tsana irin taga wani abu na ci gaba ya samu maman,har yau bata dauki izina ba,rayuwar maman kullum sake inganta take,don hindatu kadai tafi dukkan nin yayan da ita ta haifa wadanda duk suka dawo gabanta,daya ce gidan aure saboda rashin kyakkyawan training na zaman auren,hindatun bata bar maman nasu ta nemi wani abu ta rasa ba,ta sake inganta rayuwarta fiye da da,ta sani rashin adda maryam dinta ne a akusa da ta tabbatar maman ma sai ta fi haka,duk da a yanzun ma ko hasidin iza hasada sai ya daga mata qafa

Shirun taci gaba da yi har sai da huwaila ta fito daga kitchen dinsu wanda zuwa yanzu hindatun ta gyara musu shi duk da maman ta bata girki ciki,tayi me saboda babanta da kuma huwailan wadda a yanzu ta saduda,tun ranar da aka gyara kitchen din inna hadiza tabar girki a cikinsa saidai tayi daga waje
''sannunku da zuwa''inji huwaila dake wanke hannunta bakin famfo
''yauwa,don Allah maman maryam tana nan?''
''eh tana cikin daki ina tsammanin sallah take,ga dakin nata nan ku shiga''ta fada tana musu nuni da shi suka amsa kana suka shige
''an dai ji kunya wlh,an zama 'yar kora da haka za'a qare''
''ba komai,don ma zama 'yar korar amina ai tafi minke,don qaruwar da nayi da ita banyita da ke ba''ta sa kai ta shige dakinta don tasan halinta idan ta tsaya sai su raba abun fada yanzu ba kunya take ji ba
Chapter 72 · 0% Book details