Sashe 40
Abadan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [9/17, 12:54 PM] 80k: *ABADAN*36 *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* © *HASKE WRITERS ASSOCIATION* *_home of expert and perfect writers_* *_annabi muhammad s a w ya tambayi sahabbansa_* *_''shin ko kunsan waye matsiyaci?''_* *_sai sahabbai suka ce''matsiyaci shine wanda bashi sa dirhami ko dirane''ma'ana bashi da cin yau bare na gobe_* *_sai annabi yace musu''matsiyaci shine wanda zaizo ranar qiyama,yayi azumi yayi sallah yayi sadaka yayi zakka yayi hajji saidai kuma ya cuci wancan ya zalunci wancan ya zagi wancan yaci dukiyar wancan,sai Allah ya dinga dibanadan wadancan ayyuka na alkhairin da yayi ya dinga rabawa yana biyan wadanda ya zaluntar har sai ya tashi bashi da komai cikin aikin ladansa,ga ragowar wadanda ya zalunta ba'a gama biyansu ba,sai Allah ya dinga diban zunubinsu yana bashi da haka da haka har sai ya tashi bashi da komai face kayan zunubi sai Allah ya jefa shi a wuta''_* *ya ubangiji kayi mana tsari don isarka* Har mami ta dawo daga gidan maman farida ta shirya bai gama nashi shirin ba,sai da ta leqa ta masa magana,ta leqa dakin maryam ta taddatakwance ''ya kike a kwance mu da zamu fita?'' sai ta miqe zaune ''bana jin dadi sosai mami'' ''ashsha,Allah ya sawwaqe,ki kwanta ki huta qila gajiyar tafiyar ce bata sake ki ba,Allah ya qara sauqi ma fita gobe ba damuwa,ungo wannan ajjiye min''ta miqa mata baqar leda,kayan bacci ne masu azabar kyau guda hudu ''maman farida ce ta bani su,nikam ina ni ina saka wadan nan qannnan tsirarar ai sai ku'' kunya ce ta kama maryam ta karbi kayan fana sunne kai,sanann ta tashi tayiwa mamin rakiya zuwa falo,sgi din ma ya fito sanye da qananun kaya,t shirt ce mai gajeran hannu baqa wanda a gaban rigar akayi rubutu gwara gwara kamara haka *we all have story to tell*,sai baqin trouser da ya saka,sun masa kyau aoaai kasancewarsa fari sai suka haskashi,qofan ta maida ta rufe ami tace sai sun dawo kusan wuni sukayi ranar a waje har maryam ta qosa da zaman kadaitakar,duk da cewa ko a gida ma idan duka suka fice kusan haka ne amma acan wani okaci takan fice gidan baaba uwani susha hirarsu,da zaman shirun ya isheta sai ta fito valcony din gaban floor dinsu tayi zamanta tana qarewa unguwar tasu kallo basu suka dawo gida ba sai da suka kammala siyayyar lefe kaf baki daya,hatta da akwatunan basu bari ba,daga can kuwa gurin da zasu dora kayansu a jirgi suka zarce basu ko dawo gidan ba,sun zabi zuwan kayan ta iska wato ta jirgin sama don shine mafi sauri,tunda kafin su koma za'a kai kayan suna sa ran kuma idan ta jirgin saman ne bazaya wuce kwana hudu zuwa biyar ba yaje sabanin ta jirgin ruwa da,zaya dauki watanni sai da mami ta tabbatar komai ya kammala sannan ta karbi wayar abdallah ta kira qanwarta hajiya ruqayya ta mata bayanin kaya sun taho,tayi qoqari don Allah da sunzo a shirya komai yadda ya kamata aje a kai lokaci yana qurewa a mugun gajiye suka dawo don haka suna dawowa wanka sallah da cin abinci kawai sukayi,cikin qanqanin lokaci gidan ya sake zamowa shiru saboda yau babu zaman hirar daki kowa ya shiga ya kwanta Washegari dukkansu su ukun suka fita kai tsaye kamfanin sarrafa kayan gado suka shiga,katafaren kamfani ne da suka qware wajen qera da sarrafa kayan daki da suka hada da gadaje sif madubi zuwaafiyayyun kujeru iri iri,inda suke ajjiyesun bayan sun gama sarafa su aka shiga da su,mami ta bawa maruam dama ta zabi irin wanda takeao,duk sai ta duburbuce ta kasa zabar kowanne daga ciki sun kusa shafe awa guda saboda girman gun ba tare sa ta iya zabar koda kala daya ba daga ciki abdallah ne ya ja tsaki ''yarinyar nan fa wahal da mu kawai take yi mqmi,kawai ki fidda mata wanda kika ga ke ya miki'' ''meye naka a ciki dakina ko naka ko kuma dakinta ita zata zabi abinta'' ''Allah ya baku haquri''ya fadi yana kewayesu ya barsu a gun ya nufi inda ma'aikatan ke zaune ma'aikata biyu da leburorin gurin guda biyar suka qaraso inda suke tsaye ita da mamin,daya daa cikin su yace da mami cikin harshen nasara ''madam,ku zaku yi signing a nan za'a fitar da kayan,motocin kamfaninmu zasu kaimuku har inda kuke buqata suna wajen kamfanin suna jira''ya fada yana miqa mata wata yar matsakaiciyar takarda,ta amsa ta duba kana ta kalleshi cikin arahen nasaran itama ta maida masa ''ai bamu kai ga zabar wadanda mukeso din ba ai'' ''yallabai ya riga ya zaba har ma ya biya kudaden''yayi maganar yana nuna wasu tsadaddu kuma tsararrun kayan gado dake gefan hannun damansu,kala biyu ne kujeru sif gado da madubi curtains,dressing chair da bedside sai abun maqale jakankuna dukkan kalolinsu light and dark purple ne sai wasu set din kamar haka amma su blue black ne da light blue ba qaramin burge mami kalolin sukayi ba har ta tsaya kallinsu saboda kyawun da sukayi mata,abdallah ya iya zabe kamar mace,ta daga kai sai ta hangoshi can sama wata kujera mai siffar kwano mai azabar tsawo a zaune hannunshi riqe da cup din glass yana shan lemo,kashe mata ido yayi ya langwabar da kai alamun bada haquri tare da nuna mata agogo lokaci na tafiya kenan kana ya mata alama da hannu na kayan sunyi?,dariya ma ya bata sai ta daga masa girarta alamar eh,hannunshi ya sake dagawa ya mata alamar i love u,murmushi ta kuma yi ta girgiza kai kana ta samu gefe ta zauna tana fara signing din paper din zuciyarta cike da tunanin mahaifin abdallah,wani lokaci idan hayi wani abun sai taga ya koma mata alh abdulkareem sak,barewa batayi gusu danta ya rarrafa ba ta fada cikin zuciyarta duka cikin kamfanin suka nufi bangaren kayan kitchen anan kam dama kawai ta basu nasu hada mata duk wani abu da yake,da amfani cikin kitchen,cikin lokaci qanqani sai gasu da,kaya bila adadin sukayi total ta biya,yawan kudin da maryam taga mamin ta kashe mata shi ya sake raunata mata zuciya sanyata kuka,kuka sosai ta saka har ta kasa magana ma,hatta da abdallahn dan garari tsayawa yayi yana kallonta,karo na farko da ta bashi tausayi,jawota mamin tayi jikinta sai ta ora kanta a kafadarta,hawaye naci gaba da zuba,itama mamin kasa magna tayi sai bayan maryam din da take dan bubbugawa a hankali cikin sigar lallashi,har cikin zuciyarta tanq jin ciwon rabuwa da maryam din,idan banda aure batq jin akwai abinda zata lamunce ya tsinke zamansu mai dadi da suka fara washe gari ma baccinsu suka sha sai yamma sanan mamin tace su shirya su fita maryam ta danga gari,kada tazo ta kuma koma bata san ya garin yake ba babu musu ta shirya cikin doguwar riga dark blue da adon golden din duwatsu saqar india ce,ta haskata qwarai,saidai kasala da rashin dadin zuciya da take ji ya rage walwalarta qwarai,wanna fargabar ta aure sai yqnzu taji ta fara shigarta daga lokacin da tayi tozali da kayan dakin aurenta,Allah ya sani ba zata yiwa Allah butulci ba amma tilas amatsayinta na budurwa taji fargabar aure kamar yadda kusan kowacce soya mace take ji a auren farinta a rayuwa da qafa suka dinga tattakin suna taba hira kadan kadan cikin sassanyar la'asar din,yanayin garin ami kyau ne,babu ruwan wani da harkar wani,kusan hirar dake gudana jefi jefi tsakanin mami ne da abdallah,bata ankara ba sai da taji shirun na maryam yayi yawa,a hankali ta juyo ta dubi maryama dake hannun hagunta ''maryam'' da sauri ta juyo tamkar mutumin dake cikin tunani aka katse masa,nazarinta tayi na yan sakanni kafin tace ''lafiya kike kuwa,daga jiya zuwa yau naga duka kin canza,ko bakijin dadi ne?''kai kawai ta iya girgizawa tayi qas da kan nata tana qoqarin mayar da qwallar data cika mata idanu,hannunta mamin ta kama ta jata kan kujerar dake girke daura da su yayin da abdallah yayi tsaye hannayenshi harde a qirjinsa yana kallonsu,bai iya jin me suke fada amma yana iya ganin me ke gudana,motsawar bakin mami da gyada kan maryam,a hankali ta dinga share hawayen idanunta qarshe ta buge da murmushi kana suka taso suka iske shi mami ta dubeshi ya wani hade rai yayi kitchen kitchen,ta dan ranqwashi qeyarsa ''kai kuma da wa mai aljanun sauyin yanayi''dariya taso qwacewa maryam har sautinta ya dan fita,tayi gaggawar gumtse bakinta ganin yadda ya zuba mata harara cikin shan mur ''nifa mami gaskiya ina da kishi,don me za'a tafi ni a barni ni kadai a tsaye kamar maye bayan da can ba haka kike min ba,kawai don an samu wasu'' ''maganarmu ce ra mata bai kuma cancan ci kaji ba ehe,ciwon 'ya mace na 'ya mace ne,sannan wasun ma da ka kafawa qahon zuqa suka tsole maka idanu sun kusa tafiya su baka sararin gurin kaga qarewarta sai ka koma shan nono kace ma ko yaye ka banyi ba''sosai mami ta bashi dariya har sai da ya dara yana fadin ''ni na isa,amma dai nasan tattalin da ake min irin na da zai dawo,kinga na zama dab lelen murum biyu,ga na my dear ga naki,thank god'' Da daddare suka hada dukkan wasu kayayyakinsu washegari jirgi ya debesu sai qasa mai tsarki,washegarin ranar da suka je suka sauke faralin ibadarsu ta umara,hakan bai sanyasu shiga wasu sabgogin ba sai da suka kwashe kwana biyar basu rabo da masallaci wanka ko cin abinci ke fiddasu,har gwara mami wani lokacin ta dan koma ta runtsa,maryam kuwa bata bawa kanta wannan hutun ba,tun mami na mata mita kan ta huta harta gaji ta barta,cikin kwana biyar din nan sai da tayi saukar alqur'ani biyu,dukkan alkhairi babu wanda bata roqawa mami mamanta raliya hindatu da ita kanta ba kwana uku sukayi a madina ziyara,daga nan suka hada ya nasu ya nasu,mami tace itafa sai ta sauka a sudan tukun,cikin alamun tuburewa yace ''me zamuyi kuma a sudan mami,dear fa ta matsanta tana da buqatar gani na,i have alort to do mami a gida,inaga tafiya zanyi nikam sai kin taho'' ''wa salaam wa kitabi,nima na huta da qorafi kama gabanka Allah ya miyaye hanya sai mun taho''anan suka raba jaha da shi,maryam batasan me zasuyi a sudan ba sai da suka je,unguwar tamkar tana cikin qasarta haka ta gani,sai dai 'yan bambance banbance da ba'a rasa ba na suturu abinci da