← Book details Abadan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 103

Sashe 21

Abadan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

shiru ta danyi cikin shakku,bata son ta fiya zura kanta cikin harkokin masu hannu da shuni, tana gudun wulaqanci,duk da tayi amanna cewa mami sam ba haka take ba,ta yarda da karamci da kuma son jama'a irin nata,to amma shi uban tafiyar fa wanda sam tasu batazo daya ba?
''yaya ne maryam naji kinyi shiru ko baki da sha'awa?''
girgiza kanta tayi
''a'ah mami,duka abunda kika yanke mami dai dai ne,amma zanso na fara sanar da baba da mama naji me zasu ce akai''
''gaskiyarki,wannan dai dai ne,amma duk da haka ki fara hada min takardunki nasan bazasu qi ba,babu wanda zaiqi ilimi wa dansa,ina da qawa a jami'ar b u k sanate ce so insha Allau babu matsala''

''to mami na gode Allah ya saka da alkhairi ya qara girma''
''no maryam,diya ta nayiwa kinga babu buqatar godiya''gyada kai tayi fuskarta qunshe da murmushi
sallamar nene ce ta maida hankalinsu bakin qofar,nenen ce kiwa cikin doguwar riga mai zubin buba mai taushi saidai wannan nada hannaye gajeru da alamu shigar barci ce tayi
''maraba da nene''
''yauwa...mami''ta fada tana zama cikin daya daga cikin kujerun falon dake,daura da inda mami da maryam din ke zaune,a mutunce suka gaisa
''zuwa nayi na diba yarona abdallah kwana biyu banjin duriyarsa''nene ta fada tana murmushi

mami ta rufe computer tana cewa
''abdallah na nan qalau aiki ne ya sashi gaba,da wuri yake fita kuma bai shigowa da wuri,yanzun na zancanshi muka gama da maryam''
ta juya ta dubi maryam sai a lokacin ta gaidatakanta na sunkuye a qasa,sam batason kallon idanun natar,haka nan sai taji fargaba ta kamata,second talatin idanunta na kan maryam din tana saqa a kanta kafin ta dauke kabta ta maida ga mami
''lafiyanshi dai qalau ko?''
''lafiya qalau yake''mami ta bata amsa cikin jin dadin tambayar tata,wadda har ga Allah tayi tsammanin ta mata ita ne da zuciya daya

ta miqe tsaye tana cewa
''tiw,ni zan wuce dama abunda na shigo naki kenan,sai da safenku''
''Allah ya bamu alkhairi nene an gode ki gaidamin su zubaidan kwana biyu ma bata leqo min ba,zahariyya dama sai wani abun ya kawota''murmushin yaqe nenen tayi cijin zuciyarta tana cewa
''bintu ki guji ranar gamuwar mu dake,gamon mu dake bazai ma rayuwarki daidai ba''

''abdallah na bani kunya wlh,dubi yadda baiwar Allahn nan ke sonshi take damuwa da shi,amma shi bashi da abun wulaqantawa sai diyarta,idan baiyi wasa ba na kusa masa auren dole''
'yar qaramar dariya ce ta subucewa maryam
''ai mami ba'a yiwa namiji auren dole''
itama dariyar ta tayata
''to za'a fara kan abdallah''

mintina ashirin basu cika da fitar nene ba abdallan ya shigo,ya sauya shiga ba wadda ya fita da ita bace,indai mami taga hakan to a gajiye ya dawo ya fara shiga sashensa yayi wanka ne
kan table maryam ke serving nashi yayin da shi da mami ke hira jifa jifa,ta kammala tana shirin sauka ta basu guri taji yace
''ke...mene wannan din?''ya fada yana nuna abincin da ido,kafin ta bashi amsa mami ta karbe zancan
''dambun shinkafa ne mana''
ya bata fuska kamar yadda yara keyi ya dubi mami
''gaskiya mami ni bazanci wani abu dambu ba''maryam ta kalli farantin don sake gano aibun dake tattare da dambun da ta bata lokaci a kitchen tana girkawa,dambun shinkafa ne da aka masa hadin vegtables sosai saboda ta sonshi da son gayayyaki,cabbage ne carrot zogale green beans harda gyada da wadatacciyar albasa sai dafaffen nama data yankashi qananu ta zuba a ciki,mamaki tayi cikin zuciyarta duk da bata nuna ba kan fuskarta,ta lura tsirfar da ya tsuro da ita kenan cikin yan kwanakin nan

''amma kaifa dazun kace shi kake sha'awar ci ayi maka?''
''am sorry mami na,dambu ayanzu is too heavy na cishi na kwanta ai sai ya kashe miki ni''
dariya ma ya bata,bata zaci konai ba don yaune ya fara wa marya din a gaban idonta
''is ok,maryam yi haquri kinji taimaka ki sama mishi wani abun mai sauqi da sauri''
''no mami,ni zan zaba akwai abunda nake sha'awar ci''
''uhmm''ta fadi tana kallonshi
''sakwara nakeso miyan agushi''bata fuska mami tayi
''kai lokaci fa ya qure gaskiya ba zata girka ma sakwara a yanzu ba saidai ka barwa gobe''
''tunda kin roqa mata shikenan tamin jallop din supaghetti with serdine''bai qarasa ba ma ta sauka tayi kitchen

girki ba baqonta bane cikin minti ashirin ta kammala ta,tun kafin ta fito qamshi ya soma cika qofofin hancin abdallah amma sai ya dake
''mami,dazu munyi waya da abida,ta ce nan da kwana uku zata zo nijeria''
farinciki sosai maryam ta gani fuskar mami
''masha Allah,gaskiya ta kyauta qwarai kuwa da gaske,kaga ta baka kubya kai da kaqi zuwa''
''to mami me zanje na mata''
''any way dai tunda tace zata zo magaba ta qare,fata na idan tazo din wannan karon konai ya daidaita,canki cankar da kake tayi wa muta ne ta qare''
''haka nake fata,na soma gajiya da qulafucinsu naci da rashin zuciya,inason nima na huta mami na samu peace of mind''

kafadarshi mamin ta buga''ja'iri sai yanzu kasan da hakan...am maryam''
''na'am''
''insha Allahu nan da kwanaki uku zamuyi baquwa abida diyar ambassador muhammad mukhtar kuma idan tazo zata dan zauna da mu na wani dan lokaci,so ya kamata kinga na sanar miki haqqinki ne sa'an nan daura da dakinki zata zauna kinga ke zaki karbi baquncin,ina son kuma a sake tanadin sabbin girki,duk na san ban da matsala dake,ke din ba baya bace''ta qarashe maganar cikin sigar zolaya tana murmushi wa maryam din
murmushin ta maida mata
''insha Allahu mami babu damuwa''

''mami a maida abincin nan kawai kitchen nina qoshi ma''inji abdallah bayan ya gana jagulashi da cokali
harararshi tayi
''baki isa ba ko zaka ci kayi amanshi sai ka ci,maryam tafiyarki kije ki kwanta Allah ya bamu alkhairi,gobe insha Allahu zamu tattauna''sallama ta yi mata tayi shigewarta yayin da mamin ta ja plate din ta soma nado taliyar cikin pork tana cusawa abdallah,shikam ya bude ciki ya dinga diba,dama yana so kasuwa kawai yake kaiwa
''almiri ashe kana ci din kenan shegen girman kai yasa kace baka ci''mami ta fada tana dubanshi
dariya ya qyalqyale da ita ya kanne ido daya
''so nake dama mami ta bani da kanta nasan sai yafi dadi''
''Allah ya shirya min kai abdallah''ta fadi tana murmushi

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

tafiya take bata ko ganin gabanta saboda takaici da baqinciki,wai sai yaushe ne burinsu zai cika kan abdallah?,sai yaushe zasu samu nasarar kau da abdallah daga doron duniya,da wannan tunani ta samu da qyar ta maida kanta bangarensu

adnan da zahariyya dake dakon zaman jiranta cike da buri da fatan jin daddadan labari suka taso
''yaya nene?,anyi nasara kuwa?,rashin ganin nashi nada nasaba da aikin mu kuwa?''saida ta fada jabar saman kujera kafin tace
''mun sake fadu wannan karon ma babu nasara,rashin nasarar kuma yafi na kowanne lokaci''
adnan ya sake matsowa gabanta
''yaci dinne bai mutu ba?''
''ina ma yakai ga cin,ai ko ci baiyi ba,kuma hakan baya rasa nasaba da wannan tsinanniyar mai girkin da na rasa inda bintu ta samota,yarinya sai shegen kwarjini''
''oh shit!''adnan ya fada bayan ya dunqule hannunshi ya daki tafin hannunsa,zahariyta kuwa kasa magana tayi face bin sahun uwarta da tayi ta fada saman kujera

a sukwane ya koma shina ya zauna bayan yayi qasa da muryarshi
''nene,nifa na gaji da wannan shirin kisan ta bayan fage,ki barni kawai na tari abdallah na kasheshi da hannuna''
''kai dalla gafara can''nene tayi hanzarin katseshi
''ashe baka da hankali?,waye ya gyamaka kashe mutum kamar abdalla abune da yaje da sauqi har haka?,ka manta matsayinshi?,ka manta wayeshi a nijeria,bama haka ba,ka mance qirar qarfin da abdallah ke da ita,wanda na tabbatar idan aka barka da shi naushi daya zai maka saidai mu dauki gawarka ba kai din ba''shiru adnan din yayi don yasan haka maganar maman tashi take

zahariyya ta furzar da wani rin huci
''tsinanne matsiyaci,ni da zai amince ya auri waccar yarinyar zubaida ai da kinga komai yazo mana da sauqi,mu kasheahi hankali kwance,idan da rabo ma har sai ta haihu kinga tuwo namu miya ma tamu,to amma shegen girman kai da jin ajinsa bazai barshi yaso zubaida ba,to amma nene mai zai hana mu nemi hadin akn ita kukun tashi ko zata amince kamar yadda na baya suka amince,idan yaso itama musa a mata daurin baki idan ta amshi kwangilar ta yadda koda lamari ya baci zata gaza ambato sunansu kamar wadancan kukun''

ajiyar zuciya nenen ta saki
''hmmm,yaro yaro ne,duka tunaninku babu wanda ya kwanta min,wannan yarinyar tasha banban da wadancan kukun nasu na baya kallo daya na mata jiki na ya gaya min haka,abunda zai faru shine ni da kaina nake so ku bani lokaci zanyi tunanin mafita,na rantse da Allah wannan karon ko bata hanyar guba ba *SAI NA SALWANTAR DA ABDALLAH*

_TOH FA_🤔
Chapter 21 · 0% Book details