Sashe 24
Abadan Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
komawa taji tace ''ke zokiyi serving mutane,kin shige daki kin zauna sai kace baki san aikinki ba'' bata tanka mata ba sai da suka isa teburin,a sanyaye cikin jerartun maganganunta masu cike da nutsuwa ''idan baki sani ba sunana maryam don Allah ba ke ba,aiki kuma ba naki aka umarceni da inyi ba,ba don ke nazo gidan nan ba,so please don Allah mu girmama juna,tunda dukkanin mu 'yan adam ne,halitta mai qima da daraja agun Allah'' ''naqi na kirakin da hakan,kuma ni ba sa'arki bace kada ki kuma hada kanki da ni,ki dubeni ki dubeki mana,tundaga sutura ai kinsan da banbanci,kada ki kuma gigin hada kanki da ni'' shiru tayi mata domin ta fuskanci abidan tayi nisa,gwana ce itama gun girman kai,amma bata jin zata iya jurewa shararta ba sam,da iliminta itama da shekarunta,ba jahila bace bare tace zata dinga shiga gonarta tayi mata kashi ta qyaleta,ta kammala zuba musu tuwon semo miyar kubewa danya sai farfeaun kan rago a plate daban,a yatsine abida ke duban abincin ''meye kuma wannan?''tayi tambayar tana duban maryam,banza tayi mata tamkar bata jita ba,don,kanta da ta gaji da shirun tace ''ni wlh soulmate bazan ci wanna abun ba,na manta wanne lokaci ne na qarshe,da na cishi,kinga malama ki ahiga kitchen ki dafa min wani abun'' ''awoyin shiga kitchen dina na yau sun qare,amma babu damuwa idan zaki iya jira zuwa gobe'' daga haka ta miqe tabar musu teburin,ahi kansa abdallah dan binta yayi da kallo ganin yadda yai take maida raddi babi kinkiri,fana iya jiyo ihun abida na zage,zage da hausa mixs da,harshen nasara wani lokaci harda turkanci ''oh god,pls don Allah ki yiwa maqogoronki afuwa,baki gajiya da fada?''abdallah ya fada bayan ya tallafe kumatunta ya sanya zazzafar qwayar idanunshi cikin tata,laqwas jikinta yayi,farinciki ya maye gurbin bacin ranta,tuni ta sanya hannu ta aoma kwasar tuwon sai gashi qarshe ta bige da santi ta cusa kanta cikin pillow ta sake rubtse idanunta akaro na barkatai,har yanzun dai bata daina jiyo tashin hayaniyar ba daga dakin abida muryar abida ce wani lokaci data abdallah,kuka take tun kusan rabin awa das,uka shuhe,sun hanat a bacci,ta kuma gaza fahimtar meke faruwa ''wallahi abdallah ko baka aureni ba indai ka kwanta da ni burina na duniya ya gama cika,don Allah abdallah ka amince wallahi zan iya rasa raina ayau idan ban samu cikar muradina ba,muna da dama abdallah muna da lokaci isashahe,mami bata nan daga ni sai kai kawi abdallah,pls ka taimaka min'' mamaki baqinciki da takaici suka sake cikashi,gumi ya kuma karyo masa,kimanin awanni biyu yana fama ta rabu da shi amma ta qiya,tun yana lalashinta yana qoqarin fahimtar da ita har ta soma bashi haushi,da ya miqe ta yago shi,har ta rabaahi davtshirt din jikinshi sai singlate kamar tsohuwar mayya,bayason gwada mata qarfi ne amma ya fuskanci sai ya biyo,mata ta hakan cikin zafin nama ya miqe ta sake yunqurin kamoshi,tuni ya watsar da ita ya fice kana ya maida maqulli ya rufe dakin,dai dai da fitowar maryam kenan wadda tayi niyyar barin dakin nata ta canza makwanci sakamakon hayaniyar da ta hanata sakat tasu a tsorace ta dubeshi idanunta cikin nashi,ganinshi a jargitse ga sautin kukan abida dake fitowa cikin dakin da ya kulleta,sai ta dan ja baya kadan zuciyarta ta soma harbawa,shi din ma ita yake kallo *mrs muhammad ce* [9/17, 12:52 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺🌺 🌺💖🌺💖🌺 🌺💖🌺💖 🌺💖🌺 🌺💖 💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖💖💖💖💖💖💖 *WRITTEN BY* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* 💖🌺💖🌺💖🌺 💖🌺💖🌺💖 💖🌺💖🌺 🌺💖🌺 🌺💖 🌺 ▶2⃣7⃣