← Book details Abadan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 103

Sashe 68

Abadan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ta fara binsa da gudu keken na sake tafiya da shi saidai yana fuskantarta fuskarsa kuma dauke da murmushi,sai da sukayi tafiya mai nisa kana keken ya tsaya cak,sai taji an,dafa kafadarta da sauri ta waiwayo,maryam ta gani tsaye kusa da ita tana murmushi,ta nude bakinta zata kira sunanta bat taga sun bace mata gaba dayansu,dube dube ta dinga yi amma ta nemesu sama ko qasa ta rasa,wani rami ta gani a gabanta ta tafi a hankali ta keqa sai ta hangosu ciki suna zaune,ji tayi luuu ta tafi itama zata fada ciki

firgigit ta farka tana ambton sunan Allah gami da dafe kanta dake sara mata kamar zai tsage gida biyu,tafi minti talatin a haka sannan taji sannu a hankali ciwon kan yana raguwa yana raguwa har ta daina kinsa gaba daya,sai ta jita sawai kamar wadda aka kunce daga sarqa
''abdallah,maryam''ta fada a hankali

Kamar wadda aka tsikara ta dago da kanta ta miqe da sauri ta sanya hijabinta ta fito,hanyar sashen abdallahn ta nufa kanta tsaye tana tafiya wasu abubuwan da suka faru suna fado mata tamkar mutumin da yayi mafarki yake tuna abunda ya faru,kallo daya ta yiwa sashen nasa jikinta ya gaya mata ba lafiya ba,qofar na nan a lallauye yadda su muugu suka yi mata ranar da suka zo nemansa,jikinta babu qwari ta shiga ciki ta dinfa duba ko,ina da ina ta,iya qurar da bangaren yayi kawai ya isheta amsar cewa gidan ya dade babu mai rai a cikinsa,hotunan abdallahn ta dinga bi tana kalla bata ankara ba kuka ya subuce mata,zaman dirshan tayi saman carfet hawaye masu dumi suka shiga turereniyar fita daga idanunta

''ina ka shiga abdallah,ina ka tafi ka barni''abinda ta donga fada kenan a hankali cikin kukanta
mafarkin da tayi dazun ya dinga dawo mata tar kamar a lokacin takeyinsa,babu shakka ta tabbatar abdallah da maryam duk inda suke suna da buqatarta,suna da kwadayin ganinta
maganganun nene suka sako kai suma
kada kuyi mata magana,shikenan kun karya min asiri
asiri?
asiri wanne iri take nufi,wa aka yiwa asiri kuma akan ne ya karye?duka daga shigowarta gidan a tau tunaninta ke ta mata shawagi,mutanen da ta gani sun fita daga gidan kamar ta taba ganinsu cikin gidan,cikin wani dare cikin kuma wata rayuwa data yi a baya,rayuwar data dinga jinta kamar rayuwar cikin mafarki,cikin rayuwar ta dinga tsinto halin da taga abdallah,abunda ya faru da ita ranar da zata soma rayuwar mai kama da mafarki,a hankali tunaninta ya dawo zuwa yau,maganganun nene sunqi daina yi mata amsa kuwwa a kunne,a dazun sam hankalinta bai nasu muhimmanci ba sabanin yazun data dage kai da fata sai ta tuna dukkan wani abu da nenen ta fada,ficewar da adnan yayi da sauri daga gidan
''taurin ran abdallah ne duka ya jawo mana halin da muke ciki,idan da ya mutu salin alin da mun huta''
maganar nenen ta qarshe kenan sanda take surkuda mata allurar bacci
taurin ran abdallah?
ya mutu?abdallah kenan abdallah na?

tambayoyin sun mata tsauri da yawa,saidai data hada dukkan abubuwan dake wulgawa cikin idanunta sai taso sansano qamshin wani abu wanda ya sata ta qarasa shugewa rudani na haqiqa,ita kadai ke fadin duk inda abdallah yake sai ta nemoshi
ba zata iya rayuwa,cikin duniya ba cikin salama ba tare da tasan ina abdallah yake ba,wanne hali yake ciki?,a kullum addu'arta shine Allah yasa ta riga abdallahn mutuwa,zata masa addu'ar samun juriya da qarfin gwiwa kan rashinta,sabanin ita da bata da wanda zai mata wannan addu'ar,ta yaya zata jure rasa abdallah da mahaifinsa ta iya ci gaba da ingantacciyar rayuwa cikin dunuya

A hanzarce ta kima sashenta ta wuce bedroom dinta kai tsaye,kayan jikinta ta sauya ta dauki muqullin motarta,haqiqa dukkanin wani zatonta game da yadda rayuwarsu ta cukurkude lokaci guda ra dorashi ga nene,duk da ta sani wani bawa,bai isa ya dora maka wani abu ba face da izinin ubangiji amma akwai silar komai,nene ita ce sila haka zuciyarta ke gaya mata
ta bude motarta ta shige tana qoqarin tashinta usaini ya qaraso
''hajiya zaki fita gasu ibrahim kuma na zuwa''ta dubeshi kana tace
''idan sum qaraso kowa ya koma bakin aikinsa na maidashi,gobe idan Allah ya kaimu zamu tattauna da ku duka''ta samu damar fada sakamakon ambaton Allah da take yi cikin zuciyarta wanda hakan ya taimaka qwarai da gaske wajen zaunar da nutsuwarta cikin jikinta
Allah yana fada cikin alqur'aninsa mai girma
(KU SAURARA,TABBAS DA AMBATON ALLAH KADAI ZUKATA KE NUTSUWA)
Babu inda yafi dacewa ta dosa irin gidan kawunta wanda yake a yanzu tamkar mahaifi a gareta,mutum ne mai nutsuwa qwarai da fahimta babu bata lokaci ta fice a gidan kanta tsaye ta nufi can

🍃🍂🍃🍂🍃🍂

Ranar wunin gaba daya akanta ta qare tana zaune qofar gidan ta tasa uban ruwan dake ambaliya agabanta,tun tana zuba ido taga ta inda jirgin agajin su nene zai dira har ta sare baki daya,ta sake laluba wayarta da niyyar kunnata ko zata iya kira saidai sama ko qasa ta nemi wayar ta rasa,wasa wasa ta miqe ta hau zazzage zazzage saidai ko qyallin kalarta bata hango na,abu kamar wasa sai da ta zazzage dukkan akwatunanta amma babu ita babu alamarta,dariya taji ana qyqyata mata ta dago kanta da sauri,malam na hayi ta gano yana keta ruwan yana takashi da qafafunsa tamkar wanda yake kan tsandauri ba ruwa ba,ya qaraso gabanta ya ya daga hannunshi sai ga wayar
''duk abinda kike aiwatarwa yau na sani,kina tsammanin kubuta daha hannu na ne?,to kinzo gidan da idan aka shiga saidai a fidda gawarka,ina jinku habiba ta baki labarin abunda ya faru da ita ko?,wato wanna bai zamamiki izina ba ke yar masu taurin kai,bari na baki shawara qwaya daya a taqaice,ki fidda sa dan komawarki gida muna tare mutu ka raba,koda yan uwanki ma sunzo basu isa su gane hanya ba haka zasu qaraci walagiginsu su koma,mune maganin makwadaitan mata irinku masu butulcewa hanyar Allah,kunqi Allah muma munqi shi kinga kenan mu muka fi dacewa da ku,kin riga da kin zama matar malam na hayi na zama mijinki''

cikin zafi ta bude bakinta da niyyar yaba mishi rashin kunya,bakinta cike yake fal da maganganu masu zafi da takeson ta gaya masa,raahin mutunci ta nado mai uawa zata masa wanda tana tsammanin tunda yazo duniya ba'a taba yi masa makamancinsa ba,da saurinsa ya daga hannunshi na hagu take bakinta ya rufe qam
''daga yau ba zaki sake magana ba sai idan na baki izini ko naso,ba zaki sake min musu ba ko wani ma ba ni ba''kai kawai take gyada masa kamar bawa da ubangidansa
''wuce ki tafi dakinki,daga gobe zaki amshi girki,yau na daga miki qafa kiyi jimamin rabuwa da gida irin na amare iya na yau kawai''nan ma kai ta gyada masa ba tare da tace komai ba ta tsugunna zata kwaahe akwatunta
''shiga ciki kawai,kafin ki isa su sun riga ki isa''nan ma kai ta gyada kana ta juya sum sum sum ta shige cikin gidan,ya isa gaban kayan ya dafa su take suka bace a gun bat,wata magaukaciyar dariya ya saki yaba yiwa kansa kirari kala kala,sai kuma ya dinke fuskarsa cikin yan sakanni tamkar bai taba dariyar ba ya juya ya shige cikin gidan

🍂🍃🍂🍃🍂🍃

Su biyu ne ita da inna wuron zaune qarqash bishiyar lalle take kwabawa innan wanda zata saka a qafarta saboda dawiqar tsoho alhaji gobe daga qasa mai tsarki,har mamakin tsohuwar take bata ganin tsufan kanta ko na mijinta,adonta take daidai shekarubta wanda zai burge mijinta,dazu ta saka sabulu mai qamshi ta wanke kanta tas tace maryam din zata yi mata kitso

Tun kafin ta dago ta jiyo muryoyinsu,gabanta ya soma faduwa don ko kusa ko alqma bata sha'awad ta bude ido taga yarinyar,haka suka shigo cikin gidan tana tura wheelchair din suna hira abinsu,tunda ta dago kanta suka hda ido da abdallah ta dauke kai bata sake marmain kallonsu ba,miqewa tayi tsam ta isa bakin rijiya ta wanke hannunta sai tayi shigewarta daki duk da ba wani abun zatayi cikin dakin ba,tsaye tayi tana jin uadda suke hirarsu su ukun sun ma maisheta tamkar wata bare,kada ma abdallah yaji labari wanda a a yanzun ya koyi zuwa masallaci daga nan idan yaga damq yayi zamansa qofar gidan nenen suyita hira da samarin qauyen,idan kuwa ya tashi dawowa to mawuyacibe ka ganshi ya dawo shi kadai ba tare da mero ba,duk yadda taso danne zuciyarta da hanata jin kishin abdallah abun ya faskara yafi qarfinta,daga qarshe ta yiwa kanta hukunci ta yarda tana kishin abdallah saboda amanarsa da mami ta barta amma ba wai don so ba

Ko daya bata ji shigowarsa ba sai gyaran murya da ta ji a bayanta,ta dan waiwayo da sauri wanda hakan kadai ya isa ya gaya maka tunani takeyi
''excuse me madam''ya fada yana nuna mata hanyar da zai wuce din ba tare da ya kalli fuskarta ba
sai ta janye gefe ta zauna saman kujera ya qaraso ya wuce bangon dakin inda laptop dinshi ke ajjiye,tayi qasa da yawa hannunsa bazai iya kaiwa ba,tayi zaton wannan karon zai nemi taimakonta sabida gaba daya yanzun duk abinda hannunshi zai iya da kansa yake yi,ta manta yaushe rabon da ya sata wani abu,ko kwanciya ce ko dorashi saman kujerarsa mustafa ke taimaka masa

Bata ankara ba taji yana kiran mero,cikin rawar jiki ta qaraso dakin ganin maryam sai jikinta ya mutu kuma,ta soma rabe rabe
''shigo mana,wancan computer din zaki dauka min da ita zamu tafi saboda hoto ko?''sai ta washe haqoranta ta rave maryam ta wuce ta dauko conputer tana qare mata kallo din ba qaramin burgeta tayi ba ta miqa masa suka fice a dakin,wani dubqulallen abu ne ya tokare mata wuta ya hanata ta hadiyi koda yawu ne,tana jiyo su suna yiwa inna wuro sallama sun tafi rafi sai kawai ta qarasa zamewa ta kwanta gaba daya kan kujerar tana hawaye sosai

''meramu fito,ki saka min lallen nan mana,so nake na cireshi kafin mangariba ki kitse min kan nan,don malam alhaji saukar hantsi zaiyi''ta jiyo inna wuro tana fada,da zata iya da ta cewa inna wuron ba zata iya fitowa ba ta saka da kanta,tilas ta miqe ta goge fuskarta bayan ta sake saka kwalli duk don kada innar ta gane ta fito
Chapter 68 · 0% Book details