← Book details Abadan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 103

Sashe 2

Abadan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sanye take da pakistan riga da wando wanda rigar tasa ta kai mata har gwiwa,dan kwalin pakistan dinne daure a kanta,duka hankalinta ta tattarashi kacokam kan wayarta da tayi googling din wasu sabbin girke girke,shirun da dakin da ma gidan baki daya da yayi shi ya qara mata nishadi da fahimtar abunda take karantawa,

sallamar da ta jiyo anayi cikin tsakar gidan ita ta ja hankalinta,ta sauke wayar tana amsawa tare da cewa ''a shigo''
mai sallama ta sake maimaitawa lokacin da take shigowa rumfar tasu,da sauri maryam ta sauke wayar a gefanta fuskarta dauke da murmushin farinciki wandayayi sanadiyyar bayyanar dimple dinta ta miqe
''radiya..saukar yaushe kenan mutanen south africa?''
harara wadda aka kira da radiyan ta cilla mata
''hmmm,babu wani nan,wlh baki da abinda zaki kare kanki da shi,yanzu ma ni ba gunki nazo ba,mama na kawowa jikanta ta ganshi''
''oh ni maryama,laifi baya qaremin,me kuma nayi''ta fada cikin murmushi da dafe kai
harararta dai ta sakeyi''kinfi kowa sanin laifinki maryam,sati na guda da dawowa qasar nan amma ko mai kama da ke ban gani ba,ina dira nigeria kece ta farko da na fara yiwa tex amma ko matsayin reply ban samu ba''

''yanzu dai yo haquri don sonki da annabi ki zauna tukun,don mama bata nan ta tafi kitso''ta fada tana karbe kyakkyawan baby boy din dake sabe a kafadarta,tare suka zauna idon maryam na kan yaron''masha Allah laquwwata illa billah fadil''yana kan kadarta ta shiga kitchen din su ta dauko mata ruwa da lemon sobo cikin fridge din da daqyar ta shawo kan mama da dadin bakin hindatu aka siyoshi suke lemon siyarwa a kuma fita kunyar baqi idan anyi

''bismillah''tace da ita bayan ta tsiyaya mata lemon
''bani dana kawai na wuce''
''haba sister,kada fa ayi mana dariya a ganmu a rana''
''ke kika jawo hakan ai''
''kinsan Allah banga saqonki,ki yarda dani bani da lokaci wallahi yanzu isashshe idan ba weekends ba saboda aiki''
da qyar ta samu ta shawo kan radiya bayan ta mata alqawarin zuwa mata a wannan weekend din wanda daga nan suka fada hirar duniya

radiya ta ajiye glass cup din bayan ta kalli maryam
''maryam har yanzu dai batun aure shiru?''sakin ajiyar zuciya tayi sannan ta tabe baki
''hmmm,barni kawai radiya,samun miji na gari yanzun ya zamo wuya,mazan yanzu duka 'yan garari ne,yawancinsu ba aure ke kawosu gurinki ba''
''anya maryam,bana manta fa yawan samarin da kike da su tun muna school''
''radiya kenan......manta da wannan,na fada miki yawa yawansu ba don Allah suke sonki ba,sun lallabo ne kawai su kwashi abunda suka kwasa na rasa wannan masifa kamar hadin baki?kamar ni kadai sukewa haka,ke dai ki sani kawai a addu'a radiya''ta qarashe maganar muryarta na dan rawa alamun kuka keson zuwa mata
''shikenan maryam,insha Allahu na miki alqawari ba zan fasa sakaki cikin addu'o'ina ba,komai yayi farko yana da qarshe''

a hankali suka fada wasu hirarrakin nasu a haka maman ta cimma su,tunda ta dauke fadil bata dawo da shi ba sai da zasu tafi,sabulai ta bawa radiyar sinqi biyu da turare,hannu biyu amsa tayi mata godiya sannan maryam ta amsheshi ta biyo radiyan qofar gida don raka ta
''ke da nasir fa muka zo''
cikin mamaki take kallin radiyar''amma baki da mutunci,ki bar bawan Allah a mota duka lokacin nan yana zaman jiranki''
fuska ta yatsina''rabu da shi,fada mukayi da shi sulhu yake nema shi yasa''
''Allah ya shiryeki radiya ''abunda ta samu ta iya fada kenan don sun qaraso gaban motar''

gidan gaba ta shige ta dora mata fadil saman cinyarta suna gaisawa da nasir din
''munfa yi fushi maryam gaskiya''
sassanyan murmushinta tayi''to ayi haquri tunda na wanke kaina next week ina tafe insha Allahu ranan sunday''
''to Allah ya nuna mana''
sallama sukayi ta koma cikin gidan radiyan na jaddada mata ta cika alqawari fa

tana cusa kai gidan suka ci karo da *BINTA*
dauke da botikin awara zata fita inda aka fi kaurin,maryam dince ta fara ja da baya don tasan bata qi ta bangajeta ta wuce ba,duk da hakan ma dai bata tsira ba daga tsaki da harar da qanwar bayanta ta saba jifanta da su ba koda zasu hada hanya ne sau miliyan

ta rasa me ra tsarewa yaran da iyayensu,gaba daya anbi an cika zukatansu da qinsu,qannenta ne duka amma babu daya dake ganinta da gashi,saidai duk da haka rashin mutunci wani yafi na wani
ga tsantsar rashin tarbiyya da qin karatu da aka dasawa zucoyoyinsu,ta rasa wannan wacce iriyar rayuwa suka zabawa kansu,da wannan tunanin ta qarasa falonsu ta zube saman kujera tana rowon Allah daukinsa kan halin da take ciki

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚✍🏻✍🏻✍🏻
[9/17, 12:49 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖💖
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖 *ABADAN*💖
🌺💖🌺💖🌺

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
🌺💖🌺💖🌺💖🌺
🌺💖🌺💖🌺
🌺💖🌺
🌺💖
🌺

▶3⃣

sanye take da material silk dark pink wanda aka yima ado zane na qaqen flowers manya,yayin da ta yane kanta da mayafi baqi tayi rolling dashi wanda ya maisheta tamkar jinsin larabawa,qaramar jaka ta sagale a gwiwar hannunta sai baqin toms mai kyau,sosai shigar tayi mata kyau tamkar bata da wata matsala a rayuwarta

a rumfa ta tadda mama tayi mata sallama tace mata a dawo lafiya ta gaida fadil da mamarshi,suna zaune a tsakar gidan kamar ko yaushe ko wacce ta maida hankalinta kan kayan sana'arta,wanda da zaki tambayesu suk cikinsu babu wadda zata iya gaya miki taqamaimen inda yaranta suke,sana'arsu ta fiye musu komai

da sauri ta fara qoqarin ficewa daga gidan don bata fatan daya daga cikinsu ta,ganta balle ta jefeta da kalmar da zata bata ranta,saidai duk iya saurinta bata ci nasara ba sai da huwaila ta ganota
''uhmmm,mutanen burtali,an fita kenan''
bata fasa sauri don ta fice a gidan ba kamar yadda bata ko waiwayo ta dubesu ba

cikin soron sukayi kacibus da *AZARA*,qanwar ta ce ta hudu wadda tayi aure da yaranta uku,ba laifi mijinta na iya bakin qoqarinsa duk da wasu abubuwan bai iya dauke nauyinsu,sai kuma Allah ya hadashi da mace mai izgili izza da rainuwa,azara akwai rainuwa da izgili saidai ba laifi rashin kunyanta da sauqi akan ta sauran yaran,tunda ko babu komai idan sun hada zata tsaya su gaisa koda zata jefeta da habaici a fakaice

yanzun ma hakance ta kasance,fuskar maryam din fadade da murmushi ''maraba da mutanen fanshekara(unguwar da take aure)''ta fadi tana miqa hannu zata amshi yaron axaran yaqi zuwa saboda dan banzar qiwar da yakeyi,azaran tace
''hmmmm,sannunku kuma''
''azara yaron nan qiwa yake haka?''
''ko ba ya qiwa aike yayi miki tunda ba ganinki yake ba,mu ko nsmu gidan ba'a zuwa saboda bamu da komai''
murmushi maryam tayi,don ta fahimci inda tasa gaba
''ko daya ba haka bane azara,kinsan bani da lokaci sai weekends,to su din ma sai wani zarafin ya shigo ya cinye wunin naka duka''ta kawar da maganar don kada tayi nisa ta hanyar cewa
''ina sauran yaran?''
''kunun aya ne bai qare ba na,barsu su qarasa saidawa don kada ya lalace shi yasa ma ban taho da su ba''

wani abu ya tokare maryam,wato irin rainon da aka mata shi zata yiwa nata 'ya'yan,a maimakon ta bata amsa da sun tafi islamiyya don a yanzu lokacinta ne sai tage gaya mata ta barsu gun talla?,du du du yaran nawa suke?,kamar tayi mata magana kuma sai taja bakinta ta tsuke don kada cibi ya zama qari
''sai ina kuma?''azaran ta tambayeta bayan ta gama qare mata kallo
''wallahi zani gidan raliya ne''
''hmmm,babban goro sai magogin qarfe,su ai sun isa ayi da su din,bari na qarasa ciki ko,sai kin dawo''
danne zuciuarta tayi ta murmusa
''to shikenan,idan na dawo na tadda ke to''
''o'o,anya zaki tadda ni kuwa,wannan fitar taku ta manya wa yasan ranan dawowarku''
''to ki gaida gida''
''gida zaiji''

tana tafe a layin zuciyarta cunkushe da tunane tunane,hasbunallahu wa ni'imal wakeel ta dinga karantawa har ta iso titi,akwai qarqncin motocin haya kan titin nasu ko kuma ace kusan duk wadda tazo cike take da 'yan makarantar boko da suke dawowa gida,kusan motoci uku ne suka tsaya don bata lift saidai ko kallo basu isheta ba,hakan,na yawan faruwa da ita kasancewar unguwar nasu na maqotaka da unguwar nasarawa G R A,duk sanda hakan ta faru takan yawaita neman tsarin Allah,sannan takaici mamaki gami da tsoron maza kan sake yawaita cikin zuciyarta,basu da burin da ya wuce suga sun samu damar da zasu shiga rigar mutuncinki su wuce su barki babu batun aure

da qyar ta samu wata da yara yan makaranta biyu a ciki,ta masa kwatance inda zai ajjiyeta

cikin murna raliya ta tarbeta,cikin falonta suka zube bayan ta cikata da kayan ciye ciye suka hau hirarsu da bata qarewa fadil na bisa cinyarta,
''kinga kawo fadil din na riqe miki shi tunda yayi bacci ki samu kici wani abun,idan ba haka ba bazai barki kici komai ba''
''a'ah qyalemin shi''
cikin haka wayar raliyan ta soma tsuwwa,ta cirota ta duba screen din tana fadin ''abban fadil ne''
magan sukayi ta tsawon minti biyar sannan ta kashe tana duban maryam bayan ta miqe
''yace yana miki sannu da zuwa,bari,na saka miki wani film ya dan debe miki kewa ni shiga kitchen ya kamani,abban fadil ne zaiyi baqi''
''haba kema raliya naji zancan shiga kitchen kuma na zauna,ai kinsan sai anyi da ni''
''sannu uwar madafa''ta fada cikin zolaya
''na karba,ko kin manta kan abinda na samu degree kenan''
''wannan gaskiya ne,bani fadil din to na kwantar da shi sai mu wuce kitchen din ko?''

qarfe hudu da mintina ashirin suka kammala,lafiyayyen girki ne wanda maryam ta gwada basirarta akai,ita kanta raliya komawa tayi gefe tana kallonta don bata zaci qawar tata takai haka ba,biyar saura ta suna falo,ta soma hada kayanta don tafiya gida ''amma diyana(haka suke kiranta wani lokaci a makaranta)ki sake wanka mana wannan aiki da kika sha''
''ai dole ne,amma fa idan na isa gida''
''ai ko wlh anan zakiyi''
murmushi tayi wanda har dashashinta sai da ya bayyana
''kinsan dai bana wanka na maida kayan da na cire,ni kuma ban taho da spare ba''
''tsarabarki ta south africa tana nan,saiki zabi daya a ciki kisa''
duk wayon,maryam sai da raliya ta sata yin wankan ta kawo mata ledar tsarabar ta zabi doguwar riga guda daya da tasha adon jajayen dutsina masu yawa da sheqi
Chapter 2 · 0% Book details