Sashe 41
Abadan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
al'adu. kallo daya zaka yiwa matar ka tabbatar da 'yar sudance gabanta da bayanta,saidai mamakin da maryam tayi yadda hausa radam ta kama bakinta yanayin karyewar hatshen bw kawai zai nuba maka ba yarenta bane ara tayi ta yafa,ba abun mamaki bane jin yaren gausa bisa harsukan wasu al'umma ko qabilun da ba ahalin hausa ba,saboda yaren hausa yare ne sha kundum da ya fantsama lungu da saqo na fadin duniya,kusan a yanzu shine yare na biyu ko na uku da akafi amfani da shi,babu inda zaka tsoma qafarka a duniya ka rasa wanda ya iya ko yakejin yaren gida ne babba mai bangare biyu bangare daya na matar ne daya bangaren kuwa harkar sana'arta kawai take gudanarwa,gyaran jiki gyaran gashi lalle ne kayan gyaran jikin na mata turaruka na ruwa dana ice da humra na tsuguno harda na wanka,kai hatta da kitso idan kana da buqata akwai mai yi maka,yadda maryam taji suna hira da matar tana tambayar mamin bayan saduwa ya fahimtar da ita lallai sun san juna dama can da mami,tunda har taji tana tambayar matar wata najwa tace taje daarfur sai gobe zata dawo,hajiya laila ita kewa mami irin wadan nan gyararrki zamanin alh abdulkareem mai nasara nada rai,gayu kam da gyaran kai mami ta yishi lokacin da mijin nata ke raye shi yasa ta zama ta gaban goshinsa,duk da a yanzun ma bata saki gayunta ba saidai ta daina wasu abubuwan tunda babu mijin cikin kwana uku matar ta fara tsuma maryam,gyara take mata bana wasa ba tunda ta san haj bintu akwai sakin hannu idan harka ta hadaku,wani irin daddadan qamshi ta zaunar a jikinta wanda ko zama tayi a gu sai qamshin ya nasheka,farar fatarta ta canza yanayi farin nata ya saje armashi kyau gami da daukan hankali,sati guda ana mata gyararrkun taki wanne b'angare kafin suyo gida nijeria bayan haj laila ta hada muta wasu hade haden da zata ci gaba da amfani da su koda bayan bikin ne bayan sun koma boyonta mami ta dinga yi,tuni ta daina komai a cewarta bataso nan da kwanakin da suka rage biki wani abu na gyaran da akayi mata ya samu naqasu,baaba uwani ita ta goyi bayan mami tayi uwa tayi makarbiya take komai sunyi waya da mama da hindatu,mama cewa tayi sai tazo godiya don sam bai canci ta yiwa mami godiya iya ta waya kadai ba,amma da maryam ta sanar da mamin sai tace sam wallahi kada tazo,idan kuwa tazo din to ta nuna ba ita ta haifi,maryam ba,karamci da mutuncin mamin sunyi yawa har suka sa mama ta rasa ma me zata ce ko ta saka mata da shi?,hindatu amarya kam babu zama,ita da qawayenta ke gudanar da komai,don hatta da rabon kati su suka dinga yi,saboda mami ta riqe maryam tace babu yawon rabon iv da zata ta bata jikinta,ganin komai take tamkar a mafarki,wai tau ita maryam ce ake kira da sunan *amarya*,lallai babu wani abu da yake tabbatace sai mulkin ubangiji bata fidda ran ganin irin wanan lokacin ba saidai koda wasa bata taba kawoshi nan kusa ba haka,dukka kayan da zata saka raliya ta fidda takai dinki,duk wata sabga da ya zamto ita zatayi raliya ta tsaya kan komai ita keyi kan jiki kan qarfi kamar a itace maryam din,kyakkyawan amincin da aka gina shi bisa turbar gaskiya da amana kenan,yakan iya kai ku zama qasan inuwar al'arshin ubangiji ranar da babu wata inuwa sai taahi Biki ya rage saura kwana uku da daddare tana gurin baba uwani ta kai mata wasu kaya da take son bata ita da yan jikokinta kiran hindatu ya shigo wayarta ''kinyi tsada adda maryam,mami ta tsaya miki''inji hindatu cikin salon tsokana ''kema mama ta tsaya miki ai ya akayi ya gidan'' ajiyar zuciya tayi ''lpy lau,gida alhmdlh don har wasu daga 'yan gaya sun fara sauka,saidai ta wani bangaren ba lafiya lu ake ba''sai da gaban maryam din ua tsinke ya fadi,cikin sakonni zuciyarta ta fara raya mata faruwar abubuwa marasa dadi masu yawan gaske kuma duka akanta,muryarta na rawa t tambayeta mai ya faru dariya hindatun ta qyalqyale da ita ''kwantar da hankalinki adda mana,na gaya miki mu lpy muke alhmdlh,bangaren da babu lafiyar su inna huwaila ne da baaba hadiza,kinsan watan baqincikinsu ya kama,yanzu haka jamila na daki ita da sauran yan uwanta anata mata ruqiyyar banza da wofi ta tada aljanun qarya,wai wlh indai na auri jabir sai ta kashe kanta,ni kuwa nace shashasha ki kashe kan naki mana kanki da uwarki kika yiwa asara,ita kuwa inna huwaila sai zirga zirga take ta fita aje ta dawo ta kasa zaune ta kasa tsaye,zuwa dare saiga aminiyarta uwani sai ji mukayi tsakiyar tsakar gida tana cewa,ke kika kawo kanki kikace na kaiki gun bokan nan bani na jawoki ba,don aiki bai ci ba kuma zak nemi tijara ni gaban kishiya?,to ai ramuwar gayya tafi ta gayya zafi shi yasa na biyoki ayita mai kankat kema kowa yaji,mugun qullin da kika so qullawa,ta fayyace duk abinda suka qulla din sannan ta dora da fadin,bola kuma na bogi ne kudi kuma muni babu yadda kika iya,aminad da kuke baqinciki da ita daga ke har hadizan ai ta fiku,yanzu gashi data miqawa Allah kukanta ta jadiye baqicikinta na shekara da shekaru Allah ya yaye mata damuwarta ba tare da tayi hasarar sisin kwabonta ba,ku kuwa haihuwar asara babu kudi babu biyan buqata ga asarar imani,sallolin kwana arba'in a ajejere kun rasa ta kusan kwana dari bakwai,amina Allah ya sanya alkhairi ya tsone idon maqiya,kuma wallahi ni da ku dukanku ke da hadizar shege ka fasa,naci uwar mace a iya tijara da ramuwar gayya,duk kuma wadda take jin ta haifu da jini uwarta ta haifeta ta fito ta tanka wai in gaya miki adda saiga inna huwaila ta fito da borin kunyarta waisai sun daky wallahi bugu daya uwale rayi mata sai gata tayi plate a qasa''hindatu ta fada tana sheqa dariya ''wai kuma ta sumewa mutane jadiza tayo kanta wai huwaila kinci amanata ta hau dukanta,lubabat u kuwa itama tayo kan,hadizar ke in taqaice miki labari kowa sai ya ahigarwa uwarsa gida ya zama na wrestling,ina ta laluben wayata in miki vedieo don,kada ayi babu ke saiga babamu nan ya shigo shi ya raba cakwakiyar,kowacce da dogon bakinta ta taho zungi zungi zata yi masa bayani don ya bata gaskiya yadda suka saba yace babu wadda zai saurara,wanna ya ishesu ishara,mama ce......'' ''haba aku mai vakin magana,sai kace na kunna freedom?''inji maryam tana murmushi bayan ta katse hindatu ''kefa adda ba'a miki abun arziqi'' ''to ai wanna ba baun arziqi bane'' ''wallahi nikam abun arziqi ne tunda na gano tashin hankalinsu ranar kawo lefenki,da farko da suka ga anfara shigowa da qananun akwatuna har sun fara yada habaici,da suka ga dai shigowara ke sai suka fara lissafi suna tabe baki,qarshe da suka lissafi akwati ashirin da hudu cif manya da qananu sai aka nemesu aka rasa,inna hadiza na quryar daki suna safa da marwa huwaila kuwa anyi tsamo tsamo an rasa na kamawa,ana cikin haka saiga nawa lefen akwati sha uku,qarshe saiga inna hadiza na dora hannu aka tana xunduma ihu huwaila a taya ta da sharbe hawaye da fyace majina,a gaban idon mutane fa abin mamaki da dariya,ko kunya babu''ta sake qyalqyalewa da daria don tuna abun da tayi ''Allah ya rufa asiri,yanzu ya abubuwa suke tafiya?'' ''komai na tafiya daidai,amma wlh adda kizo ki kalli lefanki'' ''kai hindatu,me kike ci na baka na zuba,abinda za a ajjiye maka su a dakinka wataran har sai ka gaji da su'' ''to ai shikenan,dazu yaya abdur rahim yazo ya kawo kudin dinkunanki,dazu naje gidan adda raliyan na kai mata,har ta fara karbo wasu ma ta bayar an goge miki,gaskiya adda raliya tayi wallahi,akwai zumunci tayi qoqari'' ''gaskiya ne Allah ya bar zumunci ya saka mata alkhairi'' ''ameen'' nan take aya mata kayan gadonsu da aka siya duka an hada mata sun zama biyu kenan har kayan kitchen dinsu,madyam din tace yayi babu laiciya zama dakin baqi kenan da naki dakin tunda kince shima jabir din ya zuba naahi furniture din,jibi insha Allah nima zan taho gidan gaba daya ai,ki gaida mama'' ''Allah ya kaimu,zata ji insha Allah'' daga haka dukkaninsu suka katse wayar *mrs muhammad ce* [9/17, 12:54 PM] 80k: 💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 🌺 *ABADAN*🌺 💖💖💖💖💖💖 🌺🌺🌺🌺🌺🌺 💖🌺💖🌺 💖🌺💖 🌺💖 💖