← Book details Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 28

Sashe 9

Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yi haƙuri hankalina ne ya yi gaba....uhmm ammm ni fa dama wayarka naso na ara ko ta Nawwarah sai na ga zan takura muku. Bayan haka ma ni bana son na yi aro azo ana dizga ni a mutane. Yi sauri ka kashe min ɗaya na wuce."

Babu ɓata lokaci kuwa Usman ya hau yi mata hotuna,har sai da ta gaji ta gudu. Tafe take tana yanga tana karya ƙugu kamar ƴar wani hamshaƙin a layin. Tana zuwa kan layin su Yasmin da yake akwai kwalta shimfiɗe saboda zamowarsa layin masu hannu da shuni sai ta sauya taku. A hankali ta ɓalle jakarta ta fito da wayar da ta sato ta riƙe a hannu tana yanga. Duk inda ta wuce taron maza masu zaman bakin titi sai an bita da kallo. A haka ta isa gidansu Yasmin,tun daga gate ɗin gidan ƙirjinta ya fara wani irin bugawa da ta rasa dalili. Hannu ta sanya a ƙirjinta ta dafe tana ƙoƙarin daidaita kanta. Da ƙyar Nasibah ta samu nutsuwa ta kalli motocin dake gefe da gefen titin gidansu Yasmin. A hankali take taku har ta isa bakin gate ɗin gidan. Tsayawa ta yi a wajen gate ɗin ta juya tare da zaro wayar hannunta ta ɗauki kanta hotuna guda biyu masu kyau tana murmushi. Tana gamawa ta riƙe wayar a hannunta ta shiga gidan tana rarraba idanuwa. Idanuwanta na sauka akan Yasmin da taron mutanen dake wajen gabanta ya yanke ya faɗi idanuwanta suka firfito waje kamar za su faɗo ƙasa..........
[9/19, 9:21 PM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA.

NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️

PAGE 7.

Gaba ɗaya idanuwan mutanen wajen sai suka koma kan Nasibah dake takowa zuwa cikin gidan a hankali kamar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki. Tana zuwa daf da mutanen Yasmin ta tafi wajenta cike da murna ta kama hannunta ta juya tana kallon ƴan'uwanta za ta yi magana. Hannu Yayarta ta ɗaga mata ta ratso cikin mutane ta iso gaban Nasibah da jikinta ya fara rawa ta mayar da hannunta mai riƙe da waya bayanta tana ja da baya a hankali. Yayar Yasmin na isa gaban Nasibah ta ɗaga hannu ta wanke ta da wani irin mugun mari. Cike da tashin hankali Yasmin ta damƙe bakinta,nan take idanuwanta suka hau zubar da ruwan hawaye. Cikin kuka ta ce.

"Haba Yah Yusrah! Ƙawata ce fa da nake ta baku labarin ta matsu ranar nan ta zo itama a yi....."

"Ki tambaye ta me ta yi na mare ta mana. Mara kunyar banza da wofi."

Yusrah ta mayar da kallonta kan Nasibah dake zubar da ruwan hawaye kamar da bakin kwarya. Tunda take a gidan duniya bata taɓa tozarta da muzanta ba irin wannan rana. Da wanne ido za ta dubi mutanen wajen idan Yusrah ta gama fallasa abinda ta yi a gaban kowa? Ya Yasmin dake ta faɗi tashin ganin ta mallaki duk wani luxury abu ta zo bikin saboda kada a rainata za ta ji? Ashe haka mutum yake shiga tozarci da muzanci idan aka kama shi ya yi sata? Wani irin kuka ne mara sauti ya kuɓuce wa Nasibah. Danasani da nadamar yin abinda bata taɓa aikatawa ba tun yarintar ta ne ya tattara ya lulluɓe ta. Ji take yi ina ma tarazon dake tsakiyar gidan yaa dare ya nitsar da ita ya bi ya kulle kansa da ita a ciki?

Kafin wani ya sake cewa komai a wajen suka ji muryar wani a bayansu yana faÉ—in.

"Ke Yusrah da ƙawar Yasmin ku same ni a ƙaramin parlour."

Ƙwafa Yusrah ta yi,domin ta riga ta gama fahimtar abinda Yayan nasu yake nufi,idan ta kuskura ta saɓa umarninsa zai yi mata hukunci. Dan haka rai a ɓace ta juya ta yi hanyar da mutumin ya bi. Cikin sauri Yasmin ta kama hannun Nasibah ta ja ta har zuwa bakin ƙofar wani sashe dake gidan ta buɗe ƙofa ta tura ta ciki. A hankali ta ce.

"Ki yi sauri ki bi bayanta kafin ta ɓace miki."

Kamar wadda ake tunkuɗawa haka Nasibah ta hau bin bayan Yasmin,sai da suka wuce parlour guda ɗaya babba mai ɗaki biyu a cikinsa,sannan suka shiga wani madaidaicin parlour ƙarami mai ɗauke da zallan kujeru da manyan hotunan ahali guda biyu a jikin bango. Tsugunnawa ta ga Yusrah ta yi a parlourn tana cika tana batsewa tare da zabga wa Nasibah harara kamar idanuwanta za su faɗi ƙasa. Sai da suka kai kimanin mintuna biyar sannan ya fito yana goge glass ɗinsa da ƙaramin tsumman dake cikin gidan glass ɗin. Yana gamawa ya saka a idanuwansa ya zauna a kujera mai cin mutum ɗaya ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.

Kallon Nasibah ya yi,bai san lokacin da ya saki wani irin murmushi mai sauti ba;har sai da suka ɗaga kai a tare suka kalle shi. Nan take gaban Nasibah ya yanke ya faɗi har sai da ta dafe ƙirjinta. Girarsa ɗaya ya ɗaga mata ya ce.

"Nansy Ƙaya ko?"

Da sauri Nasibah ta sauke kanta ƙasa ta hau wasa da bayan wayar Yusrah. Numfashi ya sauke kafin ya ce.

"Miƙa mata wayarta ki bata haƙuri. Kuma daga yau sai yau kada ki sake gangancin ɗaukar abinda ba naki ba;domin ba dan na san da case ɗin ba kuma Allah Ya sa ina gida da police station za su kai ki. Kin ma san tsadar wayar da kika ɗauka?"

Cikin sauri Nasibah ta ciro Sim card ɗin Yusrah zata saka mata,tana yi tana girgiza masa kai. A hasale Yusrah ta ƙwace wayarta da Sim card ɗin tana ƙwafa. A hankali Nasibah ta ce.

"Don girman Allah Yah Yusrah ki yi haƙuri ki yafe min abinda na yi,bansan alaƙar ki da Yasmin ba da ba zan taɓa miki waya ba. Kuma na rantse da...."

"Save it please. Ƙarya kike yi,na san ba yau kika saba ba ai kawai...."

"Allow her to finish apologizing please."

Nan take Nasibah ta marairace fuskarta ta kalli Yusrah idanuwanta na zubar da hawayen nadamar abinda ta aikata ta ce.

"Na rantse da sarkin da yake busan numfashi ban taɓa sata ba,ban taɓa ɗaukar abun kowa ba ko da kuwa iyayena ne. Wannan ɗin ma a tawa wautar ba sata na yi ba aro na yi,ina da niyyar idan aka gama bikinki sai na mayar da wayar saloon na gudu. Na tabbata mai wajen za ta nemo ki ta baki. Don Allah ki yi haƙuri na ɓata miki rai ba zan sake ba."

Jikin Yusrah ya ɗan yi sanyi,zafin Nasibah da take ji a baya ya ɗan ragu,amma har a wannan lokacin bata gamsu cewar Nasibah bata taɓa sata ba. In ma bata saba ba,to akan wannan da yiwuwar ta ci gaba da yi.

Gyaran murya ya yi ya kalle su ya ce.

"Duk wanda aka cuta shi ake ba wa haƙuri,lil sis please ki yafe mata. I will make sure daga yau har abada bata sake taɓa abun kowa ba,ina so ki rufa mata asiri kamar yanda Allah Ya rufa miki asiri ya baki arziƙin da zaki sayi irin wayar nan ko guda nawa kike so. Ki tashi ki je ana jiranki."

A tare suka tashi za su tafi suna ta yi masa godiya. Cikin wani irin yanayi ya wurga wa Nansy kallo sai ta samu waje ta zube a wajen ta sadda kanta ƙasa. Yusrah na fita Yasmin ta hau tambayarta ina ƙawarta. Cike da takaici ta kalli Yasmin ta ce.

"Daga yau sai yau kada ki sake gayyato mana wannan Æ´ar matsiyatan gidan nan,kuma ki tabbata tana fitowa daga sashen GiÉ—aÉ—o kin saita mata hanya kin ji na faÉ—a miki."

"To Yah Yusrah me ƙawata ta yi miki da kika tsane ta haka?"

Tsaki Yusrah ta yi ta shige gida ta bar Yasmin na saƙe-saƙe a cikin zuciyarta.

A can ciki kuma Nasibah na nan duƙe kamar mai ɗaukan gafara ta ji ya ce.

"To na kashe case ɗin Yusrah saura nawa da ke. Kin tuna ɓarnar da kika taɓa yi min shekara ɗaya zuwa biyu da suka gabata?"

Cikin sauri Nasibah ta kalle shi tana haɗe girarta tana son tuna wace iriyar ɓarna ta yi masa a shekarun baya. Ita dai ta san a ranar da ta fara ganinsa ko kusa da juna basu tsaya ba,ballantana ta yi masa wani abun. To wacce ɓarna ta yi masa da be manta ba har tsawon wannan shekarun?

Murmushi ya yi,domin yanayinta ya gama tabbatar masa da cewar bata tuna ɓarnar da ta yi masa ba sam. Dan haka sai ya kalli agogon hannunsa ya miƙe tsaye ya ce.

"Ok tunda baki tuna ba,ki tashi ki tafi,amma ina son ki sani ina binki bashi,ko bajima ko ba daÉ—e za ki biya ni abunda kika lalata min."

Tura baki Nasibah ta yi gaba ta ce.

"To amma ai kaima za ka iya yin haƙuri kamar yanda ka taya ni ba wa ƙanwarka haƙuri ko?"

Ido ya kafe ta da shi zuciyarsa na tunano masa matsayin Yusrah a wajensa. Haƙoransa ya haɗe waje ɗaya ya taune har sai da jijiyar kansa ta shata layi. Nan take fuskarsa ta sauya daga fara'a zuwa ƙunci,ba tare da ya sake cewa komai ba ya nuna wa Nasibah hanya. Kallonsa ta yi ido cikin ido ta karya wuya ta ce.

"Don Allah Yayah Me kyau ka yi haƙuri ka yafe min duk laifin da na yi maka,wanda na sani da wanda ban sani ba ko Allah Ya sa na cika da imani."

Nan take kalamanta suka saukar da fushin zuciyarsa ya saki murmushi mai sauti. Kai ya gyaÉ—a mata ya ce.

"Jeki na yafe miki. Allah Ya sa mu cika da imani baki É—aya. Kuma ni ba suna na Yayah me kyau ba."

Cikin murna da sakin jiki Nasibah ta ce.

"To meye sunanka?"

"Ki je ƙawarki ta sanar da ke suna na."

Da sauri Nasibah ta juya za ta fita daga parlourn. Shi kuwa Yunus gaba ɗaya ya tattara hankalinsa da nutsuwarsa a bayanta yana kallon yanayin takunta mai ɗaukan hankalin mai kallo. Tana ɓacewa ganinsa ya saki murmushi mai sauti ya ce.

"Haba GiÉ—aÉ—o she is a child for God sake."
Chapter 9 · 0% Book details