Sashe 15
Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Asalin iyayen Samir mutanen garin Jos ne,a can aka haifi mahaifinsa Alhaji Yusha'u Muhammad,wanda mutane ke yi wa laƙabi da Gwamnati saboda takarar Gwamna da ya yi har dau huɗu a garin Jos amma bai samu nasarar hayewa ba ko sau ɗaya. Alhaji Yusha'u Gwamnati na daga cikin mutanen dake son ganin jihar Jos ta samu kwanciyar hankali da zaman lafiya. Domin yana sane da cewa rikicin garin babu abinda yake kawo shi face saɓanin addini da ƙabilanci. A cikin shekarar da mummunan tashin hankalin da ya raba su Samir da Jos ne aka yi wani taron haɗin kan al'umma a wata local government dake da yawan mabiyan addinin kiristanci da Musulmai. A wajen taron ne aka bawa babban baƙo wato Alhaji Yusha'u Gwamnati damar bada cikakken tarihin garin Jos da mutanen da suka kafa garin. Bayan Alhaji Yusha'u Gwamnati ya tashi ya ɗaga hannunsa yana murmushi sai ya isa wajen da aka tanada domin masu yin magana a taron. Abun magana ya karɓa ya yi sallama sannan ya ce.
'Bayan sallama da gaisuwa tare da fatan alkhairi a gare mu baki É—aya;nake yi mana addu'ar Allah Ya bamu zaman lafiya a wannan jiha tamu mai albarka. A yau ina so na ba wa Æ´aÆ´anmu da jikokinmu tarihin da basu sani ba,wala'alla wannan rashin sanin shine yake jawo mana tashin hankula da kashe-kashen rayuka tare da asarar dukiyoyi. A yau zamu É—akko tarihin jihar Jos tun daga tushe domin wayar da kan matasanmu.
Asalin tarihin garin Jos yana da ɗan rikitarwa kaɗan, amma ga bayani a sauƙaƙe yanda matasa za su fi fahimtar ya abun yake.
Tun kafin zuwan Turawa, yankin Jos ba wani babban gari bane kamar yanzu. Akwai ƙabilu na asali (indigenous people) da suke zaune a wurin,wato ƙabilar Berom,Afizere (Jarawa) da kuma Anaguta.
WaÉ—annan su ne asalin masu yankin Jos, kuma a wancan lokacin suna da addinansu na gargajiya wato (traditional religion). Su É—in ba Musulmai ba ne kuma ba Kiristoci bane.
Lokacin zuwan Turawa (Colonial period) a farkon ƙarni na 1900 Turawa (Birtaniya) sun gano tin (ma’adinai) a Jihar Jos,sai suka fara gina gari da tsarin zamani suka kawo mutane daga wurare daban-daban domin su yi musu aiki. To anan kun ji yanda Musulmai da Kiristoci suka shigo cikin Jihar Jos.
Musulman da suka zo Jihar ta Jos a wancan lokacin yawancin su Hausawa/Fulani ne daga arewa suka zo aikin turawa,a hankali masu kasuwanci ma suka fara shigowa.
Kiristoci kuma yawanci daga kudu suka zo,sannan yawancinsu ƙabilar Igbo da Yoruba ne suka fi yawa. Mishan da inyamurai da Yarabawan da suka zo daga kudu sune suka kawo addinin kiristanci a garin Jos,kun ga kenan ba Musulmai ko Kiristoci ne suka kafa Jos ba. Asalin garin Jos na ƙabilar Berom, Afizere, da Anaguta ne. Sannan har yau babu wanda ya san a tsakanin Musulmai da Kiristoci wanene ya fara shigowa cikin Jihar Jos.
Kun ga kenan addinan nan namu biyu wato Musulunci da Kiristanci sun zo ne daga baya,sai kuma mutane suka ɗauki abun ta fuskar da ta jawo ake ta ɓarnar rayuka da dukiyoyo duk dan kare ɓangaranci. Ina so matasa da mu dattijan kammu mu fahimci cewa wannan zama fa Allah ne ya haɗa shi,a gaba ɗaya addinan mu mun san cewa Allah Ya sanar damu shine ya yi nufin hakan ta kasance,to me yasa muke bijire wa umarnin mahaliccinmu? Me yasa muke so dole sai ɗaya ya tashi ya bawa ɗaya waje? A yanzu haka mu duba personal buƙatunmu na yau da gobe,dole muna buƙatar junanmu,domin akwai abubuwan da dole sai musulmi bahaushe ne ya iya su,kuma Inyamuri ko bayerabe yana son wannan abun. To idan muka rabu ta yaya zamu rayu? So muke yi idan muna buƙatar junanmu sai mun yi tafiya mai nisan gaske sannan mu samu biyan buƙatar mu? Me yasa ba za mu yi koyi da sauran juhohin da suka ci gaba ba saboda zaman lafiya da ƙaunar junansu da suke yi?
Daga ƙarshe ina yi mana nasiha da mu ji tsoron Allah mu so junanmu,mu zauna da juna da amana da zuciya ɗaya. Ta haka ne jihar mu ta Jos za ta zamo abar alfahari wajen ƴaƴa da jikokinmu masu tasowa.'
Alhaji Yusha'u Gwamnati na kammala jawabinsa wajen ya kaure da kabbara da tafi tare da ihun matasa. Sosai maganganunsa suka yi tasiri a cikin zuƙatan mutanen dake wannan wajen. Sai dai ita fitina mutum ɗaya ɓata gari idan ya kunna ta;sai ka ga ta ja ra'ayin mutanen kirki su afka mata ido rufe,sai bayan ɓarna ta faru ne kowa ya dawo cikin hayyacinsa nadama da dasani suke lulluɓe wanda suka biye wa son zuciyarsu.
Bayan wata ɗaya babban rikicin ya ɓarke mutane suka manta da wannan taro na haɗin kan al'ummar Jihar Jos suka yi ta kashe junansu. Wasu ma uwa ɗaya uba ɗaya suke,amma banbancin addini sai ya sa su gayyato ƴan'uwansu da suke addini ɗaya su lahanta wanda baya cikin addininsu. Daga masu kashewar har zuwa wanda aka kashe duk basu san takamaimai akan me suke yin faɗan ba. Haka suka ɗauki tsawon sati suna abu ɗaya. A wannan faɗan ne Alhaji Yusha'u Gwamnati da Hajjah Barirah suka rasa danginsu na kusa,tun daga nan zaman garin ya fita daga ran Alhaji Yusha'u Gwamnati domin da ƙyar shima iyalansa suka tsira daga wannan tashin hankalin.
Bayan wata uku ƙura ta lafa ya tattara Hajjah Barirah da ƙanwar mahaifiyarsa Gwaggo Yabi dake wajensa a lokacin da Samir ɗan shekara tara sai Samirah mai shekara biyar suka dawo garin Kano da zama. Tun daga nan sai Alhaji Yusha'u Gwamnati ya haƙura da harkar siyasa ya kama aikinsa na gwamnati da kasuwanci tare da harkokin NGO's ya riƙe da kyau. A shekarar da suka dawo Hajjah Barirah ta sake haihuwar ƴarta kyakkyawa,ranar suna aka saka mata Sakinah,tun daga nan haihuwar ta kulle bata sake ko da ɓarin wata ba har Alhaji Yusha'u Gwamnati ya bar duniya. Bayan rasuwarsa babu yanda manema basu taso mata ba kamar za su cinye ta. Amma haka Hajjah Barirah ta toshe zuciyarta ta hana kowa shiga cikinta. A cewarta ta gama aure kenan har abada,domin babu wani namiji da zai maye mata gurbin mijinta a cikin rayuwarta da ta ƴaƴanta. Duk yanda Hajjah ke yi wa Gwaggo Yabi biyayya saboda kasancewarta ita ce wadda take kalla a matsayin danginta;amma haka ta toshe kunnenta ta yi mata tatas a lokacin da ta matsa mata akan ta yi aure ko dan tarbiyyar yaranta ta inganta. Daga ƙarshe ma sai ta dena hulɗa da Gwaggo Yabi ta yi mata kyautar gida a nesa da unguwar da suke. Haka Gwaggo Yabi ta haɗa nata ya nata ta koma gidan. Bayan shekara biyar da komawarta gidan suna zumuncin nesa ciwon sugar ya yi ajalinta. Sosai rasuwar Gwaggo Yabi ta daki Hajjah Barirah,dan haka sai ta yi ƙoƙari ta mayar da gidan da Gwaggo Yabi ta zauna ya koma islamiyya ta bayar da shi kyauta da niyyar Allah Ya kai ladan gare ta. Tinda Hajjah Barirah ta yi wannan abun sai idanuwan mutane suka dawo kanta,masu zuwa neman taimako suka dinga tururuwa zuwa wajenta. Ido Hajjah ta rufe ta ci musu mutunci tare da zage su tass ta ce ita bata kira kowa ya zo wajenta neman taimako ba,gidanta ba charity house bane kowa ya je ya nemi na kansa. Wasu mutanen sun ɗauki maganarta da muhimmanci wasu masu nacin kuwa sai suka ƙi jin maganarta suka kafe suke ta zuwa neman taimako. Daga ƙarshe da ta ga abun ya ƙi ci ya ƙi cinyewa sai ta nemi taimakon ƴan sanda,hakan da ta yi ne sanadiyyar raba ta da nacin mutane. A fili Hajjah ke nuna tsanar talaka da duk wani abu da ya shafi rayuwar talaka. Wannan shine dalilin da ya sa duk wanda ya zo neman auren su Samirah idan ta bincika ta ga bai fi su arziƙi ba sai ta ƙi. Tun ana zuwa neman auren nasu yanzu gashi ƙafa ta ɗauke mazan sun dena zuwa. Ita hakan sam bai dame ta ba,a cewarta da ta aurar da su su sha wahalar gidan miji gwanda ta barsu a gabanta su yi rayuwarsu cikin wadata da walwala.
Rayuwar Samir ta lalace ne saboda sakacin Hajjah akan tarbiyyar yaranta,tunda ya kammala sakandire ta kai shi ƙasar turawa domin ya ci gaba da karatunsa,a can ya koyi shan giya da neman mata babu kama hannun yaro,hakan sam bai taɓa damun Hajjah ba,domin a cewarta rayuwarsa ce yana da ƴancin yin duk abinda yake so. Babbar damuwarta da Samir shine ya yi aure domin ya samar wa kansa Magajin dukiyarsa. A kullum fatanta bai wuce duk macen da zai aura ta haifa masa ɗa namiji ba. Lokuta da dama ƙawayenta na nuna mata sangarcin da take nuna wa Samir ya yi yawa,ita kuwa duk girman wadda ta yi mata magana akan Samir to daga wannan ranar za ta yi wa mace tatas kuma alaƙarsu ta yanke. A wajen ta soyayya ita ce sakar wa yaro duk abinda ya ja da kuma kashe wa yaro duk dukiyar da ya nema matsawar akwai ta. Idan kuma babu a cewarta uwa ko uba haƙƙinsu ne su shiga su fita domin ganin yaransu sun samu abinda suke so komai wuyarsa komi tsadarsa.