Sashe 10
Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Zama ya gyara a kujerar yana tuna ranar farko da ya fara ganin Nasibah. Murmushi ya dinga dokawa yana tuna yanda ta danganta shi da wani har tana faɗin ai shi ɗin bai kai wancan kyau ba. Sai gashi kuma yanzu tana kiransa da Yayah Kyakkyawa. Ƙarar da wayarsa ta ɗauka ne ya katse masa dogon tunanin da ya faɗa. No Goggoji ya gani tana yawo a wayarsa. Gabansa ne ya yanke ya faɗi har sai da ya furta.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil."
A fili. A hankali ya amsa kiran nata ya kara a kunnensa,yana gama sauraronta ya ce.
"Eh Goggoji na gama,gani nan shigowa mu gaisa."
Katse kiran ya yi ya miƙe tsaye yana gyara karin hularsa. Cikin tafiyar isa da ƙasaita tare da izza irin ta cikakkun mazaje ya isa wani ɗaki ya zaɓo takalmin da ya dace da kayan jikinsa ya sanya,sannan ya cire na ƙafarsa ya mayar da su mazaunin da ya dace ya fito.
A waje ya tarar da Yasmin da Nasibah da ta hana su shiga cikin taron mutane,dan ji take yi kamar Yusrah ta gama sanar da kowa abinda ya faru,kawai shiru suka yi dan suna tsoron Yayansu. Suna nan tsaye suna hira ƙamshin turarensa ya yi musu sallama. Da sauri Nasibah ta juya ta kalle shi ta saki murmushi,shima murmushin ya sakar mata ya zo wajensu zai gifta. Cike da girmamawa Yasmin ta durƙusa ta gaishe shi. Nasibah kuwa sai ta ce.
"Yayah Mai Kyau na san sunan ka yanzu."
Har ya gota su ya tsaya cak. Hannu Yasmin ta hau yarfewa tana kallon Nasibah. Shi kuwa Yunus sai ya juyo ya kalleta ya ce.
"Uhumm meye suna na?"
"Yayah Yunus,ko kuma na ce GiÉ—aÉ—o. Au Yayah GiÉ—aÉ—o."
Kai ya jinjina ya kalli Yasmin ya ce.
"Lallai Yasmin ta yi ƙoƙari."
Daga nan bai sake cewa komai ba ya yi gaba. Yana tafiya Yasmin ta ja hannunta ta zaunar da ita a saman wasu fararen kujeru ta ce.
"Ke dai Nasibah ban san wace iri bace ke. Yanzu don Allah me ya kai ki yi masa magana bayan na faÉ—a miki he is not in a good mood?"
"To ni be nuna min wani mood ɗin da zai hana ni yi masa magana ba;don me zan ƙi yin magana?"
Waigawa Nasibah ta yi hagu da dama taga babu wani a kusa da su,sai ta yi ƙasa da murya ta ce.
"Ke ni fa yunwa nake ji,na gaji da yi miki kawaici."
Dariya sosai Yasmin ta yi ta ce.
"Jira ni anan ina zuwa."
Cikin gida Yasmin ta shige da sauri ta bar Nasibah a wajen tana kallon Zuri'ar kyawawa,kamar yanda take kiransu a cikin ranta. Babu jimawa sosai Yunus ya fito daga main house ɗin ransa a matuƙar ɓace. Kai tsaye wajen wata mota ya nufa wadda aka rufe ta,yana zuwa ya yaye rigar ya yi wurgi da ita a ƙasa ya buɗe motar ya shige. Yana juyawa da motar ya juya ya kalli wajen da Nasibah ke zaune tana kallonsa hankalinta na kan tuna laifin da ya ce ta taɓa yi masa. Fuskarsa da ke ɗaure ce ta fara sassautawa daga fushin dake samanta. A hankali idanuwan Nasibah suka sauka akan rubutun da ta yi masa wanda ta rubuta.
'MoTar NaNSy ƙAyA.'
Idanuwanta ta zaro waje ta damƙe bakinta,tare da miƙewa tsaye. Murmushi Yunus ya sakar mata sannan ya tada motar ya bar gidan a guje..........
[9/22, 8:13 AM] HAERMEEBRAERHâ¤ï¸: ZAWARA.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨âœï¸
PAGE 8.
Koda Yasmin ta dawo É—auke da abinci sai ta tarar da Nasibah a tsaye tana zaro idanuwa waje. Girarta ta haÉ—e waje É—aya kafin ta ce.
"Yah Yusrah ta sake yi miki wani abun ne Nansy?"
Girgiza kai Nansy ta yi cikin sauri ta ce.
"No babu abinda ta yi min. Ammm yauwaa kin kawo abincin,zauna mu ci ko ke kin ƙoshi?"
Sakin jiki Yasmin ta yi tana murmushi ta ce.
"Inaa,ai nima nan da kika ganni yunwar nake ji,ni tunda aka fara maganar bikin nan na su Yah Yunus fa ban zauna ba ballantana...."
Yanda Nansy ta waro idanuwa waje tana neman shaƙewa da abincin da take ci ne ya sanya Yasmin dakatawa da kalamanta ta ce.
"Ke lafiya wai kike ta yin abu kamar me aljanu? One minute kina dariya, another minute za ki sauya fuska. Me yake faruwa ne?"
Yaƙe Nansy ta yi tare da sake ɗiban fried rice ɗin da ta ji haɗi ta kai bakinta. Sai da suka yi nisa a cin abincin sannan Nansy ta gyara zama ta ce.
"Ni kuwa in tambaye ki mana Yasmin."
"Uhum?"
"Wai takamaimai auren wa ake yi ne a gidan nan? Don ni dai a iya sani na bikin Yayarki Yusrah kika ce min za a yi,to kuma na ji kin soko wani zance É—azu da ban gane kansa ba."
Murmushi Yasmin ta yi kafin ta ce.
"Yau dai bari na baki cikakken tarihina,domin ta haka ne za ki fi gane abinda yake faruwa a gidan namu. Yauwa,kin ga dai da farko kamar yanda kika riga kika sani suna na Yasmin Ibrahim Yunus. Mahaifinmu ɗan asalin jihar Gombe state ne,kasancewar Kano cibiyar kasuwanci ce shi ne dalilin da yasa kakanninsa na ɓangaren uwa da uba suka dawo nan suke kasuwancinsu. Tun daga nan ahalinsu suka fantsama a cikin garin Kano,sai dai duk da haka basu taɓa watsar da danginsu na can Gombe ba,kuma har yau idan kin kula muna yin yaran fullanci a gidan nan.
Yah Giɗaɗo ya ci sunan Kakan mu ne,shi yasa ake kiransa da Giɗaɗo. Mamansa ta rasu da jimawa tun yana sakandire a shekararsa ta ƙarshe. Gwaggoji Kakarmu da ta haifi Abbah,ita ce ta ci gaba da kula da shi,bayan rasuwar mahaifiyarsa,a lokacin ta so ƙwarai da gaske Abbah ya ƙara aure amma ya ƙi,sai da ya shekara goma kafin Gwaggoji ta shawo kansa ya auri Hajiya Yalwa wato mahaifiyata. Hajiya Yalwa ta jima tana zawarci a gaban iyayenta,domin kuwa mijinta ya rasu ya barta da ƴa guda ɗaya mai suna Yusrah. Kasancewar Yusrah na ƙarama sosai mahaifinta ya rasu sai Mama ta ƙi yarda ta yi wani auren. A cewarta tana so ta ba wa ƴarta ingantacciyar rayuwa. Shi yasa ta dinga faɗi tashi tana rayuwar neman na kanta har dai daga ƙarshe suka haɗu da Abbah a lokacin da ta je Lagos saro takalma. Tun da ya dawo ya sanar da Gwaggoji zai yi aure,sai ta yi ta murna. A yanda Gwaggoji ta ke bamu labari da haɗuwar Abbah da Mama ba a fi wata ɗaya ba aka ɗaura aure ta tare da ƴarta Yusrah. A lokacin Yusrah na da shekara sha tara a duniya, dan har ta kammala sakandire jami'a za ta shiga. A lokacin da Abbah ya auri Mama ya yi ne kawai dan ya cika burin Gwaggoji na son ya yi aure,shi yasa ma ya auri macen da ta manyanta,sai gashi babu zato ko tsammani an wayi gari Mama na ɗauke da cikina. Hankalinta ya tashi ƙwarai da gaske,domin ita ta cire rai da sake haihuwa a duniya. Dan haka sai ta riƙa kuka da addu'ar zubewar cikin kada ƙawayenta su ji su yi mata dariya.
Cikin rashin samun nasara ciki na nan daram bai zube ba,sai ma girma da ya dinga yi cike da ƙoshin lafiya. A wannan lokacin ne Mama ta samu soyayyar Abbah ta gaske har ya saki jiki da ita,dan haka sai ta haƙura itama ta rungumi cikin jikinta cike da so da kulawa. Watarana Mama ta sa Abbah ya kirawo Yah Giɗaɗo dan ta gansa,domin a kullum suka zauna Abbah bashi da wata magana da ta wuce ta Giɗaɗonsa. Dan haka sai Abbah ya kirawo Yah Giɗaɗo daga Abujah inda yake karatun Masters ɗinsa,duk da cewa Yah Giɗaɗo na ta ƙoƙarin dojewa zuwa gida;kan dole ya zo,saboda ya san ko bajima ko ba daɗe sai ya haɗu da Mama tunda alaƙar aure ta ratsa.
A lokacin da ya zo ya samu labarin cikin da Mama ke ɗauke da shi sai kunya ta kama shi,gaba ɗaya sai ya ji gidan ya fita a ransa. Ga uwa uba takura da matsin lamba da ya fara samu a wajen Yusrah da ta nuna masa so a karon farko da ta fara ganinsa. Kwanansa uku ya tattara ya koma Abuja. Tun daga wannan ranar bai sake dawowa gida ba;har sai da Mama ta haife ni Gwaggoji ta kirasa a waya ta yi masa faɗa sosai. To a sannan ne ya zo ya ganni cike da tsarabar kayan jarirai. Yah Yunus ya ce a ranar da idanuwansa suka sauka akan ƙaramar fuskata ya ji dikkan baƙincikin dake cikin ransa ya yaye,a ranar ya ji babu wata halitta da yake so sama da ni,soyayya yake yi min wadda uba zai yi wa ƴarsa. Dan haka Abbah sai ya koma ɗan kallo.