Sashe 14
Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ikon Allah ne kawai ya kai Luƙman gida,domin kuwa nan take wani irin mugun zazzaɓi mai zafin gaske ya kama shi. Yana zuwa gidansu ya samu waje a parlour ya kwanta yana karkarwa tare da numfarfashi. Mahaifiyarsa da ke zaune tana jiransa ya dawo sai ta miƙe a tsorace ta hau kiran mahaifinsa dake cikin ɗaki. Cikin ƙanƙanin lokaci suka rufu akansa suna tambayarsa abinda yake damunsa. Kuka mai tsanani Malam Luƙman ya fashe da shi murya na rawa ya ce.
"Mahaifinta ya ci min mutunci,ya ce kada ya sake gani na da Æ´arsa ya raba tsakanina da ita rabawa ta har abada Ummi."
Da jin haka sai Mahaifiyar Luƙman ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ta zauna a gefen kujerar da ya kwanta,kansa ta ɗauka ta ɗora a saman cinyarta tana shafawa a hankali. Cikin sassanyar muryarta mara hayaniya ta ce.
"Na jima ina sanar da kai zuwan wannan ranar Luƙman,shi yasa tun kafin soyayyar taku ta yi zurfi na ce maka ka rabu da ita amma ka ƙi,hujjarka shine yarinya tana son ka ba za ta bari a raba ku ba. Kada fa ka manta Luƙman duk yanda yarinya take son ka idan iyayenta ba sa son ka daga ƙarshe sai kun rabu,idan kuma ka ga kun yi aure to tsananin rabo ne ya sa auren ya ɗauri ba da son ransu ba;ko kuma yaran su gudu su bijire wa iyayensu. Dan haka ka yi haƙuri ka taushi zuciyarka. Ƴar abokin mahaifinka da yake ta yi maka magana akanta tana nan tana karatunta,da zarar ta kammala sai a yi komai cikin mutunci ko ba haka ba Malam?"
Cike da gamsuwa da maganar Ummi Abbah ya ce.
"Ƙwarai da gaske maganarki na kan hanya. Allah na tuba dama ina Makaɗi ya ke da darajar da zamu haɗa zuri'a da shi? Kawai dai dan ka dage ne ya sa muka haƙura domin mu barka da zaɓin ranka. Amma tunda an yi haka ka bar masa ƴarsa ya jiƙata ya shanye,kai kuma ka auri daidai da kai."
Duk da cewa Malam LuÆ™man ya san gaskiya iyayensa suke faÉ—a,amma shi sam bai aminta da auren wadda suka zaÉ“ar masa ba. Dan haka sai ya yi shiru kawai ya lumshe idanuwansa yana sauke numfashi da sauri da sauri. Maganin zazzaÉ“i mahaifinsa ya É—akko ya bashi da ruwa. Mahaifiyarsa kuma ta É—akko masa abincin dare ta zauna ta dinga bashi a baki yana ci yana zubar da hawaye. KaÉ—an ya ci ya juyar da kansa ya miÆ™e da Æ™yar ya nufi É—akinsa ya kwanta yana tunanin ranar farko da ya fara ganin Nasibah a rayuwarsa. Kuka ya fashe da shi domin shi ya sani har abada babu macen da zai sake yi wa irin soyayyar da ya ke yi wa Nasibah,ya so ta tun bata san ciwon kanta ba,ya so ta tun bata san ma'anar saka hijabi ta suturce jikinta ba,ya ci gaba da son ta duk da ya san halayenta na rashin ji da Æ™iriniya tare da É—aukan magana,ya sha biyan kuÉ—in ta'adi ko asarar da ta yi wa mutane a wajen faÉ—a,shi kuwa waye zai nuna masa ya san Nasibah sama da shi bayan iyayenta? Sai dai duk da irin wannan soyayyar da yake yi mata dole ne ya koya wa zuciyarsa haÆ™uri da rashinta ko dan ya tsira da mutuncinsa da na iyayensa da aka zage tas.........[9/30, 4:19 AM] HAERMEEBRAERHâ¤ï¸: ZAWARA.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨âœï¸
PAGE 11.
Samir na hanyarsa ta zuwa gida Nuh ya kira shi,kamar ba zai ɗauka ba daga baya ya daure ya amsa wayar a dake. Ran Nuh a ɓace ya ce.
"Amma dai babu É—an iska sama da kai Samir. Ta ya za mu zo waje da kai ka tafi ka barni bayan ka san bani da abun hawa a nan?"
Yatsina fuska Samir ya yi ya ce.
"Ka ga Man ka samu abun hawa ya kawo ka gida dan ni yanzu haka kai na ba a daidai yake ba."
Tsaki Nuh ya ja sannan ya ce.
"Kai dama yaushe ne kanka yake daidai a jikinka? Ka dai yi a hankali kada ka manta tuƙi kake yi ka sha abunda zai ja maka matsala."
Katse kiran Samir ya yi ya bar Nuh da takaicin halayya irin ta Samir. Kan dole ba dan ya so ba ya nemi adaidaita sahu ya shiga dan ya kai shi gidansu Samir.
Lokacin da Nuh ya isa gidan ya tarar da gidan a rufe,sai da ya fita ya sallami mai adaidaita sahu sannan ya ƙwanƙwasa mai gadi ya buɗe masa. Gaisawa suka yi Nuh ya ce.
"Ya dawo kuwa?"
Da sauri mai gadi ya risina ya ce.
"Ah ah! Alhajin bai dawo ba."
Kai Nuh ya girgiza sannan ya shige cikin gida. A zazzaune ya tarar da Hajjah Barirah ita da ƴammatan ta Samirah da Sakinah suna kallo. Nuh na shiga Samirah wadda ke bi wa Samir ta miƙe zaune tana yanga ta ce.
"Yah Nuh sannu da dawowa. Na kawo maka abincinka nan ne ko za ka je dinning room?"
Harararta Hajjah Barirah ta yi kafin ta ce.
"Sannu uwar azarɓaɓi,Yayanki kawai kika gani har kike zancen kawo masa abinci ko? Kai Nuh ina ka baro ɗan amanartaka?"
Kafin Nuh ya yi magana suka ji ƙarar buɗe gate ɗin gidan. A guje Samir ya shiga da motar cikin gidan. Hakan ne ya tabbatar musu da cewar mutumin nasu ba a saiti yake ba. Tsaye Nuh ya miƙe zai fita Hajjah Barirah ta yi saurin dakatar da shi. Komawa ya yi ya zauna yana kallon fuskarta da ta sauya daga damuwa zuwa ɓacin rai. Suna cikin wannan yanayin Samir ya shiga parlourn. A zazzaune ya tarar da su sun yi shiru tare da zuba masa ido. Fuska a ɗaure ya kalle su ya ce.
"Kun samu labari na kashe wani ne da duk kuka taru kuka zuba min ido?"
"Daga ina kake Samir?"
Shine tambayar da Hajjah Barirah ta wurga masa fuska a É—aure tamau. Dariya ya saki sannan ya gyara tsayuwarsa yana kallon Hajjah ya ce.
"Daga gidan su matar da zan aura nake Hajjah."
Cikin sauri Hajjah Barirah ta dafe ƙirji ta ce.
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un! Samir yanzu a haka ka je gidan surukan naka? Me kake tunanin za su ce akan ka uhum?"
Zube wa ya yi a kujera mafi kusa da shi ya saki hamma sannan ya ce.
"Ban gane me kike nufi ba Hajjah? Ni mahaukaci ne da zaki ce a haka na je musu? Hajjah bari ki ji na faÉ—a miki wata magana,kin ce zaki aura min Munirah ko ina so ko bana so matsawar ban kawo matar aure ba a shekarar nan. To ina so a yau ki kashe maganar aure na da Muni saboda na samu matar aure,macen da nake muradin aura ta zamo uwar yarana ba Æ´ar bariki kamar Munirah ba."
Baki Hajjah ta washe ta ce.
"Ka dai ji da shi,ina ce ta sanadin son da take yi maka ne ta zamo haka? Bayan haka ma duk maitar na raba ku da nake yi ko mata huɗu zan aura maka na sani ba za ku taɓa rabuwa da Munirah ba. Ku ɗin ƙaddarar junanku ne."
Murmushi Samir ya yi ya ce.
"Wannan karon da gaske nake yi,zan rabu da Muni rabuwa ta har abada in dai na samu na auri zaɓin raina."
"To Allah Ya sa. Ita yarinyar da za ka aura a ina take kuma Æ´ar gidan wanene?"
Samir yi ya yi kamar bai ji tambayar Hajjah ba,domin ya san halin ta sarai akan ƙin talaka da duk wani abu da ya shafi harkar talauci. Miƙe wa ya yi tsaye ya kalli Sakinah wadda duk abinda ake yi bai ɗaɗata da ƙasa ba ballantana ta saka musu baki. Cikin bada umarni ya ce mata.
"Ke ki kai min abinci sashe na. Kuma ki haÉ—a min da tea ki matse lemon tsami guda biyu a ciki."
Ba tare da ta amsa shi ba ta miƙe ta mufi dinning room ta fara haɗa musu abincin shi da Nuh,Nuh na ganin yanda take ɗiban abincin da yawa ya ce.
"Kar ki haÉ—a mana,bari na zo na ci nawa a nan."
Kai kawai Sakinah ta ɗaga ta ci gaba da abinda take yi. Tana gamawa ta ɗauki abincin a katon trey ta nufi wata ƙofa da shi.
Nuh kuwa hanyar dinning room ɗin ya nufa yana latsa wayarsa. Murmushi Samirah ta yi ta miƙe ta nufi wajensa ta hau serving ɗinsa. Hajjah kuwa sai ta haye sama ta bar Samir da bashi da niyyar bata amsar tambayoyin da ta tasa shi a gaba ta na yi masa. Idanuwansa a lumshe ya buɗe baki da ƙyar ya ce.
"Nuh zan ci maka uwa idan kana taɓa min ƙanwa fa. Bana son iskanci,duk matan dake waje basu ishe ka ba za ka tsallake su ka dinga taɓa min ƙanwa? Ke kuma balama zo ki bar nan ko na karya ki."
Tinda Samir ya fara magana suka raba hannuwan junansu da suka sarƙafe suna aika wa juna da wani zazzafan kallo. Kame-kane Nuh ya fara yi tare da borin kunya yana zagin Samir. Ita kuwa Samira sai ta hau tura baki tana faɗin.
"Shikenan mutum ba zai yi soyayya in peace ba sai an saka masa ido."
Ta gaban Samir ta zo za ta wuce ta shige ɗakinta tana wani dire-diren ƙafa kamar za ta yi kuka. A hankali Samir ya buɗe ido ya kalle ta ya ja tsaki. Da ƙarfi ta buɗe kofar ɗakin nata ta buga tare da saka mata key. Sakinah na dawo wa ta nemi waje ta zauna ta ci gaba da kallon ta ba tare da ta kula kowa ba. Sun jima a haka kafin Nuh ya kammala cin abincinsa ya yi musu sai da safe ya wuce sashen Samir ya kwanta. Har Sakinah ta gama kallo ta kashe kayan wutar parlourn Samir na nan a zaune yana tunanin Nansy. Sosai yake jin mamakin yanda soyayyar yarinya ƙarama ta mamaye masa zuciyarsa. Babban ƙalubalen dake gabansa shine ya fi tada masa hankali,ta yaya zai fahimtar da Hajjah iyayen Nasibah talakawa ne? Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke kafin ya hau tunawa da mahaifinsu.