← Book details Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 28

Sashe 2

Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A gabana kike sheganta min ƴa Hauwa? Ke wai me yasa notikan kan ki ba sa aiki ne? Ki dube ki shirgegiya kamar bajimin Sa amma ki tsaya kina faɗa da ƴar cikinki,da Allah Ya kawo rabo da wuri ai da kin aje kamarta. Amma da yake ke ba cikakken hankali gare ki ba shine kika biye mata kuke faɗa. Ni bana son jin me ya haɗa faɗan ki kama gabanki ki koma ƙofar ɗakin tsohuwarki,tunda kin dage ke ba zaki rabu da wancan direban ba,to ga wajen zama nan,duk lokacin da ya gama zagaya duniyar ya dawo sai ya kwashe ki ku yi gaba."

Cikin sauri Nansy ta kalli mahaifinsu ta ce.

"Kuma Baba É—azu sai da su Lawal suka zo gidan nan,baka ga yanda suka dinga cin abinci ba har da zubarwa suka yi,da na yi musu magana Yah Hauwa ta kai min duka,ka ga inda ta ji min ciwooo a wuya na. Yiiiiiii."

Nasibah ta ƙarasa maganarta tana mai rushe wa da kukan zogi da raɗaɗin da ciwon wuyanta ke yi mata. A hasale Malam Sanda ya yi kan Yah Hauwa ya na surfa mata zagi tare da cin mutunci kamar ba shi ne ya haife ta ba. Cikin tsananin fushi ya ƙarasa maganganunsa da faɗin.

"Ah toh,kin dai ji na faÉ—a miki,ko ki biya abincin da shegun yaranku suka cinye min,ko kuma na ja Allah Ya isa."

Kuka mai matuƙar cin rai ne ya ƙwace wa Yah Hauwa. Cikin matsanancin kuka ta kalli Nansy ta kasa cewa komai,sannan ta juya ta kalli mahaifinta dake ci gaba da zagi da aibata mata yaranta kamar ba ƴaƴan sunnah ba. Da gudu ta bar wajen ta nufi ɗakinsu ta hau haɗa kayanta. Ta na gamawa ta zira doguwar rigarta ta saka hijabi ta fito tsakar gida. A tsaye ta tarar da Babansu yana shafa wa Nasibah rob a wuyanta,ita kuma sai wani kukan shagwaɓa take yi tana tsalle. Kilishi da takaicin su Nasibah da mahaifinta ya kai mata ko ina sai ta dinga aiki tana wurgi da kwanuka tare da habaici. Cike da takaici da baƙinciki Yah Hauwa ta kalle su ta ce.

"Baba ka yi haƙuri ka yafe wa su Lawal abincinka da suka ci yau,da yardar Allah ko bangon duniya Habu zai je neman kuɗi ba zan sake zuwa gidan nan ba. Allah Ya jiƙan Innani,da tana raye na tabbata ba za ka yi min haka ba."

Cikin matsanancin kuka ta bar gidan tana fyace majina. Jikin Malam Sanda ne ya yi mugun sanyi,sai ya sakar wa Nansy rob ɗin ya shige ɗakin Kilishi domin ita ce ke da girki a wannan ranar. Yana shiga ciki Nansy ta faɗa ɗakinsu ta samu gefen gadon da mahaifiyarta ke kwance tana baccin rana ta zauna tana ƙunshe dariya.

A can tsakar gida kuwa tuni gidan ya ci gaba da hayaniyar shige da ficen yara. Kilishi da ta cika ta yi fam saboda takaicin yanda mijin nasu yake fifita Nasibah akan duka yaran gidan,sai ta ɗauki abincinsa ta shiga ɗakin babu ko sallama ta dangwarar masa ta fito tana ƙunƙuni. Shiru Makaɗi ya yi yana tunawa da uwar gidansa da ta rasu sakamakon jinyar cancer ta mama da ta sha. Cike da jimamin abinda ya aikata wa Hauwa ya zamo bakin gado ya buɗe abincin nasa ya hau tsakura yana ci kamar baya so.

Sallamar wasu mata ne ta ja hankalin mutanen gidan gaba É—ayansu. Kallon gidan suka hau yi kafin É—aya daga cikinsu ta buÉ—e baki ta ce.

"Nan ne gidan su Nansy Ƙaya?"

Kilishi dake cike da takaicin Nansy a cikin ranta,sai ta buÉ—i baki ta ce.

"Tunda kuka shigo har tsakiyar gida kuka kama suna ai kun san kun zo inda kuke nema ko?"

Chewing gum É—in bakinta matar ta tauna sannan ta ce.

"Ok. Ina ita Nansyn take?"

Nansy dake ƙunshe a ɗaki a jikin labule tana leƙen matan sai ta ji hanjin cikinta na kaɗawa,nan da nan tsoro ya mamaye zuciyarta. Cikin ranta take ayyana.

'Me waÉ—annan Hajiyoyin matan suka zo yi a gidanmu ni Nasibah?'....
[9/15, 10:57 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA.

NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️

PAGE 2.

Makaɗi na jin muryar matan da basu yi kama da wanda suka zo da maganar wasa ba,sai ya fito tsakar gida yana suɗe hannunsa tare da murje shi waje ɗaya ya ƙanƙance ido,zuciyarsa a tsinke ya ce.

"Ku kuwa bayin Allah da girmanku da kamalarku me ya sa kuke neman Æ´ar tatsisiyar yarinya kamar Nasibah?"

Murmushi É—aya daga cikinsu ta saki sannan ta ce.

"Baba babu abinda ya kawo mu gidan nan face alkhairi. Can gidan Malam Musa Nera ne ake bikin aure,to da muka zo sai muka ga yaran gidan da kitso da lalle mai kyau,muna tambaya aka ce mana nan zamu zo a yi mana,kuma sunan mai lalle da ƙunshin Nansy Ƙaya ko kuma mu ce Nasibah."

Wata iriyar ajiyar zuciya Makaɗi da Nasibah dake laɓe a ɗaki suka sauke a tare;kafin ta fito daga ɗakin tana washe baki. Har ƙasa Nasibah ta durƙusa ta gaishe su suka amsa cikin sakin fuska. Makaɗi na ganin haka sai ya jingine a jikin ƙofar ɗakin Kilishi ya ce.

"Da yake duk nan unguwar babu manya irinku masu hannu da shuni dake shigowa nan gidan wajen Nasibah, sai dai idan suna buƙatar kitso ko lallen ita ta je har gida ta yi musu,shi yasa zuwanku ya zame mana sabon abu."

Jinjina kai matan suka yi domin sun fahimci uzirinsa. Babu ɓata lokaci Nasibah ta matso kusa da su cike da jin kunyarsu ta kalle su daga sama har ƙasa ta ce.

"Ku jira ni bari na É—akko tabarma na zo,kun zo da kayan lallen?"

"Eh mun zo da komai."

Ɗakinsu ta faɗa da gudu ta hau kwashe kayan saman tabarmar dake shinfiɗe a tsakiyar ɗakin. Ƙarar kwanuka ne suka tayar da mahaifiyarta ta kalle ta cike da takaici ta ce.

"Ai dama na san Najlah ba zata taɓa tashi na ba,amma ke...ke ko baccin mutuwa nake yi sai kin tashe ni. Tun ɗazu ina jin ɓuruntunki na yi banza da ke,amma kin rantse da Allah sai na farka,to gani ki min uwar da za ki yi min."

Dariya Nansy ta yi ta ce.

"Ah ahhh Mama,banda dai baccin mutuwa,ki na can ƙiyama ana ce miki man rabbuki ta ya zaki ji ni?"

Maficin hannunta ta É—auka ta jefi Nasibahr da shi,ita kuwa da gudu ta bar É—akin tana dariya. A wajen da ta saba zama ta yi sana'arta ta yi musu shimfiÉ—a ta zauna tana faÉ—in.

"Wa za a fara yi wa?"

Kallonta suka yi suka ganta ƴar ƙarama,sai suka yi murmushi babbarsu ta zauna,dole sai da Nasibah ta koma ɗaki ta samo pillow ta saka a kujerar ta sannan suka fara kitson. Yanda take tsaga kai da kwashe kai cike da ƙwarewa ne ya sanya sauran daina rainata. Cike da gwanancewa Nasibah ta kwashe wa matar kai da kitso sannan ta kama na ƴar'uwarta. Tana gama yi musu kitso ta kwaɓa lalle ta hau zana musu irin wanda suka nuna mata a waya. Bayan awanni biyu da gama yi musu kitso suka wanke lallen. Da za su tafi suka ƙirga dubu goma suka ba wa Nasibah,wani irin farinciki ne ya mamaye zuciyarta har ta ji kamar ta kwanta musu a ƙasa dan godiya. Suna murmushi suka bar gidan zuciyarsu fal farincin samun biyan buƙatarsu da suka yi.

Su na tafiya nasiba ta zare dubu uku ta ɓoye a jikinta,kamar yanda ta yi zato kuwa,haka mahaifinta ya fito daga ɗaki yana dariya yana washe baki ya ce.

"Ikon Allah! Ashe dai baƙin arziƙi ne ba na tsiya ba. To ai hakan ya fi Nasibatuna akan kullum a zo kawo min ƙararki. Maza ƙirgo min na goro na koma bakin aiki,Yau Salihi be zo ba ni kaɗai nake ta aikin faci gaba ɗaya na gaji."

Kuɗin ta miƙa masa gaba ɗaya tana murmushi ta ce.

"Ah ah Baba,ka É—auki abinda ya yi maka,in yaso sai ka bani na Mama da wanda zan sayi littafin da na faÉ—a maka Malamin bokonmu ya ce a siya saboda komawarmu senior section."

"Allah Ya yi miki albarka Æ´ar Baba. To ga wannan,ni kuma na É—auki wannan ko?"

Dubu uku ya zare ya bata dubu huɗu ya tafi yana farinciki a cikin ransa. Yana tafiya Nansy ta zaro wanda ta ɓoye a jikinta ta nufi ɗakinsu ta damƙa kuɗin a hannun mahaifiyarta,ganin haka sai Mamanta ta zari dubu ɗaya ta bata ta yi mata godiya sannan ta ce itama ta je ta sayi abinda take so. Sosai Mahaifiyarta ke jin daɗin yanda take da tausayi da son rage mata duk wata wahala da nauyin da mahaifinsu baya iya sauke wa a cikin gidan.

A wannan ranar da yamma Nansy na fita wajen ƙawayenta sai ta hau kashe musu kuɗin da ta karɓa a wajen Mamanta tana zabga musu ƙaryar yaran gwamna ne suka zo kitso da lalle wajenta. Sai da suka cinye kayan maƙulashensu sannan ta zauna da kyau ta ci gaba da basu labarin mutanen da suka zo kitso wajenta. Wasu sun yarda wasu kuma basu yarda ba,domin ta ce ƴaƴan gwamnan jihar Kano ne sutukum da guda suka tsallake ko ina a garin Kano suka zo wajenta kitso. Wanda basu yarda ba dole suka bar abun a ransu gudun kada ta yi musu duka a banza.

Magariba na yi kowa ya nufi gida. Nansy ta koma gida ta yi alwala ta shige ɗakinsu ta tayar da sallah. Tana idarwa ta ɗauki ƙur'aninta ta hau karantawa domin sake tabbatar da ingancin haddarta. Ta jima sosai tana karatun kafin ta ajiye ƙur'anin ta zauna ta ci abinci. Tana gamawa ana kiran sallar Isha'i sai ta gudu tsakar gida wajen Yayarta Rabi,dan ita a kaf sallolin da suka wajaba akan mumini baligi sallar Isha'i ke yi mata wahalar sauke wa,kullum ta Allah sai sun kai ruwa rana ita da Mamanta kafin ta gabatar da sallar Isha'i. Tana zuwa ta tarar da Usman yana kwashewa Rabi miya a tuwonta yana mayarwa cikin kwanonsa. Rabi da yake tana da haƙuri sai ta yi shiru ta zabga tagumi tana kallon ikon Allah. Nansy na zuwa sai ta ƙwace kwanon Usman ta kalle shi tana harara ta ce.
Chapter 2 · 0% Book details