← Book details Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 28

Sashe 13

Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kada ki damu,mu je."

Jiki a mace Nansy ta bi bayan Malam Luƙman dake da yaƙinin idan Baban Nasibah ya tsaya ya ji ta bakinsa;zai ɗaga musu ƙafa har su kammala karatunsu sai a aura musu junansu. Su na isa Malam Sanda ya daka wa Nasibah tsawa ya kora ta cikin gida. A guje ta shige tana fatan ya tsaya ya saurari masoyin nata,wataƙila ya amince da shi ya aura mata zaɓin ranta.............
[9/26, 10:07 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA.

NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️

PAGE 10.

A sheƙe Makaɗi ya kalli Malam Luƙman daga sama har ƙasa ya ga yanda wandonsa yake a ɗage. Wayar hannunsa ya kunna ya sake haska shi ya ce.

"Kai miƙe tsaye da kyau. Duk da na kula tsananin rashin tarbiyya ya hana ka durƙusa min har ƙasa ka gaishe ni."

Tsaye Malam Luƙman ya miƙe tare da miƙa wa Makaɗi hannu dan su yi musabaha. Kallon hannun Malam Luƙman Makaɗi ya yi kafin ya ce.

"Ba shakka Luƙman! Ahh ba shakka,ai dole ka bani hannu mu gaisa tunda baka samu cikakkiyar tarbiyyar girmama na gaba da kai ba a gidanku. To tsaya ka ji,ko kana da tarbiyya ko baka da ita wannan kai ta shafa. Ni Sanda ɗan gidan Uba Makaɗi ba zan baka auren ƴata Nasibah ba har abada. Ina so a yanzu ba sai anjima ba ka tattara guntun mutuncinka da nake gani a idona saboda kasancewarka Malamin ƴata ka bar ƙofar gidan nan."

Cikin tsananin damuwa Malam Luƙman ya rusuna har ƙasa ya kama ƙafar Malam Sanda ya ce.

"Baba don girman Allah kada ka raba ni da Nasibah,na girma na rayu da soyayyarta a cikin raina,kuma itama babu wanda take so bayan ni,raba mu zai iya jawo babar matsala a..."

"A rayuwarka? To ai dama tuni a cikin matsala kake Luƙmanu. Ah yo Allah na tuba akwai matsalar da ta zarta talauci ne? Dan haka ina so ka yi min adalci nima a matsayina na mahaifin yarinyar nan,ina da buri babba akanta,ba zai yu na gama shan wahala da ita ba a rayuwa ta ɓige da auren faƙiri irinka,ni talauci kai talauci to wa zai taimakawa wani?"

"Baba na yi maka alƙawari Nasibah ba za ta yi rayuwar talauci a gidana ba. Karatun Nursing nake yi yanzu haka,da zarar na kammala zan samu aiki,Baba zan riƙe maka Nasibah da amana kuma cikin wadata."

Tsaki Malam Sanda ya ja mai tsawo kafin ya ce.

"Aikin banza,yo dika-dika albashin nas ɗin nawa ne? Ƙarƙari na san cewa za ka yi zaka kama muku haya,idan ka biya kuɗin hayar da me za ka ciyar da ita har ta dinga samun na taimaka wa iyayenta?"

"Baba..."

A tsawace Malam Sanda ya kalli Malam Luƙman ya ce.

"Kai ya isa haka! Na gaji da ja-in-ja da muke ta faman yi ni da kai. Nasibah dai ƴata ce kuma budurwa,ko a musulunci ina da haƙƙin zaɓar mata abokin rayuwa ko ba haka bane Malam?"

Kai Malam Luƙman ya ɗaga jikinsa na wata iriyar tsuma saboda tashin hankalin da yake ciki. Ido Malam Sanda ya lumshe ya buɗe su a kan Malam Luƙman ya ce.

"Madallah! To ni Baban Nasibah na ce ba kai ne zaɓin da na yi wa ƴata ba,bana so na sake ganin ka a ƙofar gidana. Idan ka haifu cikin uwarka da ubanka ta hanyar Sunnah ka rabu da ƴata,rabuwa ta har abada."

Kalaman Malam Sanda sun yi matuƙar dukan zuciyar Malam Luƙman,cike da matsanancin tashin hankali ya kafe Malam Sanda da ido yana nazarin kalamansa a cikin zuciyarsa. Malam Sanda kuwa yana gama magana ya damƙe ledojin hannunsa ya shige gidansa tare da kulle ƙofa yana mita. Yana shiga ciki ya yi ido biyu da Nasibah wadda ke ta safa da marwa a tsakar gidan tana jiran Babanta ya shigo ta ji hukuncin da ya yanke akan tarayyarta da Masoyin nata,tambayar duniya Rabi da kilishi sun yi mata akan abinda yake faruwa amma ta kasa ce musu komai. Malam Sanda na ƙarasawa tsakiyar gidan sai ya kalli Kilishi ya miƙa mata ledojin hannunsa ya ce.

"Ga wannan a giddiba shi a raba kowa a bashi kason sa. Kin dai san yanda zaki raba ba sai na faÉ—a miki ba. "

Wajen da yake zama ya koma ya zauna tare da ture tuwonsa na dare gefe yana jiran kayan daɗin da Nasibah ta kawo. Nasibah kuwa ta kasa nutsuwa sai kallonsa take yi ta ga ya yi banza da ita kamar ma ba a yi ruwanta a wajen ba. Cike da shagwaɓa ta zauna a tabarmar mahaifin nata ta ce.

"Baba to baka bani labarin yanda kuka ƙare da Mine ba."

Kyaɓe baki Malam Sanda ya yi ya ce.

"Waye hakan?"

Ta gefen ido ta wurga wa Malam Sanda harara sannan ta ce.

"Baba Malam Luƙman mana. Ka ji ya faɗa maka irin kuɗin da zai yi anan gaba ko? Baba don Allah ka yarda na aure shi har fa gini yake yi min a cikin gidansu."

"To ki ji harkar tsiya don Allah. Meye wani gini a cikin gidansu? Ya wuce ya ja miki É—aki É—aya ku yi tarayyar makewayi da uwarsa da ubansa? Ke Nasibah ina raba ki da kiwon kyalla kina kyalla ta haihu ko? Yanzu ke ba za ki yi wa kanki faÉ—a ba ki yi wa kanki fatan zuwa inda zaki huta wani naki ma ya huta? Da alama tunda kika shigo baki ga Æ´ar'uwarki Hanifah a É—aki ba ko? Yo ina za ki ganta kina nan kin kasa kin tsare kina jira na na shigo miki da mugun labari?"

"Baba Yah Hanifah ce ta zo?"

Nasibah ta faÉ—a tana mai sakin fuskarta kaÉ—an. Murmushi Malam Sanda ya yi ya ce.

"Ita ce ta zo gata can a ɗaka. Da da yanda zan yi na raba ta da abinda yake cikinta ta mayar wa da ubansa shi da na yi. Dan ni ba ɗan iska bane namiji ya gama morar ƴaƴana sannan ya haɗo su da ƴaƴansu su zo su ƙarasa kassara ni. Yanzu a ce haihuwa ba ta ɗaya ba,ba ta biyu ba haihuwa ta uku sai mace ta dawo gidan iyayenta? To na ɗaga mata ƙafa ne saboda dare,gobe da sassafe idan Allah Ya kaimu zaki tattara ki koma inda kika fito,dan ni ba mahaukaci bane da zan sayar da akuya sannan ta dawo tana ci min azara."

Kayan biki Kilishi ta ajiye wa Malam Sanda da Nasibah ta wuce tana faÉ—in.

"Sai kace mutum shi baya aika nasa ƴaƴan gidan surukansa su cinye musu nasu abincin. Idan haka ne daga yau in yaran nan za su je hutu gidan namu iyayen ka dinga ƙulla abincin da za su ci da ruwan da za su sha har su je su dawo. Haba! Allah na tuba kai ai kana raye kana nema,mu kuwa iyayenmu maza duk sun kwanta dama,iyayenmu mata ke ta faɗi tashi suna neman na rufin asirin kansu."

Ran Malam Sanda a ɓace ya nuna Kilishi da ta koma mazauninta tana ci gaba da surutai da yatsa ya ce.

"Kin ga ki kama min bakinki kafin na ɗauki mummunan mataki akan ki Kilishi. Ke har kina da bakin magana idan aka zo wannan ɓangaren? Ubanki har ya koma ga Allah bai taɓa ɗaukan zakkar da yake ba wa mutane ya bani ba,ki faɗa min,hakan baƙinciki ne ko ba baƙinciki bane?"

Kuka Kilishi ta fashe da shi ta ce.

"Yanzu Malam dan na faɗa maka gaskiya shine za ka tono mahaifina kana faɗar baƙar magana akansa? To Alhamdu lillah zakka dai haƙƙin Allah ne kuma ya bayyana mutanen da za a bawa ita,kai kuma baka cikinsu,dan haka dan mahaifina bai baka zakka ba baka da dalilin ƙullatarsa har ka dinga tono min shi kana tsina."

"Ke ar tafi can dangin marowata kawai."

Gaba ɗaya ran Nasibah ya kai ƙololuwa wajen ɓaci,dan ita bata ga amfanin faɗan da Kilishi da Babanta ke yi ba. Kuka ta saki mai ƙarfi ta shure kwanon da aka zubo wa Malam Sanda abinci  ta yi ɗakinsu na yara. Tana shiga ta tarar da Yah Hanifah na sharar hawaye,domin kuwa tunda Malam Sanda ya dawo gidan ya tarar da ita yake ci mata mutunci har sai da ta gaji da ɗaukan zagin nasa ta koma ɗaki ta kwanta tana tuno mahaifiyarsu mai sanyi hali da biyayya. Kuka ta dinga yi tana jin kewar mahaifiyarsu na ratsa ta ƙwarai da gaske. Rungume ta Nasibah ta yi ta ce.

"Yah Hanifah don Allah ki dena kuka,ki rabu da Baba ba zai fasa halinsa ba,ya kamata a ce kun saba da halayyarsa ta dena damunku."

"Nasibah ke yarinya ce,dan haka ba za ki gane abinda yake faruwa ba. Ba na yi miki fatan ki shiga cikin halin da muke ciki,amma tabbas a duk ranar da mahaifinki ya nuna miki abun duniya ya fiki muhimmanci a rayuwarsa;a ranar za ki gane halin da muke ciki."

Masifar Malam Sanda da zage-zagensa ne ya karaÉ—e gidan. Cikin fushi ya ce.

"Ke Rabi miƙo min kason wannan ja'irar da ta shurr min abincina saboda baƙar mugunta na cinye."

Da sauri Rabi ta miƙa masa abincin Nasibah da yake gefen tabarmarsa. Ci ya fara yi yana lumshe idanuwa tare da faɗin

"Arziƙi ya yi a rayuwa,yo ina ma zan bari ki auri wannan faƙara'u alallalaluratin? Ai ke Nasibah kalar manya ce kamar Samir,dan haka baki da miji sai shi.",

Tashi Nasibah ta yi a hasale za ta fita ta faɗa wa Babansu abinda ke ranta Hanifah ta riƙe ta tare da girgiza mata kai. Kuka Nasibah ta fashe da shi ta rungume Yayar tata da tsohon cikinta ya bayyana a fili. Sun jima a haka kafin Nasibah ta wuce makwancinta ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Ranta baƙƙirin saboda takaicin Mama dake jin duk abinda yake faruwa amma ta zaɓi ta yi shiru saboda neman fada a wajen Baba. Ita duk abinda ya ce ko daidai ne ko ba daidai bane a wajenta daidai ne. Shi yasa suke shiri yake ce mata ƴar aljannah saboda bata saɓa umarninsa.

**********************
Chapter 13 · 0% Book details