Sashe 7
Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwana huɗu Nasibah ta ɗauka tana jinyar jiki da zuciyarta. Sai dai babban abinda ya yi mata daɗi shine rashin sake dawowar Samir gidansu domin duba ta. Tana kula da yanda Malam Sanda ya shiga damuwa sosai,amma ita hakan sam be dame ta ba,sai ma ta ware sosai ta ci gaba da sana'ar kitso da ƙunshinta. A gefe ɗaya kuma tana zuwa makarantar boko da islamiyyah.
Haka rayuwa ta dinga tafiyarwa Nasibah kamar yanda ta ke so,domin kuwa a ɓoye suke gudanar da tsaftatacciyar soyayyarsu ita da Malam Luƙman ɗinta ba tare da sanin iyayenta ba ballantana ƴan gidansu.
Bayan shekara ɗaya Nasibah ta shiga SS 2,a shekarar ne ta yi wata ƙawa ƴar masu hannu da shuni a unguwarsu mai suna Yasmin. Nasibah ta haɗu da Yasmin ne a islamiyya har ta shigar mata faɗa ta yi uwa ta yi makarɓiya a lokacin da ake gab da yi wa Yasmin duka;saboda zargin wulaƙanta ɗaya daga cikin ƴan ajinsu har ta yi mata turancin da basu san ma'anar sa ba,daga nan faɗa ya ɓarke yarinyar ta ƙeƙasa ƙasa ta ce ai iyayenta Yasmin ta zaga ta kuma kira ta da matsiyaciya ƴar talakawa,sai da aka yi kwana biyu ana case ɗin daga ƙarshe Nasibah ta raba gardama ta hanyar shigarwa Yasmin aka dambace da ita. Tun daga wannan ranar ƙawance ya shiga tsakanin Yasmin da Nasibah. Duk lokacin da ake buki ko wani taro a gidansu yarinyar ko wani occasion ɗin Nasibah ke yi mata kitso da lalle,idan aka tambaye ta inda ake yi mata sai ta ƙi faɗa saboda tana son duk inda ta shiga a ga kwalliyarta ta fi ta kowa kyau. Yasmin ita ce ta damu da Nasibah sosai,don haka ita ce take yawan zuwa gidansu Nasibah har ta kawo mata alkhairi mai yawa,a ɓangaren Nasibah kuma bata taɓa zuwa gidansu Yasmin ba. A cewarta kuɗin iyayen Yasmin ya yi yawa daga gani za su yi wulaƙanci,ita kuma a rayuwarta ta tsani duk inda za ta shiga a wulaƙanta ta ko a yi mata kallon wulaƙanci da ƙasƙanci. Shi yasa duk kuɗin mace in dai ta je yi mata kitso ko lalle ta ga tana da wulaƙanci ba za ta sake koma wa ba ko da za ta aiko sau dubu ne kuwa. Da ta gane idan ta yi ƙorafi akan halayyar wulaƙanci ko kallon ƙasƙanci da aka yi mata a gidan yana hasala Malam Sanda ya kora ta tare da gicciya mata Allah Ya isa idan bata je ba,sai ta dena faɗan abinda ya hana ta zuwa. Lokuta da dama a gaban Malam Sanda ko Mama sai ta amsa za ta je ta ƙi zuwa.
Ana haka sai aka tashi auren Yayar Yasmin wato Yah Yusrah. Sosai Yasmin da Nasibah ke rawar kai suna jin kansu kamar a lokacin za su taɓa zuwa taron aure a rayuwarsu. A wannan lokacin ne kuma Yasmin ta ɗaura aniyar gabatar da best friend ɗinta Nasibah a wajen ƴan'uwanta.
A ɓangaren Nasibah bata da wata damuwa domin Yasmin ta saya mata kayan da za ta saka a bikin da takalmi da jaka har da mayafi. Babbar damuwarta shine rashin babbar wayar da za ta shiga taron manyan matan da bata taɓa gani ba sai labarinsu da take ji a wajen ƙawarta,dan haka take son itama ta shiga cikinsu ta saje da su gudun kada wata ko wani ya kawo mata raini. Rawar kai da shisshigin da Nasibah ke yi sosai yake ƙona ran Nawwarah da Nadiyah manyan ƙawayenta da suka tashi a tare. Sai dai har a wannan lokacin suna tsananin jin tsoron Nasibah,dan ita har a wannan lokacin tana iya zagewa ta yi dambe abunta.
Nasibah ta gama tunanin inda za ta samu wayar da za ta kece raini da ita a ranar kamun Yah Yusrah; wadda a kullum take jin labarinta a wajen Yasmin.
Ana sauran kwana ɗaya bikin gidan su Yasmin Nasibah ta ɗauki kayan ankon Kamu tana gwadawa,tana gama saka kayan ta tsaya a gaban madubin da ta bawa Usman ya riƙe mata. Kallon kanta ta yi ta ce.
"Yah Usman don Allah na yi kyau? Ka na ganin idan na shiga taron masu kuÉ—i zan saje da su?"
Hararar Nasibah Usman ya yi; kafin ya ajiye madubin ya kalle ta ya ce.
"Lallai ma Nasibah,ke yanzu baki ganki ba ne ko me? Ki na da kyau,kyawun diri da cikar halitta Nasibah,gaki uwa uba farar mace alkyabbar mata. Ko kin san cewa farin Baba kika ɗakko sak babu abinda ya banbantaku dai tsufa? Kamanninki kuma gaba ɗaya irin na Mama ne. Matsalarki ɗaya Nasibah baki ɗakko tsawon gashinta ba, duk wannan yauƙin gashin naki bai da tsawo,da ace gashin kanki na da tsawo babu mai yarda ke ɗin kin haɗa jinsi da hausawa,bafulatana kawai za a kira ki."
Baki Nasibah ta tura gaba ta zauna a gefen Usman sannan ta ce.
"Kai Yah Usman ɗin nan baka taɓa yabon mutum baka kushe shi ba. An faɗa maka fulanin dukansu kyawawa ne?"
"To ai ni ba kushe ki na yi ba Nasibah,gaskiya kika tambayi a faÉ—a miki kuma ita na faÉ—a miki. Kin san Allah har kunyar jerawa nake yi da ke,abokai na baki ji tsokanata suke yi ba suna ce min É—an aikin gidanku? Don Allah dube ni,ke nima ina ga bleaching zan fara yi."
Dariya suka yi tare da shewa duka tafa kamar wasu ƙawaye. Kilishi na jiyo hirarsu daga kitchen ta ja dogon tsaki ta ce.
"Ina raba ka da shegen tsugudidi Usman baka ji ko? Wannan abubuwan da kake yi ne ya sa a kullum kake jawo wa kanka zagi wajen mutane,yanzu meye abun buga shewa da tafa cinyar? Kai mace ne? Na ce kai mace ne? Baka da aiki sai zama a cikin mata kana lauÉ—i kana gwalli? Tashi ka fita ko na zo har wajen na buga maka wannan muciyar akai,sakarai kawai marar tunani."
Sosa kai Usman ya yi ya miƙe tsaye yana karkaɗe mazaunansa,dariya Nasibah ta fashe da ita ta ce.
"Ummah leƙo ki ga abinda Yah Usman yake yi,be ji faɗan da kike yi masa ba."
Duka Usman ya kai mata ta goce ta shige ɗakinsu na ƴammata tana ci gaba da yi masa dariya. Ƙwafa Usman ya yi ya tafi waje ya bar Kilishi na ci gaba da mita akan halayyarsa.
**********************
Rana bata karya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. Tun da safe da Nasibah ta tashi ta nemi izinin zuwa Saloon a wajen Baba,shi kuma ya amince mata domin shima yana son ta fito acan-acan a bikin da za ta je. Su Nawwarah sun jima suna kwaɗaita mata zuwa Saloon a wanke mata kanta tare da gyare mata shi ta yanda zai ƙara kwantawa ya haska kyakkyawar fuskarta,amma bata taɓa baiwa abun muhimmanci ba sai wannan karon. Dan haka cikin sauri ta gama duk wasu ayyukanta ta karya,sannan ta shiga wanka ta ƙalƙale jikinta. Tana fitowa ta kalli agogo sai ta ga ƙarfe goma da rabi na safe har ta gota,cikin sauri ta zira doguwar rigarta ta abaya akan undies da ta saka,sannan ta ɗaura agogon hannunta tare da ɗaukar ƙaramar jakarta ta riƙe. Sallama ta yi wa su Mama da Kilishi dake tsakar gida suna ayyukansu,har za ta fita daga gidan cikin sauri Mama ta ce.
"Ki kama hannun Najlah ta raka ki mana Nasibah?"
Hararar Najlah dake ta binta da kallo cike da murmushi É—auke a fuskarta sannan Nasibah ta ce.
"Ni babu inda zani da ita duƙun-duƙun kamar me tallan ƙuli."
Waje ta yi tana sake gyara zaman mayafin abayar da ta yafa a kanta da yake zamewa lokaci zuwa lokaci. A ƙafa Nasibah ta isa saloon ɗin dake nesa kaɗan da unguwarsu,saboda wajen ya yi tashe ana yawan zancen mai saloon ɗin. Sai da ta yi nisa ta dinga nadamar rashin zuwa ta jawo Nawwarah da Nadiyah su raka ta.
Da wannan tunanin ta buɗe ƙofar Saloon ɗin ta shiga bakinta ɗauke da sallama. Sosai ta yaba da yanda masu saloon ɗin suka iya tarbar kwastoma. Sai ta saki jiki ta zauna a kujerar da aka bata,littafin da hotunan gyaran gashi da ƙunshi yake ta ɗauka. A hankali ta hau duba wa daga ƙarshe ta zaɓi irin wanda take so a yi mata. Babu ɓata lokaci aka hau gyara mata kai suna hira da matar jefi-jefi.
Ana gama wanke wa Nasiba kai aka fara rolling gashinta;sai ga wasu kwastomomin sun shigo. Nasibah na ganinsu jikinta ya yi sanyi ta ji ta raina kanta. Ƴan mata ne kyawawa a ƙiyasi za su kai shekaru ashirin da bakwai ko da takwas. Sai dai kyawun jikinsu da ƙaramin jikinsu ya sa ba lallai mutum ya gane su ɗin suna da shekaru ba,wani irin ƙamshi ne mai daɗi yake tashi a jikinsu,komai nasu yana screaming ɗin dukiya ne,kama daga suturar jikinsu,sarƙa da abun hannunsu,takalmansu da wayoyin hannunsu. Nasibah da ke zaune ana rolling gashinta sai ta bi ayarin masu aiki a wajen ta gaishe su. Amsawa suka yi a mutunce suka samu waje suka zauna. Hirar ƙasar waje suka dinga yi suna yaba tsarin saloon ɗin domin babu abinda babu a cikin wajen irin na gyaran jiki.
Ana gama wa Nasibah rolling gashinta sai aka saka ta a hair dryer. Tana nan zaune tana kallon dogon gashin ƴan matan wanda take da yaƙinin ƴan'uwan juna ne;zuciyarta na yi mata saƙe-saƙe kala-kala...........
[9/19, 7:57 PM] HAERMEEBRAERHâ¤ï¸: ZAWARA.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨âœï¸
PAGE 6.
Cike da ƙwarewa ma'aikatan saloon ɗin suka kammala gyara wa Nasibah gashi,ana gamawa ta biya su kuɗin su ta yi musu sallama ta fito daga wajen cikin sauri. Da sassarfa take tafiya har ta kai ƙarshen layin da za ta sha kwana ta ɗauki layin gidansu,tana ganin ta sha kwana ta tattare doguwar rigarta ta dinga baza sauri kamar za ta tashi sama. Sai da ta yi tafiya mai nisa sosai sannan ta rage saurin tana sake damƙe jakarta a hammatar ta da kyau.