← Book details Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 28

Sashe 12

Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan fiffizgewar da kike yi kaÉ—ai ta tabbatar min da yanda kike tunawa da ni a kullum. To kar ki damu,a wannan karon dama ban shirya koma wa Abuja ba tare da na je na gaishe da Baba ba,irin gaisuwar nan ta musamman."

Cikin faɗuwar gaba Nansy ta miƙe tsaye tana kallon Samir ta ce.

"Kai Malam dakata don Allah! Haka kawai ina zaman zamana za ka zo min da wata maganar da na kasa gane inda ka dosa? Me kake nufi da ni ne?"

"Aure nake nufin ni da ke mu ƙulla. Kuma da yardar Allah sai na aure ki."

"Humm ai kuwa ka shirya samun karyewar zuciya,domin kuwa ni Nasibah ina da wanda nake so da aure yake so na. Yanzu haka da nake yi maka magana har an gama maganar aurenmu ni da shi,ina gama secondary za a yi bikinmu."

Nan take fara'a da annashuwar dake saman fuskar Samir suka kau;ƙunci da damuwa suka mamaye farincikinsa. Kasa cewa komai ya yi ya tsaya yana kallon Nasibah dake tattara kayanta za ta bar masa wajen. Kafin ta ɗago daga duƙawar da ta yi Yasmin ta dawo wajen hannunta riƙe da ledoji masu yawa. Tana zuwa ta ci karo da Samir fuskar nan a haɗe kamar hadari. Cikin sanyin murya ta kalli Nasibah da ta ɗago riƙe da jakarta ranta a ɓace ta ce.

"Nansy me ya faru? Wani abu ya yi miki?"

Tsaki Nasibah ta ja ta ce.

"Ni gida zan tafi,mun yi da Mine zamu haÉ—u a hanya mu wuce gida tare."

"Ohhh soyayya ruwan zuma,nima dai Allah Ya nuna min na fara yin soyayya Nansy."

Da sauri Yasmin ta isa gaban Nansy ta yi mata raÉ—a a kunne.

"Ni fa na zaci guy É—in nan me kyau wajenki ya zo Nansy."

Juyawa Nansy ta yi ta harari Samir sannan ta ce.

"Wa ni? Allah Ya kiyaye,ni ba waje na ya zo ba,kin ga na gaji sosai Yasmin,na matsu na je gida na raba kaina da kayan nan duk sun matse ni."

"To ko na kira Malam Sadi ya mayar da ke gida ne?"

Kafin Nansy ta yi magana Samir ya isa gaban Yasmin ya karɓi ledojin hannunta ya ce.

"Kar ki damu,ni zan mayar da ita gida. Ita É—in kamar amana ce a waje na."

A hasale Nansy ta kalli Samir ta ce.

"Malam bana son shisshigi,ta ina kuma na zamo amana a wajenka?"

"A sannu za ki gane. Mu je ko?"

Hannu Nansy ta harɗe a ƙirjinta tana girgiza ƙafarta ta ƙi motsawa. Samir na ganin haka ya saka hannu ɗaya ya damƙi nata ya ja ta da ƙarfi suka fara tafiya. Cike da tsoro Yasmin ta bi su da gudu ta ce.

"Kai Malam sake ta mana,ta ce ba za ta bika ba ana dole ne?"

"Kar ki damu ba gidan Malam Sanda Uba MakaÉ—i take ba? Can zan mayar da ita da kaina."

Yasmin na jin ya ambaci sunan mahaifin Nansy sai ta tsaya tana nazarin abinda yake faruwa. Shin ko dai akwai abinda Nansy ke ɓoye mata ne? Bata dawo daga duniyar tunani ba ta ga motar da Samir ya jefa Nansy ta wuce ta gabanta. Da sauri ta ja baya ta koma cikin gida ta shige ɗakin Gwaggoji ta ɗakko wayarta ta riƙe a hannu bini-bini tana duba lokaci.

A ɓangaren su Nansy kuwa fuskar ta tuni ta jiƙe da hawaye,domin ta tsorata ƙwarai da yanayin da ta ga Samir a cikinsa. Yanayi ne da ya tsorata ta ya firgita ƙaramar ƙwaƙwalwarta. Har suka isa gida babu wanda ya sake yin magana. Suna kai wa ƙofar gidan su Nansy ta kama hannun ƙofa tana son ta buɗe ta gudu. Jin ƙofar a rufe ne ya sanya ta juyawa ta kalli Samir dake ta kokawa da ɓacin ran da ya taso masa. A hankali ya buɗe rinannun idanuwansa ya zuba su akan kyakkyawar surar jikin Nansy. Sai a yanzu ya tabbatar da cewa yarinyar na da kyau mai fisgar hankali,kuma tana da diri irin na cikakkun ƴan mata. Lallai ba zai taɓa barin ta wuce shi ba,domin nan gaba kaɗan da ta ƙara girma za ta fi haka kyau. Daga can cikin maƙoshinsa ya ce.

"Akan wancan matsiyacin kike nuna min ƙiyayya Nasibah? Ko wancan me ɗagaggen wandon ba ke yake jira ba?"

Da sauri Nasibah ta kai dubanta zuwa ƙofar gidansu,Malam Luƙman ta gani a tsaye a jikin ginin gidansu yana kallon hanya lokaci zuwa lokaci. Kuka ta fashe da shi tare da yarfe hannu ta ce.

"Shikenan yanzu za ka jawo masifa ta hanyar dasa rashin yarda a tsakani na da masoyina na gaskiya."

Gira Samir ya ɗaga yana bin Nansy da kallo,murmushi ya yi mai sauti kafin ya buɗe motar ya fita. Zagayawa ya yi ya buɗe mata sannan ya kamo hannunta ya ja ta jikinsa ya rungumeta ta gefe. Ƙoƙarin ƙwacewa take amma ina,tuni Malam Luƙman ya yi mummunan gamo. Cike da tashin hankali da damuwa Nansy ta tattara dika ƙarfinta ta ture Samir gefe. Dariyar mugunta ya yi sannan ya ce.

"Babe menene haka?"

Da gudu Nansy ta bi bayan Malam Luƙman da ya bar wajen cike da tashin hankali idanuwansa na zubar da hawaye. Ganin rigarta da ta ɗame ta ta hana ta gudun da kyau,sai ta yar da takalmanta a wajen ta tattare rigarta ta bi Malam Luƙman da gudu ta sha gabansa tana haki. Kallonta ya yi cike da karyewar zuciya ya ce.

"Nasibah ina alƙawarin tarayya dani duk rintsi duk wahala da kika yi min? Nasibah ashe ba za ki iya jira na kammala karatuna na samu aiki mu yi aure ba? Da me wannan ɗin ya fini da kika zaɓi fita da shi akai na? Na jira ki a wajen da muka yi zamu haɗu har na gaji ban ganki ba. Nas..."

"Don Allah ka tsaya ka saurare ni,abinda wancan azzalumin yake son gani kenan a tsakaninmu,don soyayyarka da Annabin Rahama ka zo mu koma mu ba wa wancan jahilin kunya,na yarda daga baya duk hukuncin da za ka yi min ka min. Ban ci amanar soyayyarka ba,ba kuma zan taɓa ci ba har abada, Yasmin ce shaida da ƙarfin tsiya ya tura ni motarsa ya dawo dani gida kawai dan yana taƙamar Baba yana son sa. Ina fatan baka manta da wannan mutumin da ya taɓa taimaka min ya kaini asibitinsa lokacin da bani da lafiya."

A hankali kalaman Nasibah suka fara tasiri a cikin zuciyar Malam Luƙman,dan haka sai ya ja gefe suka tsaya suka ci gaba da tattaunawa,a nutse Nasibah ta warware masa zare da abawa. Nan take Malam Luƙman ya fahimce ta suka shirya. Duk abinda suke yi Samir bai tafi ba,mamakin kansa yake yi sosai da ya tsaya a ƙofar gidan talakawa kamar su Nasibah,kuma har zuciyarsa ta kamu da son ƴar talakawa kamar Nasibah. Shin ihu zai yi ya daɓa wa kansa wuƙa,ko me zai yi? Shine fa Samir wanda ƴan matan Abuja yaran masu kuɗi da ƴan siyasa ke mutuwar so,shi ne fa matashi mai tashen kuɗi da ji da kansa. Wacece Nasibah da har za ta yi masa wulaƙanci akan talaka kuma ɗan talaka mai ɗagaggen wando?

Wani irin takaicin kansa yake ji saboda soyayyar Nasibah da yake jin tana sake nunkuwa a cikin ransa. Tunawa da wanene Malam Sanda Uba Makaɗi akan son kuɗi ne ya sanya shi yin murmushi. Da sauri ya buɗe motarsa ya sake fitowa a karo na biyu;sannan ya buɗe baya ya kwaso ledojin Nansy ya isa bakin gidan ya kwaɗa Sallama. Nansy dake nesa da gidan suna ta shan soyayyarsu da Malam Luƙman bata kula da abinda Samir ke yi ba.

Babu jimawa Malam Sanda ya fito yana tambayar wanda yake sallama. Ganin Samir a tsaye a ƙofar gidansa ne ya sanya shi sakin fara'a a zuciyarsa yana faɗin.

'Ai ni na san ban yi addu'a a banza ba. Gashi Allah Ya dawo da kai da ƙafafuwanka.'

A zahiri kuwa sai ya miƙa wa Samir hannu yana faɗin.

"Ikon Allah. Alhajin Allah yau kai ne a gidan nawa? Gashi kuwa ko minti ashirin ban yi da dawowa ba,yanzu haka hannu na wanke zan ci tuwon dare na ji ana ta kwaÉ—a sallama."

Murmushi Samir ya yi mai sauti sannan ya ce.

"Allah sarki. Ni ma ai ban jima da zuwa ba,ƙanwar tawa ce muka haɗu da ita a wajen biki,to shine na ce dare ya yi bari na rage mata hanya."

Nan take Malam Sanda ya washe baki ya ce.

"Allahu Akbar. To ina ita Nasibahr?"

"Ohh sorry ban sanar da kai ba ta É—an je can suna gaisawa da wani ustaz. Baba ga kayanta ni zan wuce,dama cewa na yi bari mu gaisa tunda na zo har gida."

Nan take Baba ya gane da wa Nansy ke tsaye, sosai ransa ya ɓaci,amma sai ya danne ya kama hannun Samir da yake miƙa masa hannu su gaisa ya ce.

"Allah sarki Malamin Islamiyyarsu ne,ka san da yake bana za su yi sauka,to shine yake ɗan zuwa su tattauna akan bikin saukar. Na gode da gaisuwa Allah Ya yi albarka ya jiƙan Mahaifinka. Nan gidanku ne Alhaji duk lokacin da ka so zuwa a gaisa ka shigo kawai."

Murmushi Samir ya yi mai sauti sannan ya ce.

"To na gode ƙwarai da gaske Baba,Allah kuma ya amsa addu'o'inka. Ni zan wuce."

Hannu Samir ya sanya a aljihu ya zaro kuɗi masu kauri ya miƙa wa Malam Sanda,cikin sauri kamar mai jira haka Malam Sanda ya yi ram da hannun Samir yana durƙusawa tare da yi masa godiya. Haka suka rabu Samir na murmushin samun nasara,Malam Sanda na yaƙe tare da tunanin yanda zai ci mutuncin Nasibah.

Da gangan Samir Ya haske su Nasibah dake tsaye a jikin wata falwaya suna hira cike da shauƙin soyayya. Nan take ran Malam Sanda ya sake dugunzuma ya ɓaci. Tun kafin motar Samir ta bar layin ya danna hannunsa a aljihu ya adana kuɗinsa sannan ya hau ƙwala wa Nasibah kira.

Nasibah na jin muryar Babanta sai gabanta ya yanke ya faɗi. Cikin sauri ta kalli Malam Luƙman ta ce.

"Na shiga uku Baba ya gammu."

"Ai ni burina kenan,mu je kawai na gaishe shi na sake gabatar da kaina."

"Ba za ka gane ba,Baba baya ƙaunar tarayyarmu ko kaɗan."
Chapter 12 · 0% Book details