← Book details Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 28

Sashe 8

Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin Nasibah ta isa gida ta tsaya a wani layi ta zaro jakarta daga hammatarta ta zuge ta. Hannu ta sa a ciki ta zaro wata dalleliyar waya sai sheƙi take yi saboda kyau. Murmushin jin daɗi ne ya suɓuce wa Nasibah a lokacin da ta jujjuya wayar a hannunta tana kallonta. Cikin zuciyarta take jin wani sashe na faɗin.

'Sata kuma kika fara yi Nasibah? Me ya kai ki É—aukan kayan mutane?'

Da sauri ta furta.

"Ni ba sata na yi ba aro na yi,kuma ai na san wajen wankin kan,ina gama hidimar biki na samu wayar da zan mayar da hotuna na ciki sai na koma inda na É—auka na mayar. Su kuma sai su nemi masu kayan su basu abunsu,dan na tabbata dole za su bar lambar wayar da za a kira su idan an ga wayar."

Tana magana tana neman inda ake cire sim,kafin ta kai ga buɗe wa wayar ta hau ruri a hannunta. Gabanta ne ya yanke ya faɗi,cikin sauri ta damƙe wayar tana zare ido tare da barin inda take tsaye ta ci gaba da tafiya. Tana jin wayar ta dena ruri ta yi sauri ta cire sim card ɗin ta yi masa kyakkyawan ɓoyo a cikin jakarta. Jujjuya wayar ta yi tana murna ta ce.

"Kuma matar nan kamar ta san camera kawai nake nema a wayarta,ko irin password É—in nan da na ga Yasmin na saka wa a wayarta bata saka wa tata ba."

Hannu ta kai za ta shiga gallery,sai ta yi sauri ta janye ta kashe wayar ta mayar cikin jakarta. Da azama ta ƙara ƙaimin tafiyarta, tana isa gida ta wuce su Usman da abokansa a ƙofar gida suna hira. Ta na shiga cikin gida ta samu waje ta zauna tana mayar da numfashi da sauri da sauri. Babu jimawa Faihah ta fito daga ɗaki ta ce.

"Laaa Yah Nansy yaushe kika dawo? Kaiii kin ga kan ki kuwa yanda ya yi shegen kyau?"

Faihah na kai hannu za ta taɓa kan Nasibah ta doke hannun tana aika mata harara,itama ramawa ta yi ta ja tsaki ta tafi tana ƙunƙuni. Ko kula ta Nasibah bata yi ba,haka ma mutanen gidan dake ɗakunan su suna hutawa. Rabi da ta idar da sallar azahar ce ta leƙo ta ga Nasibah zaune tana kallon ƙaramin madubi tana taɓa gashin kan nata. Murmushi ta yi ta ce.

"Inyeen baa,kin ga yanda kan ki ya yi masifar kyau kuwa?"

A hasale Nasibah ta ce.

"Don Allah Yah Rabi ku dinga cewa tubarkallah,dama abu ba abu ba sai tankawa kuke ta yi duk ya bi ya zube a banza. Haba!"

Nasibah ta ƙarasa maganarta tare da miƙe wa ta shige cikin ɗakinsu ta kwanta tana nazarin irin gayun da za ta ci da yamma. Kyaɓe baki Rabi ta yi ta wuce ɗakin Kilishi don ta taya ta ɗaura gyaɗa mai gishiri da ta fara soyawa domin sayarwa a ƙofar gida.

Nansy na kwance ta ji muryar Mama a saman kanta ta na cewa.

"Ai sai ki tashi ki karɓi wayar ƙawarki na ta neman ki tun ɗazu. Wai yanzu ace kin fita tun kusan sha ɗaya na rana kin dawo ban isa ki shigo ki sanar dani kin dawo ba ko Nasibah?"

Cike da gajiya da kasala Nasibah ta miƙa hannu ta karɓi Nokia ɗin Mama tana tura baki ta ce.

"Mama a gajiye fa na dawo. To ki yi haƙuri."

"Ke kika sani,ba dai ke kin rantse komai sai an yi miki magana akai ba? Humm Allah Ya shiryar dake."

Waje Mama ta fita ta bar Nasibah na duba wayar tata dan ta ga wace ƙawar tata ce ta kira da bata nan. Kafin ta gama bincike wayar Yasmin ta sake kira. Cikin rawar jiki Nasibah ta amsa wayar kamar ba ita ce ta gama lauɗi tana faɗin ta gaji ba. Yasmin na gama maganar da za ta yi da Nasibah ta kashe wayar,cikin sauri da zumuɗi Nasibah ta miƙe tsaye ta na tsalle ta ce.

"Kaiii amma kuwa idan har da gaske yarinyar nan ta sama min yanda zan yi na je Abuja a jirgi ba zan taɓa mantawa da ita ba a rayuwata. Maamaaaaa!"

Nasibah ta ƙarasa maganarta da ƙwalawa Mama kira ta bar ɗakin tana murna. Tana shiga ɗakin Mama ta tarar da ita ta tayar da sallahr azahar,sai a lokacin ta tuna da itama bata yi sallar ba,amma zumuɗi ya hana ta bar Mama ta yi sallar ta cikin nutsuwa,bakinta na rawa don murna ta ce.

"Mama kin ji Yasmin ta roƙi babban Yayansu za a je dani kai Amarya Abuja?"

Mama dai bata katse sallarta ba,dan haka Nasibah sai ta fita tsakar gida da gudu tana ihun murna tana sanar da mutanen gidan itama fa za ta je Abuja kai amarya a jirgi. Nan da nan Kilishi ta fito tana fara'a ta ce.

"Inyee,da alama fa maganar Babanku ce za ta tabbata a kanki Nasibah. To Allah Ya nuna mana kin je Abujar lafiya kin samo mana ɗan Abuja mu sha biki,wataƙila muma a jirgi za mu kai amarya."

"Ai Ummah kar ki ji komai jirgin zuwa Makka za ku hau;saboda kin san Malam Luƙman ɗina ɗan Kano ne kamar yanda nake ƴar Kano,ya ce min ma yana kammala karatunsa a shekarar nan zai samu aiki,kin san aikin Nursing kana gamawa da aikin ka a hannu. To da ya samu aikin ya ce zai turo iyayensa,wataƙila ma a lokacin idan Baba ya ga yana da abun hannunsa ba zai ƙi alaƙar mu ba."

Haɓa Kilishi ta kama daga baya ta hau tafa hannuwa tana salati. Cike da mamaki ta kalli Nasibah dake alwala ta ce.

"Ke yanzu Nasibah ashe baki bar ƙwalafuci da maitar yaron nan ba? Ni a gani na idan har yana son ki kamar yanda kike son sa ai zai aiko iyayensa ko da za a ce musu ah ah an dai san da tsayayyen zancensa akan ki ko? Humm bari dai na ja baki na na ɓame,kada abu ya zo ya tabbata a ƙi dafo min kazar Hausa na goge bakina."

"Ah toh! Shi ne ya fiye miki alkhairi Ummah,dan kin san kaÉ—an daga aikina yasin na hana ki kayan daÉ—in da za a dinga kawo min."

"Na san za ki aikata Nasibahr Babanta. Amma Nasibah haka ake yin shafar kai fisabillahi?"

Dariya kawai Nasibah ta yi ta miƙe tsaye ta nufi ɗakinsu ta saka mayafin abayarta ta tada sallah. A nan ma sai da Rabi ta yi mata magana saboda gashinta ya fito waje ana gani. Nan ma bata dena sallar ba sai kawai ta ja mayafin ta rufe kan har goshinta ta ci gaba da sallarta.

Tana idarwa ta cire kayanta ta ɗaura zanin wanka ta ɗebi ruwa a randa ta shiga wanka. Nasibah ta jima tana ƙalƙale jikinta kamar bata yi wanka ba kafin ta fita;sannan ta fito ta shiga ɗakinsu ta hau ɗibar kayan da za ta saka. Mama dake zaune tana jan carbi sai ta kalli Nasibah ta ce.

"Me na ji kina faɗa game da zuwa Abuja? Ke wai me yasa baki da hankali ne? Bikin ƙanin uwarki ake yi ko na ubanki da za mu barki ki tafi kai amarya har Abuja? Kin san girman Allah Nasibah;ko babanku kika bari ya ji maganar nan sai na saɓa miki fiye da tunaninki."

Murmushi kawai Nasibah ta yi,dan ta riga ta san dama Mama ba za ta bari ba,amma ita ta san yanda za ta yi saƙo ya je kunnen Baba ba tare da ta yi abinda Mama ta hana ba.

Tana gama saka kayanta ta fita tsakar gida ta zauna a inuwa ta hau tsara kwalliya. Yanda take yin komai cike da ƙwarewa sai mutum ya rantse da Allah ta koyo kwalliyar ne daga wajen ƙwararru. Sosai Nasibah ke da talent ɗin gyaran jiki,kitso,kwalliya da lalle kowanne iri ne. Tana gamawa ta ɗauki mayafinta ta ɗora a saman kafaɗarta guda ɗaya tana juyi;Rabi da su Najlah suna kallonta suna yaba kyawun da ta yi. Ɗaurin da ta kafa ta buɗe gashinta ta gaba,ta baya kuma ta yi acuci maza shi yafi komai ƙara fitar da kyawun fuskarta. Cikin sanyin murya irin na Rabi ta kalli Nasibah ta ce.

"A gaskiya ƙanwata kin yi masifar yin kyau Barakallah masha Allah. Amma dai da zaki gyara ɗaurinki ki cire acucin nan da kika yi da ya fi,saboda kin san babu kyau haramun ne,na rasa me yasa kike son take sani Nasibah."

Harara Nasibah ta banka wa Rabi kafin ta ja tsaki ta ajiye madubin a cikin kayan kwalliyarta. Kwashe su ta yi ta kai su ma'ajiyar su sannan ta shiga ɗaki ta ɗakko jakarta da ta yi wa kyakkyawan ɓoyo ta riƙe a hannunta. Ɗakinsu ta shiga da jakar ta ɗakko sabuwar jakar da Yasmin ta siya mata ta juya baya ta mayar da waya da Sim card ɗin da ta sato a saloon. Tana gamawa ta juya ta kalli Mama ta ce.

"Mamana ya kika ganni? Don Allah ai kyawunta yanzu a samu wata arniyar motar ta É—auke ni ta kaini har wajen taron ko?"

Murmushi Mama ta yi,domin babu ƙarya ƴar tata ta yi mata kyau ƙwarai da gaske. Dan haka cikin raha Mama ta ce.

"To ai sai ki kira Malam Luƙman ɗin naki ya kai ki wajen bikin a tashi motar ko?"

Turo baki Nasibah ta yi gaba ta ce.

"In sha Allahu sai Malam Luƙman ya baku mamaki watarana Mama. Zai yi kuɗi ne,kuma kowa sai ya amfana da dukiyarsa."

"Allah Ya nuna mana lokacin Nasibah."

Sallama ta yi wa mutanen gidansu ta fito za ta tafi. Usman na ganinta ya miƙe daga cikin abokansa ya je wajenta yana kallonta yana murmushi ya ce.

"Inyeee! Nansy kin ga yanda kika yi kyau kuwa tubarkallah?"

"Yauwa Yah Usman,shi yasa nake son ka. Na gode É—an'uwana,na tafi sai na dawo."

"Au yau ba zaki roƙe ni na yi miki hoto ba za ki tafi?"

Cike da yaƙe kar ya gane halin da take ciki ta ce.
Chapter 8 · 0% Book details