← Book details Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 28

Sashe 18

Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Don Allah Alhaji Samir ka taimaka min,Æ´ata ce ta zo gida haihuwa gashi abun ya zo tun cikin dare nake neman É—an sahun da zai kai ta asibiti ban samu ba,shine na ce tunda ku ne likitocin bari na sanar da kai ko akwai wani taimakon gaggawa da za ka iya sanar da ni a yi mata kafin a samu abun hawa."

Da sauri Samir ya dire ƙafafuwansa ƙasa ya ja rigarsa yana zirawa a jikinsa ya ce.

"Give me 10 minutes gani nan zuwa gidan."

Durƙusawa Malam Sanda ya yi kamar Samir na ganinsa ya ce.

"Godiya nake yi Alhajin Allah,Allah Ya saka da alkhairi."

Yana kashe wayar ya juya ya kalli Nasibah da tsoron Allah ya gama cika wa zuciya ya ce.

"Maza shiga ki sanar da su a shirya ta wannan yaron zai zo a kai ta asibiti."

Ganin Nasibah ta kasa motsawa ne ya sanya Malam Sanda leƙa kansa cikin ɗakin ya sanar da su sannan ya shige ɗakin Mama ya sanya rigarsa mai kyau tare da fesa turare ya fito cikin shirin tafiya asibiti..........
[10/6, 7:12 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA.

NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨ ✍️

PAGE 14.

Kamar yanda Samir ya yi wa Malam Sanda alƙawari haka ya zo cikin ƙanƙanin lokaci kan nan a hargitse. Tare da shi aka taimaka wa Hanifah ta shiga cikin motarsa Rabi da Nasibah na tsaye suna jera mata sannu. Ko ci kanku bai ce musu ba banda aikin kallon Nasibah dake sanye da riga da wando na bacci irin na gumamar nan da yake yi.
Suna nan tsaye Malam Sanda da Kilishi suka fito a gurguje suka shiga motar Samir ya ja suka tafi asibitinsa. Komawar su Nasibah gida babu jimawa mijin Hanifah ya kira wayar Mama ya sanar da ita gashi nan zuwa,domin kuwa tun da Nasibah ta ji abun kunyar da MakaÉ—i ke shirin yi musu ta faki ido ta kira shi ta sanar da shi duk abinda yake faruwa. Sallama suka yi ya kashe waya Mama ta samu Nasibah ta rufe ta da faÉ—a. Baki ta tura ta shige É—akinsu ta hau shirin makaranta dan bata son zama a cikin gidan Mama ta yi ta mata mita. A gurguje ta gama shiri ta fito sanye da uniform É—inta a wanke a goge kamar ko da yaushe. Ko abun karyawa bata nema ba ta saka kai ta bar gidan tana fatan Allah Ya sa Hanifah ta haihu lafiya.

Ko a makaranta Nasibah bata da wani kuzari da walwala kamar ko da yaushe,daga malamai har ɗalibai kowa ya fahimci Nansy bata cikin yanayi na fara'a,dan haka kowa sai ya rabu da ita gudun kar mutum ya taka sawun ɓarawo a wajenta. Ana tashi ta samu Nawwarah da Nadiyah ta ce su yi mata rakiya zuwa asibitin Samir dan ta ga Yah Hanifah. Da ƙafa su Nasibah suka taka har zuwa asibitin Samir ɗin saboda rashin kuɗin abun hawa. Sai dai suna isa nurses ɗin wajen suka basu tabbacin babu jimawa aka sallami su Hanifah sakamakon ta haihu cikin ƙoshin lafiya. Lokaci Nasibah ta ɗaga kai ta kalla a jikin makeken agogon bangon dake manne a reception ɗin. Karfe uku da rabi na yamma Nasibah ta gani sai ta kama bakinta ta kulle tare da sakin wata ajiyar zuciya mai karfi. Da sauri su Nawwarah suka fita daga cikin asibitin suna faɗin.

"Yau idan muka je gida Nadiyah sai mun sha faÉ—a."

Nadiyah wadda take da mugun tsoron duka sai ta kalli Nasibah ta ce.

"Don Allah ki raka ni gidanmu ki faÉ—a wa Mommy inda muka je kar ta dake ni."

Kai kawai Nansy ta ɗaga musu suka ci gaba da tafiya a ƙafa har suka isa unguwarsu. Har gida Nansy ta kai su Nawwarah sannan ta sanar da iyayensu batun haihuwar Yah Hanifah,barka suka yi mata sannan suka yi musu faɗan da sun bari sai da suka dawo gida sannan suka je asibitin,gashi sun shiga lokacin islamiyya. Gaban Nasibah ne ya yanke ya faɗi da jin kalmar Islamiyyah. Tunanin Malam Luƙman ne ya ɗarsu mata a cikin zuciyarta. Tana fita sai ta kama hanyar makarantar islamiyyar tasu domin ta haɗu da Masoyin nata ta ji yanda suka ƙare da mahaifinta. A jigace ta isa makarantar tasu ta samu ɗalibai duk an shirshiga aji,makararru kuma na nan waje su na karatu a durƙushe a bakin ƙofar ajujuwansu. Kanta tsaye ta shiga cikin makaranta ba tare da ta damu da kallon uniform ɗinta da mutane suke yi ba. Ajinsu ta nufa domin ta yi wa Malam magana dan ya fito waje su tattauna. Sai dai tun kafin ta isa ajin ta jiyo muryar wani malamin yana karatu a madadin Malam Luƙman ɗinta. Tsayawa ta yi tana nazarin dalilin da ya hana Malam Luƙman zuwa makarantar. Tana nan tsaye ta ji muryar Mami maƙociyar su Malam Luƙman na yi mata magana. A hargitse Nansy ta juya ta ce.

"Asibiti kuma? Wanne irin asibiti? Lafiya ƙalau fa muka rabu da shi jiya. To me yake damunsa?"

Nan da nan kuka ya kwace wa Nansy,abunda babu wanda ya taɓa gani a tattare da ita kenan. Domin Nansy na da matuƙar dauriya da jure wahala saboda kada a ga gazawarta a raina ta. Cike da damuwa a saman fuskar Mami ta ce.

"Tun jiya da daddare da ya koma gida in ji Mamanmu yake kwance bashi da lafiya. Shine yau da suka ga abun ya yi yawa aka kira Yah Atiku ya kai su asibiti da motarsa, É—azu da zan taho makaranta na ga sun dawo gida."

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un! Na shiga uku ni Nasibah."

Cikin sauri Nasibah ta juya ta fita daga makarantar ko hanya bata gani da kyau saboda hawaye da kukan da yake neman ya kayar da ita a wajen. Ga yunwa da ƙishirwa da suka kassara kuzarinta. A haka ta yi ta jefa ƙafa ta na tafiya cike da tashin hankali har ta isa gidan su Luƙman. Ta na zuwa ta tarar da gidan da mutane da yawa,wannan ya shiga wannan ya fita. Babu ɓata lokaci itama ta bi sahun matan dake shiga suna jimanta yanayin ciwon da suka samu labarin Luƙman ɗin yana fama da shi. Bayan Nasibah ta shiga cikin gidan sai ta samu jikin bangon ɗakin da ta ga mata na shiga suna gaishe da Maman Malam Luƙman suna yi mata jaje tare da addu'ar Allah Ya bashi lafiya. Hawaye take ta zubarwa kamar an kunna fanfo. Tana nan tsaye ta fara jin jiri na neman kayar da ita sai ta samu waje ta durƙusa tare da jefar da jakarta a wajen. A wannan lokacin ne Nasibah ta tuna da bata yi sallah ba,gashi ko gida bata je ba. Sai dai bata jin za ta iya yin ko ɗaya a ciki matsawar bata ga abincin ruhinta ba da halin da yake ciki. Tana nan tana tunani mahaifiyar Luƙman ta fito daga ɗaki ta tsaya a gabanta ta ce.

"Ke yarinya lafiya kika shigo gidan nan tun É—azu kike ta kuka? Ko kina cikin É—aliban wannan yaron ne?"

Da sauri Nasibah ta hau gyaɗa kai tana ƙoƙarin tsayar da hawayenta da suka gaza bata haɗin kai. Ido Ummi ta ƙanƙance tana bin Nasibah da kallo. Bayan wasu ƴan daƙiƙu sai ta haɗe fuskarta ta ce.

"Nasibah ko?"

Da sauri Nansy ta ɗaga kai ta kalli Ummi kafin ta yi saurin duƙar da kanta ƙasa tana ci gaba da zubar da ruwan hawaye. Murmushin takaici Ummi ta yi sannan ta ce.

"Taso mu je ki gansa kema. Ai bai kamata ki zauna anan kina kuka ba,kamata ya yi kema ki shiga ki ga halin da mahaifinki ya jefa min É—ana a ciki saboda son abun duniya."

Kai Nasibah ta sake sunne wa ƙasa tana jin dama bata zo ba. Sai dai kafin ta gama tunanin da ta ɗakko a cikin ranta ta ji an ja hannunta,babu ɓata lokaci jikinta ya bi umarnin ƙafafuwanta Ummi ta kaita har cikin ɗakinta inda Malam Luƙman yake a kwance hannunsa da robar karin ruwa a jiki. Baki Nansy ta damƙe wani sabon kuka na taso mata mai sauti. A cikin wannan halin Malam Luƙman ya buɗe idanuwansa ya kalli Nasibah. Wani irin kallo wanda ke nuni da tsantsar so da ƙaunar da yake yi mata. Itama kallonsa ta fara yi tana takawa zuwa wajensa a hankali tana shassheƙar kuka. Murmushi Malam Luƙman ya sakar mata tare da girgiza mata kai,cikin raunatacciyar murya ya ce mata.

"Ki dena irin wannan kukan Nasibah kada kema ki kamu da irin ciwon da nake fama da shi. Ina so da ni da ke mu ɗauki ƙaddara,mu yi haƙuri da junanmu,domin kuwa na fahimci matsawar ban fi mutumin da mahaifinki ya zaɓa miki arziƙi ba to fa ba zai taɓa yarda na aure ki ba."

Cikin kuka Nasibah ta ce.

"Me Baba ya ce maka ne jiya Mine?"

"I am not yours anymore Nasibah. Ya kamata ki gane hakan tun da wuri."

Malam Luƙman ya katse Nasibah cikin numfashi mai sarƙewa. Da sauri Nasibah ta durƙusa a gabansa ta ce.

"Don Allah kada ka sake faɗar haka Mine,zuciyata ba za ta iya jure rashinka ba a rayuwata. Ka sani ina son ka,ka yi min alƙawari ko bayan ka kammala karatu za ka jira na yi candy ka aure ni,a lokacin idan Baba ya ga ka yi kuɗi zai amince ka aure ni. Dan haka ina so ka kawar da duk wani tunani na ɓacin rai a cikin ranka game da koma menene Baba ya ce maka,ka mayar da hankalinka akan karatunka Please. Kai kaɗai nake son in aura Mine."

Idanuwa Malam Luƙman ya lumshe yana jiyo ƙamshin nasara da wani irin ƙwarin guiwa yana sake shigarsa. Kafin ya yi magana Ummi ta riga shi ta ce.
Chapter 18 · 0% Book details