Sashe 26
Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cike da matsananciyar damuwa Samir ya miƙe ya ce.
"Haba Baba! Ya za ka ba wa wani ƙato dama ya je har makaranta ya ɗaukar min mata?"
Kafin Malam Sanda ya ce wani abu Samir ya miƙe ransa a matuƙar ɓace ya bar gidan. Kai tsaye gidan su Giɗaɗo ya nufa zuciyarsa na hasaso masa irin kyau da kamalar Giɗaɗo. Ya san cewa Giɗaɗo na da aure, amma ba zai taɓa manta irin kallon da ya yi wa Nasibah ba a lokacin da suka je bikinsa shi da Nuh.
Tafiyar mintuna 8 ne kacal suka kai Samir gidan. Ganin gate É—in gidan a buÉ—e kuma gidan ya cika da motoci ne ya sanya shi yin parking a waje ya fito daga motar yana tunanin yanda zai yi ya ga Nasibah.
A daidai wannan lokacin kuma Giɗaɗo na kwance a saman makeken gadonsa ya saka hannunsa ɗaya a ƙasan kansa ya tallabo kan nasa yana kallon hoton Nansy da ya yi wa kyakkyawan ɓoyo a cikin wayarsa. Ajiyar zuciya ya sauke ya ce.
"NaNSy Ƙaya."
Murmushi ya saki mai sauti sannan ya sake cewa.
"Ina son rigimarki da shagwaɓarki."
Kamar wanda aka janyo haka ya miƙe zaune ya kalli bakin ƙofar shiga ɗakinsa. Rigarsa ya saka ya ɗauki wayarsa ya fito harabar gidan. A jikin gate ɗin gidan ya hango Yasmin na ta lallashin Nansy akan ta zauna za su mayar da ita gida ko da da daddare ne. Ƙi Nasibah ta yi ta na ta share fuskarta,da dikkan alamu kuka take yi. Nan da nan Giɗaɗo ya ji zuciyarsa ta ƙuntata ya nufi wajensu da sassarfa. Ya na zuwa Samir da ke takowa zuwa wajen su Yasmin ya isa wajen fuskarsa a murtuke. Tsayawa suka yi dika su huɗun suna yi wa junansu kallon kallo. Da ƙyar Samir ya danne abinda yake taso masa daga ƙasan zuciyarsa ya ce.
"Ke wuce mu tafi gida tinda an gama walimar."
Gira GiÉ—aÉ—o ya haÉ—e waje É—aya sannan ya ce.
"Kai kuma É—in wanene a wajenta da za ka zo ka ce ta bika ku tafi?"
Murmushi mai sauti Samir ya saki saboda ya kula da alama bai gane shi ba. Jinjina kai ya yi ya ce masa.
"Ni É—in mijin da zan aure ta ne. Ke! Wuce mu tafi."
Nasibah da ta ci kukan gargaɗin da Yusrah ta yi mata sai ta zagaye Yasmin da ke riƙe da hannunta ta wuce zuwa motar Samir. Har Samir ya ja motar suka bar wajen Giɗaɗo bai sake yin ƙwaƙƙwaran motsi ba. Ya jima a haka kafin ya fizgo kalmar.
"Mijindazaiaureta?"
(Mijin da zai aureta?)
Kai Yasmin ta jijjiga masa ta ce.
"Allah Yah Giɗaɗo ƙarya yake yi,ko da bikinku ma haka ya zo ya ja ta ya mayar da ita gida ba dan tana so ba."
"To amma Yasmin ke da kika saka mu zuwa har gidan iyayenta muka É—akko ta me ya sa kika saka ta kuka?"
Jiki a mace Yasmin ta ce.
"Yah ba ni na saka ta kuka ba,na hango su ita da Yah Yusrah suna magana,kafin in ƙarasa wajensu na nemi ita Nasibar na rasa,to na ma yi zaton ko gida ta tafi sai na fita waje na hau neman ta amma ban ganta ba,daga baya ina shiga ɗakina na ganta a bathroom tana kuka. Shine fa ta ce min wai na yi haƙuri da ƙawancen mu daga yau ba za ta sake zuwa inda nake ba."
Kai GiÉ—aÉ—o ya kama yana jin tsananin takaici da tsanar Yusrah na nunkuwa a cikin ransa. A fusace ya koma sashensa ya zauna a parlour. Cikin wani irin mawuyacin hali ya furta.
"Nasibah ke kaɗai ce macen da ke saka ni a cikin wani irin yanayi na farinciki wanda na rasa tun bayan rasuwar Ummina. Dan haka ba zan taɓa bari ki suɓuce min ba face na mallake ki."
Cikin zafin nama ya ɗauki makullin motarsa ya rufe sashensa ya fito waje. Malam Sadi ya kirawo domin ya tuƙa shi saboda nauyin da ya ji jikinsa ya yi masa,dan kuwa sosai kalaman Samir suka jefa shi a cikin tsaka mai wuya. Malam Sadi na karɓar makullin mota Giɗaɗo ya shiga gaba suka ja motar sai gidansu Nasibah wato Nansy ƙaya........
[10/13, 9:43 PM] HAERMEEBRAERHâ¤ï¸: ZAWARA.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨âœï¸
*A karanta wannan saƙon yana da muhimmanci.*
*Ina kuke masoya littattafan marubuciya Hadiza D. Auta? Ku matso kusa ga wata dama ta samu. Ta fitar da promo na kwana uku kacal. Littafin da ke 1000 ya koma 700, na 700 ya koma 500.*
1. Abokin Aikina 1000
2. Baƙon Yanayi 1000
3. Dakan ÆŠaka 1000
4. Gidan Aure 700
5. Dije ƙarangiya 700
6. Shagalalliya 1000
7. Bakan Gizo 1000
8. Jiki da Jini (A'isha) 1000
9. Ruwa Da Kankara 1000
10. Gidan Aure 700
11. Zubar Hawayena 500
12. Dace da Juna 700
13. Amfanin Fitila 1000
14. Tartsatsi 1000
15. Fansar Ƙauna 1000
16. Idan Rana Ta Fitowa 500
17. Umarnin Zuciya 1500
18. Kisan Mummuƙe. 1000
*9032685442 Opay Hadiza ÆŠan Auta Ibrahim. Shaidar biya ta wannan lamba: 08022014771.*
*LAST FREE PAGE.*
*Saƙo zuwa ga duk wani mai son cigaban labarin ZAWARA,a tura 700 a satin farko da fara yin payment ta 9031416423 Hamidah Sanusi Ahmad Opay,sai a tura shaidar biya ta 09031416423. Satin farko na wucewa littafin zai koma 1k.*
PAGE 20.
Sanye take da wando irin na sojoji wanda ya yi matuƙar ɗame ta ta sama,ta ƙasa kuma ya saki sannan ya tsuke tsintsiyar ƙafarta mai sanye da rufaffun takalma. Rigar jikinta baƙa ce ta ɗame duk wani lungu da saƙo na jikinta,kanta babu ɗankwali sai tulin natural hair ɗinta da ya sha gyara ta fito daga cikin motar da ta ajiye ta a bakin gate ɗin gidan Alhaji Yusha'u Gwamnati. Ƙwanƙwasa gate ɗin gidan ta yi da ƙarfi kamar za ta ɓalla ƙofar ta shiga. Da gudu Lawi ya isa bakin gate ɗin ya leƙa ta jikin ƙaramar ƙofa ya hango Munirah tsaye tana huci kamar kububuwa,jiki na rawa ya buɗe mata tare da ja da baya yana karkarwa. A fusace Munirah ta ɗaga hannu ta wanka wa Lawi mari sannan ta ce masa.
"What took you so long to open the gate for me you fool."
(Me ya É—aukeka tsawon lokaci kafin ka buÉ—e min gate É—in kai wawa.)
Shiru kawai Lawi ya yi domin ba safai yake gane irin turancin Munirah da Samir ba. Cikin gidan ta shiga ta na ƙwala wa Samir kira,sai dai shiru babu wanda ya amsa mata. Har ta ɗauki hanyar shiga sashensa ta kula da Sakinah zaune a kujera tana danna wayarta hankalinta kwance. Cike da masifa Munirah ta isa gabanta ta ce.
"Ke! Meye ma sunan ki? Whatever barshi ba sai kin faɗa ba,dan ko kin faɗa ba riƙe wa zan yi ba. Wato dan wulaƙanci kina ji ina neman yayanki shine ba za ki kula ni ba ko?"
Kai Sakinah ta ɗaga ta kalli Munirah daga sama har ƙasa ta watsar;tare da ci gaba da latsa wayarta. Rai a matuƙar ɓace Munirah ta kai hannu za ta fizge wayar, cikin zafin nama Sakinah ta riƙe wayarta tare da miƙe wa tsaye ta nuna Munirah da yatsa ta ce.
"Ke! Mahaukaciya ki nutsu,kada ki kuskura ki yi gangancin yi min wannan haukan naki da kika saba,ina so ki dinga tunawa Hajjah ce kawai ke iya tolerating wannan nonsense É—inki,sai kuma shi wanda kike baro gidan iyayenki kika biyo shi kamar ba mace ba."
Sosai kalaman Sakinah suka ƙona ran Munirah. Da ƙyar ta shanye ɓacin ranta ta ce.
"Yeh a ƙalla gwara ni ina da masoyin da nake zuwa wajensa,ke kuma da baki da kowa sai shegen baƙin hali fa?"
Nan take hayaniya ta kaure a tsakanin su kowa na ƙoƙarin nemo kalaman da za ta yi amfani da su wajen baƙanta wa ƴar'uwarta. A haka Hajjah Barirah da Samirah suka riske su. Tsawa Hajjah ta daka musu ta rufe su da faɗa. Sakinah ko ƙala bata sake cewa ba ta koma saman kujerar da ta tashi ta cigaba da latsa wayarta. Ita kuwa Munirah sai ta fashe da kuka ta faɗa jikin Hajjah ta ce.
"Hajjah don Allah ki sa Samir ya aure ni,na gaji da wulaƙancin da yake yi min a koda yaushe. Yaushe ma ya je Abujan da har zai kamo hanya ya taho ba tare da ya sanar da ni ba?"
Tsaki Samirah ta ja ta ce.
"To sannu uwarsa,haka kawai sai ya tsaya sai kin amince masa sannan zai dawo gida ko? Ko dama dan ke yake zuwa Abuja ba aikinsa ba?"
Hannu Hajjah ta É—aga musu gaba É—ayansu kafin ta ce.
"Wai kina mufin shi Samir É—in ne ya baro Abuja a yau? To ina yake kenan dan ni ban gan shi ba."
"Hajjah da gaske nake yi ya dawo,ina samun labari a wajen Nuh na sayi ticket na biyo bayansa."
Dariya Sakinah ta fashe da ita ta miƙe daga saman kujera ta wuce su Hajjah tana faɗin.
"Wa ya ga bindi,ko kunya bata ji wai na biyo shi."
Ta ƙarasa maganarta tare da karkace baki tana yanga kamar yanda Munirah ta yi.
Zama Hajjah Barirah ta yi a kujera tare da buɗe password ɗin wayarta ta nemo Lambar Samir wanda a daidai wannan lokacin yake tsaye a bakin motarsa yana riƙe da murfin ƙofa yana jiran Nasibah ta fito. Ringing wayar ta dinga yi amma Samir ya ƙi ɗaukan wayar. Nasibah na fitowa daga motar ya ce mata.
"Mu je ciki."
Juya wa ta yi tana harararsa ta ce.
"Ban gane mu je ciki ba. Ka ga Malam ka fa dena shigar mana gida kai tsaye kamar É—akinka,akwai matan aure da Æ´an matan da ba muharraman ka ba,that is in ka san menene ma'anar muharrami."