← Book details Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 28

Sashe 19

Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ah ah Nasibah kada ki ba shi ƙwarin guiwar da zai sake raunata zuciyarsa a nan gaba. Mahaifinki jiya ya yi masa iyaka da ke,duk da Luƙman bai sanar da mu abinda ya faru ba na tabbata ba ƙaramin abu mahaifinki zai yi masa ba ya haƙura da ke. Ni na haifi Luƙman na san irin zurfin cikinsa da girman soyayyar da yake yi miki. Dan haka ina so da ke da shi ku yi haƙuri da junanku,kada ku manta har yanzu kuna da sauran lokaci a rayuwarku;musamman ma ke da kike da ƙarancin shekaru,matsawar kuna cikin masu nisan kwana ba za ku rasa abokan rayuwar da za su so ku ba."

Cikin kuka Nasibah ta juya ta kalli Ummi wadda tausayin yaran ya cika mata zuciya ta ajiye makaman faɗan dake cikin ranta ta hau lallashi. Kasa cewa komai ta yi sai ta fita daga ɗakin da gudu ta nufi hanyar fita ko jakar ta bata tsaya ta ɗauka ba. Haka ta dinga haɗa hanya har ta isa gida. Shirun da ta ji gidan ya ɗauka ne kamar ba a yi haihuwa ba shi ya sanya ta tsagaita wa da kukan da take yi. Faihah ta gani zaune a bakin ƙofar ɗakinsu tana share hawayenta. Da sauri ta wuce ɗakinsu na ƴammata ta duba bata ga Yah Hanifah ba,sai ta wuce ɗakin Kilishi ta gansu zaune ita da su Rabi da Usman,da alama wata maganar suke yi da suka ganta suka yi shiru. Tsakar gidan ta koma ta shiga ɗakin Mamanta ta ganta zaune a bakin gado ta zabga tagumi. Wajen Faihah ta koma ta ce.

"Ke me ya faru na ga gidan haka kamar an yi mutuwa,ina Yah Hanifah da jaririnta?"

Kafin Faihah ta yi magana Kilishi ta fito tana É—aure kanta da kallabi ta ce.

"Me kuwa ya faru banda halin mahaifin naki da ya saba yi a koda yaushe? Wannan yaron Samir na dawo da mu daga asibiti cike da kayan arziƙi Malam ya kirawo mijin Hanifah da ya gama ci wa mutunci a asibiti ya ce ya zo ya ɗauki matarsa su koma inda suka fito;saboda shi ba za a zauna masa a gida a cinye masa ɗan abinda zai ciyar da iyalinsa ba. Duk irin kuka da magiyar da Hanifah ta dinga yi wa bawan Allah'n nan bai haƙura ba sai da ya tattara mata kayanta ya sallame ta ta bi mijiinta. Yanzu don Allah in ba dan Nafi'u mutumin kirki bane ba ai tun abinda ya yi masa a asibiti sai ya yi silar macewar aurenta."

Ran Nasibah idan ya yi dubu ya ɓaci. Ba tare da ta ce komai ba ta shige ɗakin su ta zube a soson katifarta tana jin kamar ta yi ta kurma ihu. Sosai ƙirjinta ya yi mata nauyi,zuciyarta na zafi,ga ciwon kai wanda ta tabbata zama da yunwa da ƙishirwa ne ya jawo mata su. Lumshe rinnnun idanuwanta ta yi tana sauke numfashi da ƙyar. Tana nan kwance cikin mawuyacin hali ta ji muryar Mama na faɗin.

"Wato ke Nasibah kin rantse da Allah ni zan biki a matsayina na mahaifiyarki ba ke za ki yi min biyayya ba ko? Nan nan kika shiga har ɗakina ki ka fito ba tare da kin ce min ƙala ba. Daga ina kike tun safe sai yanzu kika ga damar dawowa gidan."

Shiru Nasibah ta yi domin bata jin za ta iya buɗe baki ta ce komai. Ganin haka sai Mama ta hasala ta ɗauki abinda Nasibah ta yi a matsayin raini da jin tashen balaga. Cikin zafin rai ta fita waje ta samo bulala ta dawo ta kulle ƙofa ta hau jibgar Nasibah wadda ke zaune kamar an dasa ta a wajen ko gezau bata yi ba. Tun Mama na dukanta tana magana har sai da ta gaji tana haki tana kallon Nasibah wadda wahala ta sanya ta zube wa a wajen a sume. Kilishi dake tsaye a bakin window tana kiran Mama sai ta fashe da kuka ta ce.

"Shikenan kin kashe ta Maryama kin ji daɗinki. Sai da na ce ki yi haƙuri ki ƙyale yarinyar nan ba ji take yi ba amma kika yi kunnen uwar shegu da ni. Za ki buɗe min ƙofar na shigo ko kuwa?"

Jikin Mama na rawa ta buɗe ƙofar ta yar da bulalar a wajen ta shige cikin ɗakinta. Sosai taurin kan Nasibah ke damun ta. Saboda gudun kada ta illata yarinyar ne ya sa take ƙyale ta tana abubuwan da ta ga dama. Gashi yanzu ta hasala ta ta yi mata dukan tsiya. A hankali ta buɗe labulen ɗakinta ta leƙa Kilishi dake rungume da Nasibah tana shafa mata ruwa a jikinta. Idanuwa Nasibah ta buɗe tana fitar da zazzafan numfashi ta ce.

"Me yasa...kika ƙwace....ni...a hannunta?...don Allah...ki barta ta kashe ni....na gaji da zama da takaicin abubuwan....da...ake yi min....a gidan nan....Baba baya so na da Malam.... Luƙman....ya kore shi yanzu....haka bashi da lafiya...ni na fi so na mutu na huta da zafin da ƙirjina yake yi min Ummaaahh..."

Nasibah ta ƙarasa maganarta tana mai rushewa da wani irin kuka mai tsananin cin rai. Daga can ɗakin Mama itama kukan ta rushe da shi tana jin cewa sakacinta ne ya jawo ƴarta ta fara soyayya tun da ƙarancin shekarunta ba tare da ta farga ta yi wa tufkar hanci ba. Gashi yanzu tana ji tana gani ƴarta na neman kangare musu a cikin gidan..........

*Don Allah wai sakacin wanene yake jawo yara ƙanana su fara soyayya da ƙarancin shekaru a makaranta,wasu ma da Malaman makarantar. Shin akwai illa a soyayya da Malamai ko babu?*
[10/8, 7:15 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA.

NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️

PAGE 15.

Da misalin ƙarfe 7:13pm Malam Sanda ya dawo gida. Ya na shiga gidan tun kafin ya kafe babur ɗinsa ya kalli Najlah da ta zo yi masa oyoyo ya ce.

"Ke ina Yayarki take ban ji motsinta ba?"

Juyawa Najlah ta yi ta kalli ƙofar ɗakin Kilishi inda Nasibah take a kwance kamar ruwa ta ce.

"Ta na É—akin Ummah bata da lafiya. Baba ka san me? Mama ce ta daketa ta mutu,Ummah ta yi ta kuka ta kira Faihah ta ce ta bata ruwa, shine da Ummah ta shafa mata ruwan ta buÉ—e ido tana kuka."

Zuciyar Mama na lugude ta fito ta samu kan Najlah ta ƙoza ta tana hararta ta ce.

"To Suda sarkin zance,faÉ—i ba a tambaye ki ba,wuce ciki kafin na sumar da ke kema."

Ƙugu Makaɗi ya kama da hannu ɗaya,hannunsa ɗaya kuma ya dafe jikin babur ɗinsa yana kallon Mama ya ce.

"Af toh na ji,ita Nasibar kenan sumar da ita kika yi ko Maryama? Akan me za ki sumar min da yarinya? Laifin maita aka kama ta da shi ko na lalata?"

Shiru Mama ta yi ta durƙusa ta shimfiɗa masa tabarma,dan ta kula da fushin da Kilishi ke yi da ita ba zai bari ta fito ta kula da mai gidan nasu ba. Ta na gama shimfiɗa wa ta kalli ƙafar Makaɗi da har a wannan lokacin bai motsa daga inda yake ba,hakan na tabbatar mata da cewa bai dena kallonta ba,fuska a cure ta ce.

"An dawo lafiya?"

A hasale MakaÉ—i ya ce.

"Da masassara na dawo Maryama. Na ce da masassara na dawo. Za ki bani amsar tambaya ta ko sai ranmu ya haɗu gaba ɗaya ya ɓaci?"

Fuska a É—aure Mama ta kalle shi ta ce.

"Kai ka san taurin kai da rashin jin Nasibah Malam,shine dan an hukunta ta kake yi min tsawa?"

"Hukunci? Hukuncin ne zai kai ki ga sumar min da yarinya?"

"Ni ban sumar da kowa ba."

Mama ta faɗa tana mai shige wa ɗakinta;domin zuciyarta ta kasa yin haƙuri ta bashi abincin da ta yi niyya. Ta na shiga ciki ta dafe ƙirjinta da ke yi mata lugude,a bakin gado ta zauna tana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. Makaɗi kuwa sai ya hau ƙwala wa Nasibah kira yana taku cikin sauri,a bakin ƙofar ɗakinsu ya tsaya ya ɗaga labule yana faɗin.

"Wai Nasibah bata ji na ne?"

Cikin kuka Nasibah da ta yunƙura da ƙyar ta fito daga ɗakin Kilishi ta ce.

"Baabaa."

Da sauri Malam Sanda ya juya idanuwansa suka sauka akan Nasibah dake jingine a jikin gini tana risgar kuka. A sukwane Malam Sanda ya isa gabanta ya kunna hasken wayarsa yana duba ta. Ganin shatin bulalai a jikin Nasibah sun kwanta sun yi jawur ne suka sanya shi sakin wayarsa a ƙasa yana salati. Ji ya yi kamar ya kurma ihu. Cikin ɓacin rai ya isa ɗakin Mama wadda ta yi saurin tayar da sallah ta yi sujjah. Malam Sanda na zuwa ya ga abinda take yi sai ya ce.

"Maryama idan shekara dubu za ki yi kina sallah,ni kuma zan shekara dubu da É—aya ina jiran ki idar. Ba zaki dakar min yarinya ki ci bulus ba,a yau ba sai gobe ba za ki tattara ki tafi gidan iyayenki,ba zan É—auki wannan sabon salon fushin rashin hankalin da kika fito min da shi a gidan nan ba. Ke Nasibah zo nan!"

Ƙafafuwan Nasibah na rawa ta fara tattaki zuwa wajen Malam Sanda. Sai dai kafin ta isa gabansa ta zube a wajen tana aman ruwan kunu da tuwon da Kilishi ta ɗura mata. Hankalin Malam Sanda ba ƙaramin tashi ya yi ba,kafin Kilishi da ta fito daga ɗakinta jin Nasibah na amai ta isa gaban Nasibah Malam Sanda ya riga ta. Tallabo Nasibah ya yi yana haki ya ce.

"Wai me ya faru a gidan ne da bana nan har aka yi yunƙurin hallaka min ƴa?"

"Yanda ka ganta nima haka na ganta Malam,kawai ka kama ta ka kai ta Kemis ɗin Ɗan Small ya bata maganin zazzaɓi da ciwon jiki."

A wannan ranar Makaɗi ko tuna wa da Samir bai yi ba ballantana ya nemi taimakonsa. A gaggauce ya sunkuya ya ɗauki Nasibah a hannu ya nufi ƙofar gida da ita. Su na fita suka ci karo da Usman ya dawo daga wajen abokansa. Da sauri ya isa gaban Makaɗi ya karɓi Nasibah ya goya ta yana faɗin.

"Baba ina za ka kai ta haka?"

"Mu je ka kai ta wajen ÆŠan Small ya duba min ita."
Chapter 19 · 0% Book details