Sashe 5
Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai Baba irin ƙwaƙwalwarka gare ni,shi yasa nake gane karatu sosai har nake gyara maka wasu kalmomin idan ka faɗa ba daidai ba,kuma na sanar da kai ma'anarsu."
"Tabbas babu ƙarya Nasibah da ace ke namiji ce da sai na ce babu ta inda kika baro ni."
"Na bar maka ƙaton tumbinka mana Babana."
Dariya suka fashe da ita kafin Malam Sanda ya kai mata duka ta goce,cikin dariya ya ce.
"Ja'ira,wannan tumbin da kike yi wa tsiya kullum na kuÉ—i ne."
"Baba tun da can baka yi kuɗin ba sai yanzu da ka fara tsufa? Kuma ai na ji ƙawayena na cewa masu facin taya ba sa yin kuɗi."
"Ke yanzu Nasibah mutum ya haifi kamar ki a yi masa kallon talaka? Ai ni nan da kike gani nan gaba kaÉ—an zan zama surukin mai kuÉ—i,kin ga daga nan nima na zamo mai kuÉ—in."
Dariya Nasibah ta yi sosai har idonta na fitar da ƙwalla kafin ta ce.
"To kai Baba wa ya ce maka Malam Luƙman na da kuɗi? Shima fa talaka ne kamar mu,bashi da sisi,abinci ma Mamansa ke bashi."
Nan take Malam Sanda ya haÉ—e fuska ya ce.
"Wai Nasibah kina nufin har yanzu baki rabu da matsiyacin yaron nan ba ashe?"
Jikin Nasibah ne ya hau tsuma,tuni ta ja da baya ta sauka daga saman tabarmar da Malam Sanda ke kai ta hau sosa kai. A hasale Malam Sanda ya daka mata tsawa ya ce.
"Ba dake nake magana ba Nasibah!"
Shiru Nasibah ta sake yi ta miƙe tsaye za ta gudu cikin ɗaki. Murfin kwano Malam Sanda ya ɗauka ya riƙe,sannan ya kalli ƙofar ɗakin Kilishi ya ce.
"Rabi! Ke Rabi kina ina? Usman ku zo nan."
Da jin Malam Sanda ya kira Yayunta sai ta hau kuka tana dira ƙafa ƙasa tare da faɗin.
"Ni Baba shi nake so,ya ce fa idan ya gama makarantar nan da yake yi zai samu aiki babba sai ya turo iyayensa a saka mana rana,ina gama makaranta za a yi aurenmu da shi."
"Sai dai a saka ranar auren uwarsa amma ba dai ke da shi ba Nasibah. Ka ji min matsiyacin yaro yana fama da talauci shine yake hure min kunnen Æ´ata ta bijire min. To daga yau kin dena zuwa makarantar daren nasu;ke ta asabar da lahadin ma na cire ki wata zan sauya miki. Gwanda ki dinga zuwa can Sani Me nagge ki koyo karatun. Rabi da Usman,ku na ji na ko?"
Da sauri suka haÉ—a baki wajen faÉ—in.
"Eh Baba muna jinka."
Ido Malam Sanda ya ƙanƙance a cikin duhun yana nuna su ya ce.
"Duk ranar da yarinyar nan ta sake tsayuwa da matsiyacin yaron nan baku faÉ—a min ba sai na yi muku duka a cikin gidan nan,kun ji na faÉ—a muku. Yauwa ke Rabi kin sanar da Jabir É—in ya turo manyansa ko yaya?"
Guiwowinta ta zube a wajen ta kasa bashi amsa,domin tun daga ranar da Malam Sanda ya ce saurayin nata ya turo bai sake zuwa ba. Kilishi da ta cika ta batse da halayyar mijin nasu sai ta fito tana É—aure kanta da adiko ta ce.
"Ba fa zai yuwu ƴar so ta ɓata maka rai ka huce akan ƴaƴan ƙi ba. Lokacin da kuke ƙusƙus ɗinku ka ƙunso abu a takarda ka damƙa mata ai duk muna jinku;amma babu wanda ya tanka ku,sai yanzu da ta ɓare a tsakaninku za ka tasa min yarinya a gaba da masifa? To Jabir ya danna layar zana,tun lokacin da ka ce ya turo magabatansa ko magabayansa bamu gani ba ballantana shi."
A hasale ta kalli Rabi da Usman da suke durƙushe a wajen cike da damuwa ta ce.
"Ku tashi ku je ku yi shirin bacci. Allah Ya bamu alkhairi. Ita kuma da kake yi wa tanadin mai kuÉ—i Allah Ya bata mai kuÉ—in idan lokacin ya yi sai ku siyar da mu ku siyo wasu dabbin iyalin ku ci gaba da rayuwa da su."
Borin kunya duk ta hana Malam Sanda yin cikakkiyar magana,da ƙyar ya samu ya ce.
"Inyeeee lallai ne Kilishi wuyanki ya yi kauri."
Fari Kilishi ta yi da idanuwanta sannan ta daki cinyarta ta ce.
"In ɗakko maka wuƙa ka yanka ne Malam? Haba! Kai kenan baka da aiki sai nuna banbanci a tsakanin ƴaƴanka? Da ace gaba ɗaya yaran Maryama kake yi wa haka da sai in ce ni ce baka so,amma itan ma ka bi ka ware ƴa ɗaya a cikinsu kana fifita ta kamar da gwal aka sassaƙe ta,gashi ta sanadiyyar abinda kake yi yaran Yaya gaba ɗaya sun dena zuwa gidan nan,Hauwa dake daure halayenka take ɗan zuwa jefi-jefi itama ka kore ta da halinka,yanzu idan jikokinka basu zo gidanka sun ci sun sha ba a ina ne ya fi dacewa su yi hakan?."
Kai kawai Malam Sanda ke jinjinawa ya kasa magana,domin kuwa gaba ɗaya a kalaman Kilishi babu inda ta yi masa ƙarya. Nasibah da ta samu faɗan Kilishi ya ɗauke hankalin Baba akan maganarta da Malam Luƙman ɗinta sai ta saci jiki ta faɗa ɗakinsu na yara ta kwanta tana tunanin ko sama da ƙasa za ta haɗe babu wanda ya isa ya raba ta da masoyinta......
[9/17, 9:44 AM] HAERMEEBRAERHâ¤ï¸: ZAWARA.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨âœï¸
PAGE 4.
Washegari da safe Nasibah ƙin tashi ta yi ta shirya zuwa makaranta. Duk yanda Rabi ta yi da ita dan ta farka ƙi ta yi,daga ƙarshe ma juyi ta sake yi ta mayar da kanta baya ta buɗe baki ta ci gaba da baccinta hankali kwance. Rabi da bata da hayaniya sai ta fita tsakar gida ta hau taya Mama aikin safe. Mama kuwa babu abinda ya dame ta da shiga sabgar Nasibah,a cewar ta idan tana yawan saka damuwar Nasibah a zuciyarta watarana za a wayi gari a samu ta haɗiyi zuciya saboda baƙinciki,ko kuma ta yi wa Nasibah dukan da sai ta nakasa ta,dan haka kowa ya yi rayuwarsa a gidan kada ta shiga sabgar Mama,itama Mama kada ta shiga Sabgar Nasibah. Usman na gama ɗiban ruwan cikin gidan ya koma ya ɗebo na wankansa ya shiga wanka ya yi shirin makaranta. Hatta da su Najlah da Faihah sun gama shiri,amma gimbiya Nasibah bata da niyyar fitowa ballantana ta shirya. Duk abinda ke faruwa Malam Sanda na gani,sai dai fushin da yake yi da Nasibah ya hana shi tambayar inda take.
Lokacin da Kilishi ta tashi daga baccin safen da ta koma ta fito tsakar gida;sai ta ga kowa cikin shirin makaranta yana karyawa,amma banda Nasibah. Kallon Rabi ta yi ta ce mata.
"Ke ina Æ´ar'uwarki take? Ko kutaren ne basu sauka ba ta tafi bata karya ba?"
Kai Rabi ta girgiza,nan take Malam Sanda ya baza kunne dan ya ji amsar da za a bayar akan shalelen nasa. Kafin Rabi ta yi magana Usman ya yi dariya,cike da yanga irin ta mata ya ce.
"Tana can tana bacci ta hangame baki kamar wata Saniya."
Rai a ɓace Kilishi ta ce.
"Kai Usman bana son tsokana,kada ka sake kiran ƙanwarka da Saniya. Ke kuma me yasa baki tada ita ta shirya ba gudun kada ta makara?"
"Ummah na tashe ta fa,ita ta ƙi tashi."
Ba tare da Kilishi ta sake cewa komai ba ta zundumi wata ƴar bulala dake yashe a ƙasa ta yi cikin ɗakin,tana zuwa ta ga yanda Nasibah ta kwanta a malkwaɗe,ƙafa gefe guda ƙugunta gefe ɗaya,kanta kuwa ya yi baya sai kace matacciya. Bulalar Kilishi ta ɗaga ta zabga mata a cinya, cikin magagin bacci Nasibah ta sosa tare da faɗin.
"Yah Rabi Allah se na rama,ko na ja miki doguwa."
Juyi ta sake yi za ta ci gaba da bacci Kilishi ta ɗaga bulalar da kyau ta sake lafta mata,a gigice Nasibah ta farka tare da wage baki ta rusa uban ihu. Tana yin ido biyu da Kilishi sai ta ja baya tana ƙanƙame jikinta tare da rufe bakinta tana toshe kukanta. Ido Kilishi ta zaro mata waje ta ce.
"Tashi ki fita ki shirya dan ubanki."
A guje Nasibah ta bar ɗakin ta yi wajen randunan ruwansu ta hau ɗiba a buta tana kuka. Tana gama ɗiba ta shiga banɗaki ta kama ruwa sannan ta fito ta ɗakko brush ɗinta da toothpaste ta hau wanke baki. Ta na gamawa ta wanke fuskarta da ƙafarta da sabulu. Kai kawai Mama ta jinjina tare da faɗin.
"Allah Ya shiryar dake Nasibah."
Baki Nasibah ta tura gaba ta isa wajen Mamansu ta durƙusa ta ce.
"Ina kwana."
"Lafiya."
Shine abinda Mama ta ce mata tare da tura mata kwanon abincinta da kofin koko. Ɗauka Nasibah ta yi kamar bata so ta isa ƙofar ɗakin Kilishi ta tsugunna ta ce.
"Ummah ina kwana."
"Lafiya ƙalaou Nasibah,maza don girman Allah ki shirya ki bi ƴan'uwanki ku tafi makaranta. Ke da kika shiga SS 1 me ya haɗa ki da makara balle fashi? Ko so kike yi a bawa wata monitan ajin a hana ki saboda kina makara da fashi?"
Kai Nasibah ta girgiza, idanuwanta na cikowa da ƙwalla ta ce.
"Ummah kayana fa sun yi datti,jiya Baba ya...."
Malam Sanda dake zaune a ƙofar ɗaki ya riƙe radio a hannunsa amma hankalinsa gaba ɗaya yana wajen Nasibah,tuni ya tari numfashinta ya ce.
"Ahir na sake jin kin kama suna na a bakinki Nasibah. Ni zan yi miki wankin inifom É—in naki da za ki kira sunan Baba a maganarki?"
"To ba kai bane ka jawo ni a saman bishiya ka hau jibgata duk ka ɓata min kayana."
"Da na jawo ki daga saman bishiya janki na yi a ƙasa? Kuma idan da kin so wanke kayanki ai da na fita da kin wanke su."
Ƙunƙuni Nasibah ta hau yi tana cin abincinta tare da jaddada ita babu inda za ta je da kaya masu datti. Rabi na jin haka sai ta tashi ta shiga ɗakinsu ta ɗakko wa Nasibah wankakku kuma gogggun kayanta ta miƙa mata ta ce.
"Gashi ki saka tunda ni na gama babu abinda zan yi da su."
Baya Nasibah ta juya mata ta ce.
"TabÉ—ijam! Allah ba zan saka tsofaffin kaya ba,ni sabona za a wanke min."