Sashe 21
Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi Nasibah ta yi ta juya wa Rabi baya ba tare da ta sake cewa komai ba. Rabi kuwa sai ta zauna ta dinga yabon kyau da gayun Samir tana zuga Nasibah akan ta manta da Malam Luƙman ta amince da auren Samir. Cike da karyewar zuciya Nasibah ta juya ta kalli Rabi ta ce.
"Yah Rabi don Allah ki dena yi min irin waɗannan kalaman domin za su sa na ji kamar kema ba kya so na. Kin kuwa san irin zurfin son da muke yi wa junanmu? Har yau bashi da lafiya tun da ya zo Baba ya gaggaya masa baƙaƙen maganganu. A bakin Mami na samu labarin jininsa ya hau har yanzu suna faman zaryar zuwa asibiti."
"To Nasibah yaya za ki yi? Ai a hakan za ki yi haƙuri ki daure ki rabu da shi ya gama jinyarsa ya samu wata ya aura;kema ki auri Samir ɗinki..."
"Ni ba Samir ɗina bane. Malam Luƙman ne zaɓin raina har gaban abada. Ya min alƙawarin zai jira ni har na kammala secondary school,nima kuma na yi alƙawarin ba zan auri kowa ba idan ba shi ba."
Ajiyar zuciya Rabi ta sauke ta jingina da jikin gado ta ce.
"Nasibah ina so ki gode wa Allah domin ya kawo miki babbar damar da za ki huta wani naki ma ya huta. Kina gani ni har yanzu ko mai gyaran takalmi ban samu ba a matsayin manemin aurena,amma ke kin samu mutum kamar Samir kike ƙin sa."
"Don girman Allah Yah Rabi ki ƙyale ni da maganar wannan me kama da matan. Ni fa a rayuwata na tsani farin namiji,ganinsa nake yi kamar ni da shi bamu da banbanci. Amma idan kina son Samir ya zamo surukin Baba ki je na bar miki shi ki aura."
"Daga baki shawara shine zaki faɗa min bakar magana Nasibah? Allah Ya baki haƙuri ni na yi nan."
Rabi ta ƙarasa maganarta tare da fita daga ɗakin ranta babu daɗi. Tabbas da ita Samir ya nuna yana so ba za ta tsaya ɓata lokaci ba za ta amince,amma kuma tinda ƙanwarta yake so dole ta kama kanta,nan take ta yi wa kanta alƙawarin ba za ta sake saka baki akan rayuwar auren Nasibah ba ballantana har ta faɗa mata maganar da za ta ɓata mata rai.
A ɓangaren Samir kuwa yana fita daga gidan ya yi wa wani abokinsa waya ya yi order ɗin kayan ɗaki masu kyau har da carpet da zannuwan gado. Babu ɓata lokaci aka buga lissafi ya aika kuɗin sannan ya tura adireshin gidan Malam Sanda Uba Makaɗi. Yana gamawa ya koma gida ya hau shirin tafiya Abuja,domin gaba ɗaya Munirah ta hana shi sakat da kiran waya da saƙonni.
A ranar da yamma Samir ya bar garin Kano zuwa Abuja,daf da magariba kuma kayan É—akin da ya siya wa Nasibah suka isa gidan. Kamfanin da kansu suka shiga har É—akin su Nasibah MakaÉ—i na yi musu jagora suka fitar da kayan É—akin nasu suka share suka gyara shi tas bayan sun fitar da kayan ciki,sai suka jera wanda suka zo da su sannan suka kafa labulaye suka tafi.
Malam Sanda ji ya yi kamar ya kori yaran shi ya karɓi ɗakin,sai dai kuma yana tsoron kada Samir ya sani ya ji babu daɗi. A wannan ranar Malam Sanda har bayan Isha'i yana ɗakin suna ta hira shi da yaran nasa. Cikin hirar tasu ne yake cewa Usman.
"Ka ga abinda yasa nake son arziƙi ko Usumanu? Shi fa arziƙi har zumunta yake gyarawa,yanzu yaushe rabon da na zauna da ku irin haka a yi wasa a yi dariya uhumm? To ko da yaushe ina wajen ƙwadago,ina ka fito neman na kai ina zaka je neman na kai."
Gaba ɗaya yaran sun gasgata zancensa banda Nasibah da ta shimfiɗa tsohon soson katifarta ta kwanta a ƙasa ta juya musu baya. Lokacin da Malam Sanda zai bar ɗakin sai ya ɗaure fuska tamau ya ce.
"Ke Nasibah tashi ki haye gado kafin na saɓa miki a cikin daren nan. Ka ga min shegiyar yarinya mai kafurin taurin kai? Halayyarki fa ta fara kai ni maƙura Nasibah."
Makaɗi ya ƙarasa maganarsa yana mai nuna wa Nasibah yatsa yana ƙanƙance ido. Waje ya fita yana ci gaba da rantsuwa idan Nasibah bata hau gado ta kwanta ba sai ya koma ɗakin ya yi mata dukan tsiya. Kan dole ba dan ta so ba ta hau gadon tana gunjin kuka kamar wadda aka yi wa shegen duka. Su Faihah tuni suka yi bacci a saman gadon.
Rabi kuwa da ta ga yanda Nasibah ke cike da ƙunci sai ta yi shiru bata ce mata komai ba, bayan fitar Usman daga ɗakin sai ta sauka daga gadon ta kulle musu ƙofa. Gidan abokinsa da yake kwana ya yi wa iyayen nasa sallama ya tafi. Tun daga wannan ranar Nasibah ta saki jiki ta ci gaba da hawa gadon ba dan ranta yana so ba.
Bayan kwana biyu ta kama washegari sunan ɗan gidan Hanifah. Dan haka Yah Hauwa da Yah Lawizah sun zo gidan daga su sai kayansu,sun baro yaransu a gidan mazajensu gudun kada Makaɗi ya yi musu cin mutuncin da ya saba. A wannan ranar da ta kama lahadi babu makaranta sai gidan ya kacame da murna. Hatta Nasibah da ta saba yi musu rashin kunya ta yi murna sosai da zuwansu. Suna shiga ɗaki suka ga ƙaton gadon da aka girka a ciki sai suka hau yaba wa suna sake zuga Nasibah akan ta amince da auren Samir kawai ta manta da Malam Luƙman. Baki Nasibah ta kumbura tana ƙunƙuni ta fice waje ta bar musu ɗakin. A wannan ranar a ɗakin Mama Nasibah ta kwana saboda yanda ɗakin nasu ya cika.
Washegari da safe duka ƙannenta sun yi shirin tafiya gidan suna,ita kuma sai ta yi shirin tafiya makaranta. Ko da Mama ta yi mata magana sai ta ce.
"Mama idan an tashi daga makarantar zan wuce can,kin ga kayana nan na É—iba a jaka."
"To shikenan sai kin dawo."
Wajen Malam Sanda Nasibah ta je ta tsaya tana wani ciccin magani,shi kuwa sai ya saki fuska ya kalle ta ya ce.
"Ƴar Baba ke ba za ki je gidan sunan ba ne a samu yau a ɗaga wa girki ƙafa a gidan nan?"
"Ni sai na taso daga makaranta zan je Baba. Baba ka bani kuÉ—in break na tafi kar na makara."
HaÉ—e fuska MakaÉ—i ya yi ya ce.
"Ke matsala ta da ke Nasibah bani-bani. Yanzu fisabillahi ba za ki tausaya wa aljihuna ba saboda ciyar da bataliyar da na yi da safen nan?"
"Habaa Baba in da ina da kuÉ—i ai kai ma ka san ba zan ce ka bani ba. Rashin lafiyar nan da na yi kwana biyu ne ya sa bana iya kitso da lalle,shi yasa bani da ko sisi. Kuma Baba ka ga su Yah Hauwa duk sun yi lallen suna da sabon kitso,Yah Rabi ma ta yi sabon lalle da kitso ni kaÉ—ai ce ban yi komai ba."
Cike da hargagi da hargowa Makaɗi ya zaro ɗari biyar ya miƙa wa Nasibah ya ce.
"Ƙalatacciya ga su nan a je a kashe. Kar kuma ki kuskura ki faɗa min ba za su ishe ki ba,dan ba wasu zan ƙara miki ba."
Jujjuya kuɗin Nasibah ta yi a hannunta ta buɗe baki za ta yi magana,kamar Makaɗi zai dake ta haka ya yunƙura yana sababi,da gudu Nasibah ta bar gidan tana ɓata rai domin ba haka ta so ba.
A wannan ranar gaba É—aya ahalin MakaÉ—i suka É—unguma suka tafi suna,domin kuwa da kansa ya kulle gidan ya tafi da makulli. Cikin ransa kuwa sosai yake jin daÉ—in tafiyar su gidan sunan saboda É—auke masa nauyin ciyarwar wannan ranar.
Da misalin karfe biyu da rabi Nasibah ta isa gidan Yah Hanifah,a nan ta tarar da ƴan'uwanta gaba ɗaya suna zaune a ɗaki ɗaya an kawo musu abinci mai rai da lafiya suna ta ci suna hira hankalinsu kwance. Gaishe su ta yi sannan ta sauya kayan jikinta ta fita wajen Yah Hanifah suka gaisa. Da yamma aka kirawo me hoto ya ɗauki hotunan tarihi. Da za su tafi sai dangin mijin Hanifah dake kan abinci da naman suna suka cika musu ledoji da kayan suna har da naman suna,ɗaya daga cikin ƙannen Baban Aslam ɗin ce ta karɓa ta kai musu har ɗaki. Ta na zuwa ɗakin da su Yah Hauwa suke sai ta tsaya tana kallon su Yah Hauwa da su Mama a yatsine ta ce.
"To tinda ku ba a cin naku saboda tsiya da ta yi muku yawa gashi nan ku tafi da guziri. Allah Ya bada ladan zumunci."
Shiru kowa ya yi saboda mutuwar jiki da kunya da ta kama su. Nasibah kuwa nan take ta hasala ranta ya ɓaci. Cike da tsananin ɓacin rai ta isa gaban matashiyar da za ta girme ta da kaɗan ta ce.
"Uwarki da ubanki ne matsiyata amma ba mu ba. Shi mai kuÉ—i dama yana faÉ—a ne?"
Ƙanƙance ido yarinyar ta yi ta ce wa Nasibah.
"Ke ni kika zagar wa iyaye?"
"Ni turame kika gani a bayana da kike zaginsu ba iyaye ba?"
"To wa ya sani ko tura..."
Kafin ta kai ayar maganarta tuni Nasibah ta gaura wa fuskarta mari. Nan take dambe ya kacame a tsakaninsu. Da ƙyar su Yah Hauwa da sauran dangin mijin Yah Hanifah dake waje suka iya raba faɗan. Sosai yarinyar ta sha baƙar wahala a hannun Nasibah,banda hawaye babu abinda take yi ta kasa cewa komai. Ganin haka sai kowa ya yarda da abinda Nasibah ta faɗa,dangin mijin Hanifah sai suka ba wa su Mama haƙuri suka tattara kayan flour da lemon roba tare da naman sunan da ya zube a ƙasa suka sauya musu leda suka basu. A nan ne Nasibah ta yi tsalle ta dire ta ce ba za su karɓi kayan ba tunda aka kira su da matsiyata. Sai da Yah Lawizah da ke da zafin rai ta daka mata tsawa sannan ta shiga hankalinta ta fita daga gidan cikin fushi ta kama hanyar tafiya gida ita ɗaya a ƙafa.