← Book details Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 28

Sashe 11

Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

In ji Gwaggoji ta ce,tun Yah Giɗaɗo na kashe mana kuɗi ni da Mama tana jin daɗi har sai da kishi da ƙyashi ya shiga zuciyarta;ta fara tunanin a ina yake samun kuɗi bayan shi ɗin karatu yake yi? Lokacin da Mama ta fito da hassadarta da ƙiyayyar da take yi wa Yah Giɗaɗo a fili sai Abbah da Gwaggoji suka kira meeting aka zauna,anan ne Abbah yake sanar da Mama irin dukiyar da Yah Giɗaɗo ya mallaka na gadon mahaifiyarsa;ciki har da kamfanonin ƙera tabarmi guda biyu,da na shigo da Electronics daga ƙasashen waje dake a can Abuja. Yah Yunus ya mallaki gidan mai a garin Abuja,wanda dika yana cikin gadon da mahaifiyarsa ta bar masa. Jikin Mama sai ya yi sanyi a wannan lokacin ta rage adawa da nuna wa Yah Giɗaɗo ƙiyayya a fili. Amma har yanzu kowa ya san bata son sa bata ƙaunarsa,dan ko ni nan da take mahaifiyata ina sane da irin ƙiyayyar da Mama take nuna wa Yah Giɗaɗo. Bayan rasuwar Abbah da shekara biyar ta fara cusa wa Yah Giɗaɗo Yah Yusrah,ita ta ƙara rura wutar soyayyar Yah Yusrah a zuciyarsa,domin a kullum nuna mata take yi idan ta aure sa har ta haihu da shi kaf dukiyarsa za ta dawo wajenta da ƴaƴanta. To kin ji taƙaitaccen tarihin gidan nan. Yauwa,kuma da na ce miki shekarata sha bakwai nima ƙarya nake yi,shekarata sha huɗu a duniya,saurana watanni biyar na cika sha biyar,girman jikine kawai ya sa nake yin ƙaryar shekaru saboda na samu ƙawa daidai da girma na."

Ido Nasibah ta waro,kafin jikinta ya saki ta yi ajiyar zuciya mai ƙarfi,nan take zuciyarta ta cika da tausayin Yunus. Jiki a sanyaye ta wanke hannunta da ruwan robar da ke wajen ta ce.

"Ke ni fa ina jin ta bakin Yayarki za a yi,zuwa zan yi na adana mutuncina a gidan ubana;zama na anan hatsari ne babba."

"Hatsarin me kuma Nansy? Don Allah ki zauna a gama kamun nan da ke,baki ga har an gama deco ba masu DJ sun zo? Na tabbata jira ake a yi sallar la'asar a fara. Kin ga bani da ƙawaye,ke kaɗai ce ƙawata Please ki zauna."

Yasmin ta ƙarasa maganarta cike da shagwaɓa. Murmushi Nansy ta yi ta ce.

"Ba za ki gane halin da nake ciki bane Yasmin. Amma babu komai zan zauna,sai dai fa da na ga daga-daga zan arce na ware gida."

"Na ji na yarda,da kin gaji kawai ki sanar dani na baki abun biki ki kai wa Mama da su Najlah."

Murmushi kawai Nasibah ta yi,ta samu waje ta sake lafe wa a jikin kujerar da take kai tana hango duk abinda ake yi daga nan inda take. Suna nan zaune aka kira sallar la'asar,sai Yasmin ta ja hannun Nansy suka nufi cikin gidan. Kai tsaye sashen Gwaggoji suka nufa. Babban parlour ne guda ɗaya da ɗakuna biyu a wajen,sai banɗaki ɗaya a cikin parlour da dinning area. Banɗakin dake cikin wani ɗaki Yasmin ta nuna wa Nansy,ita kuwa ta shiga ta hau kalle-kalle tana ayyana abubuwa masu tarin yawa a cikin ranta. Kasa buɗe pampo ta yi dan ta yi alwala,gashi tana tsananin jin kunyar ta leƙa ta ce wa Yasmin bata iya amfani da pampon ba. Haka ta dinga taɓe-taɓe a wajen har ta samu nasarar kunna pampon ta ɗaura alwala ta fito. Sallah ta tarar Yasmin na yi. A gefenta ta shimfiɗa abun sallah da hijabi a ninke a wajen. Ɗauka Nansy ta yi ta tada sallah itama. Suna idarwa suka zauna suka sake tsara kwalliya tare da feshe jikinsu da turaruka masu daɗin ƙamshi. Lokacin da Yasmin ta kula Nansy na ta yaba turarukan sai ta ɗauki wasu ta bata kyauta. Tun Nansy na ah ah,tana ah ah sai da Yasmin ta dage ta karɓa. Godiya ta yi mata sosai sannan suka fito waje inda aka fara sakin kiɗa kamar gidan zai tsage. Wajen da suka zauna suka ci abinci Nansy ta nufa,sai Yasmin ta riƙe mata hannu ta ce.

"Ina kuma za ki koma?"

"Can wajen da muka zauna É—azu mana."

"Ah ah don Allah ki zo mu je ga Gwaggoji can da Mama ki gaishe su."

Cike da fargaba da faɗuwar gaba Nansy ta ja hannun Yasmin ta riƙe,cikin dabara ta ce mata.

"Haba Yasmin,ta ya za a yi a zuwa na na farko gidan nan na je na gaishe su a cikin taro? Ai sai nake ganin kamar hakan be dace ba,ki bari a gama biki lafiya,sai na zo na yi musu ban gajiya da Allah Ya sanya alkhairi,ko ya kika ce?"

Kai Yasmin ta ɗaga suka wuce wajen da suka ci abinci suka ja kujeru suka fito fili suna kallon duk abinda ke gudana a tsakiyar taron. Lokaci zuwa lokaci Yasmin kan tashi ta shiga cikin danginsu a yi hotuna da ita ta koma wajen Nansy. Suna nan zaune yamma ta fara yi sosai aka saka waƙar da Nansy ke so. Babu ɓata lokaci kuwa ta miƙe ta hau rawa a hankali tana rausaya jikinta cike da jin ƴammatanci. Har gate ɗin gidan ya buɗe motoci uku masu kyau suka shigo gidan Nansy bata dena rawa ba. Yasmin dake tsallan murna tana taɓo Nansy ta gaji da share ta da Nansy ta yi,sai ta nufi wajen motocin fuskarta ɗauke da maɗaukakin murmushi. Tana zuwa gaban motar Giɗaɗo sai ta tsaya tana jiran fitowarsa,nan da nan masu ɗaukan Video suka fara aikinsu. Giɗaɗo wanda tun shigowarsu ya ke kallon yanda mata ke ta tiƙar rawa ransa ya ɓaci. Cike da takaici ya ce.

"Don Allah Man Sadi ka duba ka ga yanda mata ke ta tiƙar rawa ana gab da kiran sallar magariba. Shi yasa na ce wa Gwaggoji ba zan zo ba,amma ta dage sai na zo tunda surukarta ta ce abinda take so kenan,danginta su ga ango. Mtwss."

Ya ƙare maganarsa da jan dogon tsaki tare da kawar da kansa gefe,murmushi Malam Sadi ya yi ya ce.

"Ai Alhaj lokacin da ka yi min waya dan na zo na same ka a gidanka,lokacin aka fara shagalin."

Kai kawai Giɗaɗo ya girgiza cike da takaici ya yi ƙwafa. A hankali Idanuwansa suka sauka akan Nansy dake shirin zama a kujera saboda gajiya da rawa da ta yi. Murmushi ya saki mai sauti,saboda ganin yanda ta ware kanta daga cikin taron da ake ta casu. Nan take zuciyarsa ta gasgata cewa Nansy na da wani ɓangare mai kyau a tattare da rayuwarta,sai dai rashin jin ƙuruciya da ya yi yawa a tattare da ita. Buɗe motar Yasmin ya yi daidai da kai hannunsa jikin hannun ƙofar,suna haɗa ido ya sakar mata murmushi ta isa gabansa ta rungume shi. Hannu ɗaya ya ɗora a bayanta ya riƙe hannunta suka fito daga motar. A haka suka isa wajen Yusrah da ƙawayenta dake ta tiƙar rawa. A gefe ɗaya kuma Managers ɗin dake kula da kamfanoninsa wanda suke a matsayin abokansa ne tafe suna take masa baya. Nan take DJ ya sauya salon kiɗan sa waje ya sake kacamewa da ihu da murna tare da bin waƙoƙin da ke tashi a wajen. Abokan ango da angon kansa sun saki bakin aljihu sosai suna ta feshin nera. Nansy dake gefe sai ta ji kamar ta shiga taron da leda ta yi ta tattare kuɗin in ta gama ta kai wa Babanta. Dariya ta yi a lokacin da ta tuna da Babanta,ta tabbata idan ya ga wannan uwar dukiyar da ake zubarwa a ƙasa gigicewa zai yi.

Ko minti biyar Giɗaɗo bai yi ba a wajen ya bar wajen zai shige sashensa. Ta gaban Nansy dake ta zabga murmushi ya gilma,amma sai ta yi kamar bata gan shi ba,dan haka kawai ta ji bata son wata mu'amala ta sake haɗa ta da shi tunda aurensa ake yi. Shi kuma Giɗaɗo sai ya ji babu daɗi a cikin ransa da yarinyar ta kawar da kai ta yi kamar bata gansa ba. Rashin dalilin da zai haɗa su yin magana ne ya sanya shi yin gaba ya shige ɓangarensa. Yana shigewa Nansy ta saki wata ɓoyayyiyar ajiyar zuciya.

Lokacin da gari ya fara duhu sai gidan ya cika da hasken fitulun wutar lantarki. Hasken sai ya ƙara haskaka mutane da kyau kamar rana. Abokan Yunus ne tafe suna hira suna tattaunawa game da yanda ƴan mata ke casu a wajen gwanin burge wa. Kamar daga sama ta ji an ce.

"Ke me kike yi anan?"

ÆŠaga kanta Nasibah ta yi dan ta ga wanda yake yi mata magana. Cike da tsananin mamaki ta ga Samir tsaye a saman kanta shi da wani siririn mutum fari tas kamar zabaya..........
[9/26, 5:57 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA.

NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️

PAGE 9

Girar ta ta haÉ—e waje É—aya tana kallonsa cike da mamaki ta ce.

"Ban gane me nake yi anan ba. Biki na zo mana ko baka gani bane?."

Kai Samir ya jinjina ya kalli Nuh ya ce.

"Abokina na fa gode da wannan gayyatar da ka yi min,kawai ka shiga ciki dama ni ba wani sani na angon ya yi ba,idan ka fito mun wuce."

Kujerar da Yasmin ta tashi ya ja ya zauna yana fuskantar Nansy da ta haÉ—e fuska tamau. Murmushi ya yi mai sauti sannan ya ce.

"Da alama dai baki gane ni ba ko Baby?"

Kallon sama da ƙasa Nansy ta yi wa Samir kafin ta ce.

"Baby kuma? Ni suna na..."

"Nasibah. Na sani ba sai kin faÉ—a min ba."

Samir ya ƙarasa mata maganar tare da lumshe kyawawan idanuwansa masu haske ya sake cewa.

"Tun lokacin da na ajiye ki a gida na wuce Abuja kike yawan faÉ—o min a rai. Na so na zo har gida na sake duba ki,to sai na yi tunanin Baba ba zai so hakan ba."

A sheƙe Nansy ta kalli Samir sannan ta ce.

"Nake faÉ—o maka a rai;ko kuma kake jawo ni? Dan ni gaskiya tun ranar da ka tafi ban sake tunaninka ba,in fact na ma manta da kai ni."

Dariya sosai Samir ya yi kafin ya shafa gemunsa da yake kashe wa kuÉ—i ya ce.
Chapter 11 · 0% Book details