← Book details Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 28

Sashe 20

Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fankam-Fakam suke tafe kamar Makaɗi zai caki ƙasa da haƙoransa. Su na zuwa wajen Ɗan Small me Kemis suka ga zai rufe wajen saboda kiran sallah da ake yi,da sauri Makaɗi ya dakatar da shi ya roƙi arziƙi ya duba masa Nasibah. Magunguna ya bata Makaɗi ya cire kuɗin da ƙyar yana jin ciwon yin hakan a ransa ya bayar. A hanyar komawarsu gida ya bi ta shagon Isiya ya siya mata Fanta suka nufi gida yana faɗin.

"Ban kashi kuÉ—in banza ba Maryama,dan kuwa sai kin cake min kuÉ—in duk da kika sa na yi asara kan ki wuce gidanku."

Ransa a matuƙar ɓace suka koma gidan Nasibah na sake langwaɓewa tana sakin numfarfashin azaba. A tabarmar da Makaɗi ke zama Usman ya kwantar da ita yana haki ya zube a gefenta yana lasar busassun laɓɓansa. Idonsa akan sanssanyar Fantar da Makaɗi ya siyo wa Nasibah ya ce.

"Ƙishirwa nake ji,ina ma mutum zai samu wani sassanyan ruwa ko lemo ya kora."

A hasale Makaɗi ya kalle shi ya danna masa harara,kai Usman ya sunne ƙasa ya miƙe tsaye ya bar wajen. Yana tashi Malam Sanda ya zauna tare da ƙwalawa Kilishi kira ya ce.

"Taho min da kofi da É—an abincin nan mu ga ko za ta iya ci."

Daga É—aki Kilishi ta amsa shi da "Toh Malam" sannan ta fito ta shiga madafa ta É—akko abincinsa a babban faranti ta ajiye a gabansa tana tambayar jikin Nasibah. Ajiyar zuciya Malam Sanda ya sauke sannan ya cire hularsa da ta yi zufa ya ajiye a gefensa ya ce.

"Gata nan ki taimaka ki kular min da ita; tinda ita Maryama yanzu ta zama abinda ta zama."

"To Malam Allah Ya bata lafiya."

Nan fa suka tasa Nasibah a gaba da lallashi da lallami har ta samu ta sake cin tuwon kaɗan ta sha fantar,sannan ta sha maganin ta kwanta. Babu jimawa baccin wahala ya kwashe ta. A nan wajen Makaɗi ya zauna har ƙarfe ɗaya da rabi na dare. Nasibah ya gani sanye da hijabi a zaune ta jingina da gini tana kuka hannuwanta a sama. Idanuwansa ne suka washe ya sake kallonta ya ce.

"Sannu Æ´ar Baba,yaushe kika tashi?"

Nasibah bata kula shi ba,kuma bata dena yin addu'o'in samun nasara akan mahaifin nata ba domin ya amince ta auri Malam Luƙman ɗinta. Buta Makaɗi ya ɗauka ya zaga banɗaki. Ko da ya fito sai ya tarar da wajen babu kowa,shima sai ya tattara komatsansa ya wuce ɗakin Kilishi ya kwanta.

A bangaren Nasibah kuwa bata sake rintsa wa ba saboda tsannanin tunani da ya cika mata zuciya. Sosai take jin tsana da haushin Samir a cikin ranta. Ana kiran sallar asuba bacci mai daÉ—i ya dinga sanÉ—ar ta,kin bashi dama ta yi ta fita ta yi alwala ta koma É—akin ta tayar da sallah. Ta na idarwa ta koma ta kwanta bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita.

A wannan ranar da safe haka Mama ta ƙaraci baiwa Makaɗi haƙuri da ban baki amma bai kula ta ba. Daga ƙarshe ma da zai fita sai ya kalli Kilishi ya ciro kuɗin cefane ya bata ya ce.

"Tinda na yi kora an ƙi bar min gidana to sai a yi ta zama,amma ba zan yarda a sake dafa min abinci ba a gidan nan,ke Kilishi ki yi girkin dare,sai na dawo."

Tagumi Mama ta zuba tare da sauke ajiyar zuciya. Kilishi kuwa sai ta hau mahaifa tana faÉ—in.

"Ba zai yiwu ba Malam, a gaskiya ni ba zan karɓi girkin kowa ba."

"Au kema nuna min za ki yi ban isa da ke ba? Rabi! Rabi ke zo nan."

Malam Sanda ya faɗa yana riƙe kan babur ɗinsa da kyau. Rabi dake ɗaki tana ninke kaya sai ta ajiye ta fito da sauri ta durƙusa a gaban Malam Sanda ta ce.

"Baba gani."

"Amshi nan ki siyo kayan miya ki yi girki,zan dawo da rana na duba jikin Æ´ar'uwarki idan ta farka."

"To Baba a dawo lafiya."

Ba tare da ya amsa ta ba ya buga babur ɗinsa tare da baɗe su da hayaƙi ya bar gidan. Kilishi ma ɗakinta ta nufa,dan itama fushi take yi da Mama,shi yasa gaisuwarta kawai ta amsa tun da suka tashi basu yi wata doguwar hira ba. Duk Mama sai ta ji ta tsangwami kanta,nadamar dukan Nasibah duk ta mamaye mata zuciya. Jiki a sanyaye ta faki idon Kilishi ta leƙa ɗakin da Nasibah ke kwance kamar ruwa. Ganin yanda jikinta ya yi ja shatin bulalai suka yi masa ƙawa sai jikinta ya sake yin sanyi. A nan take ta gasgata dukan da ta yi wa yarinyar ya yi yawa,amma kuma ai ita ce ta jawo saboda taurin kanta. Ɗakinta ta koma ta fito da nera ɗari uku ta ba wa Najlah ta ce ta siyo mata madara da milo. Da sauri Najlah ta bar gidan ta nufi shagon Isiya ta siyo ta kawo wa Mama. Ɗakin Kilishi Mama ta je ta miƙa mata kayan shayin da ruwan zafi a flask ta ce.

"Ummahnsu ga abun kari na kawo wa ƴar taki a bata,Allah Ya ƙara lafiya."

"Aje su nan."

Kilishi ta ce tana kawar da kai. Murmushi Mama ta yi ta ajiye a inda Kilishi ta nuna mata ta fita ta koma nata É—akin. Ta labulen É—akinta take ganin gilmawar kilishi tana ta hidima da Nasibah.

Haka Nasibah ta ɗauki tsawon kwana huɗu tana jinyar jiki da zuciyarta. Sai dai a zahiri kowa ya shaida ta warke babu zazzaɓi tabon dukan duk ya yi duhu ya fara ɓacewa. Amma a zuciyar Nasibah jinta take yi kamar wadda aka tattara wa dika damuwar duniya aka ɗora mata akanta. Gaba ɗaya ta rame ta ƙara haske. Babban takaicinta bai wuce yanda Makaɗi ya sanar da Samir ta yi fama da jinya ba,shi kuma sai ya saki bakin aljihu ya dinga siyayya yana kawo wa gidan. Duk zuwan da yake yi kuwa duk yanda Makaɗi zai kaɗa ya raya bata fita wajen Samir.

Yau ma kamar sauran ranakun da suka gabata,Nasibah ta dawo daga makaranta,sai ta cire hijabinta ta shiga ɗakinsu ta ajiye jakarta ta shiga ɗakin Mama ta gaishe ta. Ganin yanda Nasibah ta rame sai hakan ya ɗaga hankalin Mama,amma da yake basu da shaƙuwar da za ta kira Nasibah ta tambaye ta abinda yake damunta sai ta yi shiru tana bin ƴar tata da kallo har ta fita riƙe da kayan da za ta sauya.

Nasibah na komawa ɗakinsu ta sauya kaya ta kwanta ko abinci bata nema ba. A hankali bacci mai daɗi ya fara ɗibanta a kan soson katifarta da ba shi da maraba da tabarma. Cikin baccinta ta dinga jin wani irin sassanyan ƙamshi mai daɗi yana shiga ƙofofin hancinta. A hankali ta juya ta kai kanta saitin inda ƙamshin ke fitowa. Idanuwanta da suka yi mata nauyi saboda bacci ta buɗe ta zuba su a kan kyakkyawar halittar dake tsaye a saman kanta yana ƙare mata kallo..........
[10/10, 7:26 AM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA.

NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️

PAGE 16.

Da sauri Nasibah ta tashi zaune ta na rarraba idanuwa tsakanin bakin ƙofar shiga ɗakin nasu zuwa kan Samir da ya zuba hannuwansa a cikin aljihun baƙin wandonsa yana ƙare wa ɗakin kallo cike da ƙyanƙyami da mamakin ganin makwancin Nasibah. Muryar sa a shaƙe ya ce.

"How on earth do you sleep here comfortably?"

Harara Nasibah ta watsa masa sannan ta tura bakinta gaba ta miƙe tsaye ta ce.

"Malami ni ka je waje ka jira ni zan fito yanzu."

Murmushi Samir ya yi ya jingina da jikin ƙofar ɗakin ya ce.

"Ba zan iya yin hakan ba;saboda Baba ne da kansa ya bani izinin shigowa nan tinda baki da lafiya ba za ki iya fita waje ba."

"To ai ni na warke har makaranta na ci gaba da zuwa ma."

Ba tare da Samir ya ce mata komai ba ya hau takawa zuwa gabanta ya miƙa hannu zai taɓa goshinta domin ya ji yanayin zafin jikinta. Cikin wani irin hanzari Nasibah ta ja da baya ta dunƙule hannuwanta biyu tare da ware ƙafafuwanta ta mayar da ɗaya gaba ɗaya baya ta saita fuskar Samir ta kai mata naushi. Da sauri ya sunkuya hannunta ya harbi iska. Idanuwa suka zuba wa juna kowannensu na nishi kamar kajin dake shirin kacamewa da dambe. Sallamar Makaɗi da ke washe baki ne ta dawo da Nasibah da Samir cikin hayyacinsu. Ƙwafa Nasibah ta yi ta gyara tsayuwarta sannan ta fita daga ɗakin cikin matsanancin ɓacin rai ta shige ɗakin Kilishi ta kwanta a gadonta tana mayar da numfashi. Sosai Nasibah ta ji takaicin rashin samun kyakkyawar fuskar Samir da bata yi ba. Ƙwarai ta so ta yi wa fuskarsa tabon da daya kalla zai tuna ya taɓa haɗuwa da Nansy Ƙaya. Ƙwafa ta sake yi a karo na babu adadi ta kulle idanuwanta tana jiyo yanda Makaɗi ke zubar mata da mutunci kwando-kwando a gaban wanda yake iƙirarin za ta aura.

A can tsakar gida kuwa Samir ne ke sanar da Makaɗi zai aiko kayan gado a saka wa Nasibah a ɗakinta,dan bai ji daɗin yanda ya ganta kwance a ƙasa ba. Godiya Makaɗi ya zube a wajen yana zabga wa Samir har sai da Samir ya ɗaga shi. Cike da jin nauyin Samir Mama da Kilishi suka leƙa tsakar gidan suka gaisa. Kallon su ya yi ya amsa gaisuwarsu a tsaye sannan ya sa kai ya fita cike da takun taƙama da isa.

Yana fita daga gidan Rabi dake kitchen ta shiga É—akin Kilishi a guje ta faÉ—a kan Nasibah tana murna ta ce.

"Kaiii ƙanwata amma gaskiya na taya ki murnar samun miji irin na nuna wa maƙiya su ji haushi."

"Sai kuma aka yi rashin sa'a Nansy bata da maƙiyan da za ta nuna wa shi su ji haushi ba."

Dariya Rabi ta yi ta samu waje ta zauna da kyau ta ce.

"Da dai Nasibah kika ce,amma Nansy ai ina ga har sarkin Kano yana da matsala da ita."
Chapter 20 · 0% Book details