Sashe 3
Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Baka san inda hanyar kitchen take ba da za ka hau kwashe mata miya?"
Cike da rashin mutunci Usman ya kalli Nasibah ya ce.
"Ke ina ruwanki da sabgata? Dalla bani abincina."
Dariya Nansy ta fashe da ita ta hau kwaikwayon maganar Usman ta ce.
"Idan na ƙi baka abincin naka me za ka iya yi min?"
"Nansy kin fa raina ni,Allah zan saɓa miki kamanni idan baki yi wasa ba."
"Kaiii Usumanu ko É—andaba ka zama babu abinda za ka iya yi min kana wannan lauÉ—in kamar mace. Banza Tanko kawai."
Cikin zafin nama Usman ya yi kan Nasibah zai daka ita kuma ta tsallake shi ta faɗa ɗakin Kilishi dake da niyyar fitowa ta zazzaga wa Nasibah rashin mutunci akan aibata mata yaro da take yawan yi a gidan. Kasancewar Usman ya taso cikin mata sai ɗabi'unsa da maganarsa take kamanceceniya da ta mata,hakan ne ya baiwa mutane da yawa damar kiransa da sunaye kala-kala. Wasu na kiransa da Tanko,wasu su ce masa ɗan'daudu ko ɗan'hamsin. A cikin masu tsokanarsa ba a bar Nasibah a baya ba,shi yasa kullum suke faɗa da zarar sun zauna a inuwa ɗaya. Karo ta yi da Kilishi dake daf da fitowa daga cikin ɗakinta,nan take suka zube a ƙasa warwas. Kafin Kilishi ta damƙi Nasibah ta yi zuruf cikin zafin nama ta miƙe daga jikinta ta kwasa da gudu ta yi waje. Tana fita sai ta samu wani baƙin dutse dake ƙasan bishiyar ƙofar gidansu ta durumi ta yi zamanta. Ta jima a wajen sosai kafin ta jiyo ƙarar babur ɗin Babansu. Nan take ta hau murza ido tana kuka kamar wadda ake zare wa rai. Makaɗi na ƙarasowa ƙofar gidansa ya ga Nasibah na kuka,sai ya haɗe fuska tamau kamar hadari. A gabanta ya tsaya ya cake babur ɗinsa ya kama kan yana kallonta ya ce.
"Uhumm wanne me rabon shan dukan ne a cikin daren nan ya taɓa min ke ƴar Baba?"
Kai Nasibah ta hau sosawa tana shan majinar da babu ita;ta hau nuna ƙofar gidansu ta ce.
"Ba Yah Usman bane ya dake ni dan kawai na ce bai dace ya kwashe wa Yah Rabi miyarta ba...wai dan na ce Allah Ya saka min shine Kilishi ta rufe ni da duka,Baba ka ga bayana da ƙyar na gudo nan."
"To ita uwar taki ina take akai wannan bidirin bata tsawatar ba?"
"Haba Baba,ka manta halin Mama ne? Ko kashe ni za su yi ba za ta ce kanzil ba. Ni dai Baba mu je ciki ka sammin abinda ka siyo na É—an lasa."
Nan take fuskar Makaɗi ta sake tsukewa da ɓacin rai. Cikin faɗa da hargagi ya tura babur ɗinsa ya ce.
"To uwar ƙwalamammu babu uwar da na siyo ni. Za ki shiga ciki mu je na ji bahasin dukanki da aka yi ko kuma na wuce na barki ki ta haɗiyar yawu a iska?"
Baki Nasibah ta tura gaba tare da dafe bayan babur É—in tana turawa ta ce.
"Ai shikenan,ka ci naka nima gobe da an taso daga boko zan je gidan Alhaji Nasir na yi wa Aunty Luba kitso,kuma..."
A hasale Makaɗi ya kafe babur ɗinsa a cikin soron gidan ya kunna ƙaramar wayarsa ya haska musu zaure,cikin faɗa da zage-zage ya buɗe ledar ya ɗebo nama tsoka biyu ya dangwara wa Nasibah a hannu. Nan take ta washe baki ta danna su a baki tana tanɗe hannu ta ce.
"Ni Baba na yafe wa Usman duk abinda ya yi min duniya da lahira. Kawai ka yi wucewarka ɗaki ka ci daɗinka. Kuma gobe na yi maka alƙawari duk abinda na samo zan kasa shi uku na baka kaso biyu na ɗauki ɗaya mu raba da Mama."
Nan take fuskar Makaɗi ta washe ya kalli ƴar tasa wadda a koda yaushe yake samun alkhairi mai yawa daga wajenta. Hannu ya jefa cikin ledar hannunsa ya sake damƙo tsoka biyu ya miƙa mata ya ce.
"Allah dai Ya yi miki albarka Nasibah,Allah Ya ƙara wa hannuwanki albarka da saƙar kitso da lalle me kyau. Maza shiga ciki ki kwanta,gobe ne za ki fara zuwa SS 1,inyee su Nasibahn Baba ana ta girma."
Cike da murnar da ta kasa ɓoyuwa a saman kyakkyawar fuskar Nasibah,ta kalli mahaifinta cike da so da ƙauna ta ce.
"Duk sai na ji daren ya yi min tsawo Baba."
"Ai da kin kwanta kika rintse ido gari zai waye Æ´ar Baba."
Dariya Nasibah ta yi sannan ta ci gaba da bawa Mahaifinta labarin wahalar da ta sha a jarabawarsu ta Junior WAEC da suka yi. Ba tare da Makaɗi ya kula da lokaci ba sai ya zauna a tabarmar da Kilishi ta shimfiɗa masa ta ajiye masa abincinsa suka dinga hira da Nasibah. Ganin hirar tasu ba za ta ƙare bane ya sanya Mama fitowa riƙe da buta a hannunta ta kalli Mijin nasu ta ce.
"Malam sannu da zuwa."
"Yauwa Maryama,ya wunin gidan da yaran kuma?"
"Humm Alhamdu lillah. Ai na zaci ka manta kana da wasu yaran ballantana kuma matar aure me suna Maryama."
Dariya Nasibah ta ƙunshe ta saɗaɗa ta shige ɗakinsu ta kwanta tana jiyo hirar iyayen nata mai cike da kishi da kuma bayyana so da ƙaunar da suke yi wa junansu.
Duk wanda ya kwana ya tashi a cikin gidan nan ya san cewa Mama ita ce matar da Malam Sanda Uba Makaɗi ya fi so a kaf matansa da ya aura,ciki kuwa har da uwar gidansa wadda iyayensa suka aura masa ita saboda zumuncinsu irin na makaɗan dauri ya ƙara ƙarfi. Wannan dalilin ne ya sa a koda yaushe Mama ke adawa da yanda Malam Sanda ya tattare soyayyar da yake yi mata ya mayar da ita akan ƴarsu Nasibah. A kullum idan ta yi masa ƙorafi sai ya ce ah ah shi kam bai fi son Nasibah akan ta ba. Amma da zarar an taɓa Nasibah;ko kuma wani abu ya same ta,to anan ne gaskiyar irin soyayyar da yake yi mata take bayyana.
Babbar matsalar Malam Sanda ita ce kwaɗayi,rowa da kuma son abun duniya. Dan haka idan ka ji yo faɗansu da shalelensa Nasibah,to fa tana ƙoƙarin shiga aljihunsa ne,ko kuma tana neman hana shi nata abun duniyar. A wannan lokacin ne Malam Sanda yake zage damtse ya gyara leɓensa ya yi ta surfa wa Nasibah ashar da rashin mutunci.
Kafin Mama ta koma ɗaki tuni Nasibah ta yi bacci cike da surutai da mafarkan dake bayyana abubuwan da ta yi a wunin ranar. Washegari da asuba Mama ta yi matuƙar mamaki da ta ga Nasibah ta farka da kanta ba tare da an tayar da ita daga bacci ba. A ɓangaren Nasibah kuwa jin wannan ranar take yi a matsayin rana mai matuƙar muhimmanci a rayuwarta.
Tun gari bai gama waye wa ba ta yi wanka ta zuba uniform ɗinta sababbi da suka yi kusan sati biyu a goge. Sabuwar safarta ta saka sannan ta saka sabon takalminta. Ta na gamawa ta ɗauki tsohuwar jakarta ta rataya a kafaɗarta tana jin wani irin sabon farinciki na mamaye zuciyarta. A cikin wannan yanayin mahaifinta ya dawo daga masallaci ya tarar da ita. Cike da zumuɗi da girmamawa Nasibah ta durƙusa ta gaishe da mahaifinta,amsawa ya yi cikin sakin fuska sannan ya ce.
"Ƴan makarantar boko kenan,manyan siniya masu bawa jiniya gwale-gwale. To Allah Ya sa ki fara a sa'a ƴar baba."
"Amin Babana. Baba kai za ka ajiye ni a makaranta da babur É—inka ko? Ka ga su Nawwarah a motar gidansu za a kai su yau."
Kai Malam Sanda ya gyaÉ—a kafin ya ce.
"Ni zan kai ki mana Æ´ar Baba,maza ki je ki ci É—umame dan na san zumuÉ—i bai barki kin karya ba."
Tura baki Nasibah ta yi gaba tana juyi da jikinta,cike da shagwaɓa ta ce.
"To ni Baba yau ranar farko da zan shiga SS 1 É—in ne zan ci É—umamen tuwo?"
A ƙufule Kilishi dake jin haushin Nasibah ta mere baki ta ce.
"Shi SS 1 ɗin a wata ƙasar ake yin sa ko kuma a nan nan cikin garin Kano?"
Kallon Malam Sanda Nasibah ta yi tana matso kwallah. Nan take Malam Sanda ya ɓata rai ya ce.
"Mu je bar mata tuwonta ta ci ya kai mata har mafafa."
Nan take Nasibah ta washe baki ta bi bayan Malam Sanda suka bar gidan a babur ɗinsa. Sai da ya tsaya ya siya mata ƙosai da dankali sannan ya kai ta har cikin makaranta.
Malam Sanda na tafiya Nasibah ta tafi wajen ƙawayenta tana takun yanga kamar bata so. Duk wanda ya ganta a wannan lokacin sai ya rantse a SS 2 take ko SS 3. Nawwarah da sauran ƙawayensu na hango ta suka tafi da gudu suka rungume juna suna ihun murna. Cike da yanga Nasibah ta ja jikinta daga nasu ta na yatsina ta ce.
"Wai ku dan Allah meye haka? Har yanzu baku bar abun yarinta ba sai Æ´an junior section sun raina mu."
Shewa yaran suka sanya tare da tafawa,daga nan suka zauna Nasibah ta fito da ƙosai da dankalinta tana ci suna hira. Lokacin shiga aji na yi,suka tattara suka shiga sabon ajinsu kowa ta kama bencin da za ta zauna. Cike da zumuɗi da son karatun dake cikin ransu suka bada hankalinsu suka ɗauki darasin wannan ranar. Har aka tashi Nasibah bata ja faɗa ba,idan an yi mata abu sai dai ta yi kamar bata gani ba. Sosai hakan ya ba wa Malamai da ɗalibai mamaki. A wannan ranar suka tabbatar da abinda take yawan faɗa.
'Ni fa daga ranar da na shiga senior class zan dena duk wannan damben da neman faÉ—an da nake yi.'
Lokacin da aka tashi daga makaranta kowa ya watse,Nasibah da yaran unguwarsu sai suka kama hanya a ƙafa dan komawa gidajensu. Tun a hanya su Nawwarah ke roƙon Nasibah ta sam-mu-su durumin ƙofar gidansu da ya nuna,kamar ba za ta yi magana ba,sai ta nisa ta ce.
"To shikenan,zan baku amma sai dai idan kowa zata bani nera ashirin-ashirin."
Cike da murna suka ce za su bata. Nan take suka fara sauri domin isa gidan su Nasibah da wuri........
[9/17, 8:17 AM] HAERMEEBRAERHâ¤ï¸: ZAWARA.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨âœï¸
PAGE 3.