Sashe 17
Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Ƙaƙa-ƙara-ƙaƙa! Ga Munirah ƴar hau,ga Nansy Ƙaya my fiful. Da alama dikansu sun ci kai.*
[10/3, 6:57 AM] HAERMEEBRAERHâ¤ï¸: ZAWARA.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨âœï¸
PAGE 13.
Ajiyar zuciya Samir ya sauke mai ƙarfi ya kalli Sakinah da har a wannan lokacin ke kallon TV hankalinta kwance tana kora lemo lokaci zuwa lokaci. Miƙe wa tsaye ya yi ba tare da ya kula ta ba ya nufi sashen sa. Ya na zuwa ɗakinsa ya shige ya hau cire kayan jikinsa daga ƙarshe ya shiga wanka. Bai wani jima a wajen wankan ba ya fito yana tsane jikinsa da towel. Wayarsa dake ta neman agajin gaggawa ya kalla ya ja dogon tsaki tare sa faɗin.
"Yarinyar nan ko mayya ce ke bana dai zan rabu da ke na huta da nacin ki."
A wajen ya yar da towels ɗin da ya gama amfani da su ya sanya kayan baccinsa sannan ya nufi parlour. Ya na zuwa ya buɗe abincin ya ga gaba ɗaya sun yi masa nauyi ya ci da daren,sai kawai ya ɗauki fruit salad ya sha ya kunna sigarin sa ya na zuƙa ya na kallon wayarsa. Muryar Nuh ya ji daga ɗaya ɗakin dake cikin parlourn tana doso shi. Tun kafin ya iso ya fahimci abinda yake faruwa,dan haka sai ya sake tsamke fuskarsa yana kallon wayarsa,ko da Nuh ya fito yana magana cikin yanayi na mutumin da ya fara bacci,sai ya kalli Samir da ya haɗe fuska kudu da arewa,gabas da yamma ya yi masa nuni da kiran da hannu. Kafaɗa Samir ya ɗaga masa alamar babu ruwansa. Nan take Nuh ya wartsake daga magagin baccin da yake yi ya riƙe wayar da kyau yana faɗin.
"Look Muni kin fa fini sanin halin mutumin naki,idan bai yi niyyar amsa miki waya ba ni ban isa na saka shi ya amsa miki ba. Dan haka ina ganin ki kashe waya kawai ki yi bacci nima na samu na rintsa in peace,don Allah kada ki sake kirana bacci nake ji,gashi gobe zan dawo Abuja ni zan yi tuƙi ba wai jirgi zan bi ba ko motar haya."
Baki Munirah ta tura gaba cike da shagwaɓa irin na yaran masu kuɗin da basu samu abinda suke nema ba. Ranta a ɓace ta buɗe murya ta ce.
"Babe na san kana ji na,wai me na yi maka ne kake ta wulaƙanta ni haka?"
Kukan da ke raunata zuciyar Samir ta saki tana shessheƙa kamar za ta shiɗe. Nuh na jin haka ya kashe wayarsa ya juya ya nufi ɗakin da yake sauka idan ya zo gidan yana mita,dan ya san Samir ba zai iya ƙyale ta ta kwana tana wannan jarababben kukan nata mai ban haushi ba. Murmushi Samir ya yi ya tattara abubuwan da yake da buƙata ya kashe abinda duk ya kamata ya kashe na wuta ya wuce ɗakinsa. Ya na shiga Muni ta sake banko masa kiran waya. Ajiye kayan hannunsa ya yi a fusace ya ɗauki wayar yana haɗe haƙoransa waje ɗaya tare da hura hanci ya ce mata.
"What do you want from me MUNIRAH NAZIR ATAH?"
Cike da salon jan hankali Munirah ta kashe murya ta ce.
"Kai ma ka san kai ne abinda nake so;me na yi maka kake wulaƙanta ni haka Samir?"
"Saboda aure zan yi Muni na gaji da yawon bariki da baƙin nacin ki."
Wata iriyar zabura Munirah ta yi ta miƙe zaune tana jin kamar an shaƙe mata wuya shi yasa numfashinta ke barazanar ɗaukewa. Da ƙyar ta iya janyo kalmar.
"Aure?"
Ta furta a laɓɓanta. Kai Samir ya jinjina ya ce.
"Yes Muni! Aure zan yi,so Please ki ja jikinki ki kama kanki,idan har akwai sauran wata daraja da ta rage miki to ki riƙe ta don Allah."
Dariya mai sauti Muni ta saki tare da miƙe wa tsaye tana tafa hannuwanta dika biyun,sai da ta gama sannan ta ɗauki wayar dake dokin wuyanta ta saka ta a handsfree ta ja dogon numfashi ta fesar ta ce.
"Baka isa ka auri kowacce mace ba a duniya SAMIR YUSHA'U GWAMNATI idan ba ni MUNIRAH NAZIR ATAH ba. Ai ƙaryar ka ta sha ƙarya ka ci moriyar ganga akaina,sannan ka yada kaurenta. Ni da kai mutuwa ce za ta raba mu,ko da aure ko a bariki. Ina so ka rubuta wannan ka ajiye Samir,a duk ranar da ka auri wata macen ba ni ba za a ɗauki gawa ko na ce gawarwaki. Ko ni,ko kai ko ita matar da za ka aura,ko mu haɗu dika mu yi mutuwar kasko."
Tana gama maganarta ta kashe wayar ta yi wurgi da ita a ƙasa da ƙarfi har sai da screen ya tsage. Tsaye ta miƙe tana jin wani irin zafi na shiga kowanne lungu da saƙo na jikinta,a hankali ta hau tsiyayar da zufa kamar ruwa kafin daga baya zufar ta bar zuba sanyi ya fara shigarta. Idonta da ta waro ta lumshe tare da ɗora hannunta a saman kanta ta damƙi tulin gashin kanta ta hau kai wa da komowa a cikin ɗakin. Wani irin ihu ta kurma kamar wadda aljanu suka hau. Ido ta sake zaro wa waje sannan ta sake kurma wani ihun tare da fashe wa da kuka ta dunƙule a ƙasan wajen tana kama ƙirjinta da take jin yana barazanar rabe mata gida biyu.
Ƙarar buɗe ƙofar ɗakinta ne ya sanya ta snapping ta ɗaga kanta ta kalli bakin ƙofar. Mahaifiyarta ta gani tana ci gaba da kiciniyar sanya kimono ɗinta tana tambayar dalilin shigarta wannan mawuyacin halin. Kai Muni ta hau girgiza wa Mahaifiyarta sannan ta ce.
"I thought he hates marriage. Ban sani ba ashe ni ce baya so Mom,ni ya tsana,ni ce ba zai aura ba. He was my first true love,i gave him everything Mom,babu wani abu da ya min saura wanda Samir bai san da shi ba. I love him so very much Mom,ba zan taɓa iya ci gaba da rayuwa babu shi ba. Mom please do something tun kafin ki rasa ni;domin idan na rasa Samir a rayuwata mutuwa zan yi Mom."
(Na zaci ya tsani aure.)
Munirah ta ƙarasa maganarta tana mai fashewa da wani irin kuka mai matuƙar ƙona zuciya. Hajiyah Nusrah ta jima da sanin cewa Samir da Munirah ƙaddarar juna ne,duk wannan burgar da yake yi ta zai yi aure dole zai dawo wa Munirah, musamman ma da bai taɓa furta zai yi aure ba ko yana da burin yin auren. Hannu Hajiyah Nusrah ta sa a bayan Muni ta hau shafawa a hankali sannan ta ce.
"Look Muni he is just pulling your legs babu wani auren da zai yi."
(Kin ga Muni kawai wasa yake yi miki)
"Mom da gaske yake yi aure zai yi ni ya barni bayan ya gama da rayuwata."
A hasale Hajiyah Nusrah ta ce.
"Stop reminding me you are not a virgin Muni! I want you to pull your self together ok? Ya taɓa yi miki zancen aure?"
(Ki dena tuna min ke ba budurwa bace Muni. Ina son ki tattara kanki waje É—aya kin gane?)
Kai Munirah ta girgiza wa mahaifiyarta ta ci gaba da kukan da take yi. Cikin sigar lallashi Hajiyah Nusrah ta ce.
"Kin gani. Dan haka ki dena wannan ɗan iskan kukan mara tushe ki ci gaba da rayuwarki kamar yanda kika saba,domin na tabbata ko aure Samir ya yi ba zai taɓa rabuwa da ke ba."
"Ni bana son ya yi auren ne Mom."
"To ba zai yi auren ba. Tashi ki hau gado ki kwanta,zuwa gobe da safe za mu sake tattaunawa akan maganar. Kafin nan ina buƙatar hutu dan na san matakin da zan ɗauka akan lamarin."
Ba tare da Munirah ta kula mahaifiyarta ba ta miƙe tana jan majina ta haye gadonta ta shige ƙarƙashin bargonta. A hankali ta sake nitsar da kanta cikin lallausan matashin kanta tana mai zubar da ruwan hawaye. Gashin kanta Hajiyah Nusrah ta shafa gently sannan ta sunkuya ta sumbaci kanta ta ce.
"Good night baby. I love you so much."
Ido kawai Muni ta lumshe ruwan hawaye masu yawa da zafi suka zubo mata. Tana kallon mahaifiyarta ta fita ta miƙe ta kulle ɗakin ta buɗe wata drawer a cikin ɗakin ta fito da wata roba mai ɗauke da ƙwayoyin magani ta buɗe ta ɗauki guda huɗu ta sha babu ruwa. Tana gama haɗiye wa ta koma gado ta kwanta tana kuka. A hankali bacci mai daɗi ya ɗauke ta.
***********************
Tun cikin dare naƙuda ta kama Hanifah amma ta ƙi sanar da kowa,fatan ta bai wuce gari ya waye ba ta koma gidan mijinta kamar yanda Baba ya buƙata. Da ƙyar ta iya danne azabar da take ji ba tare da ta tada ƙannen nata dake ta sharar bacci ba.
Ana idar da sallar asuba naƙudar ta tsananta har ta kasa jurewa. Kan dole ta saki wani irin numfashi sannan ta hau kiran Kilishi da Mama su taimaka mata. Da sauri Nasibah da ke karanta ƙur'aninta ta kalli Yayartasu ta ce.
"Yayah cikinki na ciwo ne?"
Da ƙyar Hanifah ta ɗaga mata kai ta ce.
"Ki je ki kirawo min su Mama."
Cikin sauri Nasibah ta ajiye ƙur'anin nata a mazauninsa sannan ta fita tana ƙwala wa su Mama kira. Cike da tashin hankali Mama da Kilishi suka zo ɗakin suna duba Hanifah. Nasibah dake tsaye a waje tana ganin Makaɗi ya dawo daga masallaci ta nufi wajensa tana haki ta labarta masa abinda yake faruwa a gidan. Ransa a mutuƙar ɓace ya kalli Nasibah ya ce.
"Yanzu yarinyar nan ta dage anan za ta haihu mana ko? Kaiii Allah ka raba mu da baƙar sa'a."
Baki Nasibah ta saki tana kallon Mahaifin nasu wanda yake da tsananin son kansa. Kafin ta bashi amsar maganarsa ta ga ya washe baki ya saka hannu a aljihunsa ya ce.
"Kai ku shirya ta yanzu zan kira surukina ya zo ya kai ta asibitinsa ta haihu a can. Na tabbata sosai hakan zai ƙara kusanci a tsakanin ku Nasibah."
Babu ɓata lokaci Malam Sanda ya hau nemo No Samir da suka jima da yin exchanging. Cikin magagin bacci Samir ya ɗauki wayar ya kara a kunnensa ya ce.
"Baba lafiya kake kirana da sassafe haka?"
Nan take Malam Sanda ya marairace murya ya ce.