Sashe 22
Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har bakin ƙofar gate ɗin gidan Hanifah ta rako su Mama tana sake basu haƙuri. Basu jima suna tafiya ba suka samu adaidaita sahu,Yah Hauwa ta tsayar da shi ta biya kuɗi ya ƙarasa da su gida. Ko da suka isa gida sai suka tarar da gidan a buɗe,su na shiga Malam Sanda ya washe baki yana yi musu sannu da zuwa. A tsakar gidan suka baje suna ba wa Malam Sanda labarin yanda sunan ya kaya,amma basu bashi labarin faɗan da Nasibah ta yi da ƙanwar mijin Hanifah ba. Kilishi ce ta raba kayan da suka dawo da shi Faihah ta miƙa wa Makaɗi nasa ya hau ci yana faɗin.
"Shine da ake so a tatattaro ta dawo gida mu yi raba daidan kuÉ—in lalurar iyalinsa ko? To da ban matsa ta koma ba kun je ku ci ku sha har ku yo guziri?"
Shiru suka yi masa ya ci gaba da surutansa yana jefa naman suna a bakinsa. Sai da ya kusan cinye wa sannan ya ce.
"To wai ina kuka baro min Nasibah?"
Kafin su bashi amsa Najlah ta ce.
"Da ƙafa ta taho bayan sun gama dambe da Lailah ƙanwar Baban Aslam."
Cikin sauri Malam Sanda ya ɗaga kai ya ƙure su Yah Hauwa da ido,ransa a matuƙar ɓace ya ce.
"Ku kuma kuna uban me har dangin mijin Hanifah suka yi wa Æ´ata taron dangi?"
"Baba ba fa taron dangi aka yi mata ba,ita yarinyar ce ta zo ta mana rashin kunya shine Nasibah ta kama ta da kokowa suka yi dambe."
Da hanzari MakaÉ—i ya tari numfashin Lawizah ya ce.
"Ku kuma taron tsintsiya babu shara sai kuka zura ido har aka daki Æ´ar'uwarku baku É—auki mataki akai ba ko?"
"Haba Malam ta ya za a yi mu haÉ—u dika mu yi faÉ—a a gidan surukai? Itama Nasibar dan bata jin magana ne..."
"Dakata min Maryama kada ki ƙara ɓata min rai don Allah."
Shigowar Nasibah gidan fururu ne ya katse musu ka-ce-na-ce ɗin da suke yi. Nasibah na jin yanda Malam Sanda ke faɗan barota ita kaɗai da aka yi tun a soro,shi yasa ta shiga gidan tana ɗingishi ta na hawaye. Nan take ran Malam Sanda ya ƙara ɓaci. Fuska a cure ya ce.
"To ku tabbata da safe kowaccenku ta tattara nata ya nata ta koma É—akin mijinta."
Lawizah na jin haka ta miƙe tsaye tana faɗin.
"Ni dama ko baka ce ba Baba gobe da sassafe zan koma gidana."
"Lawizah ni kike mayar wa da magana ko?"
Tura baki ta yi gaba ta shige ɗaki ta saki labule tana ƙunƙuni. A hankali tsakar gidan ta watse aka bar Nasibah da Malam Sanda yana ta faman rarrashinta.
Haka rayuwar gidan Malam Sanda Uba Makaɗi ta ci gaba da tafiya har aka kai lokacin da Nasibah ta kammala SS 1 ta shiga SS 2. A wannan gaɓar ne kyau da cikar halittar Nasibah suka ƙara bayyana. Hakan sai ya ƙara gigita Samir ya ƙara tabbatar wa da kansa duk duniya bashi da matar aure sai Nasibah. A ɓangaren Nasibah kuwa har a wannan lokacin bata cire rai za su yi aure ita da Malam Luƙman ɗinta ba,sai dai rashin wata mu'amala a tsakaninsu na ɗaga mata hankali sosai tana jin kamar haƙonta ba zai cimma ruwa ba.
Lokacin da suka shiga second term aka saka ranar auren Nadiyah. Sosai su Nasibah suka dinga murna suna tsara yanda za su cashe su raƙashe a bikin Nadiyah. Bayan sati biyu da sanya ranar auren Nadiyah da yamma Nasibah na gida tana kitso Nawwarah ta je gidansu cike da tashin hankali. Da ganin haka sai Nasibah ta miƙe ta ja hannun Nawwarah suka shiga cikin ɗakinsu na ƴammata ta ce.
"Ke me ya faru na gan ki haka?"
Yatsa Nawwarah ta kai cikin bakinta tana cizgar farcen hannunta ta ce.
"Wai kin san kuwa wa Nadiyah za ta aura Nasibah?"
Murmushi Nasibah ta yi ta ce.
"Ba ta ce mana É—an abokin Babanta za a aura mata ba?"
Hannun Nasibah Nawwarah ta kama ta zaunar da ita a bakin gado sannan ta zaro wayarta ta kunna,nan take hoton Nadiyah da Malam Luƙman ya bayyana a saman screen ɗin wayar Nawwarah. Wani irin bamagujen ashar Nasibah ta saki jikinta na rawa ta karɓi wayar Nawwarah tana kallon Malam Luƙman ɗinta yana yi wa Nadiyah murmushi kamar dama can sun jima suna soyayya tare.......
*Ku yi haƙuri da ji na shiru da kuke yi please.*
[10/10, 9:46 PM] HAERMEEBRAERHâ¤ï¸: ZAWARA.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨âœï¸
PAGE 17.
Ganin yanda Nasibah ta fito daga É—aki a gigice kamar wata mahaukaciya sabon kamu,sai yaran da take yi wa kitso suka takure waje guda suna zare ido. Kilishi dake bakin makwarara tana wanke maburgi da muciyar da ta gama amfani da su sai ta saki soson hannunta ta kalli Nawwarah ta ce.
"Ke me yake faruwa na ganta a haka?"
Cike da matsananciyar damuwa Nawwarah ta ɗora hannuwanta a ka ta kasa furta komai sai nuna wa Kilishi hanyar waje da Nansy ta ɗauka take yi. Tsallake kwanukan dake wajen Kilishi ta yi ta nufi ɗakinta da gudu ta zaro mayafinta dake a saman ƙyauren ɗakin ta bi bayan Nawwarah da ta fita da gudu tana kiran Nasibah.
Nasibah kuwa tinda ta yi mummunan gamo da masoyinta na yi wa ƙawarta tsadadden murmushin da ita kaɗai yake yi wa irinsa ta dena fahimtar komai. Babban fata da burin ta bai wuce ta ganta a gaban Nadiya ba a wannan lokacin. Duk inda ta wuce mutane sai sun tofa albarkacin bakinsu a kanta,musamman ma da suka ganta babu mayafi ko hijabi, ballantana ƙafarta ta samu arzikin takalmi.
Tun daga nesa Nasibah ta hango Malam Luƙman a jingine a ƙofar gidan su Nadiya,nan take wani irin abu mai matuƙar nauyi da zafi ya soki zuciyarta, ba tare da tunanin komai ba ta rage saurin da take yi ta ƙarasa har jikin gidan su Nadiya. Muryar Malam Luƙman ɗinta ce ta sake tarwatsa duk wani sauran buri da ƙwarin guiwar da take da shi akansa. Cikin wani irin salo Malam Luƙman ya ci gaba da cewa.
"....dan haka na faɗa miki ki saki jikinki a yi wannan lamarin a gama cikin sirri. Ni na tabbata idan muka roƙi Nawwarah kada ta faɗa mata komai har sai an gama biki to ba za ta sanar da ita ba,ni kuma ta ɓangare na dama tuni na yanke duk wata alaƙa da ita,kuma ko ɗaurin aure ne ma zan roƙi Baba na ce ayi idan yaso da kun yi candy sai a yi walima a tare ba shikenan ba?."
Muryar Nadiya na rawa ta ce.
"A gaskiya ni dai ina jin tsoro,ka fa san halin Nasibah sarai da jidali da tashin hankali. Na rantse har yanzu zuciyata bugawa take yi dan na zaci Nawwarah ta gammu É—azu. Kai ni fa gani nake yi kamar wani zai gammu tare ya je ya sanar da ita. Ni dai don Allah ka dena zuwa da rana,ka dinga bari sai dare ya yi sosai,ko kuma mu dinga yin waya kawai."
Tafi Nansy ta hau yi tare da ƙarasa wa gaban Nadiya dake maƙale a cikin soron gidansu. Nadiya na yin ido huɗu da Nasibah sai ta faɗa cikin soron gaba ɗaya ta manne a bango tana kuka mara sauti. Malam Luƙman kuwa suna haɗa ido da Nansy ya sauke kansa ƙasa yana kallon ƙafar Nasibah da ta yi fururu kamar wadda ta yi tafiya a cikin sahara. Majina Nasibah ta sha ta ce.
"Ki kwantar da hankalinki Nadiya ki auri Malam Luƙman ba tare da fargabar komai ba;domin ni Nasibah idan har na haifu cikin Maryama da Sanda Uba Makaɗi na barka kenan bari na har abada Luƙman. Na yi zaton kana so na, na yi zaton ni ce mahaɗin rayuwarka kamar yanda kake faɗa min a kullum,na yi zaton ni ce bugun zuciyarka Luƙman,ashe dama ƙarya kake yi min ashe dama kai mayaudari ne? Ashe dama...."
Wani irin kuka ne ya ƙwace mata sosai har sai da ta duƙar da kanta ta rufe bakinta da hannunta na dama. Hannu Malam Luƙman ya ɗaga zai riƙe wa Nasibah hannu,cikin sauri ta ja da baya tana watsa masa wani irin kallo mai wuyar fassara, ƙwalla ta gani a kwance a cikin idanuwansa. Dariya ta yi mai sauti hawaye na zuba daga idanuwanta ta ce.
"Ai murna za ka yi tinda ni Nasibah na san abinda kake lulluɓe wa. Ina so ka sani na so ka Luƙman,ina son ka har yanzu,amma ni Nasibah zuciyata bata da gwani,a yau idan na ga dama zan iya maye gurbin ka da duk wanda na so,kada ka yi tunanin soyayyar ka numfashi na ce da idan babu ita ba zan rayu ba. A yau na tabbatar da karin maganar Bahaushe da ya ce Namiji ƙanin ajali ne. To ni dai Nasibah na fi ƙarfin namiji ya yi ajalina sai dai ni na yi ajalinsa. Ina son ka sani ba a banza ake kirana da Nansy Ƙaya ba,na yi maka alƙawarin sai soyayyata ta maƙale maka a zuciyarka kamar yanda ƙaya ke maƙalewa a maƙoshi."
Kilishi na ƙarasowa wajen sai ta yi turus tana kallon ikon Allah. Nawwarah kuwa dama tinda ta iso ƙofar gidansu ta je ta tsaya tana hango yanda Nansy ke magana ta na kuka,ga Malam Luƙman tsaye ya shiga cikin matsananciyar damuwa. Jikinta har rawa yake yi zuciyarta na tabbatar mata da rashin kyautawa akan abinda ta aikata na ɗaukar hoton Luƙman da Nadiyah a ɓoye ta nuna wa Nasibah.
A ɓangaren Nasibah kuwa juyawa ta yi za ta tafi ta ji kalaman Malam Luƙman a cikin dodon kunnuwanta.
"Kada ki ga laifina Nasibah ke kin sani babu macen da na taɓa so a kaf ƴan matan da suka nuna min so sai ke kaɗai. Ke ce macen da ni na gani da idanuwana na kamu da soyayyarta a kallon farko. Nasibah na so ki tun baki gama sanin menene kalmar so ba. Ina so ki sani duk son da nake yi miki idan aka taɓa martabar iyayena dole ne na haƙura dake. Mahaifinki ya faɗa min kalaman da ko ni shege ne dole zan ji zafi ballantana ina da uwa da uba a raye."