Sashe 27
Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nasibah ta ƙarasa maganarta tare da shigewa cikin gida. Ta na shiga ta ga ƙannenta suna ta bada labarin yanda Baban nasu ya zauna ya cinye kazar da Samir ya kai masa shi kaɗai bai bawa kowa ba,yana gamawa ya sha magani ya buga babur ɗinsa ya bar gidan. Cike da takaici ta shige ɗaki ta zauna a bakin gadon ɗakinsu tana hango irin kallon da Giɗaɗo ke wurga mata ta madubi. Kalamansa masu nuna tsantsar kulawa sai amsa kuwwa suke yi mata a cikin dodon kunnenta. Hannu ta saka ta toshe kunnen sannan ta miƙe ta kwanta da kyau a gado. Muryar Samir ta jiyo a tsakar gida suna magana shi da Kilishi tana sanar da shi Malam Sanda baya nan. Cike da matsananciyar damuwa Samir ya ce.
"Don Allah a sanar da shi gobe zan dawo da azahar wajensa;za mu yi wata muhimmiyar magana da ni da shi."
"To shikenan in Allah Ya yarda zan sanar da shi da zarar ya dawo."
Cikin sauri Samir ya fito daga gidan yana danna Lambobin wayar Malam Sanda ko zai same shi ya sanar da shi inda yake sai ya je su haɗu. Sai dai cikin rashin sa'a baturiya ta tabbatar masa da cewa wayar a kashe take. Tsaki ya ja zai shiga motarsa kenan ya hango motar Giɗaɗo na shigowa layin. Nan take zuciyarsa ta hau bugawa da ƙarfi yana jin kamar ya yi bindiga saboda damuwa da takaici. Gani ya yi motar ta tsaya na wani ɗan lokaci kafin daga baya ta juya da sauri ta bar layin a guje kamar za ta tashi sama. Wata iriyar wawuyar ajiyar zuciya Samir ya saki tare da jingina a jikin motarsa ya fashe da dariyar farinciki. Cike da ba wa kansa ƙwarin guiwa da yaƙini ya ce.
"In dai kuÉ—i na mallaka wa mutum abinda yake so;to Nasibah bata da miji a duniya sai ni Samir Yusha'u Gwamnati."
Yana gama magana ya buɗe motarsa ya tayar da ita sannan ya fara tafiya yana jijjiga kai tare da bin waƙar dake tashi a cikin motarsa,a hankali ya sa hannu ya ɗakko sigari a mazaunin da ya yi mata na musamman a motar ya kunna ya hau zuƙa cike da nishaɗi. Har cikin ransa yake jin son Nasibah,kuma a wannan lokacin ya yi wa kansa alƙawarin aurenta a gobe,domin ba zai bari zuciyar Makaɗi ta karkata zuwa kan Giɗaɗo ba ya rasa ta.
A ɓangaren su Giɗaɗo kuwa suna gab da zuwa gidan su Nasibah wayarsa ta fara ruri,ya na duba wa sai ya ga lambar Goggoji na yawo a saman screen ɗinsa,jiki a mace ya amsa kiran. Muryar Hajiyah Yalwa ya ji cikin kuka tana faɗin.
'Ka yi sauri ka zo asibiti Goggoji ta faÉ—i GiÉ—aÉ—o.'
A rikice GiÉ—aÉ—o ya tashi zaune da kyau ya ce.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil,garin yaya ta faÉ—i Hajiyah?"
'To ni ma dai ban sani ba,amma mu na zargin sugar ko hawan jininta ne ya hau kwarai da gaske,gata nan likita ya sa an shigar da ita emergency room,don Allah ka zo da wuri i am helpless GiÉ—aÉ—o.'
Hajiyah Yalwa ta ƙarasa maganarta tare da rushewa da wani sabon kukan. Cikin sauri Giɗaɗo ya yi wa Malam Sadi umarnin su juya su je asibitin da aka saba duba Goggojin.
Ko da suka isa asibitin sai GiÉ—aÉ—o ya fito daga cikin mota da sauri ya shiga cikin asibitin. Kai tsaye emergency room ya nufa,a bakin dakin ya tarar da Hajiyah Yalwa,Yansmin da Yusrah suna ta kuka. Hajiyah Yalwa na ganinsa ta nufe shi ta faÉ—a jikinsa tana mai rushewa da kuka. Cikin kuka ta ce.
"GiÉ—aÉ—o bana so na rasa Goggoji ita nake gani a matsayin uwa da ubana nake jin daÉ—i."
Idanuwansa ya rintse yana jin ƙirjinsa na bugawa,Goggoji ita ce rauninsa,kuma duk wani masoyi da maƙiyinsa ya san da hakan. Cikin wata iriyar murya mara karsashi Giɗaɗo ya ce.
"Me ta ci a wajen partyn ko kuma me aka yi mata da ya tada hankalinta jininta ya hau? Shi yasa na ce bana so a yi wannan bidi'ar kuka ce abu ne na É—an lokaci."
Kai Hajiyah Yalwa ta sadda ƙasa ta ce.
"Shi yasa zan ƙare sauran rayuwata ina nadamar tursasawrar da na dinga yi a yi partyn nan. Da na san abinda zai faru kenan da ban matsa ba."
Fuskar GiÉ—aÉ—o da ta ji jawur ya shafa ya ce.
"Me ta ci!"
A razane Hajiyah Yalwa ta ja baya saboda tsorata da furucin GiÉ—aÉ—o ta ce.
"Ca...ca..cake ta ci. Tsaya ka ji kowa na gani sai da na hana ta,ita ta matsa ta ce É—an kaÉ—an za ta ci."
Wajen Giɗaɗo ya bari ya isa daf da bakin ƙofar emergency room inda su Yasmin suke tsaye ya dinga leƙe ko zai iya hango Goggoji. Bai jima da tsayuwa ba likita ya fito,tafiya suka fara yi da Giɗaɗo yana yi masa bayanin yanayin sugar ɗin Goggoji da ya hau fiye da ƙima. Cike da damuwa Giɗaɗo ya ce.
"To yanzu likita ya ake ciki?"
"Alhamdu lillah tinda sugar ne kaÉ—ai jininta bai hau ba,mun samu Allah Ya bata ikon farfaÉ—owa,sannan mun bata duk taimakon da ya kamata,sai dai fa ina mai tabbatar maka da cewa idan har ba a kula da cimar Hajiyah Goggoji ba da kuma yawaita motsa jikin da na ce muku tun farko tana yi akwai matsala."
"In Sha Allahu babu wata matsala da za a sake samu. Na gode Dr. Don Allah a cigaba da bata kulawar da ta dace. Kada kuma a bawa kowa izinin ganinta har sai na buƙaci hakan ."
Hannu suka miƙa wa juna Giɗaɗo ya nufi wajen Hajiyah Yalwa ya ce musu duk su tafi gida ita da yaran nurses za su kula da Goggoji. A shagwaɓe Yusrah ta isa gabansa ta ce.
"Haba Hubby ta yaya za mu tafi gaba É—aya mu barta sai kace wata marar gata?"
Ransa a matuƙar ɓace ya ce.
"Da tana da gata da ba a barta ta ci abinda zai zame mata illa a gangar jikinta ba. Bayan haka ma ni da kaina na bada order É—in cake É—in ai,sai da na tabbatar da cewa na sanar kada a saka normal sugar a yi amfani da brown sugar da flour alkama,to a ta yaya ma cin cake kaÉ—ai zai tayar mata da ciwonta har haka?"
Ido Hajiyah Yalwa ta hau matsewa tana kuka,kallonta kawai Giɗaɗo ya yi ya fuskanci tabbas akwai wata a ƙasa. Ƙwafa ya yi ya ce.
"Just go home,zan zauna har ta farka,idan na dawo zan yi bincike na gano abinda aka saka a cikin cake É—in. Duk wanda na samu da hannu a cikin jefa Goggoji a cikin wannan mawuyacin halin ba zan raga masa ba,ko wanene!"
Giɗaɗo ya ƙarasa maganarsa a tsawace. Da sauri Yusrah ta kama hannun Hajiyah Yalwa suka fara tafiya,Yasmin da ta ci kuka ta gode Allah sai ta kalli Giɗaɗo cike da rauni ta ce.
"Yah GiÉ—aÉ—o ka yafe min,na san ina da laifi a wannan abun da ya faru saboda na matsa maka a haÉ—a mata grand party."
Murmushi Giɗaɗo ya sakar mata sannan ya rungume ta a gefensa na hagu. Ba tare da ya ce mata komai ba ya samu waje suka zauna suka yi shiru suna jiran tsammani. Haka suka kwashi kusan mintuna arba'in kafin Goggoji ta farfaɗo. Ana fito da ita daga emergency room suka bi likita da nurses dake tura gadon da take kai har ɗakin da aka canja mata. Sai da aka ɗaura mata ruwa sannan nurses suka fita suka bar Giɗaɗo da Yasmin suna rige-rigen zuwa wajen Goggoji. Hannuwanta kowannensu ya riƙe suka hau jera mata sannu. Da ido take bin su da kallo,a hankali ta furta.
"Ku dena..damuwa..na ji sauƙi."
Murmushi GiÉ—aÉ—o ya sakar mata tare da sumbatar hannunta ya ce.
"Za dai ki ji sauƙi Goggoji. Allah Ya baki lafiya Ya raba ki da yawan kwaɗayi."
A hankali ta saki murmushi mai sauti sannan ta ce.
"Amin Giɗaɗo am. Ke ƴar fara...duk kin koɗe saboda kuka...ya isa haka kukan...na ji sauƙi."
Kwantar da kanta Yasmin ta yi a jikin Goggoji tana matse guntuwar ƙwallar da ta taru a idonta. Shi kuwa Giɗaɗo sai ya miƙe tsaye ya ce.
"Na ga alamun bacci kike ji,bari mu tafi ki samu ki huta ok? Na san har da gajiya ma a tattare da ke;tinda yau kika dawo daga umra kuma aka tsiri wannan shirmen."
Kallonsa ya mayar kan Yasmin da bata da niyyar tashi su tafi ya sassauta muryarsa cike da kulawa da lallashi ya ce.
"Taso mu tafi gida ko? I promise you i will bring you back tomorrow."
Kafaɗa Yasmin ta maƙale masa,dan bata son tafiya ta bar Goggoji,haka kawai take ganin da ta tafi za su rasa ta. Ganin za ta kawo masa taurin kai sai ya fito mata a Giɗaɗonsa,nan take ta miƙe ta yi waje tana sharɓen kuka. Sallama ya sake yi wa Goggoji sannan ya bi bayan Yasmin yana jin tausayinta ƙwarai da gaske a cikin ransa. A hanya tunanin Nasibah ne danƙare a cikin ransa,sosai yake son ganin mahaifinta saboda ya miƙa ƙoƙon bararsa ko zai samu dacewa ta zamo rabonsa.
*************************
Da misalin takwas da kwata Malam Luƙman ya isa gidan su Nadiya hira. Kafin ya isa Nadiyah ta sha ado sosai tare da sanya turare,sai ta saka dogon hijabi akan shigar tata ta fita. A tsaye suka tsaya suna hira sama-sama. Babu jimawa wayar Nadiyah ta fara ringing,ko duba wa bata yi ba ta ƙi amsa kiran saboda ta gane Nawwarah ce ke kira daga kiɗan da ta saka mata. Kallonta Malam Luƙman ya yi cike da ayar tambaya. Nadiyah na ganin haka sai ta yi murmushi ta bi bayan kiran. Nawwarah na ɗaukan wayar sai ta ce.
'Ke fa ƴar wulaƙanci ce Nadiyah. Tin dazu nake ta kiranki in faɗa miki damuwata amma kina gani kika ƙi ɗaga wa.'
"Subhanallah me ya same ki Nawwarah?"
Nadiyah ta faÉ—a cike da kulawa. Ajiyar zuciya Nawwarah ta sauke sannan ta ce.