← Book details Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 28

Sashe 23

Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Nasibah ta sakar wa Luƙman da Nadiyah wadda har a wannan lokacin take manne da bango tana kuka. Cikin dasasshiyar murya ta ce.

"Ina yi muku fatan alkhairi."

Tana gama magana ta yi gaba tana tafiya cikin rangaji kamar ƴar maye. Da sauri Kilishi ta bi bayanta ta rungume ta tana jin matsanancin tausayin Nasibah na ratsa zuciyarta. A haka suka isa gida Nasibah na sauke ajiyar zuciya lokaci zuwa lokaci. Kai tsaye ɗakinsu ta wuce ta haye gado ta kwanta ta rushe da wani irin kuka mai firgitarwa. Mama da ta jima a tsaye ita da Rabi tun bayan fitar Nasibah da Kilishi a hargitse sai suka ɗunguma zuwa cikin ɗakin suka hau tambayar Nasibah abinda ya same ta. Kasa furta musu komai ta yi,dan babu wata kalma da za ta iya fasalta abinda take ji a cikin zuciyarta. Faihah Kilishi ta kira ta aika maƙota ta siyo mata ruwan sanyi guda biyu. Tana kawo wa ta karɓa ta shiga ɗakin ta zauna a kusa da Nasibah ta ɗaga ta zaune ta ɓula ledar ruwan ta kafa mata a baki. Cikin sauri Nasibah ta hau kwankwaɗar ruwan har sai da ledar ta ƙare. Jikinta na rawa ta karɓi ɗayan ta miƙe tsaye ta fasa ta hau kwarawa jikinta. A ƙasan wajen ta zube tana kuka ta ce.

"Ummah zuciyata zafi take yi min. Ummah Malam Luƙman ya ci amanar soyayyarsa da na jima ina riritawa a zuciyata. Da na san irin cin amanar da zai yi min kenan da na bi maganar Baba na cire shi a raina tun da wuri."

"Ki yi shiru ki dena kukan haka ya isa,bari Baban naki ya dawo wannan abubuwan da yake yi sun isa haka."

Mama da ta kula babu mai bata amsa sai ta yi ajiyar zuciya ta ce.

"Allah Ya kyauta Ya kawo mafita."

Daga nan ta sa kai ta bar ɗakin. Sai dai duk da cewa ta bar ɗakin amma gaba ɗaya hankalinta yana kan ƴar tata tana hango irin matsananciyar damuwar da take ɗauke da ita. Da ƙyar Kilishi ta lallaɓa Nasibah ta fita ta ɗaura alwalar sallar magariba. Ko da ta dawo ɗaki sai ta sauya kayan jikinta ta saka hijabi ta tayar da sallah. Tana idarwa Makaɗi na dawowa gidan. Fuskarsa a sake ya shiga gidan yana yi wa su Najlah wasa. Idanuwansa ya dinga jefa wa a tsakar gidan amma bai hango ƴar rigimar tasa ba. Murmushi ya yi ya ce.

"Ke Faihah ina rigimatun gidan take ne yau na ji ko ina tsit kamar an yi rasuwa?"

Cikin fushi Kilishi ta fito daga É—akinta sanye da hijabi ta ce.

"Ba dole ka ji ko ina tsit ba tinda kana neman ka jefa yarinya ƙarama a cikin mawuyacin hali? Wai kai don Allah Malam in tambaye ka mana. Shin me kake da shi a lokacin da ka je gidan iyayenmu neman aurenmu gaba ɗaya? Ina ce a wancan lokacin banda ruƙon ganga babu abinda kake yi wa mahaifinka? Da kuɗin kiɗa aka aura maka uwar su Hauwa ni kuwa...."

Kafin Kilishi ta ƙarasa maganarta Malam Sanda ya katse ta cikin wani irin matsanancin fushin da bata taɓa ganinsa a cikinsa ba ya ce.

"Ke dakata min Malama! Me yake faruwa a gidan da har za ki zauna kina neman zagar min asali da yi min gorin arziƙi?"

"Yo meye ma bai faru ba Malam? Garin leƙen jar miya a maƙota kana neman ka babbake taka tallen. Ina so ka sani a auren yanzu ƙwarya ta bi ƙwarya ake yi ba wai auren je ki dangwalo wa dangi arziƙi ba,shi kansa yaron nan da kake maitar haɗa Nasibah aure da shi baka da tabbacin iyayensa za su yarda ya auri ƴar mai facin taya jinin makaɗa."

Jinjina kai Malam Sanda ya yi ya ce.

"Afff tohh! Yanzu na gane inda maganganunki suka dosa. To ina son ki buɗe kunnuwanki ki ji ni da kyau Kilishi. Ko na mutu na bar wasiyya wa ƴan'uwana da abokaina Nasibah bata da wani mijin da ya wuce Alhaji Samir,dan haka ki adana duk wasu kalamanki na rashin arziƙi da kika tanada domina."

"Au haka ma za ka ce Malam?"

"Haka kuma za a yi ba."

"Malam wannan yaron ne fa Lukman zai auri aminiyar Nasibah."

"Allah Ya basu zaman lafiya. Itama idan tana so wani satin sai a É—aura nata auren da Alhaji Samir."

Shiru gidan ya É—auka,banda kukan Nasibah da ke tashi baka jin komai. Mama na É—aki ta zabga tagumi tana jin kamar ta je ta tunkari MakaÉ—i a yi wadda za a yi. Muryar Kilishi da ke sake yi wa MakaÉ—i magana ce ta sanya ta zama saboda kar ta nuna rashin kara. Haka Kilishi da MakaÉ—i suka yi ta sa-in-sa a tsakaninsu har ya fusata ya fita ya bar gidan. Tinda ya sa kai ya bar gidan bai dawo ba yana can wajen mai shayin dake saman layi yana hira da abokansa.

Fitarsa ke da wuya su Mama da Kilishi har da rabi da Usman sai suka zauna a tsakar gida suka hau tattaunawa akan lamarin Nasibah da Malam Luƙman. Mama ta ce bata ga laifin Malam Luƙman ba domin Malam Sanda da kansa ya kore sa ya yi masa iyaka da ƴarsa. Ita kuma Kilishi ta ce dama can baya son Nasibah tinda ya yarda da auren aminiyarta ba tare da ya ji shakkar yin hakan ba. Rabi kuwa sai ta ce to da dikkan alamu dama can yana son Nadiyah faɗa ne bai yi ba,jira yake yi sai ya auri Nasibah daga baya ya yo mata kishiya da Nadiyah. Usman kuwa kukan da Nasibah ke yi ne ya ɗaga masa hankali har ya kasa cewa kanzil a lamarin,daga sauke ajiyar zuciya sai dogon tsaki ya dinga ja har taron nasu ya tashi kowa ya nufi makwancinsa.

Malam Sanda bai dawo gida ba sai da misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi na dare,fuskar nan a murtuke ya shiga gidan da ita gudun kada ma Kilishi ta ga ƙofar kawo masa wata maganar mara tushe da amfani. Jin gidan shiru alamun kowa ya yi bacci ne ya sanya shi ajiye ledar da ke riƙe a hannunsa a saman randar tsakar gida ya ɗauki buta ya zaga bayan gida. Ya na fitowa ya ɗauki kofi da plate a kwandon wanke-wanke ya juye shayi da soyayyar indomie da kwai sannan ya nufi ɗakin su Nasibah da yake a buɗe. Kai tsaye gaban gado ya zauna a inda Nasibah ke kwanciya ya ce.

"Tinda na shigo na ji alamun idanuwanki biyu Æ´ar Baba, taso mu je ki ci abinci ki kora da shayi haÉ—in kauri dan na san baki ci abinci ba kika kwanta."

Hawaye Nasibah ta share ta juya wa Makaɗi baya ba tare da ta ce masa komai ba. Makaɗi kuwa bai sare ba sai ya ci gaba da lallashin Nasibah har sai da ta sakko daga gadon ta na kuka suka fito tsakar gida suka zauna a shimfiɗarsa. Da ƙyar take shan shayin dan kuwa ko da wasa bata gwada kai Indomie bakinta ba. Sai da Makaɗi ya gama cinye indomien tass sannan ya murje hannuwansa ya yi gyatsa ya ce.

“Nasiban Baba ina so ki buɗe kunnuwanki ki saurari dalilin da ya sa na zaɓar miki miji kamar Alhaji Samir. Na farko dai ni na san ba kya ƙaunar kishiya a rayuwarki duba da yanda kike rayuwa da ƴan'uwanki a cikin gidan nan. To shi kuwa wa talakan Malam Bahaushe babu wanda ya kai sa yawan aure. Amma idan kika auri mai kuɗi,kyau da cikakkiyar nasaba kamar Alhaji Samir za ki tsira da talauci da kishiya,ga shi uwa uba zaki dinga taimaka wa iyayenki da duk abinda kika samu a ƙarƙashin mijinki. Idan kuma ki na ganin zaɓina bai yi miki ba Nasibah ni Malam Sanda a yau na yi miki alƙawari zan aura miki duk kalar mijin da kike so."

Shiru Nasibah ta yi tana kallon kofin dake riƙe a hannunta kamar tana son hango maƙerin kofin. A hankali ta yi ajiyar zuciya ta ɗaga kai ta kalli Malam Sanda ta ce..........
[10/11, 9:27 PM] HAERMEEBRAERH❤️: ZAWARA.

NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️

PAGE 18.

"Ni Baba babu wanda nake da burin aure a yanzu,karatu nake so na yi mai zurfi ko kuma idan na gama secondary school ka buɗe min saloon,ka ga shikenan sai na ci gaba da sana'ar kitso da ƙunshi....."

"Nasibah kin ƙunshe min bakinki kin adana shi ko sai ƙunsa miki duka a cikinsa da daren nan? Ke wai wace iriyar yarinya ce ana gabas kina yamma? Ke! Tashi ki je ki kwanta tun kafin ki jawo na kamu da ciwon hawan jini,Allah Ya tashe mu lafiya."

Tura baki Nasibah ta yi ta hau ƙunƙuni kafin ta miƙe ta shige ɗakinsu. Ƙwafa makaɗi ya yi ya ce.

"Wannan yarinya Nasibah Allah Ka shirya min ita. Ki sa a ranki auren Samir kamar kin yi kin gama,idan ma abinda ya fi saloon ne idan kun yi auren ya buÉ—e miki a can."

Da wannan maganganun Malam Sanda ya gyara kwanciyarsa a tsakar gidan ya ja babbar rigarsa da ta gaji da duniya ya rufa. A can cikin ɗakin Kilishi kuwa tana zaune tana gyangyaɗi saboda ta yi alƙawarin komai dare idan Malam Sanda ya shigo sai ta yi masa magana akan lamarin Nasibah. Cikin dare ta farka ta ga ɗakin daga ita sai halinta Malam Sanda bai shigo ba. Salati ta yi tare da zabga hamma ta sauka daga saman kujera ta fito tsakar gida. Kwance ta ganshi har ya fara sakin munshari hankalinsa kwance. Haɓa Kilishi ta kama ta ce.

"Au Allah! Ni ina can ina jiransa ashe shi yana nan ya hangame baki yana bacci a tsakar gida sauro na walima da jininsa. To ai shikenan Allah Ya tashe mu lafiya."

ÆŠaki ta koma ta saka sakata ta yi kwanciyarta tana tunanin rayuwar gidan mijin nasu mai murÉ—aÉ—É—en hali.
Chapter 23 · 0% Book details