← Book details Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 28

Sashe 4

Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su na isa ƙofar gidansu Nasibah sai ta hana kowa hawa bishiyar ta ce ita za ta hau ta ciro ta basu da kanta gudun kada su kwasa da yawa. Hijabinta da jakarta ta cire ta miƙa musu suka riƙe mata ta kama bishiyar kamar ƴar biri ta haye. Tunda ta fara hawa bishiyar su Nawwarah suka fara yi wa Nasibah waƙar.

"ÆŠan biri daka tsalle,ya haye ladidi."

Nasibah na saman bishiya tana tsinko musu durumi tana wurgowa tare da taya su raira waƙar. Ta jima tana watso durimin suna waƙoƙinsu tare; can ta ji shiru babu mai yi mata amshin waƙar ɗan biri,sai ta hau ƙwala musu kira ɗaya bayan ɗaya bata ji an amsa ta ba. Ta na leƙo kanta ta ga Babanta a tsaye fuskar nan ta yi jawur kamar an kara masa ita a wuta. Gaban Nasibah ne ya yanke ya faɗi,sai ta yi sauri za ta koma saman bishiryar,ƙafarta Malam Sanda ya riƙe ya ce.

"Sakko ƙar dan ubanki,wato ɗan biri daka tsalle ko? Ki rasa waƙar da za ki yi a ƙofar gidana sai waƙar da ake ambato sunan uwata da ta mutu kuma ake danganta ta da biri Nasibah? Shaƙiyancin naki ashe ya tsallake kan mutanen unguwa ya dawo kaina Nasibah? Mu je ciki to yau zaki yaba wa aya zaƙinta."

A wannan ranar duk yanda Nasibah ta so ta yi amfani da abun duniya;tare da soyayyar da mahaifinta ke yi mata abun ya ci tura. Suna shiga cikin gidan ya samu wayar rediyo ya dinga shauɗa mata a baya yana kumawa,tun Nasibah na daurewa ita a dole ta yi fushi da Baban nata,har ta saki baki ta dinga ihu tana tsalle. Malam Sanda bai ƙyale ta ba sai da ya tabbatar ya lallasa ta ta yanda gobe idan wani ya ce ta kira sunan Ladidi ba za ta saurara wa mutumin ba,sannan ya ƙyale ta ya ɗauki abincinsa ya bar gidan.

Haka Nasibah ta ƙarasa wunin wannan ranar cikin ƙunci da ɓacin rai. Duk wadda ta zo kitso ko ƙunshi gidan sai ta ce a je a ce su dawo jibi,har gidan Aunty Luba da ta yi mata alƙawarin za ta je ta yi mata kitso da lalle har gida da ta aiko ce mata ta yi a ce sai jibi. Da yamma Najlah Autar su na ganin lokacin zuwan su makarantar dare ta yi,sai ta shiga shiri tana kiran Nasibah don ta shirya su tafi tare. A ɓangaren Nasibah kuwa bata da niyyar tashi daga inda take,saboda tana son Babanta ya dawo ya ga har a wannan lokacin bata dena fushi da shi ba.

Kilishi banda masifa babu abinda take yi wa Mama akan halayyarta ta rashin nuna wa yaranta ɓacin ranta akan duk wani abinda za su aikata ba daidai ba. Murmushi kawai Mama ta yi ta ce.

"Kilishi kenan,ki dena damun kanki akan halayen Nasibah, dika-dika Nasibar nawa take? Watan nan na mauludi idan ya zo ne fa za ta cika shekaru sha biyar a duniya,kin ga kuwa har yanzu akwai ƙuruciya a tattare da ita. Kin san Allah watarana idan aka ce ta yi dika waɗannan abubuwan ƙaryatawa za ta yi."

Cike da takaici Kilishi ta ce.

"Humm Allah Ya kyauta."

Ɗaki ta shiga ta kira Rabi ta ce ta leƙa ƙofar gida ta kira Usman su wuce makarantar dare. Babu ɓata lokaci Rabi ta leƙa ta kira Usman ya shigo suka kammala shirinsu Rabi ta kama hannun Faihah da Najlah suka tafi makaranta. Daga Mama har Kilishi babu wanda ya sake bi ta kan Nasibah. Ɗaki suka shige kowa ta kama sabgar gabanta.

Wani irin bacci ne mai daɗi ya fara ɗibar Nasibah daga zaune,dan haka sai ta kashingiɗa a wajen ta takure a waje ɗaya ta hau yin abunta. Cikin bacci ta ji ana tashinta a hankali,tana buɗe ido ta yi tozali da Nawwarah tsugunne a gabanta tana tashinta. Cikin yin ƙasa da murya Nawwarah ta ce.

"Wai ke yau ba za ki je makaranta bane?"

Tura baki Nasibah ta yi gaba tare da matso ƙwallar takaicin dukan da ta sha ta ce.

"Ni babu inda zan je sai Baba ya dawo ya bani haƙuri."

Baki Nawwarah ta kama kafin ta gyara zaman jakarta a kafaÉ—arta ta ce.

"Lallai Nasibah kina zuba mulki a gidan nan,wato kin yi laifi an dake ki amma jira kike yi a zo a baki haƙuri ko? Sannu sarauniya. Ko kin manta ke da bakinki kika ce Baban ku ko takwara ya ƙi yi wa Mamansa saboda kada tsautsayi ya sa a zage ta ko a dake ta?"

Kai Nasibah ta É—aga tare da furta.

"To ai ba ƙarya na yi masa ba Malama."

"To kin ga kenan laifi naki ne,mu ma da mun tsaya na tabbata sai ya dake mu. Ke kin ga ba wannan ba ma,kin san dukan da kika yi wa Bultuƙa ya jawo yara duk sun raina ta? Har wanda ta yi wa duka a baya yanzu ganin wallen ta suke yi. Yanzu haka na baro Nadiya tana can za ta rama dukan da ta taɓa yi mata lokacin da aka yi musabaƙa da ƴan unguwarsu."

Da jin haka Nasibah ta ware tana dariya,ba tare da ta yi shawara da kowa ba ta faɗa ɗakin Mama. Tana shiga ta tsuke fuska tana cika tana batsewa ta sauya kayan jikinta ta saka na gida. Jakar makarantar dare ta ɗauka ta fito daga ɗakin ta zari hijabinta a saman window ta ja hannun Nawwarah suka bar gidan da gudu. Tafe suke suna hira Nawwarah na fatan Allah Ya sa ba a gama dambace wa ba Nasibah ta shigar wa ƙawarsu Nadiya.

Lokacin da su Nasibah suka isa layin makarantar tasu sun tarar da yara sun taru a wajen damben da ake yi. Nasibah na zuwa yara suka hau ihun kiran sunanta wato Nansy Ƙaya,hakan sai ya gigita Bultuƙa jikinta ya saki saboda tsoro,Nadiya na ganin haka sai ta shatale ƙafarta ta yarɓar da ita a ƙasa ta hau jibgarta kamar an aiko ta. Suna cikin wannan halin Malamin Islamiyyar su wato Malam Luƙman ya lallaɓo da dorinarsa ya shiga tsakiyar filin ya hau shauɗawa duk wanda rabonsa ya tsaga. Nan take wajen ya kaure da ihu yara suka watse. Nasibah kuwa tun kafin Malam Luƙman ya ƙaraso wajen ta hango shi,dan haka sai ta sunkuya ta bi ta bayan taron ta shiga aji. Ko da su Nawwarah suka iso tuni Malam Atiku ya tare hanya. A wajen ya sa suka rage tsawon su ya bi su da bulala biyar-biyar sannan ya ce su shiga aji. Nawwarah da take ƴar masu hannu da shuni bata saba da duka ba,tuni wajen da aka dake ta ya tashi ya yi jawur,sai haska hannun take yi a hasken fitilar ajinsu tana matsar ƙwalla. Nasibah da ta kalli ƙawayen nata sai ta fashe da dariya ta kifa kai a ƙur'aninta tana kaiwa da kawowa kamar mai yin karatu.

Lokacin da Malam Luƙman ya dawo ya tarar da yaran na ta karatu,sai ya zauna ya ci gaba da ƙara wa wanda ke da buƙatar ƙari karatu. Kafin lokacin tashi ya yi ya tsayar da yaran ya yi musu faɗa da nasiha akan yawan faɗan da suke yi a tsakanin unguwannin Sani Me nagge,Tal'udu da su ƴan Mandawari. Daga nan ya tashe su kowa ya kama hanyar gidansu.

Yau ma kamar ko da yaushe idan an tashi; Malam Luƙman ya fito da litattafansa ya yi tsaye a wajen da suka saba haɗuwa da Nasibah, sai su jera suna tafe suna hira har ya mayar da ita gida sannan su tsaya a ƙofar gidansu Nasibah su taɓa hira,daga nan sai su yi sallama ya tafi gida,itama ta shige nasu gidan. Shiru-shiru Malam Luƙman bai ga Nasibah ba,ballantana su Najlah,dan haka sai ya haƙura ya tafi gida yana saƙa da warwara a cikin ransa.

A ɓangaren Nasibah kuwa ana tashi ta bi Rabi suka wuce gida,saboda bata son haɗuwa da Malam Luƙman a wannan ranar ya ji muryarta a shaƙe ya gane ta yi kuka. Su na shiga soron gidan ta ci karo da babur ɗin Babansu,nan take ta langwaɓe ta shiga gidan tana ɗingisa ƙafa. Baba dake zaune a tabarma a ƙofar ɗakin Mama yana ganin Nasibah ya gane nemansa take da sharri a cikin wannan daren. Murmushi ya saki ya girgiza kansa ya ce.

"Ƴar Baba me ya samu ƙafar taki kuma na ga kina ɗingishi?"

Nan take Nasibah ta ɓare baki ta rushe da kuka kamar wadda aka daka. Daga can cikin ɗakin Kilishi ta bugo tsaki ta ce.

"Allah Ya wadaran naka ya lalace dai."

Harara Nasibah ta wurga wa ƙofar ɗakin Kilishi tana murguɗa baki kamar tana ganinta. Ba tare da ta kula ta ba ta isa shimfiɗar Babansu ta zauna a gabansa tana shagwaɓe fuska ta ce.

"Baba ba kai bane ka janyo min ƙafa ta daga bishiya ɗazu sai da ta ce ƙasss."

Baki Malam Sanda ya kama ya ce.

"Subhanallahi! In ce dai ba targaɗe kika yi ba ko tsagewar ƙashi?"

"Baba ƙafar fa karye wa ta kusa yi,da ƙyar na iya takawa na je makaranta."

Shiru ya yi ya zira hannunsa a aljihunsa ya zaro mata wata leda ya miƙa mata,a tare suka ɗora yatsansu manuni a bakinsu suna dariya ƙasa-ƙasa. Nan take Nasibah ta buɗe ledar ta tarar da kilishin da ba zai wuce yanka huɗu ba. Cike da farinciki ta tashi ta shiga kitchen ta ɗakko abincinta na rana da bata ci ba ta juye kilishin akai ta zauna suna hira da Babanta kamar babu abinda ya shiga tsakaninsu na ɓacin rai.

Bayan Nasibah ta kammala cin abincinta sai ta hau bawa Malam Sanda labarin sabon ajin da aka kaisu da Malamansu da abinda aka koyar da su a wannan ranar. Cike da alfahari da jin daÉ—i Malam Sanda ya ce.

"Allah mai girma! Yau ni jinin makaɗa wanda na taso ina taya mahaifina ɗaukan ganga da kalangu,mai yawon kwararo dan kaɗa ganga ni ne ke gane wasu kalmomin turanci duk ta dalilin samun haziƙa kuma fasihiyar yarinya kamarki Nasibah."

Dariya Nasibah ta yi cike da jin daÉ—i ta ce.
Chapter 4 · 0% Book details