Sashe 6
Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ran Mama da bata cika saka baki a sabgar Nasibah ba tuni ya gama tafasa da takaicin abubuwan da take yi. Babu zato ko tsammani Nasibah na ƙoƙarin tashi ta je ta wanke hannunta ta ji saukar itace akan ta. Ihu ta kurma tana neman wajen guduwa amma Mama ta damƙi hannunta tana ta zabga mata itace. Da gudu Kilishi ta fito har zaninta na neman faɗuwa. Malam Sanda kuwa da tsoron Allah ya cika masa zuciya tuni ya ƙame a wajen baki sake yana kallon ikon Allah.
Nasibah banda tsalle babu abinda take yi tana ba wa Mama haƙuri. Cikin fushin da suka jima basu ga Mama ta yi irinsa ba Mama ta karɓi uniform ɗin hannun Rabi da jikinta ke ta rawa ta wurga wa Nasibah ta ce.
"Kin tashi kin wuce kin shirya ko sai na sake daka ki da wannan itacen? Haba! Wannan iskancin naki ya ishe ni haka Nasibah. Ke kenan kullum akwai iya shegen da za ki dasa sabo dal a cikin gidan nan? Ga yayyenki nan ga ƙannenki babu wanda yake bamu ciwon kai sai ke. Amma ba laifinki bane,laifin me ɗaure miki gindi ne ki ci karenki babu babbaka."
Mama ta ƙarasa maganarta tare da wurgar da itacen ta koma kitchen tana huci. Malam Sanda tuni ya tattare kayansa ya shiga ɗaki ya samu Nasibah tana shiryawa yana ta bata haƙuri kamar shima idan ta hasala shi baya jibgarta. A haka ta gama shiri ta fito ko kuɗin break bata nema ba. Tana fitowa Malam Sanda ya fito ya wuce kilishi dake bawa Mama haƙuri yana ta wani tsumewa yana ɗaure fuska.
Ko da ya fita tuni Nasibah ta yi gaba tana tafe kanta a ƙasa ta janyo hijabinta gaban goshinta. Har ta bar layinsu Malam Sanda ya same ta a hanya ya tsaya ta hau babur ɗin ya wuce kaita makaranta. A hanya Nasibah sai ta ɗora kanta a bayansa tana ta sharɓen kuka sai kace wadda aka yi wa mutuwa. Su na isa ta sauka daga babur ɗin za ta shiga makaranta Malam Sanda ya saka hannu a aljihu ya ɗakko ɗari biyu ya bata. Karɓa ta yi ta shige makarantar ba tare da ta ce masa kanzil ba. Malam Sanda na nan tsaye har sai da ya dena hango Nasibah sannan ya tayar da Babur ɗinsa ya wuce wajen aikinsa. Dan ya yi alƙawarin sai ya nuna wa Mama kuskurenta na dukan Nasibah da itace da ta yi,tunda dai ƴarsa ba ɓarauniya bace ba kuma mayya ba. Wajen Mai ƙosan gefen wajen facinsa ya je ta soya masa na ɗari biyar ya ci ya sha kokon nera saba'in ya koma bakin aikinsa. A wannan rana Malam Sanda ya samu kasuwa sosai. Ga kuma babban kwastomansa ɗan unguwarsu ya zo a cika masa iskar gaba da bayan motarsa. Gyaɗa suka siya suna ci suna hira kamar wasu sa'anni. Malam Sanda na gama saka iska a motar kwastoman nasa ya miƙe tsaye riƙe da abun buga iska zai mayar da shi mazauninsa. Nasibah ya hango ita kaɗai tana tafe kamar za ta kwanta a saman titin. Cike da damuwa Malam Sanda ya nufi inda take da gudu ya riƙe ta,babu ɓata lokaci Nasibah ta saki jikinta a hannun Malam Sanda ta hau tsiyayar da ruwan hawaye. Sosai hankalin Malam Sanda ya tashi saboda jin wani irin zafi da jikin Nasibah ya ɗauka. Suna ƙarasowa Kwastomansa ya ce.
"Ah ah Baba wannan ba Æ´ar ka ba ce Nasibah? Me ya same ta na ganta haka?"
"Da alama bata jin daÉ—i ne Alhaji Samir. Kai ÆŠan Tiye zo ka kula da wajen nan bari na kai ta asibiti."
Cikin sauri Kwastoman Malam Sanda ya ce.
"Saka ta a mota Baba na kai ta asibitina,daga nan sai na wuce da ita gida."
"Ah ah Malam Samir a yi haka? Na ji ka ce yau za ka koma Abuja ko?"
"Eh yau zan koma,amma sai ƙarfe biyu jirginmu zai tashi."
"To shikenan Alhaji Samir na gode Allah Ya ƙara yi wa rayuwarka albarka. Gata nan idan kun je kada ma a sha wahalar rubuta mata magani dan ba sha take yi ba,allurar ma sai ka yi da gaske za ta tsaya a yi mata."
Murmushi Samir ya yi ya ce.
"Babu damuwa Baba zan kula da ita. Allah na tuba ita da bata da lafiya ƙarfinta duk ya ƙare ina ita ina hana a yi mata allura?"
"Hummm."
Malam Sanda kawai ya ce ya ja baya yana ɗaga musu hannu har suka ɓace wa ganinsa.
Su na isa private hospital ɗin Samir sai ya fito waje ya rufe motar,ya buɗe baya inda Nasibah ke kwance male-male kamar ruwa. Tashinta ya yi ya ga ko motsawa bata yi ba,cikin sauri ya leƙa cikin asibitin ya kira nurses mata suka ɗaga ta suka saka a wheelchair suka tura ta zuwa cikin asibitin. Su na zuwa suka shigar da ita inda Sameer ke duba marasa lafiya. Sai da ya duba ta ya fuskanci duka ne ta sha har ya saka ta yin zazzaɓi,ga wajen da aka dake ta nan duk ya yi jawur ya kumbura. Ransa a ɓace ya haɗa alluran da zai yi mata yana ta mitar sai ya yi ƙarar Malaman makarantar su Nasibah,domin basu da ƴancin dukanta irin haka har su jawo mata jinyar dole. Cikin abinda bai fi ƙiftawar ido ba Nasibah ta miƙe zaune tankar-kar tana zare ido tare da faɗin.
"Baaa na son alluraa."
Nan take hawaye ya hau kwaranya a saman kuncinta,ga bakinta sai rawa yake yi saboda sanyin zazzaɓi da take fama da shi. Cike da tsananin tausayawa Samir ya riƙe hannunta a hankali ya ce.
"Nansy kalli cikin idona."
A hankali Nasibah ta buɗe rinannun idanuwanta ta zuba su a saman fuskar Samir,kasa ɗauke idanuwanta ta yi saboda wani irin maganaɗisun kyau da cikar halitta da Samir yake tattare da shi. Samir ba baƙi bane,kuma ba fari bane shi. Yana da fuska mai tsawo mai cike da gemu da gira kamar an zana masa ita. Yana da cikakkun laɓɓa masu faɗi da duhu kewaye da su,ta cikinsu kuma sun surka da ja. Idanuwan Samir sune suka fi tafiya da hankalin Nasibah. A daidai lokacin da ta mayar da kallonta zuwa saman gemunsa ta ji shigar allura jikinta. Rintse idonta ta yi ta saki ƙara tare da ƙanƙame shi jikinta na rawa. A hankali ya juye mata ruwan allurar sannan ya zare ta yana murmushi mai sauti ya ce.
"To har an gama ai sai ki buɗe idon kuma ki dena kuka;saboda kada zazzaɓin naki ya ƙaru. Idan kuma kika ci gaba da kuka zan sake yi miki allura."
Da sauri Nasibah ta sakar masa riga tana lailaya wajen allurar tana jan zuciya tare da ƙoƙarin danne kukanta. Murmushi Samir ya yi,domin shi yarinyar dariya take bashi. Sai da ya bar Nasibah ta yi baccin awa ɗaya sannan ya tashe ta suka nufi motarsa. Tana shiga baya shi kuma ya shiga mazaunin direba ya yi wa ma'aikatansa sallama ya wuce. Sai da ya tsaya da ita a wani shago ya yi mata siyayya sannan ya mayar da ita gida. Ba tare da Nasibah ta juya ta yi masa godiya ba ta shige cikin gida ta wuce ɗakinsu ta yi kwanciyarta. Yaran da suka shiga da abinda Samir ya siyo mata tuni sun juya da gudu suna murnar kuɗin da ya basu.
Mama dake aiki a tsakar gida sai ta kalli Kilishi dake tsefe kanta ta ce.
"Ikon Allah,waye ya kawo wa wannan marar kunyar kayan nan kuma oho? Ta shigo balam-balam kamar balama ta wuce mutane babu ko magana."
Kai ƙarshen kalamanta ya yi daidai da shigowar Malam Sanda da yake cike da Mama. Cikin fushi ya ce.
"Wanda za ta aura ne ya kawo mata kayan ko kina da tacewa ne? Ko kuma yanzun ma itacen zaki É—auka ki yi ta shirgarta kamar an kama tsohon kwarto a gidan soja?"
Girarsu suka haÉ—e waje É—aya cike da mamaki Mama da Kilishi suka ce.
"Ban gane wanda za ta aura ba?"
Nasibah ma tuni ta fito daga É—aki bakinta na rawa ta ce.
"Wanda zan aura kuma Baba?"
Cikin dakiya Malam Sanda ya ce.
"Ƙwarai shi na zaɓa miki a matsayin mijin aure. Idan kin ga baki auri Alhaji Samir ba,to dama can Allah Ya rubuta ke ɗin ba matarsa bace. Samir saurayi ne mai abun hannunsa, kin dai gansa yana da kyawunsa bashi da makusa,kowacce mace ta same shi a matsayin miji ta gama yin dace."
Kuka mai cin rai Nasibah ta saki tana ihu ta ce.
"Ni dai don Allah ku kashe ni na huta da wannan baƙincikin da kuke ƙunsa min a cikin gidan nan. Jiya ka dake ni,yau ta dake ni da itace kamar ɓarauniya,kuma yanzu ka zo da maganar dake barazanar fasa min zuciya."
KafaÉ—a Malam Sanda ya É—aga ya ce.
"To idan zuciyar taki ta fashe sai mu ce Allah Ya jiƙanki Nasibah,amma dai a idona kin gama yin mijin aure. Samir shine wanda na zaɓa miki. Kuma muna nan da ke,shi da kansa zai dawo ya ce yana sonki da aure."
Ƙafafuwa Nasibah ta hau direwa tana yarfe hannuwa ta shige ɗakinsu tana kuka ta faɗa soson katifarta. Mama da Kilishi kuwa baki suka saki suna ji da ganin ikon Allah a wajen mijin nasu. Malam Sanda kuwa cikin farinciki ya bar gidan ya koma bakin aikinsa zuciyarsa na ci gaba da fata da addu'ar Allah Ya sa Samir ya so Nasibah ya zo da kansa ba aike ba ya sanar da shi ita ce muradin ransa...........
(Iyaye da dama na yin kuskuren zaɓarwa ƴaƴansu mata mijin aure saboda kawai mutum na da; dukiya,kyau,nasaba,ko wani abun duniya. Wasu iyayen ba sa duba halayya da nagarta su dai kawai inda ƴarsu za ta huta suma su huta shi suke nema.)
[9/19, 9:15 AM] HAERMEEBRAERHâ¤ï¸: ZAWARA.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨âœï¸
PAGE 5.