Sashe 1
Zawarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[9/15, 10:09 AM] HAERMEEBRAERHâ¤ï¸: ZAWARAH.
NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨âœï¸
PAGE 1.
Wani irin gudu motar su ke shararawa a saman titi kamar za ta tashi sama. A daidai wannan lokacin kuwa Yunus dake zaune a bayan mota yana buga tsaki ya ɗaga hannunsa ya sake duba agogon hannunsa tare da jan wani dogon tsakin a karo na babu adadi. Cikin ransa yake jin kamar ya karɓi tuƙin motar ya ratsa ta lunguna ko Allah zai sa ya yi saurin isa gida da wuri domin ya samu sallar juma'a akan lokaci. A ƙagauce ya kalli Malam Sadi direba ya ce.
"Man Sadi ko za mu yanki wannan layin ne mu tsaya kawai mu yi sallahr mu a masallacin Shaikh Shu'aib; domin na kula idan muka ce sai mun je gida lokaci zai ƙure mu rasa sallar juma'ar gaba ɗayanta."
Jinjina kai direban ya yi ya ce.
"To Alhaji duk yanda ka ce ayi ai haka za a yi."
Cikin abinda bai fi mintuna biyar ba Malam Sadi ya kutsa kan motarsu cikin babban layin dake unguwar Gadon Ƙaya yana fatan su isa da wuri dan su samu sallah akan lokaci. Sun yi nisa da tafiya ya hango cincirindon mutane a gabansu wanda da damar mutanen wajen yara ne suka fi yawa a wajen. Tsaki direban ya ja ya ce.
"Nan kuma ko taron me ake yi haka suka tare wa mutane hanya oho?"
A ƙagauce ya hau danna horn ɗin motar dan taron ya watse su samu su wuce,amma ga mamakinsa ko gezau yaran nan basu yi ba ballantana su basu hanya,wasu yaran ya hango daga lunguna da saƙon unguwar suna sake fitowa suna leƙen tsakiyar taron. Kafin ya ce wani abu Yunus da ya gaji da jira ya ce.
"Je ka ka leƙa ka ga me yake faruwa Please dan na ji har an gama khudba."
Da sauri Malam Sadi ya kashe motar ya buɗe ƙofa ya fita har yana haɗa wa da gudu. Yana isa wajen taron sai ya dinga leƙa wa yana janye yaran dake ta leƙe suna faɗin.
"Ku casu arna ku casu,ku casu ba mai raba ku,duk wanda ya raba faɗan Nansy Ƙaya tamkar ya raba auren tsohonsa da tsohuwarsa ne."
Yana isa tsakiyar filin ya ci karo da wata yarinya fara wadda ba za ta wuce shekaru sha uku zuwa sha huɗu ba a duniya,yarinyar tana da matsakaicin tsawo da girman jiki. Zaune take a saman wani bokiti tana zane a ƙasa kamar babu abinda ya dame ta a gidan duniya. A gefenta na hagu kuwa wata ƙatuwar yarinya ce wadda za ta girme mata tsaye tana cika tana batsewa tare da faɗin.
"Kin ga dai na ce miki ki É—aga min bokitina na tafi gida jirana ake yi ko?"
Kai yarinyar dake zaune a saman bokitin ta ɗaga tana zabga wa ƙatuwar dake girgiza ƙugu harara ta ce.
"Ai na faɗa miki idan kina da ƙarfi to ki yi amfani da shi ki ɗaga ni sama ki ɗauki bokitinki. Sai dai da dikkan alamu kurin banza da cika baki kawai kika iya."
Malam Sadi na shirin yiwa yaran magana Yunus da ya gaji da jiransa ya biyo bayansa sai ya kama hannunsa tare da girgiza masa kai. Kafin su juya su bar wajen yarinyar nan dake zaune saman bokiti ta yi kukan kura ta kwashe ƙafar ƙatuwar nan ta zubar da ita a ƙasa;sannan ta bi ta ta zauna a ruwan cikinta tana duka kamar an aiko ta. Nan take yaran dake wajen suka kaure da ihu da sowa suna faɗin.
"Da kyau Nansy Ƙaya sa ƙato kuka;mata da sun ganki su ɓuya a bayan uwarsu."
Jinjina kai kawai matashin nan ya yi suka koma wajen da motar su take suka yi parking a gefe sannan suka ratse taron yaran suka nufi masallacin a ƙafa. Suna isa liman na tada kabbara,dan haka babu ɓata lokaci suka shige masallaci suka shiga cikin sahu.
Bayan sun idar da sallah sai suka zauna suka yi azkar sannan Yunus ya fito waje domin ya saka takalminsa su wuce. Ta gabansa Nansy Ƙaya ta zo za ta wuce ita da ƙawayenta tana basu labarin yanda ta yi wa Nabila Bultuƙa dukan tsiya. Yaran sai yaba mata suke yi suna jin daɗin yanda ta zane yarinyar da kowa ke jin matsanancin tsoronta a kaf layin da ma sauran unguwannin dake kusa da su. Babu zato babu tsammani ya ji muryar Nansy tana faɗin.
"Ke dalla wannan ɗin ne kyakkyawa? Ba dan kar na rantse Allah ya saka ni a wuta ba da sai na ce Luƙman ɗina ya fi sa kyau."
Dariya sauran yaran suka fashe da ita,cikin dariya É—aya daga cikinsu ta ce.
"Ashe dai kin san ƙarya kika yi,shi yasa kike tsoron kada Allah Ya saka ki a wuta."
Juyawa ta yi cikin sa'a idanuwanta suka shiga cikin na Yunus dake kallonsu yana murmushi. Cikin sauri Nansy ta É—auke idanuwanta daga nashi tana haki tare da tattare zaninta ta kwasa da gudu ta sha kwanar layin dake kusa da inda suke. Nan take Yunus ya fashe da dariya mai sauti ya kalli Malam Sadi ya ce.
"Mu je ko?"
Gaba ya yi Malam Sadi na biye da shi yana mamakin sauyawar uban gidan nasa a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Ko da suka isa wajen motarsu sai suka ga an yi rubutu a jikin motarsu cikin salon haɗe manyan baƙi cikin ƙananan baƙi an rubuta.
"MoTar NaNSy ƙAyA."
Ran Malam Sadi a ɓace ya kalli mai gidan nasa ya ce.
"In Allah Ya yarda wannan ja'irar yarinyar ce da suka yi dambe É—azu ta yi wannan aika-aikar."
Murmushi Yunus ya yi ya shafi jikin rubutun ya furta.
"Nansy Ƙaya."
A hankali,sannan Ya kalli Malam Sadi ya ce.
"Mu je ko?"
Ba tare da Malam Sadi ya sake furta komai ba ya shiga motar yana cin alwashin ko a hanya ya sake ganin yarinyar,sai ya yi mata shegen duka. Motar su na barin layin fuskar Yunus ta sauya daga farinciki zuwa ƙunci da damuwa. Ta madubi Malam Sadi ya hango uban gidan nasa,cikin sanyin murya ya ce.
"Ranka ya daÉ—e ko dai na kai ka gidanka kawai ka huta?"
Murmushin yaƙe Yunus ya yi ya ce.
"Ah ah,kai ni gida na gana da Æ´an'uwana."
Kai kawai Malam Sadi ya jinjina ya É—auki hanyar gidan Gwani Ibrahim Yunus Gombe.
*****************
A guje Nansy ta shiga gidansu kamar wadda aka koro ta da makamai. Tana zuwa tsakar gidan ta ci karo da bokiti cike da ruwa,ba tare da tunanin komai ba ta ɗauki bokitin tare da ƙarasawa ƙofar ɗakinsu ta ɗauki kwandon wanka ta faɗa. Tun tana cire tufafinta take jin wani irin sululin azaba a wuyanta. Tana gama tuɓe kaya ta duƙa ta kindimi ruwa da kofin wanka ta kwara tun daga saman fuskarta ya sauka har zuwa ƙafafuwanta da suka yi fururu. Ƙara ta saki saboda azabar zafin da ta ji a lokacin da ruwan ya sauka a dokin wuyanta da ya sha yaƙushi. Ƙwafa ta yi tare da cin alwashin wannan faɗa babu mai kashe shi har sai ta daki Bultuƙa dukan da zai wanke mata zafin ciwon da ta ji mata a wuya. A gaggauce ta gama wankanta ta fito tsakar gida tana sheƙa dariya kamar mahaukaciya. Babu abinda take tuna wa sai lokacin da ta cika bakin abokiyar dambenta da ƙasa,ga kuma jini yana zuba da yawu mai yauƙi. Da ta kai mata sabon naushi sai ta ce.
"Nansy ki bariii,kin ga dai aike na aka yi bana son faÉ—a ban shirya baaa."
Tana tsaka da dariya ta ji an sakar mata ƙoso a tsakiyar kai. Da sauri ta dafe wajen ta juya a fusace tana huci kamar kububuwa. Cikin tsananin ɓacin rai Yah Hauwa ta ce.
"Ke dan ubanki wa ya ce ki É—aukar min ruwan wanka na ki yi amfani da shi? Ko an faÉ—a miki uwarki ce ta É—ebo min ruwan?"
Baki Nansy ta murguÉ—a cike da tsantsar rashin kunya ta kalli babbar yayar tasu ta ce.
"Ko uwata bata É—ebo ruwa ta ajiye ba;ai a bokitinta aka ajiye ruwan,ni na ce mutum ya baro É—akin aurensa ya zo gidan mutane yana aron kayansu?"
Baki Yah Hauwa ta saki tana kallon Nansy, domin kuwa duk gidan suna shakkarta saboda ita ce babba,daga ita sai Lawizah,Sabirah da Hanifah,sannan Rabi da Usman ƴaran ɗakin Kilishi. Nasibah wato Nansy Ƙaya ita ce babba a ɗakinsu,sai ƙannenta mata biyu Faihah da Najlah. Cike da jin takaicin rashin kunyar da Nansy ta yi mata cikin zafin nama ta yi kanta a guje za ta dake ta. Sai dai kafin ta kama ta har ta isa ɗakinsu ta rufe ƙofa ta danne tana dariya. Cike da takaici Yah Hauwa ta tsaya tana haki a tsakar gidan ta ce.
"Ai sai dai idan yau ba za ki fito tsakar gidan nan ba Nasibah. Ke har kin isa ki min laifi in yi magana ki yi min rashin kunya? To ko uwarki bata isa ba ballantana ke."
Daga can cikin É—aki Nansy ta É—aga murya ta ce.
"Yah Hauwa na faÉ—a miki idan muna abunmu ki dena sako uwata a ciki ba kya ji ko?"
"Kan uban can kayyasa! Ni kike faÉ—awa haka Nasibah? Na rantse da...."
"To bismillahi,me yake faruwa ne ake ta hayaniya a gidan?"
Kafin Yah Hauwa ta yi magana,Malam Sanda Uba Makaɗi;wanda mutane ke kiransa da Makaɗi ya durƙusa ya ɗauki buta ya shiga banɗaki. Nasibah kuwa na jin muryar mahaifinta sai ta buɗe ƙofa ta fito tana karkaɗa ƙugu tana kallon Yah Hauwa tana ɓaɓɓata rai. Makaɗi na fitowa daga banɗaki ya ce.
"Ke Hauwa menene haka kike wani cika kina batsewa kamar za ki fashe iye?"
Tura baki gaba Yah Hauwa ta yi,sannan ta ce.
"Baba ka shiga tsakanina da wannan yarinyar,idan ba haka ba zan karya ta na nakasa shegiya a banza."
Cikin sauri Nansy ta kalli Baban nasu ta kyaɓe baki tana wani irin kuka,kai da ka ji kukan ka san na tsantsar makirci ne. Nan take Makaɗi ya ɓata rai ya kalli Yah Hauwa ya ce.