Sashe 9
Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƴan matan nan duk sun sha jinin jikinsu, me ɗinki kuwa da fitowar Sadiya ta mantar da ita abin da Inna ta lafta mata a fuska da wuyanta tsabar tsoro, gabaɗaya ya mata baƙiƙƙirin a fuska kamar ta shafa baƙin gawayi dama ga ta sha uban bilicin sai ta koma kamar wata jimina.
"Yauwa ga kakanninsa nan" Imra n ya yi saurin faɗa ganin su Mama sun shigo. Idanun Mama da na Hajiya ne suka sauka a hannun Sadiya da ke riƙe da miciji, gabaɗaya wani tsoro ne ya rufe su dan su bai taɓa sawaya a gabansu ba, sai dai a basu labari ita kuma Hajiya dama ita ce me cewa ko ya zama miciji babu abin da zai yiwa mutane, sai dai ganinsa yau muraran ya kaɗa mata hantar cikinta, Mama kuwa cikin ficewar hayyacin ganin ƙaton miciji riƙe a hannun ɗiyarta ta buɗe baki ta ce.
"Sadiya me zan gani haka? Hassan ɗin ne ya zama wannan ƙatoton micijin kamar wata mesa? Kuma kika kama shi kika riƙe a hannu, me ye amfanin ubansa da yake tsaye?" Mama da soyayyar ƴa da uwa tasa ta manta cewar Hajiya na wurin ta faɗa tana kallon micijin.
"Haba Mamar Sadiya ai ana barin halak ma dan kunya, kuma uwa ai ita ce tushen ɗa, kuma da ita da Imran ai duk ɗaya ne ma in ta riƙe babu komai" Hajiya ma da son ɗanta ya rufe mata ido ta faɗa ita ma idanunta a kan Hassan ɗin.
"Wai ni kam me yasa kuke haka, ta yaya ma za a ce uwa ce rushen ɗa haba Amina wannan ma ai ba maganar ɗauka bace, uba ai shi ne tushen ɗa, lokacin da ya ɗirkawa ƴar mutane ciki take riƙitu da tsohon ciki baki ce haka ba sai yanzu da take riƙe da miciji aka ce a bashi ya riƙe?" Cewar Inna tana hararar Hajiya Amina da sai yanzu ta ga wautar ta amma ai da gaskiyarta ya za a yi a riƙe miciji da bbau tabbas a kansa.
Hajiya da ke shirin maida martani ta rufe bakinta ruf, ganin wani uban ƙwacewa da micijin ya yi daga hannun Sadiya ya wani zabura ya yi sama kamar wata iska ya bar hannun Sadiya. A tsakiyar mutanen nan ya tsaya tare da fasa kai yana wani wawwaiga idanu. Kowa ya matuƙar razana da yanayin yadda micijin ya yi, Mama kallon ƙofar gidan ta yi amma cikin rashin da'a sai ta ga a kulle dan dama Imran na shigowa sai ya manta bai rufe ba su kuma suna shigowa sai suka maida ƙofar suke rufe jamlock ɗin ya shiga.
Dan haka babu hanyar fita dan yadda jikin kowa ke karkarwa babu inda za su iya buÉ—ewa saboda a tsorace suke gabaÉ—aya sun gama tsurewa.
Inna kuwa tana ganin hakan sai bakinta ya fara motsi leɓanta na sama ya fara gwaruwa da na ƙasa alamar dai tana rattabo du'ai.
Kowa karkarwa yake kamar sun haÉ—iyi mazari.
"Wai shin Imirana duk wurin nan fa kai ne namiji, ka yi wani abu mana " Cewar Inna cikin sarƙewar murya.
" Haba Inna in shi ne namiji ma sai ya kai kansa ga halaka, kar ki manta ni fa shi kaÉ—ai gareni, ga uwar yaro kya ke cewa wai shi namiji ne ai Sadiya ma mace ce me kamar maza kwari ne kawai babu" Hajiya ta faÉ—a har rana yin in'inna tsabar a ruÉ—e take.
"Oh ni Azumi na ga abin da ya turewa buzu naɗi wallahi yanzu Amina ƙin gaskiya ƙiri-ƙiri to wallahi ki ji tsoron Allah dan faga ƙin gaskiya sai ɓa...
Wani uban zillo da micijin ya sake yi tare da maida kansa ya kwantar a ƙasan sai kuma ya ɗaga jelar sama, shi ya dakatar da Inna daga maganar da take son ƙarasawa. Kowa ɗif ya yi babu me cewa uffan amma da ka gansu ka san a matuƙar tsorace suke. Imran kuwa sunkuyawa ya yi ya ajiye wayarsa a ƙasa ya ɗago tsaye ya sanya hannunsa na dama a haɓarsa ya shiga shafa haɓar da shi kansa bai san dalili ba, shafawa yake ba ƙaƙƙautawa daga gefe zuwa gefe, bakinsa kuwa sai mismismis yake shi kaɗai ya san me yake faɗa. Inna kuwa hannu ta sanya ta toshe hancinta da ke zubar majina, idanunta a kan me ƙunshi nan da take karkarwa fitsari na biyowa ƙafafunta sai buɗe baki take tana kuka amma marar sauti zuwa lokacin lallan ya gama haɗa mata fuska da baƙi ta yi baƙiƙƙirin da ita.
"Shegiyar yarinya ji yadda ta koma kamar bunsurun ɗan akuya, gabaɗaya ta yi baƙi kamar ta shafa baƙin bula, sai ta zama kamar irin baƙin bunsurun nan gemu ne kawai babu" Cewar Inna a zuciyarta tana dariyar ƙeta duk da halin da ake ciki amma fa ka kalli me ƙunshin nan sai ka kai zuciya nesa ne dariya ba za ta ƙwace maka ba. Gurbin idonta kawai ake iya hangowa ita kuwa sai ɓare baki take tana da na sanin zuwa gidan ƙunshin ma gabaɗaya.
Sadiya kwa gaban micijin ta je ta durƙusa tana kallonsa hawaye na zubowa daga idanunta. Mama kuwa so take ta ce Sadiya ta tashi faga gaban micijin sai dai tsoro da fargaba ya hanata magana tana ganin kar ta yi magana micijin ya iyo kanta ya sare ta a banza ta bar duniyar a wufi, dan haka sai ta ja bakinta ta yi shiru tana ta lazimi a zuciyarta lazimin da ita kanta da za a sanya mata wuƙa a wuya a ce ta faɗa ko kalma ɗaya ba za ta iya faɗa ba, dan ta kasa banbance ma addu'a take ko karatun qur'ani ko kuwa ƙasida, wani lokacin ma sai ta ji kamar waƙa-waƙa take amma Allah ne kaɗai ya san karatun kurma.
Da baya da baya micijin ya shiga tafiya aikuwa aka dare aka bashi hanya, kowa cikinsa na É—urar ruwa ga miciji da shegen gudun tsiya idan ka ce za ka gudu idan ya biyoka ba lallai ka tsere masa ba saboda gudun da yake dashi. Dan haka sai kowa ya shiga taitayinsa aka shiga jiran ganin abin da zai yi. Sauran matan kuwa sai kuka suke marar sauti wata ta kama tsantsa wata ta É—ora hannu a ka har da wacce ta É—aga hannaye sama irin yadda ake addu'a ta baza tafukan hannaye sai wani karkata kai take tana kai kukanta wurin Allah.
Ashrof kuwa ta sanya hannu a fuskarta ta rufe fuskar da tafukan hannayenta tana kallon micijin ta tsakanin yatsada yatsa dan kar ta rufe idanun duka micijin ya iyo wurinta dan ita ganinsa kaÉ—ai ma razana ta yake. Hajiya yadda micijin ya fara ja baya haka ita ma ta shiga ja baya, a hankali har sai da ta ga babu wurin gudu sannan tana tsoron ta zuba da gudu micijin ya tsallakr kowa ya biyo ta haka ta jure tana cewa a zuciyarta.
"Allah ka dubemu ka kawo mana mafita"
"Allah ka kawo me cetonmu, a wannan gida da muke ciki a rufe ga kuma ajalinmu a tare da mu" Cewar Inna a É—an hankali kamar tana tsoron faÉ—a.
A hankali micijin ya shiga kanannaÉ—ewa har sai da ya kanannaÉ—e duka jikinsa, sai kuma cikin hanzari da zafin nama ya zura da gudu, ya shiga zagaye gefen da mutanen ke tsaye kowa kallonsa kawai yake sai da ya zagaya kusan sau uku, sannan cikin tafiya É—aya biyu ya yi sai gashi a gaban Imran yana zuwa ya fasa kai ya dakata a wurin ba tare da ya matsa ba.
"Ka min daidai Hassan, gwara da ka je gun ubanka da kan ka yau za mu ga ƙarshn ƙarya" Cewar Inna a zuciyarta tana ƙwafa.
"Wayyo Allah É—ana, É—ana guda É—aya da nake da shi duk duniya yau ya haifi abin da zai zama ajalinmu" Cewar Hajiya a zuciyarta tana tana share hawaye.
"Gwara da ka je wurinsa tun da ba ita kaɗai ta haifeka ba da za take jigilarka ita kaɗai" Cewar Mama a zuciyarta a fili kuma sai ta dakata da motsin bakinta ta danne gefen keɓenta da haƙori, irin ka min daidai ɗin nan.
Imran kuwa wasu hawaye ne masu kamar an musu dole su fito suka shiga surnano masa a fuska, sai na ido É—aya ya gama gangarowa sannan na É—aya idon ma ya gangaro.
"Alwudu'u, alwala, kaifa tatawadda'u, yaya za ka yi alwala" Cewar Imran yana sakin kuka dan yau ya sadaƙar sai dai gawarsa tun da har kicijin ya je gabansa da kansa.
"ÆŠan karan uwa É—an gwafar uba da baka karanci yadda ake alwalar ba sai yau, to duk sallaolinka na baya aradu ka yi su a wofi tun da sanda ka yi baka iya ba alwala, sai yau da ka ji uwar bari, ka fara tuna karatun alwala ai bari ba shegiya bace da ubanta" Cewar Inna a zuciyarta.
Sauke kai micijin ya yi daga fasa kan da ya yi, ya wani kaiwa ƙasa sara sau biyu da mugun ƙarfi.
Imran idanu ya ƙwalalo tare da ɗauke numfashinsa ganin micijin ya sari ƙasa kusa da ƙafarsa, duk tunaninsa ma shi ya sara sai da ya zare idanu da kyau sannan ya gane ƙasa ya sara, sai dai yana rayawa a ransa shi ma ana daf da saransa. Ƙafafu ya ƙame a wuri ɗaya yadda sojoji ke ƙamewa, ya ɗaga hannu biyun duka ya ka gefen kansa yadda sojoji ko ƴan sanda ke yi idan za su sarawa oganninsu, amma shi da hannu biyu ya yi, a wannan ƙamen ya shiga jero taken Nigeri'a ba ƙaƙƙautawa, shi kansa ya tsinci kansa ne yana faɗa ba tare da niyyar hakan ba saboda gabaɗaya ya rasa me zai ce ma.
"Kai jama'a yau ake yinta, lallai gulma yau ya ƙare tun da uwar gulma ta yi cikin shege, wato saboda ɗaurewa Nigeri'a da harshen nasara tsantsa kaima yadsa abokinka sojojo ya yiwa Nigeri'a baitika kaima hakan take" Cewar Inna a ranta tana tuno yadda aka kwashe da soja da Hassan ranar nan.