Sashe 29
Yar Zaman Wanka Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ikon Allah ni ma mai ya kaini tambayarka dan na san ko dai dai na faÉ—a ba zaka faÉ—i gaskiya ba uban mugun halin tsiya haushi kake ji na baiwa Abida labarinka to ya za ka yi da ni ai ni na ci dubu sai ceto" Ta faÉ—a tana cigaba da fito da kayayyakin.
"Wai dan Allah Inna wa ya baki kayan nan, ranar nan kin ce wanda suka É—auke ki ne suka baki yau kuka fa"
"Oh ni Azumi na ga ta kaina, yanzu Halima dole sai kin tambaya saboda niyya, to yau É—in ma É—aukeni aka yi" Ta faÉ—a hankali kwance.
"Haba Inna kullum dai kika fita sai an É—auke ki sai ka ce kuÉ—i"
"Ke dalla can yau sojojo ne abokin Imirana ya aiko sojoji suka ɗauke ni a mota suka kai masa ni, shi ne na yi yadda na yi na ƙwato kaina"
GabaÉ—aya kallonta suke da mamaki sun san sai tabbas Inna babu yadda za a yi ta haÉ—a wannan maganar"
"Wai da gaske Inna" Cewar Sadiya tana kafe ta da ido shi ma Imran É—in kallonta yake.
"Yo ƙarya zan miki ɗiyar nan wallahi da gaske, aikuwa sun ga tijara gaba da gabanta aljani ya taka wuta, hummm ai ni Azumi an buga an barni"
Nan Inna ta kwashe labari kaf ta faɗa musu, daga Sadiyar har Imran ɗin dariya suke yadda Inna ta yi wasa da hankalin sojojin kaɗai ya isa ya baka dariya, basu sha dariya sosai ba sai da ta fito da micijin nan ta hura ta ajiye shi suka yi ta dariya suna jinjina ƙoƙari da kuma ƙarfin hali irin na Inna.
Tun da aka yi sallar isha'i Inna ta kwaɓa lallenta dan ta ce da shi za ta kwana a ƙafarta dan ya kama sosai. Haka ta jiƙa lallen ta tanadi ledoji tana ta rawar ƙafa za ta yi ƙunshi gobe suna. Bayan ta kwaɓa lallen suna zaune da Sadiya suna ɗan taɓa hira Imran ya fita lokacin, Inna ta kalli Sadiya ta ce.
"Ke yanzu Sa'adiyya ina iliminki na mahammadiyya a ce kina da ilimin addini amma kin bari ana kawo miki Malamin da bashi da wani ilimi gida duk da dai ba da son ranki aka kawo shi ba, ai kamata ya yi ki zauna ki tofe ɗanki da addu,'a dan matsawar yaron nan yana siffar miciji to kuwa ƙwara ma ki haƙura da taron sunan dan duk wanda ya ganshi to tsoro zai sa ya gudu wasu ma ko tunkaro gidan ba za su yi ba.
" Cewar Inna tana kallon Sadiya da ta yi shiru tana saurarenta.
"Hakane Inna bari to na gani" Cewar Sadiya cikin sanyin murya, ta tashi ta É—akko Hassan É—in daga bedroom ta kawo shi falon inda suke. Gadon dama kawai ta É—akko
Sadiya ta yi bismillah ta fara karanta ayatul kursiyyu, falaq da nas da sauran ayoyin kariya cikin hikima ta ubangiji tana cikin yi sai yaron ya fara sawaya a hankali a hankali da haka ya koma mutum sak, a take a wurin aka shiga bashi nono ya sha aka wankeshi aka musu shirin bacci.
Inna sai da za ta kwanta ta ƙunsa lallenta ta ƙulle da leda ta kwanta da shi.
*DARE*
Gari ya yi tsit baka jin komai sai haushin karnuka a sauran abubuwa. Imran da dama bakam ya yi babu alamar bacci ma a tare da shi ya tashi ya janyo ledar da ya shigo da ita ya ɓoye a ƙasan kujera ba tare da kowa ya sani ba. Kaya ne ya siya baƙaƙe riga da wando sai wata wacce ake ɗorawa daga sama wata buɗaɗɗiya haka ya sanya baƙaƙen kayan nan.
Sai da ya tabbatar ba ya jin motsin kowa sai tashin munsharin Inna da ke cika ɗakin. Cikin sanɗa ya ƙarasa ɗakin yana fara da addu:a kar a gano shi. Kan gadon ya tsaya ƙarewa kallo ta hasken wata ganin kowa baccinsa yake hakan ya sanya ya tabbatar har ya gama abin da zai Sadiya ba lallai ta tashi ba saboda nauyin baccin ta.
Inna da ke ta shararar baccinta na gajiya sai sakin munshari take abin ta, a hankali Imran ya yi dibarar cire mata bargon da ta rufa da shi dama ko fuskar bata rufe ba. Hannu ya kai jikin ƙafarta mai ƙunshi ya ɗan ja ƙafar shiru bata motsa ba har lokacin tana ta bacci tare da sakin munshari, ƙara jan ƙafar ya yi zuwa lokacin ta ɗan motsa cikin bacci ta ɗan janye ƙafar. Ganin bata tashi ba sai ya ƙara jan ɗaya ƙafar lokacin ne ta ɗan kai hannu ta doke inda take jin an taɓa amma idanunta a rufe suke. Duka Imran ya sakar mata ɗaɗe ai jin zafin dukan nan Inna sai gata a zaune tana rarraba ido. Kafin ta tantance abin da ke faruwa, da kuma waye wannan mai baƙin kayan Imran ya kausasa murya yadda ba za ta gane shi ba ya ce.
"A yau ne za ki koma ga Allah, za a tambayeki duk abin da kika aikata a duniya dan haka yanzu ranki ne kawai za a zare"
Wani uban bugawa ƙirjin Inna ya yi lokaci ɗaya gumi ya baibayeta, cikin tashin hankali cikinta ya bada ƙululuuuuu.
"Wayyo Allah na mala,ikan mutuwa ne, ni Azumi kenan kwanakina sun ƙare wayyo shikenan tafiya zan yi ko sunan ƴan biyun bana nan za a yi, gashi zan barwa Tasalla Malam" Cewar Inna a zuciyarta har lokacin gabanta na mugun bugawa.
Ba ƙaramin tsorata ta yi ba ganin Imran da baƙin kaya dan ƙafarsa ɗaya ya ɗora a kan gadon sai ya ɗan ranƙwafo tare da baza baƙar rigarsa hakan ya sanya Inna da ke a tsorace ta ga wani girmansa ƙiba da kuma faɗi. Gabaɗaya jikinta karkarwa yake dan a duniya Inna tana tsoran mutuwa kuma a ce yau gata ga mala,ikan mutuwa zai ɗauki ranta, babu abin da ke ɗaga mata hankali sai kwanciyar kabari wannan abu yana matuƙar tada mata hankali idan ta tuna kenan yau ita ma za ta kwana cikin kabari, yau za ta tafi inda ba a dawo wa yau za ta tafi inda iyaye da kakanni suka tafi.
Hannu Imran ya miƙa wajen ƙafarta mai lalle. Inna da tunaninta ya bata cewa ranta zai zare bata san lokacin da ta haɗiye yawun da ya taru a bakint ba ta fara ƙoƙarin haɗa kalmomi sai kawai ji ta yi ta yi ƙarfin halin cewa.
"Da lalle a ƙafar, ƙunshi ne" Wai tunaninta idan ya ji da lalle ko za a ɗaga ɗaukan ran nata wataƙila ma ba ɗaukan ran mutum idan yana da ƙunshi, amma a tunaninta.
"Ba ma son magana ki koma ki kwanta ki miƙe" Cewar Imran a fili a zuciyarsa kuma ya ce
"Ashe kina tsoron mutuwa to kuwa yau sai na tsurar da ke gabaÉ—aya kamar ydda kike surar da ni ki tsoratar da ni ki sani cikin bala'i da miciji"
Jirif kake ji Inna ta koma ta kwanta jikinta gabaÉ—aya ya saki, tana zazzare ido sai hawaye da ya fara kwaranya daga idanunta ganin ga ta ga Sadiya amma za a É—auki ranta Sadiya bata sani ba. Ita kanta ji take kamar ta tashi ta gudu sai dai ta san ba a tserewa mutuwa duk inda ka je tana biye da kai ko yau ko gobe ko É—azu ko yanzu ko anjima.
"Sa'adiyya gaki da nauyin bacci da na tada ki kin ga tafiyar kakarki Azumi mai ƙaunarki ina ƙaunarku Sa'adiyya ke da Asharofa da Malam amma zan tafi in barku fatana ake min addu'a bayan mutuwata" Cewar Inna a zuciyarta tana zubar da hawaye. Imran kuwa dariya ce ke neman ƙwace masa yadda yake ganin Inna na rarraba idanu ta saki jiki gabaɗaya ita ala dole mai mutuwa.
Ganin ya miƙo gannunsa sai jikinta ya fara karkarwa tana raya wa a ranta shikenan ita kuma tata ta ƙare shikenan ranta zai zare.
"Kai gwara dai ki miƙa hannu ki tashi Halima ai gwara dai a ce da wani a kusa da ke lokacin ɗaukan ranki lokacin da za ki bar duniya, oh ni Azumi duniya budurwar wawa duk ƙaunarka da duniya haka za ka koma ka barta to Allah kasa can ta fi nan" Cewar Inna a zuciyarta tana ƙoƙarin kai hannunta na hagu mai lalle wanda shi ne daga gefen da Sadiya ke kwance, tana ƙoƙarin miƙa hannunta kan Sadiya Imran ya lura sai da sauri ya ce.
"Ba a son motsi in ba haka ba za a zare miki ran da ƙarfi"
Da sauri Inna ta janye hannunta tana ta addu'a a ranta kar a zare mata rai da ƙarfi saboda ta san an ce fitar rai akwai azaba bare kuma a ce da ƙarfi.Hannu Imran yake miƙowa yana ƙoƙarin kai hannun jikin Inna ita kuma sai ɗan takure kan ta take tana ɗan ƙoƙarin matsawa ji take kamar ta tashi ta gudu sai dai ba dama.
Hannunsa ya miƙa ya kamo hannunta na dama saitin dantsen ta ya riƙe gam sai ya sanya ɗaya hannun ya kamo yatsanta na tsakiya, ai gabaɗaya sai Inna ta fara wata karkarwa, karkarwa take gifgifgif gadon har jijjigawa yake ita ala dole an zo mawar zare mata rai.
"La'ilaha illalahu, muhammadur rasukullahi, S.A.W" Cewar Inna tana kuka gabaÉ—aya ta sanya a ranta shikenan ita da duniya kuma an yi ban kwana tana ta fatan ta samu dacewa a can.
Wannan karkarwar da take da salatin da take ita ala dole shirin ɗaukan ranta ne da ake take yi dakyar Imran ya iya danne dariyarsa saboda bai taɓa ganin Inna ta shiga ɗimuwa da tashin hankali haka ba ya so akwai haske yadda zai ke ƙare mata kallo amma ina.
"Kai ni Azumi ashe haka tafiyar za ta zo, ashe haka mutuwa za ta zo mini ban shirya ba, duk da dai dama babu wanda yake mata shiri haka kowa ke tsintar kansa haka take zuwa ba sanarwa bare sallama, Allah sarki ni Azumi ko wasiyya ban bayar ba, shikenan sai tafiya mutuwa haka take zuwa shi ma tashin ƙiyama an ce haka zai zo bagatatan" Cewar Inna tana runtse idanunta hawaye na kwaranya.